Showing 45001 words to 48000 words out of 168506 words

Chapter 16 - luu luu Book1 by Huguma

gyran Brest magungunan sa kiba
da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin
iKon allah πŸ₯°πŸ‘ŒπŸ»
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi
bucking koda kudinki saida Rabonki
_____________________________




*_Addis ababa bole international airport(ADD)_*


Tafiyar awa daya da mintina biyar ta kaisu babban birnin na Ethiopia
wato addis ababa,wanda cikin qasa da minti talatin ya kammala komai suka baro
airport din qarqashin kulawar security din dake bashi tsaro cikin addis ababa din.


Kazanchis layout suka nufa......unguwar da ya mallakin gidan zama na
kasan kenan bayan gidan da hukumar binciken sirri suka bashi. Unguwa ce data hada
manyan mutane da qusoshin gwamnati. Baqi 'yan qasashen waje da kuma manyan
ma'aikatu na alaqa tsakanin qasashe da kuma hukomomi manya na tsaro.

Gida ne dake da wani irin tsari da zai baka sha'awa qwarai,qaramar
villa ce da batayi wani girma na azo a gani ba......amma tana da girman da za'a iya
sanya matan aure hudu a ciki suyi rayuwa cikin walwala da sakewa.

Ganawa da ma'aikatan gidan shine abu na farko da yakanyi a duk sanda
ya dawo.......yau dinma hakan yayi,saidai batayi tsaho ba,kasancewar yana sanya ran
daga yanzu zuwa kowanne lokaci zai iya fita zuwa headquarter dinsu dake cikin
kazanchis din.


*_AGADEZ_*

*NIAMY*


Tsaf ta kammala shirinta cikin wani kebantaccen guri na nusamman da aka
bawa 'yan wasan dake filin gudanar da wasan don shiryawa gabanin fitowarsu. Wata
irin shiga data sake fidda ainihin kyanta,wanda hatta da aisa da Shehnaz zama
sukayi suna kallonta.

Farin skinny trouser daya fidda shape na qugunta da sosai......wata irin
jacket data dora samansa me dogon hannu bayan riga 'yar ciki data saka. Ta daure
wannan dogon gashin nata cif a tsakiyar kanta,saita sake jelar tana lilo. Takalmin
qafarta wani tsadadden boot ne da tayi cinikinsa da Europe ba dolla ba takanas ta
saka aka kawo mata shi. Komai na jikinta fari ne qal,kamar yadda kalar thunder
(dokinta) ya kasance fari tas.......me wani irin cikar zati da ban sha'awa ga duk
mutumin daya kalleshi. Koda bakasan doki ba.......bakasan kuma darajarsa ba idan ka
kalli thunder sai ya baka sha'awa qwarai. Qosashe kuma ingarman dokin data sayeshi
daga United arab Emirates wato dubai da kudade masu nauyin gaske. Kulawa ta
musamman take bawa dukkan dawakanta da kuma me duba lafiyarsu na daban data ajiye a
Niamey da agadez. Akwai me musu regular check up da vaccination don tabbatar da
lafiyarsu,hakanan abinsu na dabanne bayan abincin ana ciyar dasu fresh fruits da
vegetables irinsu apple da carrots da sauran kayan marmari. Hatta da SULTANE yana
sha'awar dokunanta......wani irin qauna ce tsakaninta dasu. A shekarun baya kafin
ta zama busy akan kamfaninta har haka akwai ranaku na musamman da take warewa kawai
don hawa ko zaman kallonsu ko lura da lafiyarsu.

"Amma dai.......ki rufa mana asiri kada kallon tseren doki ya koma kallon
biftu....." Wani murmushi ta saki sanda take dauko wasu safar hannu guda biyu. Sai
data fara zurawa sannan fa daga kyawawan idanunta da kwallin data zizara musu a yay
ya qara musu kyau.

"Jikar muhammad agg nake......diyar muhammad hammud......akhnan.....biftu......don
kawai na na shiga gasar tseren doki sai kuma jikina ya zama me abun banza ga
kowanne kare da doki?......arahata batakai har haka ba" Ta qarasa fada tana zama
saman wata ottoman sofa tana daidaita riding globes dinta cikin hannunta.

Murmushi aisa ta saki,akwai abu guda dake burgeta game da akhnan
din......tana martaba jikinta.......tana tsananin kula da qaunar jikinta,tana bashi
kima da daraja,amma kuma wani abun na daban.....wannan izzar ta akhnan tana
burgeta......wannan izzar ta akhnan tana saka mata shakku.......anya kuwa ba da
gaske bane kuwa?,anya a yadda izzarta da alfaharin kanta yake zata iya auren wani
d'a namiji bare wataran ya ganta gayarta?,bare wataran su hada gado kamar yadda
tasha fada?......anya kuwa akwai wanda zai samu nasarar sauke wannan izzar?,anya
kuwa akwai wani qarfi na wata aba soyayya da zai sauke wannan ALFAHARIN?.....ya
cillata duniyar matsananciyar soyayya da shauqi?. Da wanann tunanin da yabar
murmushi saman fuskarta ya kaita nisan da har akhnan din ta gama qarasawa shiryawa
hankalinta bai kai ba.

"Ma sha Allah" Aisa ta furta can qasan ranta tana duban akhnan din. Wannan skinny
trouser din daya bayyana shape dinta......ta batar da wannan surar tata ta hanyar
dora wata irin riga me kama da alkyabba maras nauyi sam sam,sosai ta baje daga
bayanta ta kuma rage fitar da shape dinta yayi kwata kwata,rigar tana hade da hula
ne wadda zata aza saman Egyptian turban cap din kanta me azabar kyau da aka qawata
da adon gold stones. Daga gaban rigar me kaman alkyabba akwai wata 'yar lanqwasa da
aka yiwa ado da wani tattausan gashi tun daga fuskar hular dake saman kanta,ya
sauko saman qirjinta ya rufe tudunsu daga sama,duk da hakan bai boye shape dinta
ba....sannan ta dauki helmet dinta ta riqe a hannunta.

(08187255862 lu'u lu'u paying)

Fadin irin kyan da tayi bata baki ne.......abu daya aisa ta sake
tabbatarwa shine,da gaske akhnan din ta dabance......da gaske kuma tasha banbam da
mata masu yawan gaske.

Wani irin cika gurin yayi wanda bai taba yin irinsa ba,su kansu masu
saida ticket na shiga gurin.....jami'an tsaro da kuma masu kula da kai kawon jama'a
a gurin yawan ya rikitasu. Mafi yawan mutanen da sukazo kallon wasan sunzo ne don
PRINCESSES AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD.......don fiye da rabinsu basu santa ba sani na
ido da ido. Sunanta ba boyayye bane cikin nijer dama agazed gaba daya......amma
sanin anihin fuskarta abune da ba kowa ne zaice maka ga kamanninta ba.

Kusan ita daya ta rage bata iso gurin ba cikin jerin 'yan wasan dake
wajen......farin dokin qwaya daya dake tsaye ba maishi a kansa shima ya zama abu na
daban daya tsonewa 'yan kallo ido. Ko cikin abokan wasan nata babu wanda dokin bai
burgeba,duk da gabadayansu suna saman wasu irin qosassun dawakai da suka sha bamban
da wadanda aka saba gani.



*ADDIS ABABA*
_national intelligence and security service(NISS)_


*_Washegari_*


Wani irin sabo da horo ya yiwa ruhinsa,tun daga sanda ilimi da hankali
ya gama wadatarsa kawo yanzu. Duk daren duniya......duk inda qarfe uku na dare yayi
muddin akwai cikakkiyar lafiya a tare dashi to yabar makwancinsa izuwa saman abun
sallarsa.......a kowanne dare a kowanne guri,hakanan a kowanne yanayi. Daga sanda
ya karanta ya kuma fahimci ma'anar ayar nan ta cikin suratus sajdah aya ta sha
bakwai da Allah madaukakin sarki yake cewa
(Jukkunansu na nisanta da makwancinsu suna kiran ubangijinsu suna masu tsoron
azabarsa.....suna kuma masu kwadayin rahamarsa......sannan suna ciyarwa daga abinda
muka azurtasu). Tun daga wancan ranar zai wahala wani dare ya kubce masa ba tare da
ya rayashi ba. Abinda yayi masa tasiri sosai cikin rayuwarsa......ba wata buqata da
zai dorata saman abun sallar cikin irin wadannan dararen ba tare da yaga cikarta
ba. Wani irin haske ne ke mamaye ruhi dama rayuwarsa gaba daya. Da gaske sallar
dare na daga darajar bawa,ta sanya wani haske na musamman a ruhi zuciya dama fuskar
me yinta,ga kuma tarin nishadi da walwala da zaka wayi gari cikinsa.

Kiran sallar farko da wasu mintuna yabar saman abun sallar,ya koma
bandaki ya sake sabunta alwalarsa don samun qarin haske akan haske(alwala haske
ce......kuma itace ranar qiyama zata dinga zame mana tamkar fitila,itace kuma zata
rarrabe tsakaninmu da kafirai,so yana da kyau ki zama me yawaita yin alwala ko zama
da ita.....tana bada kariya daga dukkan sharrin me sharri).

A nutse yasa dan qaramin lallausan towel dinsa dake fidda wani
sirrintaccen qamshi daya samo asali daga turarukansa da yake amfani dasu ya goge
lemar jikinsa,sannan yabi jikin nasa da wani sassanyan turarensa da mafi akasari
shi yaf amfani dashi idan zai fita sallar asuba.
(Turare kansa sunnah ce....sunnah me qarfi,cikin abinda aka sanyawa manzon Allah S
A W sonsu akwai turare).

Qarshen layinsu masallacin yake,kuma kusan shike jagorantar sallar
asuba din a yawancin lokuta,duk da wasu lokutan yanayin aiki ma baya barinsa kwana
a gidan bare ga samu yayi musu limanci.

Cikin mintuna qalilan daddadar muryar nan tasa dake dauke da amon sautin
karatu mafi daraja ya karade area din tasu,ya sake sanya nutsuwa sosai cikin
zukatan duk wata halitta daka iya jiyo sautin nasa.

Sanda ya kammala jagorantar sallar yaso ya zauna a gurin kaman yadda
yakeyi wasu lokutan ya jira fitowar hantsi sannan yayi salatudduha(wata garabasa ce
me girma ayin haka,gwaggwaban lada ne ga bawa me yawan gaske,ladan hajji da umra
cikakkiyar lada cikakkiyar lada cikakkiyar lada haka annabi S A W ya maimaita har
sau uku,idan bakije hajji ko umra ba.....ga dama ta samu a sauqaqe na samun
ladaddakinsu daga gida)".

Dole ya koma gida,don yana buqatar fita da wuri.....akwai abubuwan da
yakeson dubawa kuma kafin ya isa headquarter dinsu.

A nutse yake takawa zuwa gidan.......qasa qasa yana motsa harshensa
cikin tasbihi ga ubangijin halitta. Sassanyar iskar asubar dake busawa tana sake
dauke duk wani nauyi dake qirjinsa,tana saukar da wani nutsuwa da nishadi sosai a
ransa.

"Tsarki ya tabbata ga ubangiji" Ya fada qasan ransa,yana tuna yadda a alqur'ani
ubangiji ke cewa a aya ta sha takwas cikin suratut takwiir

"Da asuba idan tayi numfashi(ma'anar wannan sassanyar iskar me dadi dake kadawa
tsakanin sallar asuba,ki gwada shaqarta,tana saukarwa da zuciya nishadi sosai)".

"Ya akayi masu tsaronmu sukayi ganganci bar mana zakin qasarmu haka sasakai yana
takawa zuwa gida haka gayansa?" Ya tsinci dattijuwar muryar daga bayansa.

Tun bai juya ba qaramin murmushin nan nasa dake alamta nutsuwar dake
jikinsa ya subuce masa. Koda bai juya ba yasan ba kowa bane sai alhaji muntassir
amari.

Dattijon da gidansa ke maqotaka da nasa ko nace yake kallon nasa. Dan
asalin yankinsu garinsu na jimma,wannan hadakar garin ita ta kawo shaquwa da alaqa
me qarfi tsakaninsa da alhja muntassir amari. Alhj muntassir tsohon ambassador din
Ethiopia ne a Malaysia,wanda ya dauki shekaru masu yawa yana yiwa qasarshi
hidima,bayan shekarunsa na retired sunyi ya dawo da zama cikin addis ababa da
iyalinsa gaba daya.

Yana da matar aure guda daya da yara biyar,uku mata biyu maza,ya aurar
da yaransa uku,mata biyu namiji daya,yanzun 'ya'ya uku ne suka rage masa a gabansa.
Menelik da dan uwanta yonas su kadai suka rage masa. Wani irin girmama haisam yake
saboda abubuwa biyu. Na farko kasancewarsa d'a ga sarkinsu da suke matuqar so da
bashi girma.......na biyu nutsuwa da tarin ilimin da haisam ke dashi.

A aikace haisam din yaga alamu da abubuwa da yawa suka nuna yadda
alhaji muntassir amari yakeson hada alaqa tsakanin haisam din da
menelik.......menelik din da zuciyarta ta jima da narkewa haisam din......ta dade
kuma tana addu'ar Allah ya kawo wani sanadi da alaqa zata qullu tsakaninta da
haisam. Ta sani......ba wata hanya alaqa ko sanadin da hakan zata kasance,haisam
din yayi mata tarin nisa......ya mata tazara me yawan gaske da take jin zata iya
samun isa gareshi.
Sam sam bashi cikin tsarinsa shiga shirgin mata,matan ma wadanda suke ba
muharramansa ba irin menelik din. Yana da wani tarin kwarjini na musamman.......ya
iya kuma iya tsare gida ta yadda zakayi tsammanin bai taba wani abu me kama da
dariya ba.

A wani dare da abbii dinta ya gayyato haisam din don yaci abincin
dare dasu a mazauninsa na babban mutum na musamman a wajen mahaifinta. A ranar ta
dauka tana da qwarin gwiwar iya tunkarar haisam ko yin wani motsi da zai bashi
haske a kanta.......don ta wuni tana rehearsal na yadda zata shigo da yadda zata
gaidashi,sai gashi a kallo guda daya tak da tayi masa ya rusa komai......ya ware
wannan tsarin nata. Duk kuwa da cewa idanunsa da hankalinsa suna kan mahaifinta
suna wata magana data shafesu amma sai yayi bala'in cika mata idanu harta nema
daburcewa,ba kuma wai don ya daga idanu ya kalleta ko sau daya ba,hasalima idonsa
nakan yonas dake gefenta yana amsa gaisuwarsu,duk da ya amsa musu cikin nuna
mutuntawa da karramawa.

Harta gama serving nasu komai ta juya zuwa ciki bai sake daga kanshi ko
kallon sashen da take ba,don sosai ya bawa abbii dinta hankalinsa.

Hankalinta ya tashi ya kuma kwanta duk a ranar,saboda bayan tafiyarsu
taji abbii dinta yana gayawa ummiinta ma'anar gayyato haisam gidan.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπŸ‘‘*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*

πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 24
____________________________

https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500
dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce πŸ₯°πŸ‘πŸΌ
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da
kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi
https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba
da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin
iKon allah πŸ₯°πŸ‘ŒπŸ»
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi
bucking koda kudinki saida Rabonki
___________________________



"Menelik nakewa sha'awarsa........banason tayi asara kota rasa miji irin muhammad
haisam din......duk da ina tsoron kada mutane suyimin mummunar fassara,su dauka
saboda sarauta mulki ko tarin arziqinsu nakewa". Daga ranar sai hankalinta yadan
kwanta,ta samu yaqinin a ranta,ta kuma samu tabbas tunda ga abbinta nan zai tayata
wannan yaqin,yaqin da har yau ba wani ci gaba a cikinsa,saima sake nisa da haisam
din kewa idanunta,don koda ganin gilmawar motocinsa ta samu gani a ranar daga
corridor din upstairs dinsu,to lallai ranar ta shiga cikin jerin ranakun sa'arta.

"To ya za'ayi?,barka da asuba" Haisam ya fadi yana bawa alhaji muntassir amari
hannu sunayin musabaha. Tare suka jero bayan sun gama gaisawa suna dan tattaunawa
kafin alhaji muntassir ya jefo maganar dake ransa.

"Har yanzun dai kaqi sake amsa gayyatar cin abincin dare tare damu Muhammad?" Dan
murmusawa yayi,wanda wannan karon kawai iya labbansa ne suka motsa. Yana jin nauyin
yadda alhaji muntassir ke yawaita masa tayin zuwa cin abincin da a gurinsa baida
ma'ana,ya rasa yadda zai masa bayani cikin girmamawa yadda zai gane.

Ba zuwa cin abinci ko zuwa gidansa bane matsalar..... Matsalar tana ga
yadda wancan karon ya bashi dama ya shiga har ainihin parlor din iyalinsa. A nashi
tsarin bayan yayi aure........a duniya baiga wata qwaqwarar hujja da zaa bashi ba
da zai sanya ya bawa wani baqo damar keta koda qofar farko ta gidansa wato gate
dinsa ba har kuma ya kutsa zuwa ciki. Ko bayan haka ma shi abun bai burgeshi
sam,uwa uba kuma ba wani sassauci ko hutu daya samu daga hukumarsu da zai samu
lokacin zuwa ziyarar cin abinci,don haka ya hanke bashi uzurin qarshe kawai

"Rashin lokaci ne kawai......ina fata kuma zaayi mana afuwa?". Murmushi alhaji
muntassir ya saki,y fahimci bai iya wani boye boye ba,kai tsaye yakeyin maganarsa
da dukka gaskiyarsa a yawancin lokuta.

"Karka damu....qanwarka ke yawan tambaya dama,tana ganin kamar mun wareka,baka kusa
da gida". Sai ya bashi hannu suka sake gaisawa ya taka a hankali zuwa qofarsa.

A parlor dinsa yayi zamansa,zaman da kaman jira akeyi saqo ya shigo
wayarsa,abinda kuma ya janye masa hankali kenan


Tunda ya samu saqo daga abba muhammad dawuud da wasu taqaitattun kalmomin
da su kadai suke gane ma'anarsu ya fahimci yanason ya rigashi isa office ne......na
biyu yau ya tsara suyi zaman da zasu tattauna yadda tafiyarshi zata
kasance......don haka yau din yana son yayi monitoring shige da ficen hukumar gaba
daya bisa tsari na sirri yadda suka saba. A cikin ma'aikatansu waye ya shigo?,waye
ya fita?,qarfe nawa ya shigo kuma qarfe nawa ya fita?.

Tafiya ce me tarin muhimmanci ga hukumar tasu,saboda kasancewarta wani
tsohon case da aka dauki shekaru ba tare da gano hasken komai ba a kai sai yanzu.

Yau hatta da omari raba tafiya sukayi. Ya gama komai nasa akan lokaci
ba tare da sanin dukka hadimansa bama,don ko breakfast bai tsaya beruk shugaba
cooks dinsa ya kammala shiryawa ba ya fice.

Shi daya ya zai motar da yake jin fita yau a cikinta ya fice abinsa.
Sai yake jinsa yau sakayau.......ba guards ba hadimai.......daga shi sai shi sai
kuma qira'ar qur'anin daya kunna a motar yana bi sannu a hankali yana tuqi cikin
cikakkiyar nutsuwa da matsakaicin gudu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login