Showing 150001 words to 153000 words out of 168506 words
qiris garin jan
numfashi ta hada harda zuciyar dake qirjinta. Karo na farko da irin wannan kalmar
ta fita a bakinsa zuwa gareta.
Ta sani,he was a caring person......yana da tausayi musamman ga
mace,amma bai taba gwada gaya mata kalma irin haka ba,sai kawai ta kifa fuskarta
saman cinyoyinta zuciyarta na wani irin bugu,ko kalaman NA GODE da zuciyarta ke
bata shawaran gaya masa bata samu damar fadi ba,don dama yana gama fadin hakan ya
yanke kiran.
"Har kun gama wayar?" Muryar Anani ta ratsa kunnuwanta. Kanta ta daga da sauri suka
hada idanu da Anani din,sai ta kashe ma saame idanu tana dariya qasa qasa.
"Muddin kikace zaki fara narkewa da soyayyar captain obbo......na rantse nan gaba
zaki koma tamkar ruwa ne.......ni nasan irin su captain sheikh..........saamee...."
Sai kawai Anani ta gaza qarasawa tahau girgiza kai.
Ranar data fara duba daya daga cikin rubuce rubucensa akan
soyayya,cikin wani irin tsari na a addinance yadda zaka kama zuciyar mace tabbas
banda yayanta ne uwa daya uba daya tayi imanin ba abinda zai hanata fadawa
soyayyarsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Wasu irin kalamai da aka shiryasu da harshen larabci,sannan akayi
translating nasu da yare biyu English da oromo,sai da tayi kwana uku tana duba
littafi daya,daga qarshe data fuskanci idan batai wasa ba littafin zai iya sauketa
daga karatunta daga qwallafa rai zuwa bigiren fara soyayya ba shiri,saita lallaba
ta maida masa littafin sa ba tare da yasan daukowar da mayarwar ba,wanda yana dab
da gama rubutunsa yayi publishing nasa aikin tafiya agadez ya tsaida komai.
Har yanzu idan ta kalleshi kalaman take gani saman fuskarsa. Wannan
miskilar fuskar da babu fara'a murmushi ko sakewa a cikinta,fuskar da baki samun
cikakken kallo daga gareta,da wadannan idanun masu wani irin nauyi,ashe sunsan
tasirin soyayya har haka?.
Kasa cewa komai saamee tayi da tsiyar da Anani ta sakata a gaba tana
mata,illa dai ta miqa mata wayar nanay kawai ta wuce dakinsu,don idan ba haka ta
yiwa Anani ba tabbas zata uzzura mata ne kawai.
Saman gadonta ta fada,ta kuma jawo pillow ta rungumeshi sosai cikin
qirjinta. Ba ita kadai ba,tasan akwai tarin tulin 'yammatan da suke cikin irin
wannan yanayin saboda shi.
Tayi imanin a duniya ba macen da zata ganshi taji baiyi mata ba,saidai
idan dama tasan ba zata samu bane. Babu wata halitta da zata kasa qaunatarsa,yana
da wasu irin halaye da qualities masu tsananin tsadar da yake nasarar sace zuciyar
duk wanda ya mu'amalanceshi. Hatta da qannaneshi sonshi suke,saidai su za'aci
soyayya ce irin ta 'yan uwantaka,saidai duk da hakan tsakanin hussam da Aarif ba
wanda ya samu irin soyayyar da dukkaninsu sukewa Muhammad haisam din.
Numfashi taja sosai cikin hunhunta. Idan tana imagination na ranar da zai
kalleta yace INA SONKI SAAMEE,tana jin komai ya tsaya mata,ta kuma tashi daga
wannan duniyar zuwa wata. Idan tana hasashen ranar da zata zama mallakinsa,sai taji
kaman duniya gaba daya tata ce ita kadai.......to amma wanna fargabar tana nan.
Wannan alwashin yana nan,batajin kuma akwai abinda zai canza shi. Tana
buqatar ya gamsu da soyayyarta da kanshi. Tana buqatar suyi exchange na
soyayya,bawai ita kadai tayi dakon soyayyarsa ba. Tana babban mafarki da buri na
auren namijin da duk duniya itace burinsa......itace zabinsa,itace mafarki da dukka
muradansa. Koda ita batajin hakan,idan ta samu wadancan abubuwan a tare da
namiji.....zata yarda zata aminta ta rayu dashi,wataqila nan gaba zuciyarta ta cika
fal da soyayyarsa kamar yadda yake mata.
*MAMMINA*
Yau da kanta ta shirya kanta a daren da zuciya da qirjinta ke cike da
tarin lissafe lissafe da burace burace.
Wannan zuwan,wannan tafiyar da zatayi da buqatar akhnan zuwa gaban
sultane......a zahirin aiken na akhnan ne zallah.......a badininsa kuwa,wani babban
buri ne......wata babbar buqata ce da take da burin cikarta fiye da girman buqatar
da akhnan din keda ita.
Hannu ta sanya ta jawo jewelry organizer dinta tana laluben abun
hannun da zata sanya,wanda zai dace da yanayin shigarta.
Har hannunta ya tsallake kansa,sai kuma ta dawo da baya tana sake
sauke idanunta a kanshi,ta miqa hannunta ta dauka.
Wani irin bangul ne na asalin kayan gargajiya me tsananin tsadar gaske.
Banguls din qwaya biyu ne rak,suna tuna mata wasu abubuwa masu nauyi da suka shude
cikin rayuwarta. Suna da wani tsohon dadadden tarihin da babu ranar da zata dora
idanunta a kansu ba tare da sun dawo mata da komai ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 75
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________
Sultane yana sonsu qwarai........duk kuma da son da yake musu takan jima
bata sanyasu ba,amma a yau din sai taji zuciyarta ta cika da sha'awar sakasu,ta
daga hannun damata ta zurasu a nutse tana sakin murmushi ganin yadda ya sake qawata
hannuwan nata.
Tana maida jewelry organizer din taji an murda handle din
dakin,kafin ta waiwaya kuma motsinta ya gaya mata ko wacece.
A hankali cike kuma da mamaki ta juya tana dubanta. Akhnan ce,sanye da
wata farar Malaysian Avaya. An mata wani irin kyakkyawan ado da gold din zare daya
sake fidda kyau da qawatuwar rigar. Maqale mayafin rigar yazo a kafadarsa,kuma iya
shi kadai akhnan din ta yafawa kanta,wannna ya bawa gashinta me sulbi dake kwance a
agadon bayanta daman bayyana saboda wuyanta a bude yake saboda yadda tadan dora
mayafin kawai ba tare data wani daidaitashi saman kanta ba.......hakanan kana ita
gabin baqar sumarta data fara daga gaban goshinta,ba wani cirewar gashi kaman
dasashi akayi.
Wani irin kyau tayi,kyan daya dauki hankalin mammina ya kuma tuna mata
da ranar farko data fara ganin SAFEENA a rayuwarta,ranar da har yau har kwanan gobe
ba zata taba gogewa daga cikin kundin rayuwarta ba......ba kuma zata taba gogewa
daga jerin sahun ranakun qaddararta ba.
Idanunta ta lumshe tana controlling emotions dinta.
"Ya akayi biftu?" Ta kirata da wani nau'un tausasawa cikin muryarta,tana duban
fuskarta da tayi fayau tadan fada kadan,saidai hakan kuma sai ya zame mata kaman
ado ya qawata shape din fuskarta lips dinta da hancinta gaba daya.
"Zan biki.....zanje na roqu sultane da kaina......" Ta fada da salon miskilancin
nan nata da yau ya nuna muraran.
"Me yasa?,baki yarda da zan iya samun nasara a kanshi ba da kaina?" Kai ta
girgizawa mammina,tana zama a sanyaye gefan sofa bed.
"Bana tunanin a duniya akwai wata halitta mafi soyuwa a ran sultane.....halitta
mafi daraja,halittar da tafi qarfin yayi mata kalan kowacce alfarma kamar ni,idan
zaiyimin zai iya yiwa kowa......idan bazaiyimin ba bazai iya yiwa kowa ba.....na
duba littafin da mahaifiyata ta barmin yau a karon farko,a shafin farko kadai dana
duba kuma na fahimci haka". Idanu mammina ta janye daga kan akhnan,tana son tuna
wanne littafi ne wannan da ita ta mance dashi?,wanne littafi ne da ita bata
mallakeshi ba?,wanne littafi ne haka daya halitta mata sabon tunani cikin qaramin
lokaci.
Tattara komai tayi ta hadiyeshi tana sake jinjina kai.
"Gaskiyan ki ne,mu tafi tare,yana da kyau" Ta fada tana miqawa akhnan hannu,ba tare
da tayi qasa a gwiwa ba ta miqawa mammina din itama cike da fatan tabbatuwar
nasara.
★Cikin shigar cikakken qasaitaccen basarake yake zaune cikin parlor din
nasa,sanye da tufafin zaman gida,saidai kuma duk da sun kasance na zaman
gidanne,amma na dabanne dake dauke da tambarin qasaita,tun daga yauqin da yadin
yakeyi zai gaya maka tsadarsa da darajarsa.
A nutse ya dauke idonsa daga saman tanqamemiyar Tv din dake
aiki,wadda yake kallon labarai daga tashar France 24 dake haska labaran duniya ya
maida ga bakin qofar yana amsa sallamar nutsuwarsa da kwarjininsa yana tasowa.
Wani abu ne ya sauka zuciyar mammina,ganin yadda ya zuba musu ido a
nutse yana kallonsu ita da akhnan din,yayin da kwarjininsa ya daki idanu da zuciyar
akhnan din,har ya sanya ta motsa kadan tana lafewa a bayan mammina.
"Barka da warhaka bajimi namijin zaki" Ta fadi tana sauke wani sassanyan murmushi
saman fuskarta.
Martanin murmushin ya maida mata,yana kuma dauke idanunsa daga kan akhnan
dake takowa kaman wadda ke takawa wani abu me santsi da take tsoro kada ta zame.
"Barkanki......barka da warhaka giwar agadez" Ya amsa mata cikin ransa zuciyarsa na
ayyana masa komai kafin takai ga cewa ko aiwatar da komai din. Saidai har qasan
zuciyarsa yana sake jaddadawa kansa,indai abinda ya shigo da ita kenan zaya basu
mamaki su dukansu.
Yadda ya maida mata kirarin ya mata dadi sosai,ya kuma sake qara mata
qwarin gwiwa,sai taci gaba da takowa har zuwa daura dashi. Gefen mammina ta
zauna,tana rabewa sosai a jikinta,kamar qaramin yaron dake bala'in qyuya yake kuma
tsoron kada a tabashi.
"Barka da wannan lokaci toron giwa......ina fatan za'ayi mana uzuri,za kuma a bamu
dama,don zamu shiga lokacinka kadan". Idanunsa ya dauke daga kan mammina din,yana
sauke basaraken murmushin nan nasa dake qara masa kwarjini,ya gyara zamansa sosai
cikin tattausar sofa din da aka sake shimfida wani tattausan abu a samanta saboda
nuna girma da martabawa ga wanda zai zauna akai din. Qaramin numfashi ya sauke dake
nuna dattijantaka.
"Bawa iyali lokaci ai abune dake da matuqar tasiri da kuma alfanu,saidai kawai ina
fatan lokaci ya zamana an qarar dashi akan wani abu dake da tarin muhimmanci". Ba
jiya ko yau aka raini harshe da kwanyarta ba,ba kuma jiya ko yau take zaune cikin
yankin agadez ba ballantana ta gaza fahimtar harshe da kuma sigar daya watso
maganganunsa akai ba. Sai ta jinjina kai,tana sake lanqwasa kanta cikin yanayin da
tasan yana matuqar sassauto mata dashi a duk sanda yahau wani tudun naqi din nasa.
Dukkan wani siffa da yanayi da tasan yana karya mata sultane din......dukkan wani
yanayi da tasan yana mata jagoran samun nasara tattare da sultane din......gaba
dayansu ta aro ta lulluba saman fuskarta .
Wani yaqi ne da bawai ya shafi akhnan bane kai tsaye......a badini ma
wannan yaqin.....wannan zaman nata ne....duk wani alfanu dacewa ko kuma hasara da
faduwa da za'a samu NATA NE bana AKHNAN bane,akhnan ce kawai a fuskar,amma a
lullube......a bayan fuskar a bayan manufar MURADANTA ne a shimfide.
"In sha Allah.....ba zakayi dana sanin bamu lokacinka ba.....kuma nayi imanin zaka
sauraremu da dukkan kunnuwanka masu cike da adalci da tausayawa na qasa dashi".
Motsawa ya sakeyi kadan yana lanqwasa yatsunsa,already ya fahimci maganan data
kawosu,to amma yana da wani irin nutsuwa da dattijantaka a jininsa,bazai hanasu
magana ba,tunda ya riga ya gama yanke hukunci,baya tunanin kuma akwai abinda zai
sauyashi.
Da qyar ta tattara duk wani qwarin gwiwarta,ta sauke qanta qasa,da
wannan tattausar muryartata dake da wani irin amo me sanyi akhnan din tace.
"Barka da warhaka bappi". Kadan ya dubeta,cikin bagararwa kaman baiga wani canji
tattare da ita ba yace.
" Barkanki,kina lafiya?" Tambayar da yayi mata saita tsinkar mata da zuciya.
Sultane yana nufin shi baiga komai tattare da ita ba?,baiga girman tashin hankalin
data shiga ba?,baiga yadda nutsuwarta ke neman wargajewa ba?,baiga yadda komai nata
ya sauya ba?. Bama wadannan ba duka,ita din da idan tazo agadez,duk wani motsinta
na wunin ranar......duk yadda sultane yakai ga yin busy,duk yadda itama takai ga
shigewa wasu hidimomin.....koda sau daya ne a qalla a kowacce rana sai taxo sunci
abinci tare,walau na safe ko na dare?,wasu lokutan ma idan ya samu sukunin ayyuka
da kyau sukanci na rana ne tare.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tana zama ta sake sosai dashi fiye da yadda take sakewa da kowa,wani
lokaci fiye ma da yadda zata sake da mammina.....sama da yadda zatayi hira da ita.
Ya bata duk lokacinsa,ya saurareta,ya kuma bata shawarwari. Wasu shawarwarin sun
shafi rayuwarta ne,wasu sun shafi sahel couture,wasu kuma fadakarwa ne da jan
hankali dangane da rayuwa,amma yau duka sultane ya ruguza wadannan abubuwan don
kawai yana so tayi aure?. Yafi kowa sanin auren nan ba wajibi bane......bai zama
wajibi a kanta ba,amma ya matsanta ya daga hankalinsa,to ko sultane ya fara gajiya
da ita ne?. Ta tambayi kanta da kanta,bata kuma kai ga lalubo amsar ba muryar
mammina ta sauka a kunnenta.
"Ranka ya dade.......alfarma mukazo nema" Ta fada tana sake qanqan da kai. Kansa ya
daga a nutse ya kalli mammina.
"Allah yasa zancan bame tsaho bane,don ina da baqo me muhimmanci da na gayyata
zamuci abincin dare dashi" Ya qarasa maganan yana kallon katafaren agogon dake
tsaye da qafafunsa wanda akayi da wani irin qarfe daya bada shape na gidan sarauta.
Wani irin bambarakwai sukaji maganar ta saukar musu,girman maganar a
kunnuwansu ya sanya suka kalli juna a sanda idanun sultane yake kan agogon,kafin ya
janyeshi a hankali ya maida dubansa kan mammina din.
"Wacce alfarma ce?,Allah yasa batafi qarfina ba......bata kuma shallake iyakoki na
ba" Ya fada hankali kwance,yana barin kwanyar akhnan dama ta mammina da lisaafin
wanne irin baqo ne haka me tsananin muhimmanci a gurin sultane?,har yana batun su
gaggauta fadin buqatarsu don lokacinsa na baqonsa ne kenan?. Wani abu akhnan taji
ya tsaye mata a wuya. A iya saninta,ita kadai ce,ita daya ce keda tarin wannan
muhimmancin a gurin sultane,to amma waye haka ya samu nasara ya shammaceta,yake
kuma neman daidaito kan matsayinta da ita kadai ta cancanci ta sameshi?.
Wani abu me qarfi mammina ta hadiye tana qoqarin saisaita
muryarta,tare da bad da tunanin dake neman yin wasa da kalaman data tanada saboda
lokaci irin wannan.
"Ba wata buqata da zatafi qarfinka Allah ya baka yawan rai......komai yana biyayya
ne ga umarninka......haka nan jin qanka......ya ta'allaqa ne akan kowa,ballantana
kuma kan iyalinka da kuma shalelenka" Takai qarshen maganan tana nuni da akhnan
dake zaune bata ko qwaqwaqwaran motsi.
"Karki damu da dukka wadannan bayanan,jeki kai tsaye ga bayananki" Ya fadi yana
qara nesanta fuskarsa da dukkan wata fara'a.
"Me martaba......muna neman kayi mana rai.....kayi mana alfarma,ka janye zancan
hakeem daga kanmu.......ka dubi......."
"Zaituna" Kiran da sultane yayi mata kenan,wanda ya sanya gabanta wani muguwar
faduwa. Sautin daya kirata dashi,da kuma kiran da yayi mata kai tsaye ba sakayawa
ya tabbatar mata cewa.....lamarin yayi wani irin zama cikin zuciyarsa......hukuncin
ya samu dukkan tabbatuwar da babu alamun janyewa.
"Zaituna......daga yau daga kuma yanxu.......inaso ki janye kanki daga cikin wannan
batun.....bama ke ba,inason duk wani wanda yakeson ya tsira daga fushina ya cire
hannunsa.....wannan din hukuncina ne......wannan din zartarwa tace da babu wani abu
da zai canzashi. A wannan shekarar,zan aurar da diyata ga wanda na gamsu na kuma
nutsu da addininsa tarbiyyarsa da nasabarsa,zan aurar da diyata kamar yadda
musulinci ya baawa uba daman zabawa diyarsa budurwa miji......saidai idan zata nuna
masa iyakarsa ne.......zan aurar da khadeeja kamar yadda kuma musulunci ya
tsara......ba shawara nake nema ba bare a kawomin mabanbantan ra'ayi". Ya fadi da
wani irin yanayi dake nuna babu sassauci ko canzawa a maganarsa.
Wani irin kalar tashin hankali ta dinga ji yana sauko mata. Ba abinda
ke gilmawa a idanunta a sannan sai gata an daura mata igiyar auren HAKEEM. Gata a
qarqashin inuwar bagidajen mutum irin hakeem din,tana karba daga umarninsa,tana
kuma gaza yin komai da haninsa.
Wani abu ya harba cikin kanta,taji kamar an samu allura ne an soka
mata. Taji wani energy a jikinta da yake bata cewa......tayi dukkan me yuwuwa wajen
nunawa sultane batason auren HAKEEM,tayi dukkan abinda zatayi don tabbatarwa da
sultane qudurinta da kuma ra'ayinta,ba tare da jiran shawara ta biyu ba ta miqe.
Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki kai tsaye ta zarce tana takawa
zuwa inda sultane yake zaune. Da mammina da sultane din binta sukayi gaba dayansu
da kallo,ta qarasa,sai ta sulale a hankali tana zubewa a gabansa kaman me neman
gafara. Ta sadda kanta qasa,zuciyarta na tsananin bugawa da yadda taga sultane ya
zube mata dukka idanunsa.
Wasu zafafan hawaye ne suka subuce mata a sanda bata shiryawa zubarsu
ba,kawai sai taji bata da wani sauran jarumtar boyesu ko hanasu zuba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 76
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_________________________
*SHEIK HAISAM*
★★Wani sashe ne na musamman cikin gidan dashi kansa tsarinsa ya burgeshi. Na
musamman din da zai sake tabbatar maka da hakan saboda kalar masu tsaron dake
kowacce qofa da kusurwa da zai taka ya wuce.