Showing 63001 words to 66000 words out of 168506 words
da kalaman nanay,bata tana zaton haka
abun zaizo da sauqi ba daga bangaren Nanay,duk da ita din me sauqi ce.......sai
gashi yazo mata da sauqin fiye da yadda ta zata ko tayi hasashe ma.
"Na gode nanay.....na gode" Ta fada cikin matsananciyar kunyar data sanya takejin
ba zata iya tashi tayi tafiya a gaban nanay ba.
★banda Dim light din da dakin yake bayarwa,ba wani sauran haske ko fitila
data rage idan ka cire ta system din dake gabanta.
Su ukune cikin dakin,tsakanin qarfe goma zuwa goma da rabi na daren
ranar.
Aisa akhnan da kuma shehinaz......kusan dukkansu su ukun,duk da suna
zaune ne a mabanbamtan kujeru amma hankulansu yana kan system din dake gabansu
wadda ta nuna maballai biyu. ACCEPT da kuma REJECT.
A yadda suke zaunen da yadda dakin ya dauki wani irin shuru saika
rantse da Allah suna tsoron suyi qwaqwaran motsi kada wani abu me matuqar firgici
ya dirar musu.
Blue eyes dinta da hasken system din ya qarawa wani irin haske me
qyalli kawai take rabawa tsakanin fuskokin aisa da shehinaz wadanda suma junansu
take kallo.
Tashi tayi ta zauna sosai tana sake fuskantar system din,sannan ta
miqa hannu a nutse ta dannan maballin ACCEPT din,abinda ya sanya aisa fidda dukka
idanunta waje tana dubanta.
"Biftu......kinsan me kikayi kuwa?" Zagayayyun idanunta ta daga a nutse hankali
kwance ta zubewa aisa su,ta lumshesu sannan ta budesu,wanda iya hakan ya sanarwa da
aisa tana nufin eh......nasan me nayi.
"Akhnan........wancan lokacin fa.......alfarma....."
"Alfarma?" Akhnan ta fada a nutse tana dauke hannunta daga saman system din tana
zubewa aisa su a karo na biyu.
"Alfarma aisa?......" Ta sake maimaitawa tana maida bayanta jikin kujerar tayi
relaxing tana fidda manyan idanunta waje.
"Akwai wani abu dama da za'a yiwa akhnan alfarmarsa a duk duniyar nan?" Ta qarashe
maganar da sigar mamaki cikin muryarta. Duban juna suke ita da aisa na wasu
sakanni,kafin aisa din ta dauke kallonta daga kanta
"Alfarma ko ba alfarma ba.....koma meye biftu,last time nayi kawaici ne kawai,kina
tunanin idan sultane yaji kina shiga irin wadannan abubuwan ko mu zamu kubuta daga
laifi a gurinsa?" Ta qarashe maganar tana dubanta sosai itama.
Yatsunta kawai akhnan take muzawa,ko meye aisa zata fada....ko meye
aisa zata ce ta fadi din......daidai da ita ne,amma ta janye kalmar alfarma a
maganarta,shine kadai abinda zai sanya ta fahimceta.
"Alfarma aisa....." Ta sake fada tana duban tafin hannunta da rashin hasken dakin
yasa bata iya ganinsa sosai.
"Yes" Aisa ta fada kanta tsaye. Shuru ya kuma wanzuwa tsakaninsu,cikin qasa da
minti daya ta yunquro da wani irin zafi zafi a muryarta.
"Yayi daidai.....kici gaba da alfarma din ko kada kici gaba.....ki zabi duk abinda
kika zaba......koda wannan shine tsere na qarshe da zanyi sai na yishi" Akhnan ta
fada tana soma sarrafa system din da zafi zafi tana cike duk wani abu daya kamata
ta cike tayi submitting.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Ita kanta tasan cikin murna da alfaharin sake amsar gayyatarta
suke,saboda ta tabbatar wani abu ne da bazasu taba tunanin zai yuwu ba.
"Haka kika ce?" Aisa ta fada ranta a bace sosai.
"Haba aisa mana......mubi komai a hankali don Allah" Shehinaz ta fada karon farko
tana duban aisa din.
Tsam Aisa ta miqe tana dubansu,kafin ta ajiye kallonta na qarshe
akan shehinaz.
"Ko meye zai faru......kada sunana ya fito a ciki gurin sultane ko nannie......babu
Aisa a ciki sam". Daga haka tayi gaba abinta ba tare data ko waiwaye su ba.
Shehinaz ta wannan bangaren,duk da irin sabaninsu a abubuwa da dama
ita da akhnan.......amma ta wasu fannonin a ra'ayinsu da kawunansu yafi zuwa daya.
Kamar a wannan bangaren......shehinaz mutum ce mesonh abubuwan da zasu bata nishadi
gami da sakata walwala,don haka tseren ke nishadantar da ita itama,to amma ita
kanta ba zataso sunanta ya fita wajen sultane da nannie ba.......ga morsa a gefe
data tabbatar azabarta zata iya shafe ta kowa.
"Akhnan" Shehinaz ta kirata da nufin gwada kwatanta mata bayanin tabar wannan race
din.
"Kada kice komai.......na gama cike komai na tura musu......damuwata daya
shine......bansan abokin kara wasan ba......bansan wanne me gangancin bane yakeson
sai munyi wannan wasan ba......na tabbatar nayi kuma imanin yayi hakanne don ya
zubar dani,ya kuma ramawa wadanda na zubar haushinsu a kaina" Akhnan ta fada a
nutse tana sake duba bayanai a kansa,saidai kuma blank take gani,don babu koda
cikakken sunansa ma bare wani abu daya shafu tarihin wasannin daya taba yi,wanda
wannan shine ita kuma zai bata nata hasken..
Abinda ya dauki hankalin shehinaz kenan itama,ta manta ma da batun bawa
akhnan shawarar ta haqura din,suka shiga bincike akan komai daya shafi abokin
wasan,saidai har suka gaji da ita da itan ba wanda ya samu komai a kansa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 32
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________
"Na tabbatar akwai manufarsa........bawai hakanan komai ya tsara kanshi
ba.......amma na yiwa kaina alqawarin saina bashi kunya kamar yadda sauran na
bayanshi suka kunyata" Ta fadi tana rufe system din cikin cin matsanancin alwashi.
Alwashin da ko a wancan wasan bataji tana da sha'awar ta cishi ba,tunda wancan
wasan wasane kawai da ita a karan kanta ta yishi ne kawai saboda nishadi,sabanin
wannan da taji yana neman canza salo.
★Cikin kwanakin ta rufe duk wani hanya ko dalili da zai sanya a nemeta a
agadez........ta kuma maida hankalinta wajen gwaji da qara qwarara kanta a babban
filin dake cikin gidanta. Sam bata kawo aisa a matsalarta ba,bata ma sake bi ta
kanta ba. Ba wannan ne karon farko da suke samun sabani irin haka ba,kuma suzo su
shirya kansu kaman bai taba faruwa ba.
Duk yadda aisa takai ga cika baki tasan ba zata iya komai ba,ba zata iya
tona mata asiri ba. Ba kuma aisa kadai ba,a tsakaninsu su ukunñ babu wani wanda
yake iya tonawa asirin dan uwansa,kowanne irin laifi daya kuwa yayi,wannan ya sanya
nannie ke kiransu da MUNAFUKAN 'YAN UWA.
Sunan yana bawa sultane dariya,ya sani gaskiya anne ta fada,kuma sunan
ya dace dasu,amma yakance
"Ayi musu haquri,a canza musu suna".
★★★ *HIPPODROME NIAMEY*★★★
Duk girma fadi da tsahon gurin amma hakan bai hana mutane cike gurin cif cif ba.
Wani irin cika gurin yayi,irin cikar da bai taba yin irinta ba a tarihin gurin.
Gurin kuwa baiyi cikar banza ba,don kuwa wasan ya zama wani na
musamman,fiye da ma da wasan da akayi wancan satin. Ninkin mutanen da sukazo wancan
wasanne suka halasci wannan wasan,don da yawa gulma ta fita game da wacece 'yar
wasan......sunanta da sunan mahaifinta,harda tambarinta a matsayinta na
mamallakiyar katafaren kamfanin suturun mata masu aji.....mata masu abun hannu wato
SAHEL COUTURE.
Mintina talatin din farko kawai akayi aka tafi hutun farko,amma sai
mintunan suka zama wasu na musamman a zukata da idanun 'yan kallo. Kamar yadda suka
zama na musamman a wajen akhnan da wani madaukakin farinciki ganin score din data
samu tun a zagayen farko.
Wani irin wasa daya zama baqo a idanun masu kallo......su biyu ne rak
mahayan......wadanda gaba dayansu ba wanda kake iya ganin fuskarsa saboda helmet
din dake kawunansu. Mahayin doki na farko kana dubansa zaka fahimci namiji
ne,saboda qira da zubin jikinsa daya bayyana a kayan hawan dokin dake
jikinsa.....yayin da ta biyu ta fita a suffar mace sak......tun daga yanayin
qirarta da kuma launin suturar jikinta.
Yana sane yake bada dukkan wata dama ga abokin karawarsa.......ba
tare daya tantance macace ko namiji ba......yana sane yake dage qafa saboda ba
nasarar tseran dawakai bace ta shigo dashi niger........nasarar aikin hukumar
binciken sirri ne ya kawoshi.
Cikin muhallin da aka basu saboda hutun mintunan,hakeem ne ya miqa
masa bottle na ruwa,cikin murya qasa qasa yace.
"Sun saka hope da yawa akan dan wasansu......ban tantance sunan na mace bane ko na
namiji.......amma da alama yana da cika baki da yawa......kayi wani abu mana akai"
Hakeem ya qarasa fada qasa qasa yana ranqwafa kanshi saitin haisam.
Haisam din baice komai ba illa karbar ruwan da yayi. Sam wasan ba shine a
gabansa ba,ba wanda kuma zai fahimci hakan a cikin su,bayaso kuma su fahimta
din,faduwa ko nasarar bashi yake hange ba,yadda a yau zasu fice daga Niamey,subi
jirgin da zai sauka a agadez kai tsaye ne damuwarsa.
"Hakeem" Ya kira sunansa a nutse.
"I beg you" Hakeem ya fada da yaren turanci yana hadewa haisam hannuwansa guri
guda.
Cikin wani irin nishadi ta sauke helmet din nata tana ajiyeta a gefe.
Gashinta ta kama ta tattarashi da kyau tana daureshi,fuskarta washe da wata irin
fara'a da take jinta har tsokar zuciyarta.
Dukka kunnenta suna sauraren bayanan Shehinaz dake kwatanta mata yadda
take sarrafa thunder da wani irin qwarewa gami da miqa mata ruwa.
Sai data saki miskilin murmurshin da iya sakin da fuskarta kadai tayi
shine kawai zai alamta maka murmurshi tayi.
Ita kanta basai an gaya mata ba.......wasan yayi mata ba zata,saboda
yazo mata da wani irin sauqi da bata taba zata ba. Ta zaci abun zai zame mata me
tsananin wahala walagigi dashi,sai gashi cikin sauqi tanata samun damarmakin
wuceshi. Da farko sanda yake fitowa don hawa nashi dokin sanye da helmet data hana
mata ganin fuskarsa ta tsorata,sosai gabanta ya fadi,wata irin baquwar faduwar gaba
da bata san da ita ba.
Ba yau ta saba ganin maza giant ba,Giant ne kuma ingarman da tsaiwarsa
kawai zata baka labarin jarumtar dake gangar jikinsa da zuciyarsa,batasan me yasa
take jin wani irin kwarjini yana hudata ba,wani irin yanayi da ya sanya tun a farko
ta dinga jin faduw warwas a gasar.
Faduwarta kuma daidai yake da kafawa kanta da kanta tarihin abun
kunya......kamar ita zai zamana wani babban abun Allah wadai ace wani da batasan ko
wayeshi ya cinyeta a wasan da wancan satin ta zamana cikin tafin hannunta.
Izzarta da qasaitarta tana tare da ita,tana kuma zagayawa a
jininta,wannan ya sanya taqi maida hankalinta ko idanunta ta sake kallonsa koda sau
daya ne kuwa. Sai a yanzun cikin maganganun Shehinaz ta samu amsar
"Ko sau daya bai kalleki ba bare har ya damu da yadda kike tsere masa.......wallahi
wannan ko waye shu'umi ne......kuma bansan me yasa bai dauki hankalinsa ya dora
akan race din ba" Kai ta jinjina,ranta kuma ya fara mata saqe saqe.
Ko yaya ne bata son taci nasara cikin sauqi......ko yaya ne tana son su
gwabza......tana sha'awar su fafata ta finciki nasararta koda tsiya ne a hannunsa.
Abu na biyu ta sanya masa qatotuwar ayar tambaya......anya ba wani shiri a qasa?.
Bata da wani zabi illa ta san yadda zata tona koma meye a zuciyarsa a wannan
zagayen qarshen.
Saidai kuma akwai wani abu daya da tayi noticing.......ta fahimci kamar
akwai wani sirrintaccen sirri tattare dashi......sirrin da ya zuba masa wani irin
kwarjini na musamman. Bata iya ganin komai nashi,koda kuwa hannuwansa ne dake
lullube da safar hannu irin ta masu hawan dawakai......hakanan qafafunsa ballantana
fuskarshi,amma tana jin wani abu me nauyi game dashi
"Matso kiji Shehinaz" Akhnan ta fada tana murmushi gami da yafito Shehinaz din.
★Cikin sarewa gami da son wasan yazo qarshe hakanan ya sake hawa dokin.
Saidai tun wasan baiyi nisa ba waqen da kambamar qasar da al'ummar gurin suka fara
yi ya soma ruda kwanyarsa.
Yana da wani irin kishin qasa da ya sanya sake zama na musamman a
NISS......yana da kishin qasar da baya yarda ko ya aminta ka zagi ko kaci mutuncin
qasarsa.......qasarsa nada muhimmanci a wajensa.
A hankali tutocin qasar niger suka fara dagawa a gurin,suka soma yiwa
gurin rumfa saboda dukka wanda yake kallon wasan ya gama yiwa wasan alqalanci. Bata
yadda za'ayi abokin buga wasan ya farke wannan wasan,sun gama miqa wuyan bai iya
komai a wasan ba.......akhnan din ita ke da nasara......da gaske ita din kallabi ce
tsakanin rawuna.
Wuceshi da tayi da waiwayowa da tayi ta masa wani sign da hannuwanta
ya fusgi hankalinsa. Abubuwa guda biyu ne suka tabashi. Na farko sign din data masa
alamun raini ne ga duk wanda ke buga wasan horse race........abu na biyu kuma har
cikin jikinsa yaji hasashen da yakeyi tun dazun......yanayin da jikinsa yake bashi
yaji yana sake tabbata. Tun dazu jikinsa yake bashi wannan din da suke wasan
macace,ba namiji bace,yanayin sarrafa dokinta da yanayin sarrafawar mace yayi masa
kama.
"Me yasa omari?" Yaji ranshi yana baci da abinda omari yayi masa. A hankali
idanunsa suka sauka akan team
dinsa.....maleek,mutallab,omari,amjad,khaleed,khadeem. Tutar Ethiopia suka ware me
fadi sosai.....kowannensu kuma yana riqe da wani bangare nata,sun kuma dan bada
tazara a tsakanin su,abinda ya bawa tutar damar bayyana sosai.
Idanunsa ya zare a hankali,qasaitaccen murmushin nan nasa yana kubce
masa,take yadda ya dauki wasan a ransa ya canza cikin qasa da second biyar. Ko basu
ce komai ba yasan me suke nufi.....yasan saqon da sukeson aika masa.
A wajensa ba wani wasa bane me muhimmanci ba,wasa ne na samun damar
shiga agadez da niger gaba daya ba tare da kowa ya gane ba.......amma a yanzun a
ranshi shima yana jin koda hakanne,bai kamata ya bari qasarsa tasha kayi ba,bai
kamata qasarsa taji kunya ba. A yanzun su suke wakiltar Ethiopia gaba daya,duk da
duka dukansu a filin irgen yatsun hannu ne......amma ya kamata su barwa al'ummar
niger suna da tambarin ETHIOPIA.
Ta saki jiki sosai,ta kuma bada amanna tana sarrafa dokinta hankali
kwance......saijin iskar wucewarsa tayi,kafin tayi kowanne yunquri kuma ya soma
mata nisan daya sanya hankalinta tashi,ta kuma qarawa thunder qaimi.
Murmushi ya sake ajewa ta cikin helmet dinsa,yana iya jiyo sautin takun
dokinta,koda bai waiwaya ba kuma yana iya qididdige adadin tazarar data rage da
zata iya bata damar taddoshi,don haka sai yayi mata qofar rago kawai.
Tana daf da iskoshi ya sake bata badda mata tunani,ya cilla da wani
irin salo daya dauki hankalin kowa,ya sanya filin yin shuru ba tare da kowa ya
shirya ba,ya kuma sauya akalar magana da tunanin me sharhin dake can sama yana
ganin yadda abubuwa suke so su canza a mintunan qarshe na wasan.
Wani irin wasa da hankali ya soma yi da ita,wani walagigi ya fara yi
da nutsuwarta da dukkan qwarewarta. Cikin mintuna qalilan gaba days ya ruda tunanin
ya kuma rudata. Tsalle kawai zuciyarta keyi cikin qirjinta,wani irin tsoro taji
yana saukar mata. Tunda take bata taba ganin salo irin wannan ba,ya toshe duk wani
tunanin ta inda zata cimmashi ma bare ta gotashi......ya toshe duk wata kafa da
zata tsammaci nasararta a kusa.
Fargabarta ta sake qaruwa da ganin adadin qananun mintunan da suka rage
wasan ya tashi gaba daya..... Tashin hankali ne taji yana lullubeta a
hankali,RASHIN NASARA yana daya daga cikin tarin abubuwan data tsana.......ta tsani
FADUWA ta kuma tsani A FITA. Ta rayu ne a saman nasara......ta rayu a tudun
fifiko,ta bude idanunta ne ta tsinci rayuwarta saman ta wasu......ta tsinci
rayuwarta a qulle data wasu.....ba zata taba lamunta ba ace wani can yazo ya
kunyatata a tsakiyar 'yan qasarta ba......a gaban talakawansu ba........wannan ya
bata qaimin data miqe saman dokin ta kuma bashi wani irin qaimi da ya gigita
hankalin dokin ya fita daga tsari da kuma horon da aka bashi.
Yadda dokin yake misbehaving ya mugun tsoratata ya kuma daga mata
hankali,ta sake riqeshi da dukka hannuwanta tana jin wani gumi yana tsarto
mata,domin ta tabbatar a irin wannan yanayin ta sake ta fadi ba shakka sunanta
gawa.
Wani irin abu me nauyi ne taji ya saunar mata sanda dokinsa ya tsallakar
iyakar dake tabbatar da kasantuwar nasara a hannunsa. Sautinsu amjad a amsa kuwwar
da baisan inda aka samota ba da taken qasarsu ya sake ruda tunaninta da wani irin
kalar zallar tashin hankali.
Tayi zaton dokin zai dakata daga inda ya cimma wannan layin
shima......amma aah sai ya zarce yaci gaba da shillawa da ita da wani irin gudun
walqiya.....daidai da sunan data bashi.
Wannan karon zuciyarta tsinkewa tayi gaba daya da wani irin tsoro,take
ta fara