Showing 144001 words to 147000 words out of 168506 words
abun
tausayi sannna ya juya ya soma takawa. Har yakai qofa ya tsaya.
"Ko kace na yafi zan dawo obbo.....Allah bazan iya zama can gidan ni kadai
ba.....zan dawo,Allah obbo zan dawo" Ya qarasa fada da sauri yana fita a sassan don
kada ma haisam din ya fadi abinda zai karya tsarinsa.
Murmushi kawai yabi bayan abdii dashi,ya sani dama indai abdii ne
saidai kawai yayi haquri ya qyaleshi,to amma dole ya kiyaye wasu abubuwa muddin
zamansu yana so ya yiwu,dole ya ajiyewa abdii wani jadawalin tsare tsare.
A nutse yaci gaba da bincike dukkan wani loko da saqo na sassan,yana
kuma nazartar komai. Saboda qwarewa da yadda aikin sarrafa tsaro yabi
jikinsa......ba wani guri da yake sauka hakanan ba tare daya karanci kimiyyar
yanayi da kuma tsarin gini dana tsaron gurin ba.
Kusan komai yayi masa,ba wani abu da yaji zuciyarsa bata gamsu dashi
ba,don haka ya soma takawa yans fitowa da nufin karantar dukka farfajiyar dake
kewaye da ginin kafin ya wuce zuwa makaranta.
*AKHNAN*
A qalla ta kusa mintuna goma Idanunta a runtse,tana kuma jin yadda iska
ke wasa da gashinta daga hagunta zuwa damanta.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
A yau cikin rad'in kanta taji buqatar fitowa daga sassanta zuwa
wannan kebantaccen gurin,wani guri da yake daga baya kuma daga qarshen sassanta
wanda yayi linking da sashen dake maqwaftaka da nata,sashen daya zamana ba kowa a
ciki iya saninta tsahon sanda aka ginashi,don haka take matuqar son zaman gurin a
lokuta da dama saboda akwai privacy sosai a gurin.
Kowanne zaren tunani da kuma tarin lissafe lissafen mafita ne suke
kai kawo cikin kanta. Mammina din dai,ita kadai lissafinta yake bata duk inda taje
ta bugashi ta dawo.......ita daya ce mafitarta dake tafin hannunta. Hatta da
mamminan an sanar mata zuwanta kusan sau hudu,amma taqi yarda a barta ta shigo
ballantana ta samu damar ganinta,amma a yanzu zuciyarta na jaddada mata ita kadai
ce dai zata isar da ita ga muradinta........MORSA ce kawai keda wannan
matsayin,amma bata fatan abinda zai sanya ta roqi kowacce alfarma daga gurin morsa
safiyyan har abada.
Tun daga nesa data zuba mata idanu sosai,sai take ganin wani sashe na
kamanceceniya tsakaninta da safeena dinta,abinda ya karyar mata da zuciya kenan,ya
taso da wani irin yanayi me qarfi ya azashi saman zuciyarta.
A nutse ta iso gabanta,duk da akhnan din taji alamun taku amma hakan
bai sanyata ta bude idanunta ba,saboda ta sani,koma waye yake shigowa gurin cikin
mutum biyu ne mafiya muhimmanci a rayuwarta,mammina ko sultane,wanda bata sanya ran
zai tako inda take a cikin irin yanayi da suke ciki ita dashi yanxu.
Tsaiwar takun ya sakata bude idanun nata a hankali,saidai kuma wadda
ta gani din bata taba tsammanin ganin nata ba.
Abinda tafi hasashe da tunanin zata iya aikatawa shine,ta miqe kawai
ta matsa daga gurbin da matar ke tsaye,don ba wani dalili ko hujja na hada muhalli
da mutumin dake adawa da dukkan wani jin dadi da kuma walwalarka......bashi da
amfani musayar numfashi da mutumin da yayi sila ko sanadin shigarka wani
qunci,saidai kuma komai ya sauya......wannan tunanin ya canza daga sanda idanun su
suka gauraya dana morsa safiyya.
Kallon kallo suka yiwa junansu,kowannensu abinda yake yawo daban a
ranshi. Batasan me ya hanats tashi ba har zuwa sanda morsa safiyya ta tako a
hankali ta zauna a gefanta.
"Biftu" Ta kirata a tausashe,sunan da haruffan kuma suka sauka har cikin kunnen
haisam dake takawa ta gefan farfajiyar a hankali yana duba wasu irin furanni da aka
zagaye katangar gurin da aka samar da ita ta wannan bangaren da itacen bamboo masu
daraja. Kadan yadan juya,amma fuskantar ba wani bane a gurin,murya ce daga can wani
guri sai yaci gaba da abinda yakeyi din hankalinsa kwance ba tare daya damu da
neman daga inda sautin yake ba.
"Biftu.....me yasa zaki daga hankalinki har haka?,me yasa zaki nemi cutar da kanki
akan abinda yake ibada ne?......biftu,ki kori shaidanin da yake miki saqa a mugun
zare,ki yaqi baqin tunanin dake wahalar da kanki da kuma rayuwarki mana......ba ta
inda aure yake qasqantar da darajar diya mace,face ma daga mata martaba da kima da
yakeyi,koda bata samun dukka abinda tayi buri ko hasashe a cikinsa.......amma
martabar wannan igiyar da darajar sunan AURE dake kanta kadai ya isheta girma da
alfahari......don Allah biftu,ki kyautata zato a rayuwarki ta gaba.....kiyi haquri
ki fahimci zahirin rayuwa.......muna buqatar ganin wanzuwar jinin safeena......muna
buqatar zuri'ar safeena ta wanzu a doron duniya a doron qasa kaman yadda kowannenmu
ya samu nasa rassan.......safeena ce kawai bata samu wannan ba.....ki tausaya mata
ta zamu zuri'a mara yankewa,ba wanda zai mata wannan sai ke......ba wanda yake da
wannan ikon a hannunsa yanzu sai ke......inda ahmad yana raye......dukkan fatanmu
da burinmu zaifi karkata a kansa fiye dake,amma zuwa yanzu,duk wani me sauran FATA
da BURI akan AHMAD ya gama sarewa,ya gama lullube babin taba wanzuwarsa a
masarautar AGADEZ. Daidai da sultane bashi da wani sauran BURI ko mafarki a
kansa.....ke dindai.....ke kadai ce yanzu duk wani burinmu game da zuri'ar SAFEENA"
Morsa safiyya ta samu takai qarshe da qyar muryarta na rawar dake nuna bayyanuwar
raunin nan nata dake da wahalar bayyana.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
Page 72
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________
Idanu alkhnan din ta zuba mata,duban morsa safiyya takeyi fes kanta
tsaye. Fata take.....so take ta tashi tabar mata gurin salin alin ba tare da tace
komai da ita ba,amma a yanzu da takejin zuciyarta na cike da ita......tana jin a
yau kadai data samu dama ta furzar mata da wani abu ko yaya ne......ta gwada mata
bata buqatar wannan alaqar.....wannna dangantakar gaba daya,ahalin salsalar da
nasabar dukka basu cikin buqatun rayuwarta da suka zame mata dole.
"Karki bari zuciyarki da shaidan su raya miki komai........safiyya
ce.....shaqiqiyar safeena......qanwa a gareta,qanwa mafi kusanci mafi shaquwa ga
mahaifiyarki......kisa dukkan hankalinki da nutsuwarki a wannan karon na
roqeki......ki karbi shawarata koda sau daya ne tak a rayuwarki,nayi miki imanin ba
zakiyi dana sani ba......"
"Wannan shine babban danasanin da zanyi a rayuwata irin wanda ban taba yinsa
ba......" Ta furta da wani irin calmness,saidai kuma idanunta suna qaryata nutsuwar
dake tattare da kalamanta.
Wani irin shock morsa safiyya taji,tayi sak tana duban alkhnan duba na
zallar mamaki. Duban da take matan sam bai sanya ta rusuna,ko taji bata aikata ba
daidai ba,kota rage kaifin kallon da take mata ba.
"Don Allah....." Ta motsa labbanta tana sake fadi da wani irin sanyi.
"Don Allah wannan dangantakar.....wannan alaqar.....wannan ahalin na
safeena......wannan dangin dukka bana buqatarsu,don Allah.....nima ina
roqonku.....ni khadeejatul akhnan......a yau,a karo na farko cikin tarihin
rayuwata,na karya record dina......ban taba roqar kowa komai ba.......ban taba
tambayar kowa yayimim komai ba,amma a yau ina roqarki momma safiyya me laqabin
qanwa ga mahaifiyata......ku janye ku kuma fita daga dukkan wani sabga daya shafi
rayuwar akhnan ".
Wani irin harbawa yaji wannan jijiyar dake gefen kanshi yaji tayi har
cikin qwayar idanunsa. Harbawar da yawanci idan tayi to ba shakka ransa yakai
maqurar baci. Da sauri ya jefar da furen daya ciro a qasa,wanda ya tsinko shine don
ya tantance launin qamshinsa,jifarwar da zaka zaci kunama ya kama bawai fure ba.
Idanunsa ya daga a hankali yana kallon katangar da yake kyautata zaton itace ta
rabashi da ganinsu,yana jin yadda idanunsa ke masa zafi zafi.
Tun daga sanda yaji fitar sunanta daga bakin matar da bai tantance wace
ba......tun daga sanda ya fahimci yana jin maganganun wasu ne da zai iya yiwuwa
sirrinsu ne da bai kamata wani yaji ba,ya qara kuzarinsa na duba dukkanin flowers
din yabar gurin,don yasan zai wahala ya iya sake dawowa ya duba din idan yabar
gurin,yana da abubuwa da yawa daya tsara cikin satinnan.
"Calm down.....calm down" Ya samu wani sashe na zuciyarsa yana gaya masa,yana kuma
ji har cikin kunnensa.
"A'uzu billahi minash shaidanirrajeem......la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu
minazzalimeen" Ya furta yana ja baya a hankali yana qauracewa gurin. A hankali yaji
yana dawowa saitinsa,ya soma tuhumar kansa kuma da rashin gaggauta barin gurin don
gujewa jin abubuwan da zasu bata ranshi irin wannan.
"Astagfirullah" Ya samu kansa da furta a hankali yana motsa kyawawan labbansa.
Wani irin girgiza morsa safiyya tayi da wani nau'in madaukakin
mamaki......kalaman akhnan a yau sai takejin sunfi komai yi mata muni a
rayuwa......ba ita morsa safiyya kawai ba......dukkan family din DIOURI ta hada
tace bata buqata?,wannan wacce irin mummunar illa mammina ta yiwa ahalinsu?.
Tunanin yazo qarshe da wani irin tawagar hawaye cikin idanun morsa safiyya,saidai
kuma cike da wannan sadaukantakar tata ta soma maidasu cikin cikin idanunta a
hankali a sanda ta jiyo muryar mammina din tana shigowa gurin.
"Biftu?......biftu??" Tana kiran sunan akhnan din da wani yanayi dake nuna hankali
sam ba'a kwance yake ba,yayin data kafe bayan wanda take gani da kallo.
Bata iya ganin fuska ko wani sashe na jikinta,face shimfidaddiyar rigar
data suturta jikin morsa safiyya din.......amma already tun kafin ta fito zuwa nan
din ta samu cikakken bayanin morsa safiyya din tana tare da akhnan din a
madaidaicin kebantaccen lambunta.
"Biftu?......wanne irin shashanci ne haka?,wacce irin wauta ce wannan kika
aikata?,kinsan adadin dagin hankalin da kika sani?" Mammina ta furta tana dafa
dukkan kafadun akhnan ba tare da tabar wata alama da zata gwadawa morsa safiyya
cewa ta ganta ba.
Iya wanzuwar mammina a gurin ya karya zuciyar akhnan gaba daya,sai
takejin dukkan gatanta kamar ya dawo,sai takejin kamar matsalarta taxo qarshe,don
haka ta sanya fuskarta jikin mammina din tana riqeta da kyau gami da sakin wani
boyayyen kuka da mammina din kadai taji sautinsa ta kuma fahimceshi.
JINI YAFI RUWA KAURI wata nau'in karin maganan bahaushe kenan,duk da
bataga fitar hawayen ba......duk da bataga wani alama ba.....amma har cikin jininta
taji fitar kukan daga zuciyar akhnan din.
GANIN RAUNI a tattare da ita,shine abu na qarshe da baza bari idanuwan
mammina su gani a tare da ita ba....KOMAI GIRMAN TSANANI....KOMAI QARFIN
BALA'I,wannna ya sanya ta miqe tsam daga inda take zaunen tana jifan mammina da
wani irin kallon da tsana da tsananin qiyayya ce fal shimfide a cikinsa.
"Komai nisan dare gari zai waye.....komai nisan jifa qasa zai fado.....komai girman
gona akwai kunyar qarshe. Jini yafi ruwa kauri......nasaba da gaurayar jini cikin
tsatso da tushe guda ba wani abu da zai iya sauyashi.....duk duniya ba wani
sinadarin da zai kwashe wannan tabbatuwar jinin nasabar ya sauyashi zuwa wani na
daban" Ta qarasa maganar wani sassanyan murmurshi yana fita daga saman fuskarta,kai
bakace baqar wuta ce ke zabalbala qasan zuciyarta ba a daidai lokacin.
Zuzzurfan kallon kallo suka yiwa juna na wasu sakanni,sannan morsa
safiyya ta juya a hankali tana takawa cike da nutsuwa take barin gurin,saidai ko
mintuna daya tak batayi da bawa mammina baya ba,hawayen da take maqale dasu suka
maye gurbin wannan murmurshi da tabbas tasan fake ne,na bogi ne......murmurshin da
suka d'arsa wani qaqqarfan abu a zuciyar mammina.......ta kuma gaza dauke dubanta
daga dukkan wani taku na morsa safiyya da daukeshi.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
"Na gode" Morsa safiyya ta fada a hankali labbanta suna rawa sanda ta shafo hawayen
da yatsunta ta kuma bisu da kallo,sannna ta rab'e ta wani kebantaccen guri daya
zama nata ita daya don ta rage nauyin dake qirjinta ba tare da kowa yasan da wannan
ba. Ta godewa hawayen ne saboda basu bada ita gaban mammina ba......ta yaba musu ne
saboda basu fita a sanda bai kamata su fita ba,ya kuma jinjinawa zuciyarta data iya
dauke wannan nauyin me girma bata bari anga gazawarta ba har sai data kaucewa
idanun kowa.
Zare idanunta tayi daga hanyar wucewar morsa safiyya cikin jikinta tana
jin tabbas akwai wani abu........cikin tsakiyar wannan murmurshin lallai akwai wani
abu. Ba kowanne murmurshi ne yake kasancewa murmurshi ba.....kaman yadda ba kowanne
murmurshi ne yake dauke da ma'ana ba,wani murmurshin fanko ne......wani saqo
ne......wani kuma barazana ce,wani kuma yakan kasance gargadi ne.....batasan a
wanne muhalli ko bigire zata aza na morsa safiyya ba.
Cikin nutsuwar da iyakacinta saman fuskarta take duban akhnan,cikin
dakin daya kasance babu kowa a ciki,daga ita sai akhnan din suna fuskar juna. Duban
akhnan din take tana mamakin fitar hawaye haka daga saman fuskarta.
"Biftu......" Ta kirata a tausashe,saidai akhnan din taqi barinta ta qarasa fadin
abinda tayi niyyar fada din ta soma girgiza ma mammina kai
"Wallahi mammina.......bazan iya jurewa ba,bazan iya aurensa ba.......baiyimin
ba......bana sonsa!.....bana qaunarsa,don Allah,ki gayawa sultane......karkice zaki
juyawa alqawarinmu baya" Ta fada tana kama hannun mammina din tana dubanta da
dukkan wani hope nata.
Shuru mammina din tayi,fuskarta da yanayinta suna suna nuna rashin
gamsuwa da maganganun akhnan din.
"Na roqeki mammina......na roqeki,a yanzun bani da wani fata akan kowa sai ke,bani
da sauran yaqini sai a gurinki".
" Amma biftu....kinsan yadda sultane ya dauki maganan hakeem da girma kuwa?.....ke
kanki kin sani,shawarwarin morsa safiyya na days daga cikin shawarwarin da sultane
kewa kyakkyawan riqo da gasken gaske?". Idanunta ta lumshe sannna ta budesu,tana
jin wani irin matsanancin zafin morsa safiyya cikin ranta. Daga sanda taji cewa ita
ke riqe da ragamar karbar baquncin baqonta,daga sannan tasan cewa ba wani al'amari
kuma da zai kasance me kyau a tattare da ita.
"Bana son koda jin sunan matar nam mammina.....ki daina kiramin sunanta" Akhnan ta
fada da wani irin matsanancin kaushi cikin muryarta. A zahiri idanu mammina ta
watso waje tana duban akhnan,saidai batakai ga fadin abinda zata fada din ba akhnan
ta miqe
"Basai kin sake kiramin sunanta a nan wajen ba,iya kiran sunanta a kunne na yana
daidai da kiran gagarumar matsala ko rashin sa'a a tattare dani......shikenan
mammina.......shikenan tunda ba zaki iya nema min alfarma gurin sultane
ba......shikenan na tabbata cikakkiyar maras gata data rasa tsayayyar uwa.....na
tabbata wadda tafi kowa rashin gata a duniya..." Ta fadi maganan tana dosar qofa.
Tsam mammina ta miqe,sannan ta kamo hannun akhnan din ta jawota da
baya.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 73
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________
"Indai ina raye baki rasa gatanki ba......indai ina raye kuma na shirya sadaukar da
komai a kanki muddin hakan zai sakaki farinciki.....koda hakan yana nufin sadaukar
da fahimtar junar dake tsakanina da sultane ne,zanyi iyakacin bakin qoqari na,har
sai naga abinda ya turewa buzu nadi" Ta fada tana bawa akhnan tabbaci da yaqini da
dukka idanun data zubawa akhnan din su.
Wani irin abu akhnan taji yana sauka saman zuciyarta dangane da
mammina din. Wata irin qaunarta me girma ta taso ta soma lullubeta,a duniya tana da
masoyi sama da mammina kuwa?,anya mammina batafu sultane sonta ba kuwa?,wanne abu
ne a duniya zatayi ta sakawa mammina da dimbin tarin tulin soyayyar da take
mata?,wannan soyayyar bata da kama......bata da daidai,sai kawai ta fada jikin
mammina tana rungumeta da kyau,itama mamminan saita riqeta tana dan bubbuga bayanta
gami da fadin.
"Calme-toi,tout ira bien".
★Tsaki ya sake ja sau adadin da baisan yawansa ba,sannan ya ture system din gabansa
gefe yana murza tafukan hannunsa cikin na juna.
A nutse abdii ya daga kai ya kalleshi,tunda ya shigo yakeson
tambayarsa abinda ya tabashi yau amma yana tsoron saba dokokin da aka shimfida masa
kafin ya samu ya aminta da qyar su zauna tare. Maher kawai ya zaba su zauna dashi
cikin gidan,saboda shi din ya kasance kamar wani ido ne gareshi cikin
masarautar,saidai kuma kaida fata abdii yaqi aminta ya fita,dole haisam ya
barshi,bayan ya zauna ya jera masa dukkan sharuddan da abdii kansa tsaye yace ya
amince,duk kuwa da cewa yasan ba komai bane zai iya bi ba a dokokin.
Numfashi ya zuqa sosai yana fesarwa ta bakinsa
"What wrong with you haisam?" Ya furta da wata murya da daga shi sai zuciyarsa
kadai ke iya jinta.
Sake lumshe idanunsa yayi,yanajin wani bacin rai kadan kadan yana lasar
zuciyarsa.
"Why she's so stubborn?.a silly girl.....ya akayi ta kasance d'iyar kamilin mutum
me daraja da dattako irin sultane.
"Yukhrijul hayya minal mayyit?" Ayar tazo cikin kansa. Numfashi ya sauke a
ransa,yana ji a rayuwarsa bai taba jin wani abu da yaji sam baiyi masa ba,bai taba
jin wani abu da yakejin haushinsa yana ginuwa cikin ransa ba irin yarinyar.
Totally irin matan nan ne masu tsananin girman kai?.....rashin iya
magana?.....masu jin cewa izzarsu gaban na kowa yake?.