Showing 93001 words to 96000 words out of 168506 words
nanniee(barka da yamma nannie)".
" Bonsoir,comment allez-vous?(barka da yamma,kina lafiya?)"
"Alhmdlh" Ta fadi tana hadiye wani abu a wuyanta.
"Munyi magana da bappinki.....ya gayamin kina da baqo yau ma kaman yadda aka saba
ko?" Tayi maganar da sautin da shi kadai ya fadarwa da akhnan gaba.
Shuru ta yiwa Nannie din bata amsa mata ba,hakan kuma bai hana Nannie
magana ba.
"Biftu....."
"Na'am Nannie" Ta amsata tana qoqarin tattala qwarin gwiwarta.
"Yana da kyau ki dakatar da wannan wasan kwaikwayon haka nan.....lokaci yayi,muna
da buqatar kawar daku daga gabanmu". Lumshe idanunta tayi sosai kaman ba zata bude
ba,wani bacin rai ne yake taso mata.
"Bana buqatar haka Nannie silvous plaît.......bana buqatar wannan hadakar.....zan
iya rayuwata ni kadai na,hadin baya burgeni,rayuwar bata burgeni itama" Ta fada a
sanyaye duk da akwai zafi me nauyi cikin kalamanta.
"Biftu!" Ta kirata tana tsaurara kiran wannan karan.
"Aure dole ne wuyan kowacce mace.....komai qasaitarki baki cika ba saida
aure.......kina da zabi guda biyu.....wannan sune adalci na qarshe da zamu iyayi
miki" Nannie ta fadi cikin nata zafin da akhnan din ta jima bata jita cikinsa ba.
Wuta tsaf akhnan din ta dauke kafin ta janye jikinta daga kusa da
wayar,sannan ta sulale ta zauna gefan gadon tana qoqarin gaya musu su fita a dakin
su bata guri.
Dukkaninsu sun fahimta,don hatta da buhaina da wayar ke a hannunta,wayar
da tana iya jiyo Nannie na maimaita fadin.
"Hello......hello" Haka ta fice da ita a hannunta. Bata da ikon katse kiran
Nannie,don aikata hakan babban laifi ne,dole ta ajiye wayar a gefe har Nannie din
ta gaji ta gimtse kiran da kanta.
Ta gama fahimta ta kuma gama gane komai,wannan karon al'amarin yafi kama
da taron dangi akayi mata,momma......Nannie uwa uba sultane dinma.
Zata tsammaci hakan daga momma,harma sama da hakan,amma daga sultane
kuma ko Nannie dukka baqon abu ne a wajenta.
Wai wanne dalili ne zai sanya ba zata tsani morsa safiyya ba?.......me
yasa ba zataji bata qaunarta ba?. Tana da cikkakken imani da yaqinin komai ita ta
assasashi,komai kuma ita ta shiryashi,in fact ma jikinta yana bata ita ta jawo
komai ta hadashi daidai da muradinta da cikar burinta.
Tsam ta miqe tana zare ribbon din kanta,ta kuma daure gashinta
tsakiyar kanta da wani irin zafi,jelar ta sauka gadon bayanta tana lilo. Banda
umarnin daga sultane ya fito......bata tunanin yau duk duniya akwai wani wanda ya
isa ya sanyata ta fuskanci wannan baqon. Umarnin sultane ne......zata cikashi,amma
kuma ta hanyar da takeso,ta kuma hanyar da taga dama itama.
*FALAAK*
Sallamar morsa safiyya ya sanyata daga kanta daga duba shafin littafin
dake hannunta,wanda kusan ta zauna ne kawai tana duba littafin saboda ragewa kanta
lokaci da kuma dogon zama,amma sam ba wai don tana jin dadin karatun bane.
"Ya dai?" Morsa ta tambayeta tana zama daga gefe hadi da qoqarin gyara lullubin
tattausan mayafin jikinta.
Ajiyar zuciya falaak din ta sauke tana rufe littafin.
"Gaba daya momma ji nake kaman karatun ya fita a kaina,oustaz Ousmane ya iya karatu
morsa,gani nake kaman ba zamu samu wanda ya kaishi ba". Murmushi kadan momma ta
saki tana daukan remote don sauya channel din dake aiki zuwa TRT africa.
"Ba'a gaggawar yanke hukunci,kuma kowanne dan adam da irin baiwarsa,sani ne bamuyi
ba". Kai ta gyada a hankali falaak din,momma taci gaba da cewa.
"Ya iso tun tuni,suna masallaci da sultane,bayan sallar la'asar din zai shigo,kuma
naji ma an idar da sallar.......ki yiwa baraka magana ta hada miki kansu Aafreen ku
wuce gurin daukan karatun,kar a fara saba dokarsa tun a ranar farko". Numfashi
falaak taja tana tabe baki. Wannan malamin me tarin doka da tsarin tsiya zataso ta
ganshi,zataso ta gani ta kuma san irin ilimin da yake dashi haka da har ya zarta
oustaz Ousmane yake sanya dokokin da ko shi bai taba sanya musu su haka ba.
*SULTANE*
Yadda haisam ya saba zama yayi musabaha da mutanen dake bayansa bayan
kammala salla a masallacin juma'a na jimma,haka ma yanzun yayi. Abun da ya baiwa
mutane da dama.mamaki aka shiga kallon kallo ganin yadda ya baiwa sultane hannu
kansa tsaye. Irin wannan kwarjinin da yake musu kaman sam shi bai masa ba?.
Qasan ran sultane yake murmushi,wani irin nutsuwa na shigarsa tattare
da haisam din. A cikin ayyukansa da dukka motsinsa ya fahimci yadda ilimin addini
ya wadaceshi qwarai da gaske.
"Ayi masa tattaki zuwa,sannan a sake inganta gurin karatunsu idan yanayin da aka
tanadarwa gurin bai masa ba" Umarnin da sultane ya bayar kenan. Cikin girmamawa
haisam ya rusuna,da hausarsa da bata bada miqaqqen sauti da amo irin na cikakken
bahaushe ba yace.
"Godiya nake".
Duk wani taku nasa yana tafiya ne da ilimi ankarewa da kuma karantar
kowanne motsi na gidan. Kowanne taku da zaiyi yana yinsa ne cikin sanyawa abubuwa
da yawa alama.......haddace yanayin abubuwa da kuma gilmawar kowanne mutum da
motsin iskar dake kaiwa tana kawowa.
Kafin su isa gurin ya gama rarrabe tsarin sassannin da ainihin
kebantacciyar daular da iyalin sultane ke ciki,adadin sassan ya kuma fahimci sassan
matan nasa......banbancin hadimai na kowanne sashe,duk da bai gama tabbatar da
hadiman sassan mammina da na momma ba.
Basu gama shiga gurin ba,amma tun daga farko yaji gurin yayi masa,tun
daga farkon gurin kuma yasan gurin kebantaccen guri ne na musamman koda kuwa a
cikin gidan.
Kai tsaye zaka iya kiransa da gandun daji,saboda yadda aka qawata gurin
da nau'ikan shuke shuke 'yan qasar France. Akwai wata qirqirarriyar qorama me wasu
fararen duwatsu da kifaye masu nau'ika daban daban dake kai.kawo a ciki. Ido ya
lumshe ya shaqi iskar gurin a sirrance. Saita tuna masa da nasa sassan daya ajiye
musamman a jimma,wanda yake da kwatankwacin wanna tsarin gaba dayansa.
A duk sanda yakeson duba wani babban littafi,yin research akan wata
mas'ala,ko kuma yin research game da wani security issue daya shafi security
intelligence yafi zama a nan,zai kammala komai a nutse yana kewaye da hadimai,don a
irin wannan lokacin nanay kawai yake bawa izinin ganinsa,sai kuma mooti,wanda yawa
yawan lokuta yafi zuwa ya sameshi a gurin hutawarsa dake cikin gidan,ko cikin
fadarsa idan buqatar ganin ta canne.
Kanta na sunkuye tana ta qoqarin sake duba karatuttukan baya,yayin da
har yanzu zuciyarta keta kai kawo,ta kuma kasa jin wani cikakken aminci da malamin.
Alamun takun da taji shi ya sakata daga kanta tana tsammanin ko su
aeera ne suka tashi daga gurin da zasu dinga nasu karatun da yake gefanta kadan.
Karon farko idanunta ya sauka a kansu. Mutum uku ne......da guda
biyu kawai ta sani a cikinsu. Maher daya kasance kaman dalibin oustaz
Ousmane,sannan kuma jifa jifa takan ganshi tsakanin sassansu duk da batasan me yake
zuwa yi ba. Na biyun bala ne......daya daga cikin manyan hadimansu,sai na
ukun......
Mutum na ukun daya banbanta da kowa a cikinsu,mutum na ukun da ta
ganshi ya fita daban,tamkar gold din da aka jefa tsakiyar gama garin qarafa.
Cikin nutsuwa yake maganar da bata iya jin me yake fada,amma dai ya
janye rawaninsa zuwa qasar habarsa,abinda ya bawa kyawawan labbansa masu sulbi
damar fitowa,suna kuma juyawa a hankali.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ta furta da sauri da qaramin sauti tana janye
idanunta gefe daya saboda wani mummunar faduwa da gabanta yayi zuciyarta na qara
wani irin mahaukacin bugu da bata taba jin haka a tattare da ita ba sai yanzu.
Cikin jikinta takejin qarin kusantowarsu da gurin,yayin da bugun
zuciyarta har yanzu yaqi daidaituwa,wasi wasi kuma ya cika mata zuciya tanason
rarrabe waye malamin a cikinsu?.
Bala dai ta sanshi,saboda haka ba wata magana a kanshi,Maher kam bata
tunanun oustaz Ousmane zai kawo Maher a mazaunin malaminsu bayan dalibi ne shi
kansa a wajensa. Sai kuma na ukun?.......
Sam bai mata kama da malamin da zai shiga gidan sarauta da zummar
koyarwa ba. Ta kowacce fuska kamanni dama yanayinsa. Wani irin kwantaccen kwarjini
take gani yana haska kowanni motsi nasa,irin kwarjinin da a fuskar sultane kawai
take ganinsa.
Eh akwai kamala me yawa da wata irin nutsuwa shimfide saman
fuskarsa......yanayin shigarsa ya sake tabbatar mata da yawan ilimin daya ratsa
halittarsa gaba daya,to amma......"
"Sheik haisam ya iso ranki ya dade....." Muryar bala daya tsugunna saman qafafunta
ta dauko hankalinta zuwa wajen.
"SHEIK HAISAM" Ta maimaita sunan tana motsa labbanta,tana kuma jin wani irin sanyi
da taushi a iya sunan kawai.
"Eh gashi can Allah ya taimakeki......sultane yace a gaya miki,a bashi dukkan
girmamawar da shi zaa bashi,a yanzun sheik malaminsa ne". Kai take jinjinawa a
hankali tana jin kanta kaman ya mata nauyi,bugun da zuciyarta kuma keyi yana nan
bai sauya ba. Da iya saqon sultane kadai tana iya fahimtar muhimmancin da ya bawa
abu
"Na barku lafiya" Bala ya fada yana tashi gami da juyawa suna barin gurin shida
Maher.
Shurun da taji sai muryar Aafreen kadan take tashi ya sanyata waiwayawa
kaman me ciwon wuya.
Fuskarsa shine abu na farko data soma sauke idanunta a kai. Wasu
irin zagayayyun idanuwa masu girman da suka bayyana kansu tsakanin fuskarsa data
zama circle cikin rawaninsa. Yana zaune sosai saman babban kilishin dake shimfide a
wajen ba tare daya damu ya zauna kan kujerun da aka ajjiye masa ba a wajen masu
tsananin taushi.
Aeera ce zaune a gabansa,ta bude littafinta na nuraniyya,ya dora
yatsansa akai itama haka,da alama karanto masa takeyi,sai Aafreen dake zaune daga
bayan aaera kadan,ta tallafe habarta da hannunta tana kallonsu fuskarta yalwace da
fara'a,da alama akwai abinda yayi mata dadi.
Sake janye idanunta tayi tana kiran sunan Allah. Sai take jinta gaba
daya kamar a rude take,kaman ta fita daga nutsuwarta ta dazu.
Canki canki takeyi,ita zata kai kanta?,ko kuma idan ya gama da yaran
zai nemeta?.
To amma tunda suka shigo gurin bataga wani alama da zai nuna yasan da
wanzuwarta a gurin ba,baiyi wani motsi ko yaya da zai alamta mata yasan tana gurin
ba.
Bata da wani karsashi ko qwarin gwiwa,don haka ta zabi ci gaba da zama
a gurin,ta sunkuyar da kanta kan littafin,duk da bata gane komai,bata kuma fahimtar
komai,kacokam hankalinta yana wajensu da bata iya jin tasa muryar,sai muryar yaran
kawai,su dinma yau cikin nutsuwa suke magana.
Jifa jifa tana satar kallo su,saidai ko sau daya ba wani alama daya
nuna ansan da zamanta a wajen. Ta sauke ajiyar zuciya daidai sanda taji muryar
aeera saman kanta.
"Kizo inji sheikh haisaaam". Yadda yarinyar ta furta sunan da wani irin tone sai
taji sunan ya sakeyi mata dadi,ya kuma qayatar da ita dari bisa dari,qasan
zuciyarta da dan mamakinsa na yadda ya aika tazo din ta tattare litattafanta ta
miqe tana sake satar kallonsa. Tanason ta banbance yaushe ya kalleta har ya fahimci
tana gurin ma?,saidai kuma har ta isa gurin ta tube takalmanta ta zauna a nutse
bata gane komai ba.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ya furta Kansa yana saman littafin Aafreen da
oustaz Ousmane yake basu aiki lokaci lokaci.
Qara tsanantuwa bugun zuciyarta yayi,har ta gaza yin qasa da kanta ta
daga kanta tana dubansa kai tsaye. Abubuwa biyu suka rikitata,na farko wani baiwa
dake cikin sautinsa da muryarsa da bata taba jin irinsa ba,na biyu kuma tasan yana
son gaya mata batayi sallama ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 46
__________________________
HALY JASHERU VENTURES.
munada tsuntsaye na kasashen waje masu kyau da daukar hankali kmn haka.
TATTABARU
French modain(Argentina)
Indian faintail (3in1)
indigo,opal,Andalu,Lahore,busa,Bukhara, indomie,Jacobin dasauransu.
KAJI.
Brahma,silkie,silver lace,coshine,dawisu, parrot (aku)dasauransu.
,
Munada kayan Islamic center.habbatus saudah,hulba,zaitun,qusdul Hindi,minannas,Rose
water dasauransu,dangin garinsu ,mansu yayansu ,ganyensu. munada original Zuma,yar
chad da mombila.
Munada kayan gwanjo masu kyau daga jariri zuwa babba,
Overall,Rumpers, bodysuit, sweaters,wanduna, tracksuit dasauransu,munada kaya masu
kyau na bacchi na gwanjo.
Munada Ethiopian magic hair oil 🪔 Wanda yake Kara gashi,yayi tsaho laushi,yayi Baki
drct daga Ethiopian muke kaisa ko Ina afadiin duniya.
Don Neman Karin bayani number waya
07046665338.
___________________________
Ba dabi'arta bace rashin yin sallama idan ta riski guri,sosai aunt
hairaan ta dabi'antar dasu da wannan dabi'ar. Su din rainon hairaan ne,hairan kuma
rainon morsa safiyya ne,don haka sun samu ladabi da kuma horaswa wajen qanqan da
kai me yawan gaske.
Miqewa tayi,tayi taku uku ta sake dawowa sannan tayi sallamar.
"Assalamu alaikum warahmatullah". A nutse ya daga idanunsa,yayi mata kallo daya
sannan ya maida kansa yana amsa mata,kallo guda dayan daya tilasta mata sulalewa ta
zauna saboda rauni da jikinta taji yayi mata. Ya danji mamaki kadan qasan ransa,bai
tsammaci haka da sauri ba......amma sai ya tuna da wasu daga bayanan Maher.
Zata iya cewa bata taba ganin kyawawan idanu irin nasa ba,wasu irin
idanuwa masu wani irin kwarjini a cikinsu.
"Bata litattafan da kukeyi mu gani" Ya fada yana nuna aeera. Duka ta miqawa aeera
litattafan,ta kawo gabansa ta ajjiye,ya saka hannunsa a nutse ya daukesu ya soma
dubawa bangon daya bayan daya.
Sanda ya kammala sai ya gyara zamansa. Tambayoyi ya fara jefa mata,a
nutse yake mata tambayar,bai kuma tsaurara da yawa ba,amma duk da haka a rikice
take jinta,abinda ya sanya wasu tambayoyin ta amsasu da qyar,wasu kuma ta kasa amsa
su din saboda da gaske bata sansu ba.
Shuru yayi bayan ya gama tambayoyin,yana dan danna wayarsa a
hankali,yana ganin kimar macen me tarin ilimi sosai......hakan kuma yana
burgeshi,wannan ne ya zaba sila kuma dalilin da bai bar su rumaisa sarauta ta
sakasu sun zama daban da mutane a duniyar ilimin addini ba. Ya sake qarfafa hakan
akan noory ita dake tasowa yanzun. Duk da yayi qoqari......amma akwai tambayoyin da
yake ganin ya kamata ta amsa su compulsory. Sam ba wadannan litattafan ya kamata ta
fara dasu ba,har cikin ransa yaji ya aminta zasuyi karatu na gaske da yaran,bawai
karatun da bincike ne ya shigo dashi ba. Yadan dauki sakanni kafin ya motsa
labbansa.
"Wadannan litattafan za'a canzasu da wasu"
"To" Ta fada tana gyada kanta. Haka kawai tun daga gabar farko takejin wani sauyi a
tattare da ita.
"Hizb nawa kike dashi a qur'ani?" Ya sake tambayarta yana ajiye wayarsa a gefe a
gefe hadi da karbar aikin gwajin daya bawa Aafreen ta kuma kammala.
"Ashirin da biyar" Ta samu kanta da amsawa haka kawai tana jin nauyi. Bai sake cewa
komai ba yaci gaba da duba aikin Aafreen,yana mata bayani a nutse a guraren da tayi
kusakurai.
*_AKHNAN_*
Tanajin ne kaman bata da wani cikakken qwari a jikinta,tana jin kamar
iska ce ke sarrafata ba qafafunta ba. Ita kanta iskar kaman tasan a yanayin da
take,kamar tasan me takeji taci gaba da kadawa a hankali tana watsa sassanyan
qamshin turaren jikinta zuwa kowanne sassa na gurin.
Buhaina da birra na daga bayanta suna kula da inda take dagawa da sauke
qafarta. Daga bayansu kuma yalwa ce,tana biye dasu ne bisa umarnin mammina,ta
turowa akhnan ita ne kawai,ita ma bata ce komai ba tunda tasan wace yalwa?,wanne
matsayi take dashi a gurin mammina. Tasa a ranta mammina tayi hakanne kawai don ta
sake bata tsaro kulawa da kuma damar sakewa.
A kowacce hanya da zata sadata da inda ta saba ganin baqin
nata.......masu tsaro ne data tabbatar ba na masarautar agadez bane,sunfi kama da
masu tsaron lafiyar 'yan siyasa ko kuma masu kudin da suka ci suka tayar da kansu.
Dukkaninsu cikin baqaqen suit suke da baqin gilashi da suka manne
fuskokinsu dashi. Wasu daga cikinsu akwai bindiga rataye a qugunsu.
Ba iya gurin ba kawai,ta fahimci masarautar ma gaba daya kamar an sake
qara tsaronta sosai.
Qaramin tsaki taja,ba wani abu guda daya burgeta tun daga nan. Ba
jama'ar da suke debowa suzo dasu ba......har yanzu bata tunanin akwai wanda zai
taba fahimtarta,akwai wanda zai iya karanta mind dinta ya fahimci komai.
Lallausan gurin ma'abocin shuke shuke da akayi linking nasa da sabuwar
RAUDHA inda zai zamana gurin zaman karatun su falaak kamar yadda morsa safiyya ta
bashi suna. Daga kowanne taku irin wadancan mutanen ne data gani daga hanya suna
qame. Kusan dukkaninsu sama suka kalla ballantana kayi tunanin hankalinsu yana
kanka.
Daga can nesa kadan take