Showing 90001 words to 93000 words out of 168506 words
sauke amanar
adalin sarkinsu mooti abba jifar.
"Of eeggannoo godhaa....hin irra deebi'iin(ka kula....kada ka sake maimata hakan)"
Ya furta da yaren oromo yana dauke brown eyes dinsa da hasken rana ya sake maidasu
wani launi me fusgar hankali.
"Am dhiifama...Dhiifama naaf godhaa(kayi haquri,ka gafarceni)" Ya furta yana ja
baya.
Abdii ke binsa da kallon mamaki,yanason magana amma kuma yadda sukayi
da beeno ya sanyashi sawa bakinsa sakata. Wacce rayuwa *PRINSII SHEIK MUHAMMAD
HAISAM ABBA JIFAR* ke shirin yi a agadez?. Rayuwa ce irin ta kowanne mutum me
matsayi daidai dana dan uwansa......ya manta waye shi wai a qasar jimma da Ethiopia
gaba daya?.
Har yanzu da suke dab da SULTANE PALACE yana jin wani fargaba. Kada
dai yaje yace zaiyi rayuwa irin ta qasqantattun mutane?. Idan hakan ya kasance anya
zai iya jurar gani kuwa?,zai iya cin amanar nanay da sultane ba tare da ya gaya
musu ba?.
"Ku koma......zamu shiga ne da iya Maher" Ya bada umarnin na kai tsaye,wanda a take
dukkansu sukaja baya,banda abdii da yayi tsaye cak a wajen.
"Maaloo....(please)......." Abdii ya fadi yana duban bayan haisam da sukaci gaba da
takawa shi da maher zuwa babban katafaren qofar gidan.
"Andii!" Yadan kira sunanshi a kausashe ba tare daya waiwayoshi ba.
Duk yadda abdii keson ya bisa bazai bar shi ya soma taka gidan yanzu
ba,zai iya wargaza komai,don ba lallai yaga an masa ba ya iya dauke kanshi kaman ba
kowa ba. Koda zai fara shiga da abdii ba yanzu ba,sai yayi masa kyakkyawan training
da bazai sauka daga qa'ida ba.
Daya bayan daya suke wuce sassanni da shinge shinge na gidan,har zuwa
sanda suka fara shiga hurumin jinin masarautar kadai da na kusa dasu da kuma
wadanda aka yarjewa.
Babbar qofa ta qarshe daya daga cikin hadiman morsa safiyya ya
qaraso,a bayanshi mutum uku ne da duka marabci haisam din.
"Zamu fara yin sallah tukunna" Ya amsa musu yana duban agogon hannunsa.
"Babu laifi.....me martaba yana buqatar ganawa dakai dama kafin soma zaman
karatun.....shi dinma yana a masallacin". Kai ya jinjina kawai,ya kuma nemi su masa
jagora zuwa cikin masallacin.
Akwai ragowar lokaci,don haka ba cika sosai a masallacin,uwa uba kuma
me martaba da yake ciki yana ganawa da wasu baqin. Ganinsu tare da hadiman morsa
safiyya ya sanya basu samu wani wahala ba,dakarun dake tsare lafiyar sultane din
cikin shigar kayan sulke suka dinga janye manyan gororin hannunsa da mashi suna
basu hanyar wucewa,daga nan har zuwa ainihin cikin masallacin.
"Iyakacinmu nan.....amma kai kana iya shiga,lokacin shigarmu baiyi ba yanzu" Suka
fada suna dakatawa. Idanunshi kawai ya dauke a kansu,sannna ya juya a nutse da
zummar zare half shoe din qafarsa. Da hanzari ya murxawa Maher yatsuntsa guda
biyu,abinda ya sanya Maher din saurin tashi daga duqawar da yayi ya zummar zare
masa takalmin
(08187255862 lu'u lu'u paying)
"Hin dagatinaa" Ya masa magana da yaren oromo qasa qasa,ta yadda yayi imanin babu
me fahimta koda yaji,sai ya tsaya qyam yana daidaita nutsuwarsa,kafin su taka a
tare suna shigewa masallacin.
Wani irin katafaren masallaci ne me wani irin girma da kuma daukan
hankali. Tun gabanin su shiga cikin masallacin haisam din ya gama karantar yanayin
gininsa,gini ne da yake nuna zallar qwarinsa da kuma hikima sosai gurin ginashi.
Duk da yaune karon farko da yayi ido da ido da masallacin me tsohon
tarihi,amma ya jima yana haduwa da rubuce rubuce a kansa. Abinda yafi bashi mamaki
shine maganar bawa Allahn da ya zama jagoran ginin masallacin wato mallam zakariyya
daya bada tabbacin duk wanda yaga faduwar ginin masallacin,to ba shakka zaiga
tashin qiyama.
Ba wani abun mamaki bane gane me sarauta daga jinin wani
masaraucin,musamman ga nutsatsen mutum ne tsananin tsinkaye da dogon tunani da kuma
hangen nasa irin haisam din. Sultane din na dabanne......kamar yadda kwarjininsa ya
zama wani na daban.
Saman wata qawatacciyar shimfidar dake nuna asalin sarautar qasar
agadez din yake zaune. Yasha ado da launin kayan da suka kasance koraye ne,irin
launin koren dake da daukan hankali da idanun me kallo.
Daga hagunsa da kuma damarsa mutane ne zaune,mutanen da kana kallonsu
kasan akwai kusanci tsakaninsu daya basu daman zama haka su dashi,sai kuma alamun
dake nuna akwai magana me muhimmanci da suke tattaunawa.
Sarkin fada ne ya motsa,cikin tausasa harshe yake sanar da sultane
isowar haisam din,abinda yaja hankalin sultane din a nutse ya daga idanunsa zuwa ga
haisam wanda yake tattakowa cikin nutsuwarsa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 44
Gauraya idanunsu sukayi guri guda,,idanun sultane muhammad hammud a
kansa,yayin da haisam ya janye kallonsa daga kan sultane,saboda dabu'antuwa da yayi
na rashin girma ga sanya ido cikin idanun manya. Amma a qasan ransa yakejin wani
nauyin mutumin,mutumin da yau ne karon farko daya soma ganinsa ido da ido,duk da
baisan adadin iya hotunansa daya kalla ba a sanda bincike ya biyo dashi ta qasar a
sanda yake shirye shiryen tahowa agadez din.
Daga inda sultane yake zaune yana nazartar tahowar haisam din,cikin
jikinsa yake jin wani abu na daban game da yaron. Baiyi tsammanin ganinsa haka
ba,matashin dake da qananun shekarun da duka duka basufi talatin ba zuwa da uku,ya
dauka wani babban mutum ne zai dauki jagorancin karatunsu falaak din. A nasa son
yafison me shekaru,to amma hakanan cikin jikinsa karon farko yakejin ya aminta da
yaron.
Cloak robe dinsa yake qoqarin tattarewa don duqawa yakai gaisuwa ga
sultane. Yadda yakeyi din kadai yasa sultane yakejin kamar ya dade cikin
masarauta,sai ya daga hannu yana dakatar dashi daga qudawar da yake shirin
masa,maimakon haka hannu ya bashi direct,haisam ma kuma ya miqa masa nasa sukayi
musabaha,sannan sultane ya masa masauki kusa dashi.
Mamaki kadan ya d'arsu a zuciyar mutanen dake gurin,duk da cewa sultane
din mutum ne me karamci qwarai,yana da girmama mutane sosai,babu ma kamar ace mutum
masanin addini ne......kuma mahaddacin alqur'ani,wannan girman nasa yana ninkuwa a
idanun sultane din.
Cikin nutsuwarsa yake bin tattaunawar da sukeyi akai,sai a sannan ya
fahimci akan wasu dokoki ne na shari'a da akeson fiddasu,da wasu boyayyun qa'idoji
na shari'a da za'a yisu a rubuce,ayi kuma seminar ta kwanaki ana wayarwa da malaman
qasar agadez din kai.
Takardu aka raba a gurin,har tazo kan haisam. Idanun sultane a kansa
sanda yasa hannu ya karba,ya bude ta a hankali yana duba maudu'an da suke ciki,da
bayanan da ake buqatar warwaresu.
Murmushi kawai ya saki a nutse,ya maida takardar ya ajiye yana dora
idanunsa akan sauran malaman da suke gurin.
"Ko zaka warware mana kowanne hukunci?" Muryar sultane ta sauka a kunnen haisam. A
nutse ya waiwayo ya dubi sultane cikin girmamawa,a kallon farko kuma ya fahimci
wani gwaji ne sultane yakeson masa.
"In fada tana da buqatar hakan sai nayi ranka ya dade" Ya furta da sasanyar
nutsuwarsa cikin girmamawa.
Kai sultane ya gyada yana dauke idonsa daga kan haisam,murmushi kwance
qasan zuciyar sultane din. 'Yan qananun mintunan da yayi da yaron ya fahimci yana
da wata irin tarin nutsuwa da kuma kwarjinin da ba kasafai aka fiya samunsa jikin
kowanne mutum ba,irin kwarjinin da yafi fita ne daga jikkunan ahalin sarauta.
Cikin qwarewa da tarin baiwar fasaha da zalaqar zance haisam din ya
soma bayani da sharhi,bayanin da yaja hankalin duk wani wanda yake gurin,ya kuma
sanya sultane maida hankalinsa kacokam kan haisam.
"Bari mu fara da hukunce hukuncen dake kan bayi mata......baiwa a daraja da martaba
ba kamar d'iya take ba.......idan 'ya zatayi idda wata hudu da kwana goma,to baiwa
wata biyu zatayi da kwana biyar shine iddarta.......,idan baiwa tayi
zina,istibara'inta zai kasance haila daya ne wato jini daya,idan aka saki baiwa
zatayi idda na wata biyu ne,ba kamar 'ya da zatayi wata uku ba,idan me baiwa ya
siyar da ita ga wani,jini daya nan ma zatayi kafin ta zama mallakin wancan,sauran
abinda ya shafi 'ya shine kamar haka. Duk wanda yayi zina da mace,sannan aka daura
musu aure kafin tayi istibra'i to wannan auren batacce ne ba halastacce ba,dole a
raba wannan auren,idan kuma har ya kebe da ita to taci sadaki,dole ya biya
sadakinta,bayan ta gama istibra'i bayan rabuwarsu yana da ikon sake aurarta halal
ne......"
"Amma kuma duk wanda ya daura aure da mace tana cikin idda,sannan ya tare da ita,to
aurensu ya haramta har abada,koda ita dashi ne kawai suka rage a
duniya,kwatankwacin hukuncin ma'auratan da sukayi li'ani(tsinenenuwa),ya rantse
d'an data haifa ba nashi bane,itama ta rantse d'anshi ne,to bayan sunyi haka a kotu
a gaban alqali wannan aure ya rabu har abada,kuma sun haramta ga juna har abada"
Numfasawa yayi a hankali sannan yace.
"Iddar qaramar yarinyar daka saki,wadda bata fara al'ada ba,watanni uku zatayi
kaman yadda babbar mace zatayi,sannan iddar me kwantaccen ciki.......". Sake daukan
shuru masallacin yayi,yayin da dukka fuskokinsu ke gaya masa yadda bayanin nasa
yake shiga.
"Mace me kwantaccen ciki shekara hudu ne,zatayi shekara hudu sannan ta sake wani
auren"
"Allahu akhbar" Sultane ya fada a hankali yana girmama lamarin shari'a,tabbas ita
din sabanin hankali ce.
"Wadda ta debe tsammani da ganin haila,saboda shekaru itama watanni uku ne
iddarta.....kaman wadda take shayarwa,wadda bata haila sanadiyyar shayarwar,to
iddarta zata kasance shekara guda,hakanan macen da bata da cikakkiyar lafiya,itama
shekara daya ne iddarta.....macen da take cikin jinin cuta wato istihadha,itama
iddarta shekar daya ce". Ya qarasa fada a nutse yana sauke muryarsa qasa.
"Ma sha Allah.......ma sha Allah" Sultane ya samu kanta da furtawa. Duk wanda yake
gurin saida bayanan nasa sukayi masa dadi. Shugaban malamai ya motsa kadan yana
duban sultane.
"Allah ya taimakeka,dukka ya tattara bayanin ya gama yinsu,abinda kawai ya rage
shine rubutasu a tsare,aka rarrabasu zuwa guraren da suka dace".
" Zaka iya tsarasu a rubuce?" Sultane ya maido dubansa ga haisam. Nutsatsen
murmushi ya saki,a duniya baya ga bincike da rubuce rubucen addini ba wani abu da
yakeso yake kuma masa dadi gami da qawata lokutansa,sai kuma aikinsa na
intelligence da yakeyi.
"Ba zaya gagara ba in sha Allah,hukunce hukunce ne daya kamata a sansu a kowanne
gida,kowacce mace da kowanne magidanci susan dasu,saboda wadannan sune hukunce
hukuncen da suke tsaftace aure,kowa ya sani daga aure ake samar da zuri'a,zuri'ar
nan me kyau ko maras kyau?. Yadda za'a tsaftace mahaifa don samun 'ya'ya daga
bayyanannen tsatso kuwa yana da nasaba da samar da 'ya'ya na gari,da yawa an haifi
yaran da nasabarsu ta cakuda data wasu......an haifi yara cikin iddar auren wani,an
daura aure cikin sauran haqqin wani mijin,wannan sai yake zama sanadin haifar yaran
da suke gagarar al'umma,su gagari iyayensu,harma kaji d'a ya dauki abun kaifi ya
kashe mahaifi ko mahaifiyarsa ko 'yan uwansa,da yawa wadannan kurakuren dake cikin
idda ko saki suke jawo hakan".
"Tabbas......ko shakka babu" Sultane ya fadi yana jin wata irin gamsuwa da dukka
bayanan haisam,yana jin wata cikakkiyar nutsuwa dashi.
Kalar burikan da kowanne uba kanji akan haisam yaji ya saukar masa. Sai
yakejin inama ace d'ansa ne?,inama ace mallakinsa ne?.
"Koda bai zama d'anka ba,zai iya zama mafi kusanci sosai da kai......kana buqatar
irinsa,sosai kana buqata" Ya gayawa kansa da kansa. Ya sani mulki abune dake
buqatar mashawarta na qwarai,aqilan mutane masu nisan zangon hankali da
fahimta,tsayayyu masu tsoron Allah.
Yanaji a jikinsa kamar Allah ya aiko haisam ne cikin rayuwarsa,haka
kawai yakejin wannan feeling din da baisan dalilin jinsanba,baisan kuma daga ina ya
taso ba.
Sanda lokacin sallah ya cika tuni masallacin ya soma samun dafifi na
al'ummar agadez,masallata da suke halarta sallah a masallacin duk wunin juma'a,tun
daga sallar asuba har isha'i,wanda daga nan sai kuma wani satin za'a sake budewa da
bada daman shiga cikinsa,wannan ya sanya da yawansu a dukka wunin juma'ar a
masallacin suke duka sallolinsu.
"Bismillah" Sultane dake gefe ya fada yana nunawa haisam shimfidar da aka tanada
saboda liman. Kansa ya saukar qasa,ba kasafai ya fiya son a bashi limanci ba daga
zuwansa guri,saboda kaucewa fitina da susa cikin zukatan al'ummar gurin dama wanda
yake da ikon jan sallar
"Shiga mana ya sheikh......bismillah,umarnin sultane ne" Limamin da shike da haqqin
jagoranta ya fadi fuskarsa dauke da murmushi.
A nutse ya wuce gaba,ya kuma tsaya yana daidaita tsaiwar tasa,ya
miqan hannu ya dauko qaramin mic din yana maqalashi gaban rigarsa,kafin ya furta.
"Sawwu sufufakum(ku daidaita sawunku)" Muryar tasa ta bada amsa kuwwa daga kowanne
nahiya na unguwar gaba daya saboda qarfi da nisan amsa kuwwar,yayi kabbara da husky
voice dinsa cikin cikakkiyar nutsuwa.
Sautin kabbarar daya isa har cikin kunnuwan akhnan dake tsaye tsakiyar
dakin nata. Sautin ya bata wani irin baqon yanayin da batasan meye shi ba. Karon
farko da kabbarar sallah daga masallacin ya taba fusgar hankalinta,har kuma takejin
kamar baquwar murya ce wannan din. Kafin tace komai taji buhaina qasa qasa na cewa
da birra,birran dake qoqarin gyara zip din zubabbiyar doguwar rigar da akhnan din
ta sanya.
"An nada sabon limanne ko sabon malami?". Kai birra ta girgiza
"Banaji gaskiya,amma nima baquwar murya nakeji". A nutse akhnan ta daga kanta daga
sunkuyar dashi da tayi saboda taje mata doguwar sumar da bushira keyi.
" Aikin kula da lamuran da suka shafi masallaci dama aka baku?" Akhnan ta furta
maganar da alamun bacin rai sosai cikin muryarta.
"Tuba muke ranki ya dade" Buhaina tayi saurin furtawa. Batace komai ba,kaman yadda
bata bada kanta bushira taci gaba da gyarawa ba,har kaman ba zatayi magana ba
sannan tace.
"Ya zama na farko kuma na qarshe da kunnuwaku zasu dinga damuwa da rayuwar
wasu,harma ya zame muku abun tattaunawa.....wannandin dokata ce"
"Bazai sake faruwa ba,ki mana afuwa" Birra ta fadi cikin duqar dakai. Siririn
tsaki taja sannan ta maida kanta yadda yake tana fadin.
"Banason wani dogon fi'ili,ribbon daya zaki saka ki hademin shi yadda bazai dameni
ba"
"An gama,in sha Allah" Bushira ta fadi tana ajiye kayan adon data debo a gefe.
Shuru dakin ya dauka,kafin qarar wayarta ta katse shurun. A ladabce
barra'u ta dauko wayar takai qasa saman gwiwarta tana miqa mata.
Sunan kawai ta kalla ba tare da ta taba koda wayar ba. Shehnaz ce,sai ta
bawa barra'u umarnin daga kiran ta saka a handfree ta riqe mata da hannunta.
Hakan akayi,barra'u ta dora ma akhnan wayar saman tafukan hannuwanta,ta
kuma matsa mata dasu daidai yadda zataji dukka abinda shehnaz zata fada.
"Saluuut ma sΕur(hello sister)" Ta fada cikin nuna kulawa da kuma yanayin sabo dake
tsakaninsu.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 45
"Salut toi shehnaz....." Ta fada da nutsatsiyar muryarta dake sirkin
qasaita a ciki,kai ba zakace can cikin qasan zuciyarta zallar tashin hankali bane.
"Zuwa dare muna agadez in sha Allah,hankalinmu ya kasa kwanciya......fatan dai ba
wani abu mara kyau ko?". Idanunta fa lumshe,tana kuma qoqarin zuqar numfashi,don so
take ta daidaita kanta,ta kuma rage zafin da zuciyarta take mata.
"Akwai matsala shehnaz......amma kafin kuzo ya zama tarihi.....zai shafe tarihin
nasa ma gaba daya". Shuru shehnaz tayi tana juya maganar akhnan,idan tace akwai
matsala eh tabbas akwai matsalar........ Sau tari tana da wani irin qarfin zuciya
da ya gauraya da kafiyarta da yake sanyawa take iya tunkarar matsala komai
girmanta,bata da shakka kuma bata da saurin tsoro. Ba komai ne yake girgizata ba,ba
komai bane yake daga mata hankali ba. Matsala indai ba daga sultane ko mammina
ba,basa taba gigita nutsuwa ko tunaninta,shi yasa a yanzun dukka rauninta ya nuna
kansa,saboda sultane ne.....daga gareshi abun yake.
Kafin shehnaz ta sake cewa komai akhnan ta bada umarnin gimtse wayar,ta
dauke idanunta tana maidawa ga madubin dake ajiye a gabanta tana duban fuskarta.
A nutse take duban yanayinta,taci alwashi ko waye wannan daya nemi
gigita duniyarta saita shayar dashi mamaki,saita nuna masa illa da kuskuren abinda
ya aikata din,ba zata taba qyleshi ba cikin kawo mata tsaiko da yayi na kwanakin
nan a dukka al'amuranta,ba zata daga masa qafa ba......yadda ya kawo sabani
tsakaninta da sultane,abinda ta jima rabon da ya faru a tsakaninta dashi.
Kira na biyu ne ya sake shigowa,a nata zaton shehnaz ce still. A yanzu
kam bata da wani juriyar sauraren dogon zance daga shehnaz din ko aisa ma gaba
daya,inda zata qyaleta to tabbas zasu iso ne a daidai sanda shirinta zai
kammala,maganar ma sai yafi dadi,amma kuma ga tarin mamakinta sai buhaina tace mata
"Nannie ce". Manyan blue eyes dinta tadan bude kadan. Ba kasafai Nannie ke kiranta
haka kai tsaye ba. A wasu lokutan dabi'unta suna kamanceceniya dana morsa
safiyya,wani lokacin kuma tana diban kamannin halayyar mammina. Kai ya juya a
hankalin dake alamtawa buhaina cewa ta daga kiran,ta daga din,ta sake dawowa ta
duqa cikin girmamawa da wayar a hannunta.
"Assalamu alaikum" Nannie ta fadi da kamilar muryar dinnan da yanayin jinyar da
take ciki bai gaurayata ba.
"Wa'alaikumussalam......Bonsoir