Showing 39001 words to 42000 words out of 168506 words
ya zauna
saman kujerun concrete dake kusa dashi.
"Sai yaushe kenan zaka shirya yin soyayyar......ka shirya kuma accepting wata?".
Wannan boyayyen murmushin nasa dake cikin rawaninsa ya saki,ya kuma yi qas da kansa
yana zubawa qananun fararen duwatsun da aka qawata wajen dasu idanu kamar yanason
qididdige lokacin da zai jarrabawa wata macen ko ya bata dama a rayuwarsa.
"Not now omari......ba yanzu ba,ina da sauren abubuwa masu muhimmanci daya kamata
na gama dasu omari".
"Haisam....." Omari ya kirashi a sanyaye yana aza dukka hannayensa saman kwalin..
"Ina jiye maka haqqin 'dubban 'yammatan da wannan shu'umin murmushin naka kadai ya
jefa zuciyarsu kogin soyayya......ka kasa kuma taimaka musu da komai". Dole wannan
karon murmushinsa ya fito da wani irin sauti.
" Laifina ne omari?......" Kasa bashi amsa omari yayi......dondai da gaske kai
tsaye bazaice laifin haisam bane.......hasalima dukka cikinsu yafi kowa
takatsantsan da lamarin mata,banda jaruma kuma tsayayyar zuciyar da sukasan yana da
ita tabbas ba abinda zai hanashi soma kiransa da ME TSORON MATA.
Wani irin magnet ne cikin halittarsa dake fusgar hankalin 'yammata a
kanshi........kusan dukkansu suna da irin wannan baiwar,amma nasa kaman yafi nasu
zafi da yawa.
"Karkayi kwantai ko kayi zaben tumun dare fa?......" Omari ya fada yana fidda
idanunsa waje. Kai kawai haisam keta girgizawa kaman dariya nason qwace
masa,fararen jerarrun haqoransa da haskensu ya fita harta qyallen bakinsa suka
bayyana.......a wannan karon sai da yakai hannun nasa ya zame qyallen zuwa wuyansa
don ya bawa dariyarsa damar fitowa sosai.......wannan ya sanya qarashen cikamakin
kaykkyawar fuskarsa damar bayyana gaba dayanta.
Wani lafiyayyen ajiyayyar baqa sidik din suma ce ta bayyana data
gewaye habarsa da kumatunsa da wani iri qawataccen shape da zai gaya maka zallar
qwarewa da sanin haqqin qasumba name askinsa. Kyawawan jajayen lips dinsa dake
qyalli kamar an shafa musu man labba suka bayyana suna kuma sake zama ado ga
jerarrun fararen haqoransa.
"Ba damuwa.......sai na jira sanda d'iyarka ta farko zata isa aure saika bani ita".
Wani harara omari ya watsa masa.
"Ina ma ace akwai wani lafiyayyen abun bugu a nan?".
"Kana da hannu fa omari?......abun bugun me kake nema?" Ya tambayeshi yana dage
masa girarsa dukka biyun,amsar bayarwa omari ya rasa,daya tabbatar da haka sai ya
zare hannayensa daga aljihunsa ya hardesu a qirjinsa yaci gaba da tafiya zuwa ciki
hankali kwance.
"Ko haka na zauna ba aure......Allah bazai tambayeni dalili ba.........muddin zan
kare dokokinsa zan kuma tsare kaina......"
"Ba zaka iya ba.......na rantse da girman Allah kana cikin sahun mutanen da aure ya
zame musu wajibi" Omari daya miqe da sauri ya fada yana kuma bin sahunsa. Dariyar
mamaki ta sake kama haisam,amma saidai bai juyo ba.
"Zakayi kaffara omari......ka manta akwai manyan malaman da har suka rasu basuyi
aure ba?......manya manyan malaman musulunci........ciki harda malamin mazhabar
malikiyya imamu maalik?".
"Na sani......inajin kusan lokaci guda muka karanta littafin daya kawo sunayensu
gaba daya......malaman da suka fifita karatu akan aure........amma sam baka sahunsu
fa" Dif haisam din yayi masa ganin suna dab da fara shiga gurin jama'a,kuma zuwa
sannan haisam yana jin bazai iya ci gaba da musayar magana da omari din
ba.......don yana cikin abinda ke burge omari dama can suyita musayar ra'ayi.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 18
★★★Idan kaga yadda take shawagi cikin dokunan zaka rantse harda Allah ba diya mace
bace,ba wasu alamu da zai nuna maka shakka ko d'ari d'ari game dasu......
Daya bayan daya take zagayawa tana duba lafiyar dawakan nata guda uku
cikin dokunan hawa shida da take dasu.
Uku a agadez tare da raqumma uku da takan hau lokaci bayan lokaci,sai
wadannan guda ukun da take dasu a nan Niamey.
Wasu irin qosassun fararen dawakai da take matuqar sonsu........ba ita
kadai ba......duk wanda yasan sirrin kyan doki bazai kallesu sau daya tak yaji basu
burgeshi ba.
Sanye take da yalwataccen wandon palazzo data dora masa wata blouse
a sama long sleeve,sai ta kawo top data sauka har saman cinyoyinta me gajeran hannu
ta dora a sama. Lallausan scarf ne a kanta data nannadeshi kamar tufkar igiya tayi
wani irin dauri dashi daya bawa doguwar sumarta dake kwance a bayanta daman fitowa
sosai,saidai ba zaka samu daman ganin tsahon sumar daya bazu a gadon bayanta ba
sosai saboda wannan top din data dora a saman gashin nata.
Wani takalmi ne a qafarta,samansa kaman socks yake,qasansa ne takalmi.
Jikinta a kowanne motsi idan tayi lallausan qamshinta ne yake kadawa.
Miqewa tayi daga tsugunnon da tayi tana duba qafar daya daga cikin
dawakan nata,ta juya a nutse tana duban gabjejen mutumin dake tsaye a bayanta cikin
son cika umarninta.
"Thunder zan hau(sunan daya daga cikin dawakan nata)"
"An gama ranki ya dade" Ya furta cikin rusunawa yana sakin murmushi. Da ita za'ayi
wasan tseren dawakan.......amma ya fita qaguwa ranar tazo. Karon farko kenan data
taba yin register kuma zata shiga wasan,duk da irin qwarewarta a sarrafa doki da
kuma raqumi. Akwai kyakkyawar alaqa tsakaninta da dabbobin nan guda biyu,ta taso a
cikinsu sosai,ta kuma koyi hawansu da sarrafasu. Tana da tarin raquma da ake kiwata
mata,amma a ciki guda uku kacal take hawa da aka waresu musamman suka kuma saba da
juna. Hakanan dawakanta guda shidan nan na Niamey da wadanda suke a agadez tana
bala'in ji dasu. Sam sam yadda ta damu dasu bata damu da motocinta ba.....bata
muhimmanci ba kamar nasu.
Wayarta ce dake cikin aljihun wandonta tayi qara,ta zura hannunta ta
dauko tana duba me kiran,abinda ya saka murmushi subucewa daga fuskarta kenan,ta
fara takawa tana fita a wajen hadi da sanya wayar a kunnenta.
Daga yadda take amsa wayar kawai zai shaida maka da wani me muhimmanci
take magana.......hankalinta kwance take barin sashen dawakan zuwa parlor din gidan
da wayar a kunnenta.
A nutse ta murza handle din parlor din ta wuce ciki,daga baki bakin
qofa ta zare takalmin qafarta ta sauyashi da wani,sannan taci gaba da shigewa zuwa
main parlor na farko.
Shehnaz kadai ta gani saman dining da alama lunch take. Don yau tun safe
bataga gilmawarta ba,duk da kwana biyun nan ma ba wani magana sukeyi sosai ba.
Haushinta takeji akan Jamaal shi yasa take shareta......tana ganin sam bai dace
shehnaz ta ragi rayuwarta damarta kimarta da martabarta ba wajen auren jamaal din
ba.....wayayyen namiji tafi dacewa dashi......wayayyen namiji take da buqata ba
jamaal ba. Sai ita kuma shehnaz din tayi kamar bata gane abinda yake faruwa
ba......sam taqi ta nuna wata alama na ta fahimci akwai wani abu.
"Munyi magana da mommonki morsa safiyya......." Daga daya bangaren wayar mata da
suke kira da Nannie ta furta da muryarta me cike da nutsuwa. Lumshe idanunta akhnan
tayi tana dawo da tunaninta kan wayar da sukeyi da Nannie din. Kiran sunan morsa
safiyya kadai kuma ya dawo da nutsuwarta jikinta.
"Me matar nan taje ta fadawa Nannie a kaina ne?" Akhnan ta raya a ranta kafin ta
sake jin maganar Nannie din.
"Na bawa shehnaz saqo......ina fatan ta gaya miki ko?". Sai data aza idanunta akan
shehnaz dake kai abinci bakinta tana kuma danna waya da daya hannun kafin ta dauke
idanun tana ansawa Nannie
" Aah Nannie.......batace komai dani ba".
"Don qaniyarta ban gaya mata ta gaya miki ba?" Nannie ta fada da alamun daukan zafi
kadan a muryarta. Kai akhnan ta karyar gefe jin Nannie din zata dauki zafi da
shehnaz,duk yadda sukakai ga fada da junansu basason wani yaga laifin dan
uwansa,don haka a shagwabe tace.
"Fada mukayi Nannie.......batason kulani shi yasa bata gayamin ba......"
"Yoni ina ruwana da wannan shashancin naku da zata saka maganata a ciki?....."
"Nannieeeeee.....bada gangan bane ba" Akhnan ta sake fada a narke kaman zata sakewa
Nannie din kuka.
"Sannu me 'yar uwa........ni naga gyada ma sarkin goyo" Nannie ta fadi tana jin
haushin yadda ko laifi akayi tsakanin su ukun ake rasa gane waye me laifin waye me
gaskiya.
"To abinda na gaya mata ta gaya muku......naji fes abinda ya faru zuwan yaroncan na
garin tahoua........wannan shashancin ya ishemu hakanan......kuma tabbas don bana
agadez wasu abubuwan ke faruwa,nace ta gaya miki keda aisa din gaba daya......Ku
maida hankulanku jikinku......lokaci yayi da zamu miqaku dakunan aure.....don ba
zamu zuba idanu ku dinga rayuwarku yadda duk kukaso ba". Duk wani walwala da
nishadi da ta tashi dashi a yau Nannie ta warware mata shi tas,sai kawai tayi shuru
tana sauraren sababin da Nannie din takeyi harta gama.
"Sai anjima" Nannie ta rufe da fada tana katse kiran.
Ba yau ko jiya ki shekaran jiya tasan Nannie ba.......tsayayyar mutum
ce me wani irin kafaffen ra'ayi.......tana tsananin sonsu da qaunarsu.......to amma
a hakan fa idan abunta ya motsa kowa ma bi take ta kanshi. Qanwa ce guda daya tal
data ragewa sultane muhamma hamud a duniya,kuma itace mahaifiyar
aisa.......mahaifiyar shehnaz ke bin Nannie,kuma shehnaz kawai ta Haifa ta rasu,don
haka shehnaz Nannie kawai ta sani a mazaunin mahaifiya.
Sunan Nannie na asali bilkissou......Nannie ya samo asali ne daga bakunan
shehnaz da aisa.
"Soni masoyi......soni ka sani ranka.....domin so da yardaaaaaa" Muryar aisa da
akhnan batasan da zamanta a gefe ba ta soma motsawa cikin baitocin waqoqin
fitacciyar mawaqiyar qasarsu.
A nutse ta juya tana duban aisa din,ta tabbatar da ita take......kuma da
biyu tasan takeyi. Rasa me zatayi mata tayi,kawai saita jefeta da wayar hannunta.
Dukka idanunta aisa ta fidda bayan wayar tadan sameta a qafa kadan tana
bin wayar da kallo kafin ta kalli akhnan.
"Vous ne savez pas à quel point elle est coûteuse(bana tunanin kinsan
tsadarta),kike jifa da ita haka?". Manyan almond shape eyes dinta ta ware ta
watsawa aisa din,saidai kafin suce komai shehnaz dake can a zaune ta fara magana a
nutse
"Vous êtes tous invités aux courses de chevaux spéciales, présentation du nouveau
cavalier de la famille royale, Akhnan Muhammad Hammud".
Yadda tayi shuru bayan ta kammala karantawa haka falon ya dauki
shuru,kowa a cikinsu ya rasa me zai fada. Tsam akhnan din ta miqe,don batason kowa
a cikinsu ya maido mata tunaninta baya,da nutsatsiyar muryar nan tana da ta dace da
innocent fuskarta da sam bata dace da attitude nata ba taurin kanta da kuma
kafiyarta ba tace.
"Tous sont invités(eh.....dukkaninku ana gayyatarku" Sai ta fara wucewa hankali
kwance.
"Biftu.......sanarwa ne fa na gasar tseren doki fa aka karanta miki.....da sunanki
da na sultane a mazaunin babbar baquwa 'yar tsere......what if me martaba yaji?".
Zagayayyun idanunta ta juyo ta zube musu.
"Idan ke kika gaya masa ba......ba wani gurin bane.....cikin Niamey ne......cikin
Niamey din ma cikin hippodrome.....ba wani bangon duniya ba".
"Tare da maza ne fa biftu" Aisa ta sake fada fargaba na bayyana saman fuskarta.
"Et puis?(sai me?).....C'est mon rêve(mafarkina ne),zan kuma cikashi ko sau daya
ne". Ta fadi hankalinta kwance,bata kuma qara ba taci gaba da takawa tana tafiya
abinta.
"Laissez-la(ki qyaleta).....ki barmu muga wasannan s'ilvous plaît(please)" Shehnaz
ta fada tana murmushi,don har ga Allah ita abun ya mata dadi. Tana ganin ba wani
abu bane me muni tunda na dan lokaci ne,kuma tafi kowa sanin yadda akhnan ke mugun
son tseren doki da yadda ta qware akai.
"Na qyaleku" Abinda aisa kawai ta fada kenan ta koma tana zama ba tare data sake
cewa komai ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 19
Sanye yake da Moroccon jallabiyya ta maza,wadda ta sa haskashi sosai tayi
masa wani irin kyau tana kuma sake haska fatarshi dake da wani irin launi,shi baiyi
haske me yawan da zai kashe maka idanu ba,hakanan baiyi duhun fata ba,don kusan
launin fatarsa yadan saba kadan data ainihin 'yan qabilae oromo.
Lallausar baqar sumarsa me santsi irin ta 'yan qabilar oromo din sai
wani sheqi takeyi da walainiya,sumar da ta take kwance saman kansa zuwa gefe da
gefen fuskarsa da kuma habarsa. Kansa wata qaramar hula ce irin ta larabawan
morocco,wanda hakan bai hana bayyanuwar baqar sumar tasa ba data yiwa fuskarsa wani
irin ado.
Shi daya ne cikin dakin,wanda kai tsaye ya amsa sunan library me wani
irin tsari me daukan hankali da gasken gaske. Wani irin ma'ajiyar litattafai ne
kewaye da ita,dauke da tarin litattafan da suka wuce ka iya qididdige yawansu,domin
kuwa kowanne bango sune......bangon kuma tun daga samanshi har qasanshi. Akwai
litattafan dake rubuce da yare kala kala......tun daga kan
English......french.....oromo.......yayin da litattafan addini na larabci suka
mamaye kaso mafi girma na library din.
Komai na library din ya bada wani irin yanayi da nature me kwantar da
hankali da daukan hankali,gurine da yafi kowanne guri sama masa nutsuwa a
duniya.........baya ji a jikinsa akwai wani abu daya mallaka da yakai wannan
library din muhimmanci a wajensa.
Yana iya rayuwarsa shi kadai a wajen.......zai iya qarar maka da
awanninsa na rana duka a wajen ya kebance kansa. Karatun addini ruhinsa
ne......fatarsa ne.....kuma rayuwarsa ne,ya kuma sameshi,don babu wani abu da yake
sanyashi nishadi kamar lokaci irin wannan. Lokacin da zai kebanta cikin yanayi na
shuru da wata irin kyakkyawar nutsuwa cikin dakin karatun,yana yin bincike da
zaqulo mas'aloli masu yawa daga mazhabobi da malamai iri daban daban.
Ya tsara wajen daidai da yadda zai dace da tsarinsa da kuma yanayinsa
da abinda yafiso. Wasu irin kujeru da lausasan carpet aka yiwa gurin ado dasu,sai
wani sashe na daban na library din da aka sake zuba wasu rukunin kujerun da kuma
teburansa,yadda zai dace da zaman me bincike.
Daga gaban kadan dan qwarya qwaryan table ne me dauke da wasu qananun
cabinet,wanda ba komai a ciki sai nau'in coffee kala kala.....coffee makers har
biyu da wasu irin mugs da trays masu daukan hankali.
Yankin jimma dama qabilar oromo gaba daya coffee yana daya daga cikin
manyan al'adunsu.......sukan ware babban fili me girman Hector me yawa suyi noman
coffee zallah. Su kullum ranar shan coffee ce a wajensu bayan rana ta musamman da
suka ware mata,ba abinda yake da muhimmanci a gurinsu irin coffee. Wannan jinin da
wannan al'adar ta gudana a jikinsa sosai,don ko cikin masu son shan coffee din shi
na daban ne.
Sake miqe dogayen qafafunsa yayi saman ottoman sofa dake gabansa yana
fidda wani sassanyan numfashi. Sosai yake jin dadin zaman nasa a nan safiyar
lahadin,duk da rabin hankalinsa yana kan wata 'yar qaramar danja dake gefansa.
Green light da yayi blinking shi ya sakashi daga kansa a
hankali,lumsassun idanun nan nasa suna sake rusunawa da wata irin nutsuwa yana
duban light din don tabbatar da motsawar da yayi. Ya sake bada green color
kuwa......don haka ya sauke qafafunsa a hankali yana rufe littafin bayan ya sanya
alama,ya miqe da cikakkiyar nutsuwarsa yana zare hular kansa ya ajiyeta saman
ottoman din,sannan ya dauki wani irin nau'in Bluetooth ya latsashi ya sakashi a
kunnensa yana nufar wata bookshelf data banbamta da nau'in da yanayin kowacce daya
dake wajen,labbansa masu sulbi dake da wani irin color suka motsa a hankali suna
bada sautin husky voice dinsa da ta rage boldness yana fadin.
"Assalamu alaikum warahmatullah" Daidai sanda ya latsa wani abu jikin bookshelf din
take ya juya kansa ya canza siffa daga bookshelf zuwa qofa,sai ya murza handle din
ya shiga sannan ya maidata yadda take bookshelf a dazu.
"Wa'alaikumussalam.........mun tashi lafiya haisam?". Babban mutumin da muryarsa
kadai ta bayyana nutsuwarsa da dattijankarsa ta bayyana sosai ya fada.
"Alhamdulillah babbo". Ya amsa yana kunna switch na dakin,take haske ya mamaye ko
ina.
Wani lafiyayyen daki ne da tun daga gininsa zaka tabbatar ya samu
ingantaccen tsari da wannan irin sirri na musamman,don hatta da windows din dakin
suna da wani irin yanayi ne,ba normal winduna na yau da kullum bane. Cike yake da
tarkacen kayan wuta iri daban daban......wayoyi tsayayyu alluna na zane.......da
sauran wasu abubuwan da ko sunansu ba lallai ka sani ba. Saidai duk da wannan kayan
komai yana ajjiye a muhallinsa a kuma tsare,don a kallon farko ma abinda zai fara
zuwa kanka shine wani office ne na musamman dake koyar da harkar na'ura me
qwaqwalwa.
"Nayita qoqarin samunka a jiya......sai omari na barwa saqo.......ka duba email
naka yanzu yanzu".
"Okay bobbo". Ya amsa masa a girmame yana danne makunnin Bluetooth din nasa sannan
ya isa a hankali gaban wata qaramar system yaja kujerar dake gabanta ya zauna.
Waving hannunsa kawai yayi a fuskarta ta kunna kanta da kanta,ya matsa
gaba sosai ya fara sarrafata. Wasu irin tarin password ya saka mata kafin ya
budeta,password din da zakayi mamakin yadda akayi suka zauna daram cikin kwanyarsa.
Wata irin nutsuwa ya bawa na'urar yana bin kowanne saqo daya bayan daya
da idanu da kuma hankalinsa,nutsuwar da zata gaya maka muhimmancin aikinsa a
wajensa da yadda komai na aikinsa yayi masa ya dace da tsarinsa da muradinsa.
Hasken screen din ya sake haska fararen idanunsa