Showing 12001 words to 15000 words out of 168506 words

Chapter 5 - luu luu Book1 by Huguma

aminta da
dukkan zuciyarta wani babban yaqi ne ya shigo rayuwarta,tun a wancan lokacin ta
sani.......jikinta kuma yake bata cewa akwai wani shiryayyen abu da zai iya
faruwa,ko a kusa ko a nesa........sai gashi a nesan da bata taba kawo irin wannan
nesan ba.

Duk yadda zuciyarta ke bata shawarar ta zauna ko zata hutar da
qafafunta ko hakan zai kawo sassauci ciki rai da gangar jikinta amma ta kasa. Tana
jin mintunan da aka diba kafin ta samu amsar yiwuwar ganin me martaba din kamar
sunyi wani mugun tsahon da suka kusa daidaita da tarin watanni.

Kasa juriyar ci gaba da tsaiwa cikin falon tayi,don haka saita matsa
da dan zafi zafin nama ta sanya lausasan takalmanta ta gyara lullubin dake saman
kanta sannan ta soma fita a parlor din.

Barka da fitowa hadimanta suke mata cikin sadda kansu qasa,ta daure
zuciyarta qwarai wajen ganin ta amsa musu yadda ta saba,duk da cewa ruhinta da
gangar jikinta ba yana a tare dasu bane sam sam.

"A dubomin buhaina a duk inda take.........a gaya mata ta shaidawa sultane ina nan
ina sauraron ganawarmu" Morsa safiyya ta fada tana hade tafukan hannayenta guri
daya,cikin qoqarin controlling abinda takeji yana mata kaikawo a zuciya.

"An gama" Nanay ta fada,Daya daga cikin hadimanta dake da wani irin zafin isar da
saqon morsa safiyya din.

Wata nannauyar ajiyar zuciyar ta sauke tana janye jikinta da idanunta
daga jikin window din,wanda yake tuna mata da abubuwa masu tarin yawa da suka
shude. Daidai lokacin da hadiman guda biyu ke shigowa buhaina da nanay.

Daga bayanta suka zube cikin girmamawa kamar yadda suka saba,sannan
buhaina ta fara magana.

"Allah shi riqa miki.......me martaba sultane yana cikin baqi masu yawa.........duk
da kusan da yawa ya sallamesu........amma gajiya bana tunanin zata barshi ya ganki
a dai.........". Wani irin suka maganarta ta yiwa zuciyar morsa safiyya,zafin daya
ratsa zuciyarta ainun. Ba al'adarta bace ganin sultane barkatai irin haka
ba........hasalima ita da sultane din akan dauki kwanaki uku ba tare data sanyashi
a idanunta ba,duk kuwa da cewa miji yake a gareta kamar yadda mammina take mata a
wajensa. Lokuta da dama a duk sanda zata buqaci ganinsa a irin wannan yanayin,tana
yin hakanne bawai don buqatar kanta ko wani kebantaccen abu da ya shafeta ba,kusan
dukka buqatar ta mutum daya ce wato akhnan,duk da cewa a idanu da zuciyoyinsu basa
kallon hakan akan buqatar kansu face buqatar qashin kai.

"Daga wanne lokaci zai iya shiga lokacin taqaitaccen hutu?". Saida buhaina tayi
qasa da kanta sannan ta amsa mata.

"Nan da mintina biyar zuwa goma ranki ya dade".

"A daukomin rigar waje" Tayi umarnin tana soma takawa a hankali tana nufar
qofa,abinda ya gaya musu cewa tana da buqatar fita kenan.

Ba jimawa mariya ta dawo da rigar da sassarfa,ta rusuna tana yafa
mata,yayin da morsa safiyya ta qarasa sakawa sannan ta qarasa lullube jikinta da
wani irin yanayi dake nuna zafin da takeji a zuciyarta dama jikinta gaba daya,suka
fara takawa suna ficewa ita da mutum uku cikin hadimanta.

Duk taku daya da takeyi tana fuskantar sassan sultane zuciyarta qara
zafi take mata. Kusan bayyanarta a wajen a irin wannan lokacin wani irin baqon
abune da ba'a saba da ganinsa ba. Mutum ce ita da zaka dauki dogon zama cikin
masarautar baka sanyata cikin idanunka ba......mutum ce da zaka jima a cikin
masarautar bakaji tace komai dangane da komai ba.......idan nace komai ina nufin
umarni hani ko kuma zartaswa. Kaf ta tattara hankalinta da rayuwarta ne dama duk
wani ikonta a kan gidanta KADAI. takan fadi lokuta da dama idan ta zauna hira da
hadimanta.

"Ba kowanne abu bane yake da buqatar kayi magana sharhi ko tsokaci akai ba. Wasu
abubuwan zaifi kyau kayi shuru a kansu,domin shurun yafi zame maka ado kima da Kuma
kwarjini hadi da cikar kamalarka a rayuwa". A tare da ita sun koyi abubuwa masu
yawan gaske,a tare da ita sun dauki wani irin darasi da babu shi a kowanne sashe na
duniyarsu.

Kanta tsaye ba kuma tare da jiran umarni daga dogarawan dake da wani
irin shiga tsari da horo na musamman ba,wadanda ke tsaron qofar da zata sadaka da
kebantacciyan parlor da yafi kama da wata fada me zaman kanta ta doshi qofar kai
tsaye,abinda ya tilastawa duk wani wanda yake gurin janye ganinsa kame kansa da
killace ganinsa daga kanta.

Koda ita din ba daya daga cikin matan dake da daraja ta farko cikin
qasar agadez ce ba.......ita din ta musamman ce,da wata irin kamala da kwarjini da
sassanyar nutsuwa suka yiwa tufafi. Tana da wani irin girma a zukata da kuma
idanunsu.......tana da wani irin matsayi da KAME KAI da tsame baki daga dukkan
al'amuran da basu shafe ka ba dama wadanda suka shafekan suke siyawa dan adam.

Ba su kadai ba.......su buhaina dukka da ta taho dasu suma nan din
shine qarshen inda aka lamuncewa takawarsu,don haka ita kadai ta tsoma qafa a
palace din da ta kebanta ga sultane muhammad hammud da kuma iyalinshi a halinsa.


Hankali kwance,cike kuma da wani irin nutsuwa ta fidda kayan jikinta ta
musanyasu da wasu kaya da birra ta ajiye mata. Dogon wando ne leggings me bin jiki
sosai,sai gown dinsa me dogon hannu data zauna das a jikinta ta kuma bude sosai
daga qasa. Birra tasan zabinta,kusan tana cikin mutum na uku data gama sanin komai
da take so,duk da har yanzun ita kanta tasan tabar birra dinne kawai ta san abinda
taso ta sani din.

Sassan nata babu motsin kowa,domin kuwa sanannen abu ne.......mutum ce
ita ba koda yaushe take da buqatar mutane a kusa da ita ba,wannan ya sanya dukka
hadimanta suke tsananin kiyayewa da dukkan abinda suka san bata so,domin ita din
zuciyar SULTANE ce,HASKEN AGADEZ kuma.

Hankali kwance ta zaba ta kuma nutse cikin jerin sofas din dake parlor
din,sai a lokacin hankalinta ya koma kan wayarta,don tayi imanin wannan matsalar ta
gama da ita kuma. Ta sani......bawai abun ya qare bane......bawai za'a tsaya iya
haka bane.......amma har cikin zuciyarta take gayawa kanta da kanta zata yiwa
tufkar hanci.....zata kuma daqile afkuwar hakan a nan gaba.

Ta gaji da ganin fuskokin mazan da suke nuna kansu a gabanta. Mazan da
zuwa yanzu ba zata iya riqe lissafin adadinsu ba,har yanzu tana ji a ranta BASU KAI
BA,wannan alfarmar tata har yanzu ba wani DA NAMIJI da ya samu nasarar taka koda
matakin farko na samunta.

Sashen adana lambobi ta nufa(contact),taci gaba da dubawa a nutse da
wani irin aji daya zame mata dabi'a koda ita daya ce a waje.

Haleesha shine sunan data tsaya akai,ta kuma danna kira sannan ta sanya
wayar a handsfree tana ajiyeta a hannun kujerar kamar yadda kusan dabi'arta ce
hakan. Ba kasafai take sanya waya a kunne ba......muddin hakan ta faru lallai duk
wanda take magana dashi din wani mutum ne muhimmanci qwarai da gaske a
wajenta,kamar sultane mammina aisa shehinaz da ire irensu.

Bugu biyu rak aka daga wayar daga daya sashen,saboda sanin illa barin
kiran ya zama miscall da zai iya jawowa mamallakiyar number.

"Barka da yammaci Madame......" Aka fadi da sautin dake nuna tsananin girmamawa.
Sai da taja fasali tana duba dogayen yatsunta,ta lumshe idanunta sannan ta budesu
kafin tace

"Ya kike haleesha?"

"Ina lafiya Madame" Ta amsa cikin jin dadin nuna qanqanuwar kulawarta a kanta.

"Yayi........an kammala karbar designs din?"

"Eh Madame......ke kadai ke jira". Kai ta jinjina,tana jin zuciyarta da hankalinta
gaba daya ya koma niamy

"Wannan tafiyar ce ta kawomin tsaiko......amma ina hanya gobe in sha Allah". Kai
haleesha ta jinjina tana mamakin dawowarta da wuri.

"Allah ya kaimu Madame.....don sosai kasuwa take buqatar kayanmu".

"Tout se passeda bien in sha Allah(komai zai daidaita in sha Allah,zan kum duba
demande(request) da kika turawa enterprisรฉ".

"Je vouse remercie Madame(na gode madam)" Haleesha ta fada cike da farinciki.

Bata sake cewa komai ba ta gintse wayar,ta maido hankalinta cikin falon
tana furzar da siririyar iska daga bakinta.

Ita kanta tana mamakin yadda take jin qirjinta wasai,duk da lokaci
lokaci tana dan jin tunanin yadda sultane zai tunkareta da batun hambarar da
lamarin altaab da tayi,duk cewa tasan bata da wata matsala ko damuwa game da
sultane....don duk abinda takeso shine cikar muradinsa......amma ita din bataso ta
sanyashi ko yaya yaji ba dadi akan wani mutum da bata jin darajarsa da d'ara ko ina
ballantana ya zama silar sosuwar ran sultane.

Irin so takewa sultane da mammina.......wani irin tattalin muradi da
kuma farincikinsu takeyi. Murdinta na cika burinsu akan duk abinda suka sanya
interest akai daban yake a zuciyarta......sai kuma akayi katari su din suka kasance
mutane ne masu fifita maslaharta da muradinta akan nasu.

Waya ta jawo,ta saka wasu taqaitattun lambobi don yin kira bangaren
hadimai da bayi,wanda cikin qasa da mintina biyar birra ta bayyana.

"Ki duba dressing room.......a canza min luggage sababbi na gaji da yawo da
wadannan.........karki sakamin komai a ciki sai inner wears din da mammina ta
aikomin dasu da sleepwears......suna cikin wani LV Luggage........gobe inaso muyi
fitar sassafe.......ki shaidawa manu.......banaso nayi sallan azahar sai a niamy".

"Angama ranki shi dade" Ta fada tana yin qasa da kanta sannan ta yunqura ta miqe.
Har birra din tayi gaba akhnan ta sake kiranta.

"Je voudrais un verre de lait,s'il vouse plaรฎt(ina buqatar cup daya na madara)" Kai
birra ta jinjina a hankali sannan ta juya zuwa can wani sashe na daban da freezers
din ke jere kamar an haliccesu ne don kawai su bautawa buqataun akhnan. Tana ciro
madarar data kasance zallar madarar shanu ce lafiyayya me kyau,duk da wasu lokutan
tafi amfani da nonon raqumi da akan tatsoshi musamman saboda ita daga lafiyayyun
raquman dake masarautar. Wasu irin raquma ne masu daraja da tsada,saboda irinsu na
musamman ne da zai wahala ka samesu ayankin nijer idan ba gidan iko irin masarutar
agadez din.
Tana mamakin yadda fiye da rabin rayuwarta ta dogara ne da shan
madara nono da 'ya'yan itatuwa. Qwarararrun Cuisiniรฉre(cook) ne da ita da suke
qarqashin jagorancin mutum guda da akullum sukan bata awanni kawai don shirya mata
abincin da zata ci wanda zai burgeta,saidai kusan dukkan a wannin nan sukan tashi a
banza,don abinda zata tsakura taci din zakayi tsammanin yau ne ta fara koyon cin
abinci.

Sunyi hannun riga da qiba ballantana kuma tumbi,saidai kuma madarar da
ta abota ta taimaka mata qwarai wajen samun wata irin lafiyayyar fata tsadadda da
skin care product din take amfani dashi suka taimaka wajen bata wani nau'in kala na
musamman koda cikin fararen matan ma,gefe guda kuma da murjajjen jikin dake da wani
irin shape da ake kira da qirar cocacola ko kuma qirar kalangu a hausance.

Sai data ajiye mata komai da take buqata sannan tace.

"Kina da buqatar wani abune ranki ya dade?,ko kina buqatar su bushira su zama kusa
dake?" Kai ta girgizawa birra,don a yanzun kadaicewa kawai take da buqatar yi ta
shaqi iskar data cakuda da iya numfashinta ita kadai. Kada kan ya bawa birra
amsa,saita juya a girmame tana fita don cika umarnin data bata dazun.

Sallamar mammina ta sanyata ajiye kyakkyawan glass cup din glass din
dake hannunta da aka yiwa wani irin ado da launin gold dake sake tabbatar da
sarauta zallarta.

Miqewa tayi tsaye tana jiran qarasowar mammina din tare da qoqarin
karantar yanayinta don sanin dame mammina tazo din. Kadan kadan fargaba nason
rabarta......tana da tabbacin mammina ta samu labarin tayi rejecting
altaab........batasani ba ko altaab din yaso ya zama zabin mammina amma tayi
rejecting nasa?,tana tsoron hakan ta kasance kuma ya zama silar bacin ran mammina
din.

Sai data sake matsowa kusa da ita sannan ta fahimci kadaran kadaham
fuskar mammina take,wannan yadan bata sukuni kadan,sukunin daya sanyata fara takawa
ta ruski mammina din ta kuma aza kanta saman kafadarta tana sauke ajiyar zuciya.

"Don Allah mammina......don Allah kada kice altaab kinso ya zama zabina". Sakanni
uku mammina ta dauka,sannan ta dora tafin hannunta saman kan akhnan tana shafawa a
hankali.

" Har abada zabinki shine nawa.......har abada ba zamu tilastaki ko mu tursasaki
zuwa ga auren wani ba.......namu shine mu nusasheki,idan kin aminta muma yayi
mana......idan baki aminta ba muma baiyi mana ba.......amma saidai......" Mammina
ta qarashe fada da wani irin sanyi a muryarta,sanyin daya Sanya akhnan daga kanta
daga kafadar mammina din tana kallon cikin qwayar idanunta.

Girgiza kai akhnan ta fara yi a hankali.

"Morsa safiyya?" Akhnan ta fada tana son gasgata hasashenta. Kai mammina ta daga a
hankali cikin alamun nuna d'ari d'ari,sai kuma ta kama hannun akhnan din ta jata
zuwa saman daya daga cikin kujerun ta zaunar da ita ita kuma ta zauna a qasa a kuma
gabanta hannunta cikin na akhnan har yanzu. Da wani irin sanyi taci gaba da magana
murya qasa qasa.

"Banaso morsa safiyya taci gaba da zargina.......banaso taci gaba da yimin wani
kallo na daban.......banason wannan alaqar.......wannan dangantakar da naketa
qoqarin gyarata tsahon shekaru taci gaba da wargajewa......"

"To idan ya wargaje sai me mammina?.......me yasa kike abu kamar kina tsoronta ne?"
Akhnan ta fadi tana ware manyan blue eyes dinta akan mammina,alamu na soma
tasirantuwar bacin rai suna bayyana qarara saman fuskarta.

Da sauri tahau girgiza kai

"Kul akhnan,kada na qara ji kada ki qara fada,ko kin manta morsa safiyya
mahaifiyarki ce?". Musawa akhnan keson yi amma bataso tayi jayayya da
mammina......saida kalmar MAHAIFIYA akan morsa safiyya ta kasa zama daidai cikin
zuciyarta.

" Mahaifiya daya mutum keda ita a rayuwa da duniya......kuma ni kece mahaifiyata"
Tayi maganar dukka wata fara'a dake saman fuskarta tana bacewa bat.

Kai mammina ke girgizawa.

"Banaso akhnan......banason wannan furucin.......banason wannan dabi'ar akan morsa
safiyya.......biftu......ya kamata ki gane tana qara nesantani da samun hadin
kawunanmu". Wani dunqulallen abu akhnan ta hadiye,ta dauke kanta daga duban mammina
zuwa gefe.

Batasan me yasa mammina ke batawa kanta lokaci ba,batasan me yasa
mammina ke damuwa da son samun yarda da aminci matar ba. Bata taba ganin soyayyar
mammina cikin idanun matar ba,duk da yadda ita din ke qoqarin ganin ta kaucewa
abinda duk zai bata ranta. Bata taba ganin damuwa da damuwar mammina cikin lamuran
matar ba......bata taba ganin alamun morsa safiyyan zata taba duba zuwa ga buqatun
mammina ba ko sau daya ne tak!.

"Ni ke kadaice momma na.....ko zan daina fadin komai wannan bazai gogu ba" Akhnan
din ta fada can qasan muryarta.

Dan qaramin murmushi mammina ta sake tana sake kamo hannuwan akhnan
sosai cikin nata. Wani abu guda daya daya gaza sauyawa daga hali da dabi'ar
akhnan......tun daga haihuwa zuwa yau data zama cikakkiyar mutum shine KAFIYA DA
TAURIN KAI. Wasu dabi'une da suka kasance mata abokai tsakanin ruhi da kuma
rayuwarta...wasu dabi'u da kowa yasan cewa wasu rubutattun abubuwa ne cikin
jininta.

Idan tace EH babu wani abu dake sauya EH dinnan har abada......hakannan
idan tace kuma A'AH shima babu wani abu dake da qarfin ikon canzata har gaban
abada. Koda kuwa hakan yana nufin samuwar wani abu da zai zame mata qalubale ko
lalura,dabi'ar da ita kadai hajiya zaitun ke iya dealing da ita......daya daga
cikin abubuwan daya sanya sultane ya sake sallama mata.


*ME KARATU?*

*WACECE HAJIYA ZAITUN(MAMMINA?)*

*WACECE MORSA?*

*MEYE MATSAYINTA GURIN AKHNAN?*

*MEYE MATSAYIN MAMMINA A GURINTA?*

*WAYE LU'U LU'UN NAN?*

*WAYE ZAI CIKA DUKKA WADANNAN QA'IDODIN DA KUMA DOKOKIN NA AKHNAN?*

*WAYE WANNAN TAURARON?*
*_WADANNAN SHAFUKAN BASU WUCE TABA KA LASHE KO D'AN D'ANO BA KADAI,DON SUNYI KADAN
QWARAI SU HASKA MAKA ME LABARIN LU'U LU'U YAKE QUNSHE DASHI_*

*TURKA TURKACE ME TARIN YAWA........MATSANANCIN KAIDI DA ZAZZAFAR SOYAYYAR DA
BAMUSAN A CIKI MEYE ZAIYI NASARA BA*

*IZZAR.....QASAITAR....... MULKIN......TUGGUN...... MAKIRCIN KO KUMA ZAZZAFAR
SOYAYYAR LU'U LU'U?*


*KARKI KUSKURA KIYI SAKACI KI KUMA YI GANGANCIN DA ZA'A BARKI A BAYA CIKIN TAFIYAR
NAN*

*_HAJIYOYINMU MASU JIRAN NA FISABILILLAHI ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚.......HAJJAJU BA GIRMA A
ABUN......DON ALLAH 700 DAI BA ZATA GAGAREKI BA.....KI ZAMA ME CAPACITY MANA,DA
KUNYA KULLUM A GANKI A GIDAN ALLAH YA BAKU MU SAMU๐Ÿ˜‚,zoki siya naki ki ki shigo
discussion group namu da capacitynki,aikin wuce a siya asanmiki_*

*ina taya wadanda suka siya nasu murna.....ina me basu tabbacin tafiyar bata wasa
bace......zamu lula zuwa DUNIYATA in sha Allah*

*na gode.....na gode*


zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*MASU BUQATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU QOFA A BUDE TAKE......AMMA TALLA NE BISA
TANTANCE INGANCIN ABINDA KAKE SAIDAWA BA SHACI FADI BA*
08187255862



*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

โœ๐Ÿฝ
*HUGUMANKU CE*

๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*

PAGE 6
(paid novel 08187255862)
__________________________

https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500
dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login