Showing 156001 words to 159000 words out of 168506 words
masa haka,yaci gaba da qoqarin maidawa beeno saqon gaggawa daya tura
masa,yayin da wani sashen na kwanyarsa yaci gaba da aikin saita daga wanne sashe
wannan kallon yake fitowa ba tare kuma daya daga kanshi ba ko sau daya.
Agogo sultane ya kalla sannan ya maida dubansa ga akhnan,cikin sautin nan
nasa dake cike da nutsuwa da kamala yace.
"Ina saurarenki.....mene kike cewa kafin yanzu?". Maganar ba iya akhnan kawai ta
daka ba,harda mammina. Ta dauka tunda baqo ya iso gurin,baquwar fuskar da babu ita
cikin masarautar maganan ya wuce.
Blue eyes dinnan nata da sukayi wani irin jirkicewa ta daga ta kalli
fuskar sultane,sai kuma ta maida kanta qasa ba tare data iya sake cewa komai ba. Ta
yaya zata bari rauninta ya bayyana a idanun wani bare?,barenma da take qarfafa
zargi me girman gaske a kansa.....wanda muddin wannan zargin nata ya tabbata,tayi
rantsuwa da ubangijin sammai da qassai saita tozartashi mafi munin tozartarwa.
((Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Duk da wani sashe na zuciyarta yana mata tantamar haka. Ba wani
kidahumin malami irin haka,da bai gama sanin kansa bama ballantana dabbobi ya iya
sarrafa dawakai haka......ya iya hawa doki da dukkan qarfin izza da qwarewa irin
haka,zuciyarta tana cika da tantama idan ta tuna wannan.....babu wani malamin
addini dake da wannan zarrar,ba wani kidahumin malami da xai iya tunkararta har ya
iya hada tsere da ita. Ko waye wanda yayi hakan,tana da imanin cewa akwai tsartuwar
jinin jarumta a jikinsa. Akwai wani yarfi na izza tattare cikin jininsa,akwai kuma
wani abu na daban ma tattare dashi da kaifin idanunsa suka kasa barinta a mafarkai
mabanbanta.
Taga maza masu tarin yawan adadi a rayuwarta......masu tsananin zallar
madarar kyau daga mabanbantan qabilu,cikinsu harda mazan qabilarta da sukayi fice a
fanni na kyau a qasarta dama dukkan qasashen africa dama duniya gaba
daya......mazan da suka yarda su sadaukar da komai nasu don ta aminta ta zama
mallakinsu,amma babu wani namiji qwaya daya da wani abu nasa ya tsaye mata a
rai,kuma wai har ya zama abokin mafarkanta sai a kansa.
A hankali cikin kuma hikima ta daga idonta ta aza akan haisam. Sam sam
kamar ma ba a gurin yake ba,kamar ma baisan wani abu dake wanzuwa a gurin ba,ya
bawa wayarsa nutsuwarsa da kuma dukka hankalinsa. Abinda ya sake sanyata cikin
mamaki,ba wani mutum da zaizo gaban sultane yayi haka,gayyata daga sultane ba
qaramin alfarma bace,a niger kake ko a maqwabtan qasashen africa,amma shi gashi
gaban sultane kuma yana danna waya?. Ko data daga kanta kuma ta dauka zata tsinciki
alamun karkatuwar hankalinsa akan sultane ko shiyyar da akhnan take,amma ga tarin
mamakinta,da dukka iya zurfin nazarinta bata hangi wata alama koda qarama ba dake
nuna haisam yana tare dasu
"Waye wannan?,wanne irin mutum ne shi?" Ta tambayi kanta da kanta,sai ta jinjina
kan tana jin qarin wasu baqin dabi'u daban data hanga tattare dashi. Koda bataga
alamun yana tare dasu ba,amma bataji yarda dashi ko kadan ba,ita din wata iri
mutum ce da samun yarda daga gurin ta yake maka wahala,samun yarda daga gurinta
yake daukarka dogon zango dogon lokaci da kuma dogon zamani. Sassauta murya tayi
zuwa ga mafi qanqantar yanayi,yanayin da mammina keda yaqinin Haisam bazaiji ba
tace.
"Ranka ya dade......ina ganin wannan maganar bai kamata a yita ba a gaban baqo kuma
bare......abune daya shafi iyali". Murmushin qasan rai haisam yayi,yana da wata
irin baiwa ta kaifin ji matuqar gaske,kaifin jin da ya dinga bawa nanay tsoro. Ko
yaya akayi magana,komai nisa muddin nisan yana kewaye da inda yake zai iya jinta.
Daga idanunsa yayi ya kalleta,sannan a hankali yakai hannunsa ya riqo hannun
haisam,sai a sannan din haisam ya daga kanshi yana duban sultane dake riqe da
tsintsiyar hannunsa.
"Nayi zaton daga yadda ya shigo ya riskemu zaki fahimci cewa daga yau SHI DIN D'ANA
NE.....na dauka iya wannan zai gaya miki yana da girman matsayin da komai baza'a
boye masa ba,na dauka kin karanci cewa ya zama DAYA DAGA CIKIN AHALINA.....komai na
iyalina......komai na ahalina yana ciki,ba wani sauran abu da za'a boye masa".
Girman bugunsu da maganan tayi ya sanya saida akhnan ta sake daga idanunta a karo
na biyu ya saukesu kan haisam ba tare data shiryawa hakan ba. Ga mamakinta har a
wannan lokacin sam bai dubi koda gefen inda take zaune ba,hakanan yanayin fuskarta
bai nuna mata abinda take zaton gani ba.
Farinciki murna da walwala take saka ran ganin kan fuskarsa,madaukakin
farincikin da samun damar shigewa jikin me martaba haka ta farat daya,samun
qazaitacciyar damar da ba wanda ya taba samun kwatankwacinta,tun daga sanda sultane
ya zama magajin muhammad agga har zuwa yau din. Saidai a maimakon hakan,ba wani
sauyi da yanayinsa ya nuna. Wannan fuskar me tarin kwarjini,wannan fuskar dake
cike da wani irin kwantaccen kyau me daukan hankali.......wannan ran dake cike da
wani izza ta sarauta cike yake da nutsuwar da zaka fahimta a karan
kanka......hankalinsa sam sam baya tare da maganganunsu.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 78
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
Wadannan idanun dai sune da suka sake haske saboda da hasken screen din
wayarsa dake shiga ta ciki.
"Zaiyi wahala ya kasance bashi bane wannan mutumin" Zuciyarta ta gaya mata kai
tsaye ba kwana kwana,da kuma irin yanayin da indai ta d'arsa mata abu dashi to daga
qarshe hakance take tabbata.
Wani irin mahaukaciyar tsanarsa tayi gangamin gayya ta sauka saman
zuciyarta,ta qanqance idanunta zuwa can ciki da wani irin kallo,tana fata koda sau
daya ne ya kalli cikin idanunta ta soma ajiye masa saqon farko,amma hakan bata samu
ba.
Bata iya hadiye fushi ba,ba kuma kasafai ta fiya ajiye abu a ranta idan
yana damunta ba,tana cikin jerin sahun mutanen da fadar abu yake zame musu sauqi da
rangwame cikin rayuwarsu,hakanan nunawa a aikace ya zame musu dabi'an da bata
canzawa.
"To amma shi din ba kowa bane bappi.......bai rayu damu ba,baisan ya rayuwarmu take
ciki ba.......hasalima ko cikakken magana da yaren abzinawa baya fita a bakinsa
yadda ya kamata,ta yaya zai zama wani yanki daga ahalinmu?,waye shi?" Ta furta
maganan Kai tsaye tana duban sultane.
Sosai maganar akhnan ta yiwa mammina dadi,kamar ta shiga rai da
zuciyarta taga kalar tambayar dake kai kawo a ranta,amma kuma tana takatsantsan da
fitar tambayar daga ranta. Irin kallon da sultane ya ajewa akhnan ya tabbatarwa
mammina inda ta yarda tambayar ta fita daga gareta ne data gama tozarta,gefe guda
kuma zuciyarta ta cika fal da fargaba,kada sanadin wannan maganar tata ya kawo
cikas gurin samun sauqin cikar muradinsu. Cikin wannan salon nata data saba amfani
dashi tayi kiran sunan akhnan.
"Biftu......kul dinki da jayayya ko qalubalantar hukuncin sultane,akwai wani abu da
sultane zai yanke hukunci akai ace bai tabbata ba?". Wani murmushin ne daga qasan
zuciyarsa da ba alamarsa saman fuska ko labbansa ya subuce masa,akwai wani boyyen
sauti cikin lafuzzan matar,akwai boyayyen yanayi da ke bayyana wani abu da aketa
qoqarin turashi nesa da zuciya nesa da mafitar magana saboda wani babban dalili na
cimma quduri.
"Wacece wannan?" Muryar omari ta ratsa kunnensa ta Bluetooth din kunnensa,cikin
hikima ya dora yatsansa kan Bluetooth din daya saje da shape din kunnensa bata
yadda zaka gani yadan latsashi,wanda daga wancan bangaren ya bawa omari sign na ya
dakata kawai,sai ya gyada kansa a hankali yana sake matso da na'urar gabansa.
"Da zaki qyaleta zaituna.....wataqila ta kawo wani abun da yafi nawa dacewa da
muhimmanci..." Ya furta muryarsa na nuna alamun bacin rai,da kuma fara tunzura da
yake dab dayi.
Ta karanci wannan,bataso kuma komai ya kwabe,batason wannan raunin nasa
da take qoqarin tayarwa ya koma ya kwanta,don haka ta miqa hannu ta matsa hannun
akhnan data motsa da zummar yin magana,abinda ya faru cikin idanun haisam daya dan
budesu cikin kallon qasan idanu da idan yana yinsa zaka tsammaci bacci yake.
"Me yasa ta hanata ci gaba da magana?" Ya ajewa ranshi tambayar yana qoqarin janye
idanunsa kan hannuwan nasu gudun wucewa iyakar kallon shari'a,saidai kuma kamar an
fusgi kallon nasa sai ganinsa ya sauka kan tsintsiyar hannun mammina din.
"Kayi mana afuwa.....kayi mana aikin gafara.....kada wannan abun ya zama silar kasa
yi mata alfarma cikin alfarmar nan taka,cikin tausayin nan naka da jin qanka,don
Allah.........muna fata ayi mana gafara" Ta fadi tana sadda kanta tare da sake
matsa hannun akhnan a karo na biyu,kalaman da suka sauka kunnuwan haisam tare da
dogon nazarin banguls din dake zagaye da tsintsiyar hannun mammina.
Idanunsa ya janye a hankali cikin yanayin da ba zaka fahimta
ba,daidai sanda ake sallama daga daga bakin qofar falon kuma aka daga labulen farko
ana neman izini.
Sautin muryar ya sake jan hankalinsa saboda jin wani sabon accent din
kamar a yankin Ethiopia yake ba agadez ba. Kakkaurar muryar data masa kama sak da
muryar mutumin da yaji a dazu.
"Kana iya qarasowa" Maimartaba ya furta yana saisaita muryarsa.
Cikin second daya ya bayyana cikin parlor,da shigar kayan sarki na
yankin agadez......amma ba abinda haisam yake gani saman fuskarsa sai qasar
Ethiopia a kalamansa,wanda sun bace bat daga kamanninsa babu ko qwara daya.
A hankali ya aza hankalinsa a yanayin tafiyarsa,yana takawa ne da
qwarin gwiwar da zata gaya maka wani ne a wajen sultane......da yanayin da zai gaya
maka yana da girman matsayi da isa a gurinsa,sannna ya qaraso gabansa ya zube da
yanayin da ya tunawa haisam ZAMAN GABAN SARAKUNAN QASAR ETHIOPIA.
Wani irin zama ne da aka gaji yanayinsa daga manyan da tsofaffin
qasar,yanayin zaman dake nuna zallar sadaukarwa......zallar bada kai.....zallar
amanna da kuma biyayya.
Idan har idanunsa sun nuna masa daidai,sai daya saci kallon akhnan
kafin yakai hankalinsa ga sultane dake fadin.
"Tamim sarkin aiki.......tamim gandun hidima" Wani kirari da yake bala'in farantawa
tamim din rai,yana kuma sake bashi tabbacin cewa da gaske yakai wani qololuwar
matsayi wajen sultane din.
"Allah ya baka kyakkyawan qarshe,ya kula da dukka sha'aninka.....an kammala komai"
Ya fada da tsantsar ladabin da ko idanunsa baya iya dagawa ya kalli sultane.
"Amma tamim.......baka fahimtar muhimman lokuta da bai kamata ka dinga tsoma kanka
a ciki ba?" Mammina ta furta da wata irin izza da qasaitar data hau kanta yanzu
yanzu tana qure tamim din da wani irin kallo,gabanta kuma yana tsananta faduwa,wani
irin bahaguwar bugun zuciya daga sanda tamim din ya bayyana,wanda batasan meye
dalilinsa ba,amma tunda har hakan ta kasance take jin yaqini a zuciyarta AKWAI WANI
ABU DA BA DAIDAI BA.
"Tamim yana da matuqar qoqari zaituna,yana kuma da amanar da idan aka bashi aiki
saiya tabbatar da gamsuwar wanda ya bashi aikin......ba laifi bane don yayi
hakan......kaje tamim....zamu ganka in sha Allah"
"Godiya nake Allah ya baka yawan rai.....ubangiji ya firgita maqiyanka". Ya fadi
yana yunqurawa da zummar miqewa,daidai lokacin idanunsa ya sauka kan haisam,wanda
har yanzu ga duk me idanun kallo idan ya dubeshi zaiga hankalinsa kacokam yana a
kan wayarsa ne.
Wani irin abu me qarfi yaji ya fusgeshi,zubawa haisam din idanu na wasu
sakanni kafin ya janye dubansa a hankali yana takawa gami da ficewa daga shiyyar.
"Inajin wannan maganar tazo qarshe......ni muhammad hammud na bayar da akhnan ga
hakeem,watanni biyu kacal na bawa kowane bangare su gama shirinsu". Wani abu taji
ya dunqule mata saman qirjinta,kamar yana shirin hanata shaqa da kuma fidda
numfashi.
*_BAYAN WASU SA'O'I_*
Cikin qasaitaccen takunsa ya isa ga sassansa,wanda yana dab da dora
hannunsa saman handle aka bude masa qofan.
Abdii ne tsaye,yana dubansa da murmushi kan fuskarsa.
"Welcomw captain obbo" Ya fadi da yanayin daya gayawa haisam a tsaye yaron hake tun
dazu yana jiran dawowarsa.
Da idanu kawai ya amsa masa,ya saka kai yana wucewa ciki abdii din ya
take masa baya. Akwai maganganu da yawa a bakinsa da tambayoyi,amma yanayin obbo
din ya nuna masa kaman akwai wata lafiyayyar gajiya a jikinsa. Mamaki kadan ya
kamashi,mutumin da ya amsa gayyatan cin abinci,meye ya hadashi da gajiya kuma?.
"Sai da safe zamuyi magana......i'm not cool now......karka sakani magana da
yawa.....,ka kira salawi ka gaya masa yazo ya daukeni,qarfe sha daya na safe,kada
ya wuce hakan." Ya qarasa fadin maganan yana tattakawa yan wucewa zuwa stairs din
ba tare daya tsaya ba.
Baki abdii ya saki kawai,shi yasa shifa yazo obbo ya barshi ya masa
rakiya can cikin gidan,don ga ganewa kansa komai da komai. Saboda yasan halin 'yan
miskilancin obbo din nasa, taba zama ya bashi labarin komai yadda yakeso
ba,gashinan ma ko zama ya masa kyakkyawan kallo baiyi ba ya wuce sama abinsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Har ya juya,sai kuma ya laluba wayarsa dake aljihunsa da sauri. Sai
yanzu ya tuna saqon da Menelik ta bashi ya isar dashi ga obbo din,sam ya manta,kuma
a girmansa da mutuncinsa da take gani bai kamata ace bai isar da saqon a daren ba
kamar yadda ya mata alqawari,don haka ya soma haurawa saman shima cike da tantama
da d'ari d'arin kada haisam din yayi rejecting dinsa.
Bawai gangar jikinsa bace ta gaji,a'ah,kwanyarsa dake cakude da tunani
da hasashe iri daban daban ce ta saukar da gajiya ga kowacce gabarsa. Akwai abubuwa
da yawa daya gani,wasu yayi hasashensu,wasu kuma jikinsa ya bashi. Cikin kowanne
jini dake harbawa zuciyarsa yana sake samun tabbaci da yaqinin samuwar
nasara.......yana ganin wani haske me girma kaman ya wulga cikin aikinsa,sai
yakejin tamkar wata tafiya ce sukayi kuma sukazo bakin gaba.
Bai shirya yin bacci da wuri ba,yana buqatar raba dare ya kammala dukka
wani hasashe na kuma next plan dinsa as document kamar yadda ya saba cikin kowanne
aiki,cikin kuma kowanne motsi. Yasa hannu ya zame amama din kanshi,take lallausan
gashinsa me sulbi ya warware saman kanshi. Hannu yasa yana balle button din
rigarsa,so yake ya zareta ya watsa ruwa me dumi da zai wartsakeshi daga duk yanayin
da yakeji,sannan ya hada da zazzafan coffee dinnan daya zama jinin jikin duk wani
d'a na asalin qasar Ethiopia.
Yana balle button din hannunsa yaji an knocking qofar,da gajiyayyun
idanunsa ya watsawa qofar kallo,bai kuma tsaya tambaya ba kawai ya taka ya murza
lock ya budeta sannan ya jawota baya yana duban bakin qofar.
Suna hada idanu da abdii din ya aza hannunsa saman tashi sumar yana
shafata gami da fara sunne kai.
"Dhiifama obbo". Da idanun nan nasa kadai ya tambayeshi dalilin knocking din,sai
kawai ya fidda hannunsa a aljihunsa ya miqa masa wata fara qal din envelope.
Duban takaddan yayi kafin ya maida duban nasa ga abdii,still da idanu
ya sake tambaya ba tare da yayi magana ba.
Har qashinsa yakejin girman kallo haisam irin wannan,da wannan body
language din nasa me dafa mutum gwara ya buda husky voice dinsa ya maka magana.
"Menelik ce obbo......don Allah karkayimin fada,alfarma tace nayi mata" Yayi
maganan idanunsa suna nuna da gaske bayason ya masa fadan. Shuru yayi kaman bazaice
komai ba,sai ya miqa masa hannunsa. Amamakance abdii yabi tattausan tafin hannun
nasa da kallo sai kuma yayi saurin aza masa takardar ya juya yana boye dariyar
farincikinsa.
Da qafa ya maida qofar ya rufe,ya juya takardar sau biyu a hannunsa,sai
ya qarasa ya jawo drawer ya zurata ya maida ya rufe. Sai da yayi hakanne ma ya tuna
wancan saqon nata ma ko budashi baiyi ba. Idanunsa yadan lumshe yana budesu gami da
kama jubah din nasa ya zare,lallausar vest dinsa fara qal ta bayyana,wadda ta tsumu
da wannan qasaitaccen unique scents din nasa.
Inda menelik zata fahimta......ba ita kadai bama,da sun samawa kansu
sassauci. Bayason kowacce mace ta tsinci kanta a wahala ta sanadinsa. Baisan me
zaiyi musu da zasu fahimci yana da sauran abubuwa da yawa a
rayuwarsa.......ayyukansa masu muhimmanci da yinsu da kuma kammalasu yake jinsa ya
zame masa tamkar Ibada,eh dole ne......don kubutar da rayuwar MOTII daga hatsari da
barazanar da yake ciki tsahon shekaru ashirin da suka shude.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 78
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
Wankan ya sakeyi da ruwan zafin,sannan ya fita parlor din dake manne da
bedroom din ya hada coffee cikin mini coffee maker din da aka ajiye masa saman dan
wani