Showing 84001 words to 87000 words out of 168506 words
kai qasa da naka shekarun.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 41
___________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*
*Assalamualaikum*
*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*
*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*ππ₯»
*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin
Aminci???*
*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*
*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana
βπ½
goma KACAL! *
*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*
*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*ππ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*
*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*
*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT
da yardar Allah*
+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791
https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
___________________________
"Ni ga tawa tsarabar......Niamey nasan basu da wani abu na musamman da
za'a iya tahowa agadez dashi" Ta fadi ba tare data tsaya duba ko tunanin batace
komai da ita ba har yanxu.
Madarar ta bude ta fiddo wasu qawatattun cups guda biyu ta zuba,sannan
a gefan ta saka wani plate din ta shirya fruit din da dukkaninsu take kyautata
zaton zabin akhnan ne.
Ido ta zubawa plate din sanda falaak ke ajiyeshi kusa da ita. Sai data
gansu ta tuna rabonta da abinci tun madarar da tasha da safe a Niamey. Duk wani
kayan alatu na ciye ciye da mammina tasa aka bata dare zuwa safiya ana shirya mata
ta gaza cin komai.
Sultane har abada sultane ne.....akwai shaquwa qauna da soyayya me
girma tsakaninta dashi,amma hakan bai canza wayeshi ba,bai canza wannan tsananin
nasa da kafiya ba.....bai canza qwarewa wajen iya hukunta mutum ba idan yayi ba
daidai ba. Duk da tasani,a yawan lokuta tana cin albarkacin qaunar da yake
mata......tana sanyashi ya runtse idanu ya sakar mata abubuwa masu yawa.....Amman
haka baya hana wanzuwar d'aci saman harshenta a duk sanda ya murde ya kuma yi wani
hukunci.
Madarar da falaak din ke miqa mata tabi da kallo.
"Karki ce ba zaki sha ba.....kyauta ce daga 'yar uwa zuwa ga 'yar uwarta" Ta fadi
tana narke murya da fuska kaman zata saki kuka. Sai bata sake cewa komai ba,ta saka
hannu ta karba,ta kai bakinta ta soma sha.
Sak irin madarar da tafiso fiye da kowacce,tayi mamaki kadan na yadda
akayi falaak din tasan haka,amma izzarta ta hanata ta tambaya. Abun baiwa falaak
ciwo ba,tunda har gashi tana sha,tunda har gata a gabanta tana mata fira kuma tana
saurarenta,hakan ya sanyawa falaak hope me yawa akan wataran komai zai canza kamar
yadda momma keda buri da kuma fata.
"Momma nata kewarki......tunda akace kinzo taketa shirin tarbarki,tana ta duban
hanya duk da batace komai ba,amma nasan tana jiran ganin shigowarki ne" Falaak din
tayi qarfin halin fada.
Yadda taga fuskar akhnan din ta gimtse sai taji abun ya tabata,kafin
kowannensu yakai ga cewa komai motsin mutum daga baki qofar yaja hankalinsu.
Mammina ce ke shigowa a nutse idanunta akan falaak,kafin ta janyesu
ta maida kan akhnan sannan ta azasu akan cup din hannun akhnan din,kafin ta kuma
saki murmushi tana cewa.
"Yauwa......gwara da kikazo ai......ta dalilinki tasha madara kenan?" Mammina ya
fadi tana zama gefan akhnan din.
Kai falaak ta daga a sanyaye tana duban mammina din kafin ta maida
idanunta akan akhnan wadda ta dora kanta a hankali saman kafadar mammina,abinda zai
gaya maka zurfin shaquwar dake tsakaninsu.
Tsam falaak ta miqe tana ajiye cup din nata hannun.
"Zan qarasa ciki yaa biftu......me zance da momma?". Maganar ta saka mammina daga
kai ta kalli falaak,shurun akhnan kuma ya zama kusan shine amsa ga falaak,sai
mammina tayi murmushi.
"Tunda sultane yayi kiranta hankalinta yake a tashe,nayita fama da ita ta shiga ta
gaidata amma taxo daki ta wani narke kaman wadda akace yankata zaiyi.....karki damu
zasu iya haduwa yanxun nan,don naga jakadiya asabe ta tafi kiranta". Kai falaak ta
jinjina a hankali sannan ta juya ta fice.
"Ki tashi ki shirya......sultane ya zauna" Maganar data saka akhnan daga kanta babu
shiri tana duban mammina. Meye hadin kiranta da sultane yayi da kuma kiran momma da
yayi?,hakan na nufin ganinta da zaiyi a gaban momma ne?.
Tsaf mammina ta karanci komai ta idanunta,saita girgiza mata kai.
"Banaso kiya wani ba daidai ba......banaso ki musanta duk wani abu da nace kiyi".
" Indai ni da sultane da ita ne......kiyi haquri mammina......bazan amsa kiran
sultane ba" Tayi maganar wani zafi yana tasowa daga qasan zuciyarta. Murmushi
mammina ta saki dan qarami.
"Harda ni...harni sultane ya kira" Maganar data bawa akhnan relief kenan.
Hannunta yana cikin na mammina din sanda suke shiga Qawatacciyar
shiyyar sultane din dake da wani irin zubi da ado na daban. Cikin wata doguwar riga
ruwan madara ta shirya,wadda qasanta yake a bude sosai yake kuma sharar qasa. Hawa
biyu ne da ita,don haka ta saman gabanta a bude yake,saidai an mata wani irin
Qawataccen aikin hannu.
Daidai bakin dakin hutawarsa jakadiya asabe ta dakata tana ja da baya
gami da rusunar da kai,yayin da mammina sukaci gaba da takawa ciki ita da akhnan da
takejin zuciyarta kamar zata fito.
Bata iya yin sallama ba,sai sallamar mammina data wakilci tata. Cikin
muryar sultane ta tsinci muryar momma din,wadda ke zaune daura da tuntum din da
sultane ya dora hannunsa dake dauke da ayabar da momma ta bare masa tana kuma yanka
abarba taba ajiyewa a plate din dake tsakaninsu.
Janye idanunta momma tayi,bata fiya son kallon mammina a tare da
akhnan ba,yawan kallon yana qoqarin wargaza mata duk wani kafiya da cijewarta da
kuma tsarinta na shekara da shekaru da take tafiya kuma take aiki a kai.
"Sannu da aiki" Mammina ta fadi tana zama daura da momma din cikin sakakkiyar fuska
me nuna kulawa da damuwa da mutum.
"Yauwa" Ta fada tana dauraye hannunta adan wani qoqo na zamani dake gefe ba tare
dako ta kalli fuskar mammina ba.
Janye ido akhnan tayi daga kansu. Har abada morsa safiyya bata da wani
buri illa ta wulaqanta mammina?,akan meye ne?,me mammina tayi mata haka?. Me yasa
mammina ba zatayi zuciya ba?,me yasa ba zata haqura ba ta daina damuwa da dukka
lamuranta ba?. Tunaninta ya tuqe sanda ta zube gaban sultane tana fadin.
"Barka da warhaka bappi.....barka da wannan lokacin"
"Yauwa barkanki" Ya fadi a yana dubanta kafin ya janye idonsa daga kanta ransa yana
motsawa.
"Barka da dare" Akhnan ta fadi tana waiwayawa sashen da momma ke zaune ba tare data
kalleta da idanunta ba.
Murmushi sosai ya wadata a fuskar momma din,cikin sakakkiyar murya dake
nuna kulawa ta amsa.
"Barka kade biftu,ina fatan kina lafiya?"
"Alhmdulillah". Ta fadi har qasan ranta bataji ita ko kulawarta suna burgeta.
"Ya baku taho dukkaninku ba?.....kamata yayi ace dasu aisa din kukazo ai ko?" Ta
qarasa maganar tana maida dubanta ga sultane.
"Ba buqata,hakanma ba laifi" Ya furta yana turawa akhnan plate din kayan marmarin.
Maganar morsa safiyya qwaya daya tak ta d'arsa wani abu saman zuciyar
mammina. Nazartarta takeyi kaman yadda zargi me girma ya d'arsu a zuciyar akhnan.
Taji a jikinta duk wani kira da sauran b'urbushin fushi da take gani daga fuskar
sultane yana da alaqa da momma din.
Wai me yasa har abada matar ba zata daina bata ciwon kai ba?,me yasa ba
zata daina zama silar bacin rayukanta ba?. A hakanne zata dauki duk wani karatu
akan girma da martabarta kaman yadda mammina da sultane sukeso ta dauka?.
Abinda ya qara birkita mata tunani shine......hira da sultane ya fara
yi shida momma din. Wani abu ya motsawa mammina,ta gyara zamanta cikin sakin
murmushi tana jefa bakinta cikin hirar tasu.
Bata taba yarda ta zama saniyar ware a gaban sultane,bata kuma yarda da
kowanne irin abu yayi mata shamaki ko katanga tsakaninta dashi ba......kamar yadda
bata laminci ki na second daya hankalinsa ya juya daga kanta ba.
Cikin second biyar kacal sultane din ya jefa tambayar data saka
kowacce jijiya tsinkewa daga jikin mammina da akhnan.
"Me yasa ba'a shaidamin shirya tseren dawakai guda biyu ba da aka gabatar a Niamey
cikin satittika biyu da suka wuce?" Yayi tambayar yana aza idanunsa akan fuskar
mammina,tambayar data fita daga bakinsa cikin wani irin calmness hankali kwance,ba
alamun fushi fada ko bacin rai,amma kuma cikin qasa da second uku tambayar ta huda
qirjinta ta kuma soma yaga bangarorin zuciyar akhnan da tsoro.
Maganar tazo mata da wani irin ba zata,ba zatar da bata taba hasashe ba.
Cikin ranta taji wannan din shiryayyen abune......wani abu ne da aka shirya
faruwarsa,don bataga ta inda maude zai fidda labarin nan ba koda dambunsa za'a yi.
Koma dai menene ita din har kullum tana juyawa ne da tsalle a tsakanin
lissafinta,bata taba bari wata lamba ko gido qwaya daya ya bacewa ganinta
ballantana lissafinta ya shiga rudu. A gaban sultane take,qasqanci kuwa muddin a
gabansa ne tayi imanin DAUKAKA ce da kuma cimma nasara me yawan gaske,don haka ta
sadda kanta,da muryar ta da tayi matuqar laushi ta fara magana.
"Tuba nake......tuba nakeyi ranka ya dade......akwai dalilai da suka......" Hannu
ya daga mata.
"Ta wuce zaitun....ta wuce,amma akwai na gaba da wala'alla basuzo ba bare su wuce"
Sai ya maida dubansa ga akhnan. A lokacin tana jinta ne kamar an tsomata a Kogin
qanqara,sai takejin ta gwammace ko wanne hukunci ne sultane ya fadeshi,wataqila ta
iya jureshi,wataqila ta samu sassucin fargabar da takeji.
"Akwai cikin masu son aurenki da zaki iya gabatarmin dashi a gobe?". Wani
gigitaccen abu taji ya dira tsakiyar kanta,ta daga idanunta a birkice tana kallon
sultane. Tayi zaton idan ya mata magana zata samu relief ne,ta dauka komai zai soma
sassauta,amma sai taji har gwara shurunsa,har gwara baice komai ba.
Kai take girgizawa da sauri tana jin wani tashin hankali. Ko kalar
wannan tambayar bata shirya amsawa ba bare ita kanta tambayar.
"Akwai?" Sultane ya sake tambayarta cikin dakewa yana dage dukka girarsa sama. Ta
kasa cewa komai sai kai da take girgizawa. Zamansa ya gyara sosai yana
fuskantarta,abu guda daya dake tabbatar mata magana zaiyi kenan da dukka
gaskiyarsa.
"Ba damuwa bace......ni ina da wanda zan gabatar miki........a gobe ne kuma
zaizo......bawai zaizo don ki gane yayi miki ko baiyi miki ba......zaizo ne don ki
shaida fuskarsa,ki kuma sakashi cikin mafarkanki na shine mijin aurenki,mijin
rayuwarki na dindindin,daga lokacin kina da damar yin tseren dokuna iya dukka
adadin gudun da kikeso idan har shi ya lamunce miki".
Bata taba yarda zama zai iya gagarar mutum ba sai a sannan. Tana daga
zaunen amma neman abinda zata dafa takeyi don ji take faduwa zatayi.
"Bappp....." Ta kasa furtawa saboda kallon daya aje mata,saita waiwaya tana duban
mammina wadda takejin ita daya ce ta rage mata,itace kawai damarta ya qarshe.
Cikin rashin sa'a saita samu mammina din kanta yana a qasa ne tun sanda
tayi magana ta farko,kuma har yanzun bata dago ba.
Abinda bata sani ba,maganganun sultanate akan akhnan din sune suka qara
mata nauyin da takejin kamar ma bazata iya daga kan nata ba har sai an taimaka
mata. Wani irin kalar tashin hankali takeji yana sakko mata yana lullube kowanne
sashe na jiki da zuciyarta
Iya sautinsa,iya kuma yanayinsa kadai ya gaya mata,ko duka duniya zasu
taru basu isa su sanya sultane yanjanye hukuncinsa ba a dadai wannan lokacin. Inda
kuma akhnan zata fuskanci hakan data hutar da kanta,da bata bata bakinta ba gurin
kiran.
"Momma......ki taimaka min". Har qasan zuciyarta takejin tausayinta yana narke
mata,to amma wata soyayyar wani nuna tausayin wa yaro bashi da wani rana,bashi da
wani muhimmanci face jagula komai da yake sakeyi.
"Kiyi haquri akhnan......darajarki kenan......mahaifinka bazai taba iya cutar dake
ba" Ta furta tana lanqwasa muryarta da zummar ganar da akhnan din,saidai a maimakon
ta gane din,sai wani matsanancin jin haushi da jin tsanar momma din ta saukar mata.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 42
____________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*
*Assalamualaikum*
*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*
*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*ππ₯»
*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin
Aminci???*
*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*
*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana
βπ½
goma KACAL! *
*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*
*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*ππ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*
*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*
*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT
da yardar Allah*
+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791
https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
_____________________________
β
Sai data tattara dukkan wani qarfin halinta da qwarin gwiwarta sannan ta
iya kiran sunanta.
Daga inda take zaunen,gurin da tunda suka shigo dakin ita da mammina
din bata iya motsawa daga gareshi ba. Tana jin gangar jikinta ne kaman ba'a liqe
take da ruhinta ba,infact tana jin gangar jikinma gaba daya kamar ba tata ba.
Abinda kawai zata iya banbancewa shine,yadda tafukan hannayenta dama na qafafunta
suka dauki dumi,kaman yadda taji fuskarta tana wani irin huci ita kadai.
Tana sake maimaita da nanata zantukan sultane ne kawai.......a taqaice
dai abinda sultane yake nufi shine.......yayi mata miji?.
Kaman an doka ganga tsakiyar kanta sanda lissafinta yazo a nan. Tana
jin komai ne kamar almara.......a ra ta takeji wannan abun bame yiwuwa bane. Bada
ita ga wani kamar kyautar kofin shayi?,bada ita ga wani mutum da batasan meye
mataki ko darajarsa ba arayuwa?. Wai waye wannan ma wanda zaiyi ganganci nutsar da
rayuwarsa cikin nata?,waye shi da har ya samu wannan galabar a taqaitacce
lokaci?,yake nema raba soyayyar dake tsakaninta da sultane?.
Yin wasan tseren doki kadai shi zaisa sultane yanke mata wannan hukuncin
da yake daidai da mutuwarta?. Ina qaunar da sultane yake mata?,ina soyayyar da yake
mata gaba daya ta tafi saboda kuskure daya tak?!.
"Biftu" Mammina ta furta tana qoqarin hadiye abinda yake mata kai kawo tana zama a
gaban akhnan.
Da qyar ta daga idanunta da suka sauya launi,wadannan kyawawan blue eyes
din da suka jirkita zuwa launin ja,ta zubawa mammina su ba tare data iya cewa komai
ba.
"Ki nutsu ki kwantar da hankalinki........sultane bazai miki auren dole ba". Wani
murmushi da sam bashi da nasaba da dangantaka da halin da take ciki ta saki,ta
zauna sosai daga sunkuyon da tayi tun a dazun.
"Ba sultane ba mammina......ni da kaina bazanwa kaina auren da banaso ba......bazan
yi musu da sultane ba,bazan kuma bijire masa ba.......amma ina me miki rantsuwa,ko
waye zaizo a goben sai ya kwashi kashinsa a hannu,zan sakashi ya banbance tsakanin
aya da tsakuwa......saina sashi yaji nadamar yunqurin neman auren gimbiya khadeeja
akhnan......wannan alwashina ne" Tana kaiwa nan ta miqe,duk da a zafi take amma
yanayin tafiyar nan tata mai cike da qasaita bai sauya ba,ta nufi dakinta kai tsaye
tana shirin maida qofar ta kulle mammina na qwala mata kira. A yau kam ko mammina
batajin zata tsaya jin abinda zata ce mata.......kwanyarta ta cika da dimbin
tunanin WAYESHI?. Me ya taka?,me kuma yake taqama dashi?,yasan wacece ita ko kuwa
ganganci kawai zai gwadawa rayuwarsa?.
Idanun mammina akan qofar har zuwa sanda akhnan ta bacewa ganinta.
Dauke dubanta tayi daga wajen,ta sauke hannuwanta ta soma takawa tana barin wajen.
Ba haka take so ba.....zamanta a daki ita daya zai sanya ta qulla wani tunanin na
daban da bashi ya cancanta yazo kanta ba,tana buqatar zamanta a kusa da ita......a
daidai wannan lokacin bai kyautu ba bai kuma kamata ta zauna ita daya ba,sai ita
kanta tana buqatar kebewa,tana buqatar ta kebe ita daya,kebewar da zata kasance
daga ita sai numfashinta kadai,wataqila zatayi wani tunanin daya kamata ya kuma
dace da ita.
Wani irin birkitattun tunani ne suke zuwa kanta sanda take shiga
qasaitaccen bedroom din nata,ta kuma maida qofar ta kulle.
"Anya bazan makara ba?" Ta furta a hankali tana dora yatsanta saman labbanta.
Takawa taci gaba dayi tamkar me tsoron taka qasa. Kai tsaye ta nufi wata qofa da
yanayinta da adon jikinta yasha banbam da