Showing 123001 words to 126000 words out of 168506 words
wanda ya
qara cikakken motsi ma,har mintuna ashirin nasu Aafreen ya cika,Aafreen din kuma ta
tako tayi kiransu rungume da books dinta.
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 61
Daga ita har badee'a cikin nutsuwarsu suka qara wajen,suka zare
takalmansu suna zama saman shimfidar da aka raba littattafai gurin zaman mutum
biyu. Koda baiyi magana ba falaak ta gama fuskanta,litattafan da zasu fara
karantawa ne ya basu ba tare da tambaya ko bin ba'asin sun siya ba?.
Wani irin burgeta taji yayi,ta buda baki ta soma gaidashi da harshen
faransanci,ya amsa a taqaice,gaisuwar badee'a ma ta biyo baya.
"Ga litattafan da zamu fara nan.....amma bana karatun banza,kowanne rana kafin mu
dora sabon karatu zaku maimaitamin abinda muka karanta jiya don nasan abinda nakeyi
din ba wahala bane" Ya fada cikin nutsuwarsa da kamewarsa data qara masa wani irin
kwarjini. Da gaske ko zakayi wasa da komai amma kada ka yarda kayi masa wasa da
karatu,baya daukan wannan kusan tsakaninsu hussam rumaisa noory dama dukkan 'yan
uwansa sunsan da wannan.
"In sha Allah" Falaak ta fadi tana daukar littafin da yace dashi zasu fara.
Iska ta shaqa sosai tana zuqar daddadan qamshinsa har cikin hunhunta.
Iya riqe littafin kawai da tayi ba tare data matso dashi kusa da hancinta ba tana
iya jin fitar wannan qamshin nasa na musamman daga jikin litattafan. Ta tattara
dukka nutsuwarta tana sauraren muryarsa dake fita da wani irin nutsuwar da dole
kaso karatunsa......dole kuma ka fahimta ko don irin taushin da amon sautinsa yake
bayarwa.
*AKHNAN*
A qasaicenta take takowa zuwa gurin daya zame mata na al'ada gurin ganawa
da baqin da suka zamewa rayuwarta alaqaqai,cikin fata da sanya ran a yau wannan din
ya zama shine baqo na qarshe da zata gani a gabanta. Duk kuwa da irin yadda
zuciyarta ke sake nanata mata cewa,hukuncin sultane fa wani abu ne da babu wanda ya
isa ya tayar dashi,duk da zuciyarta na d'arsa mata,lokaci bayan lokaci
cewa.......tana taku ne zuwa ga muhallin da zata gana da mijin da sultane ya zaba
mata......final choice kuma da take dashi,amma zuciyarta na gaya mata cewa wani abu
ne da ba tabbatacce ba.....wani abu ne da bazai tabbata ba,sultane bazai taba
aikata hakan ba,ya fadi ne kawai don ya tsoratar da zuciyarta zuwa ga karkata ga
aikata abinda yakeso.
Haka kawai ya samu kansa cikin fargabar da baisan dalili
ba.......lokacin da ya dauka yana jiranta sai yaji ya masa tsaho. Sau daya tak ya
taba samun damar ganinta,amma kuma zuciyarsa ta jarabtu da sonta sau babu adadin da
baisan yawan da zai qayyade masa ba.
Sake juya qaramin littafin hannunsa yayi,yana karantawa ne kawai don
ragewa kansa lokaci,amma ba don yana fahimtar me yake karantawar ba,sai ya sake
budewa yana ci gaba da dubawa ko hakan zai taimaka masa ya sake rage yawan lokutan
data barshi a zaune.
Akwai wani yanayi a wajen wanda zata iya cewa baqo ne a idanunta.
Batasan wanne irin baqo bane yazo gurinta,amma babu wannan securities din masu
yawa......baqin fuskokin da suke alamta cewa dukkaninsu hadimai ne kuma ma'aikata
ga baqonta.
Mamaki ya sake cikata.....wanne irin baqo ne yazo gurinta?,wanda babu
wani kwarjini a tare dashi?,babu wannan haibar da cikar yawan adadin 'yan rakiyar
da suke nuna matsayin da yake dashi.
"Waye shi birra?" Ta tambayi birra dake biye da ita kai tsaye ba tare data waiwaya
ta dubeta ba,saidai ta xubawa qofar data rage da zata sadata da ainihin gurin da
kuma inda yake.
K'asa birra tayi da kanta,har cikin ranta tana jin fargabar sanar
mata wayeshi?. Ba iya yau ko jiya ba take tare da uwar dakinnata ba,tasan dukkan
wasu zabuka nata,tasan dukkan wani buri nata......ta kuma san wanne irin nau'in
miji take lissafi?.
"Ke nake saurara" Akhnan din ta fadi tana sake ragi karsashi tafiyarta,duk da dama
tana takawa ne da salon tafiyar nan tata me kama da tafiyar dawisu.
"Tilon d'a guda daya ga limamin babban masallacin juma'a na zinder........." Birra
ta fada cikin sanyin jiki. A sukwane ta waiwayo ta zubewa birra din wani irin
kallo. Dan limamin babban masallacin juma'a?......limami kuma?......ita khadeeja
sultane muhammad?,ita biftu?.....ita din mamallkiyar hamshaqin kamfanin da kaf
fadin africa babu yashi?......ita din diya tilo ga sultane muhammad?.
Abubuwa da yawa ne suke mata kai kawo,bayan tarin tulin tambayoyin da
take dasu,saidai kuma GIRMA wani abune dake yawo a jininta......hadimanta kuma har
kullum hadimanta ne,kusanci ko mu'amalar yau da gobe ba zata sauya wannan ba,don
haka birra ba abokiyar wannan maganar bace.......ba kuma huruminta bane.
"Ki jirani a nan" Ta furta tana juyawa a nutse da qasaitaccen takunta tana sanya
kai.
Tun daga nesa ta zuba masa idanu,cikin wannan salon nata da ba kasafai
kake iya karantar kai take kalla kai tsaye ba. Fuskarsa ta mata kama da fuskar data
taba gani,amma ta manta a ina?,wayeshi?,kasancewarta wadda bame shiga hada hadar
jama'a ba. Uwa uba dukka wani abu daya hada da maza a ciki bata sanya kanta cikin
sha'aninsu,saboda jin martabarta da izzarta.
A hankali ya rage kaifin kallon da yake mata yana kiran sunan Allah har
labbansa suna motsawa.
Da gaske.......kaman yadda ta tsaye masa a rai tun a gani guda daya
tak daya taba yi mata a zahiri muraran haka take. Yadda zuciyarsa ta shagaltu da
tunani da kuma imagination nata har abun yafi gaban haka a zahiri......da gaske
d'aya ce tak cikin mata.....duk kuwa da cewa ba ma'abocin kallon mata bane shi.
HAKEEM sunan yazo kanta dab da zata isa inda yake. D'a ga limamin
babban masallacin juma'a na zinder. Tabbas wannan shine wannan hakeem din,wannan
hakeem din da sultane suka taba ganawa da mahaifinsa a satin da zata bar agadez ta
koma Niamey don kula da kamfanin da sultane din ya mallaka mata sukutum.
Idan bata manta ba,wannan hakeem dindai shine wanda mahaifinsa ke
qorafin yaqi karatun boko.......wannan hakeem din shine dai wanda mahaifinsa ke
qorafin ya zabi karantarwa,yaqi amsar dukka wata harkar business ko fita qasashen
waje da mahaifinsa keyi sai qaninsa ya dora akai.....wannan hakeem din dai shine
taji mahaifinsa na dariya yana fadin ya gaza zabar matar aure,kamar tsoron mata
yakeji,ba kasafai yake tsaiwa da mace suyi doguwar magana ba......wannan hakeem din
da shine yaqi kasuwanci duka ya miqa ragamar kula da komai nasa ga
qaninsa.......wannan hakeem din da bai iya doguwar magana da French sai larabci
kawai da asalin yarensu na zinder yaren mahaifi da mahaifiyarsa.......wannan
lusarin HAKEEM din......wannan LUSARIN MIJIN shine sultane ya zaba mata?. Tana
zaune a wani gefe daban na dakin hutawar sultane tana jira ya sallami baqonsa yayi
mata signing din da zai mata taji dukka wadannan maganganun. Ta tabe baki tana
maida hankalinta ga takardun gabanta,cike da mamakin failure irin ta wannan mutum
da suke magana a kanshi cike da mamaki.
Ya shigo ya samesu a dakin hutawar.......maganganun da sukayi a kansa
ya sanya ya daga idanu sau daya tak ta kalleshi don taga wanne irin mara sanin
ciwon kaine wannan?,a sannan ta soma ganin fuskarsa. Tun a sannan taji baiyi mata
ba,bawai don akwai wani abu daya faru ba.....a'ah,sai iya tattaunawar da taji su
sultane sunayi a kansa,tun a sannan kuma ta laqaba masa sunan KASASHE a ranta.
Ya bace mata sam akai,don tun daga wancan ranar bata sake ma wani tuna
abinda ya danganceshi ba,sai a yanxun da ta kalli fuskarsa komai ya dawo mata.
Sake jagulewa ranta yayi,ta sanya hannunta a goshi ta dafe kadan,sannan
ta dauke yana yarfar da hannuwa,tana jin yadda gaba daya bacin rai ya cika nata
qirjints,har tana jin babu wani space daya rage. Bacin ranta ya sake ninkuwa sanda
take dubansa duba irin nakai tsayen nan ganin yadda ya gaza sanya idanunsa cikin
nata. Abune me wahala ta kalli namiji irin haka,amma baqo dai irin HAKEEM rashin
darajarsa ta zarta ta kowa a gurinta.
Tabbas tun daga sanda ta samu labarin morsa safiyya ta taka wata rawa a
zuwan baqonta na yau tayi imanin babu wani alkhairi ko abun arziqi a ciki. Ba wani
alkhairi kwata kwata da zaizo daga matar zuwa gareta,sharri ce ita!.......duk kuma
wani abu daya danganceta din sharri ne.
Qoqarin gyara mata kujerar da zata zauna yayi,amma zafin naman da
takeji yau a jikinta ya sanya ta rigashi aikata hakan
"Nasan za'a rina......daga yanayin gidan gaba daya jikina ya bani wani qasqantaccen
ne yazo gareni........ashe arahata har takai haka?" Ta qarasa maganar idanunta na
nuna zallar kaifin fushin dake cikin su,ta kuma dauki qafarta daya ta dorata saman
daya cikin wani yanayin zama dake nuna zallar izzarta da kuma izgili ga hakeem dake
zaune kawai yana dubanta ba tare daya motsa ba.
Idanunsa ya dan runtse,yaji zafin kalamanta,amma kuma tunawa da yayi
itadin macace me raunin hankali sai yayi qoqarin basarwa.
"Sallama ya kamata ki fara yi koda ba zamu gaisa ba ko gimbiya?". Manyan fararen
idanunta masu blue din qwayar idanu ta watsa masa,abinda ya sanya kwarjinin nan
dake tattare da ita ya ratsashi.
"Gaisuwa......ko sallama,dukkaninsu ana yinsu ne ga mutumin madaukaki me
daraja........wanne gangancinne yakai ka gabatar da qudurinka a kaina?......har ka
nemi ganawa dani?" Ta masa tambayar tana tsareshi da idanu kaman yadda uwa kewa
d'anta.
Murmushin qarfin hali ya saki a hankali. Ya sani,tunda har bada son
ranta bane,zai iya fuskantar kowanne qalubale da kuma turjiya kafin ya samo kanta.
"Qauna ce.....da kuma son kasancewa mijinki in sha Allah". Idanunta ta janye,wani
dariya data maida gurbinsa da murmushi ya subuce mata,abinda ya sake fidda zallar
ainihin kyanta,kyan daya daki zuciyar hakeem kai tsaye.
Sakanni kusan biyar sannan ta gyara zamanta tana zube masa idanunta.
"Kai yanzun a naka ganin akhnan ta dace da maqasqancin mutum irinka?" Ta furta da
wani irin kaifi a muryarta da idanunta,kamar ta bashi damar bata amsa ne,kafin kuma
ta sake cewa
".....Na yarda......cikin nau'in mutanen da sukafi kowa son zuciya......tsaurin ido
da kai kai inda Allah bai kaisu ba irinka ne.......mutanen dake iqirarin ilimin
sanin Allah da annabi.........maha'inta masu ci da addini........inaso ka
sani.......cikin nau'in mutanen da na tsana.......bazan kuma taba iya aurensu ba
koda NI DASU KADAI MUKA RAGE A DUNIYA sune gidadawan masu ci da addini da sanya
rawani a kansu da daukan litattafai da sunan su din malamai ne......"
Ba ita daya ba,hatta da badee'a ta fahimci karatun yana shigarta
sosai,don itama ta sake nutsuwa,ta kuma tattara dukkan hankalinta guri guda. Saidai
a sanda muryar akhnan da hakeem ta fara ratsowa inda suke sai dukka hankalinta ya
soma rarrabuwa gida biyu,da wani irin nauyi da kunyar yau kuma me zata ce da
hakeem?.......yauma yana jin abinda take furtawa ko kaman jiya ne?.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 62
A nutse ya sanya hannunsa ya maida bangon littafin ya rufeshi,bawai don
sun gama karatun ba ko kuma yakai inda ya kamata ya tsaya ba. Tun daga sanda ta
fara magana da hakeem yake gayawa zuciyarsa ba huruminsa bane........ba abinda ya
shafeshi bane,wani sha'ani ne da bai shafeshi ba.......bai kuma hada dashi ba
sam.......saidai kuma wani irin suka kalamanta suka fara yi suna sauka saman qahon
zuciyarsa daya bayan daya da wani irin kaifi,duk kuwa da cewa bada shi take
ba,batasan ma da wanzuwarsa a gurin ba.
Shuru gurin ya dauka,kaman yadda baiyi motsi ba haka ba wanda ya motsa
tsakanin ita da badee'a.
Ko ina jikin falaak rawa yake,takaici da tashin hankali yana cikata.
Koda baiyi kowanne motsi ba ta tabbatar a yadda gurin yayi shuru,dukkanin
maganganun da Akhnan taci gaba da jifan Hakeem dasu suna sauka yadda ya kamata
cikin kunnuwasa.
Shurunsa na nufin abubuwa da dama,ya dunqule hannunsa guri guda yana
jin zafin kalamanta tamkar shi take gayawa. Me hakeem yakeyi?,me hakeem yaci gaba
da tsaiwa yana yi har ta samu daman ci gaba da zuba masa wulaqantattun kalamai
haka?.
Mutum nutsatse irin hakeem din,wanda yake da quality din daya tabbatar
yafi nata duk da taqamar sarautar da takeyi?!. Har abada babu wata daraja ko
matsayi da zaiyi daidai dana mutumin da yake dauke da ilimin addini a
kwanyarsa!......me hakeem yakeyi?!. Ya sake tambayar kansa yana jin yadda jijiyar
kansa ta fara tashi,kowanne kafa na jikinsa ya soma fidda gumin da hakan yake bashi
tabbacin lallai ransa ya soma baci.
Baya jin zai iya ci gaba da zama a gurin kunnuwasa suna jin furucinta
da daidai yake da zagin kowanne mutum me kamanceceniya da hakeem din
"Subhanakallahumma wabi hamdik,ashahadu an la'ilaha illa ant,astagfiruka wa'a tubu
ilaik" Kawai ya rufe da ita yana qoqarin saisaita muryarsa da yakejin yanayin fitar
sautinta ya sauya,ya miqe a nutse yana sanya takalminsa,wanda yayi daidai da isowar
daya daga cikin hadiman me martaba.
"Sheikh......me martaba yace a shaida maka......yana buqatar ganinka idan an bashi
dama". Idanu yadan xuba masa yana mamakin fitar kalar furucin daga bakinsa. Ya
sani,ba yaren kowanne basarake bane hakan......ya nema izini daga wajen wanda yake
ganin yana rayuwa ne a qasansa,umarni na kai tsaye shi sukafi ganewa,amma shi din
izini yake nema ayi masa.
Wanne irin uba ne wannan da baiyi sa'ar diya ba?,wanne irin uba ne wannan
wanda sam bai fidda iri me kyau ba?.
Kai kawai ya gyada masa,yana jin daukewar sautukanta masu zafi,wanda
yake tunanin numfasawa ta tsaya yi,ko kuma ta kammala fadin dukka abinda yazo bakin
nata ne.
"Idan burinka ko mafarkinka shine aure na......ina me shaida maka.....ni Akhnan
nafi qarfinka har abada......zaka mutu kuma da wannan burin naka ne" Ta qarashe
maganar sanda ta miqe tsaye,sannan ta juya da dan hanzari tana takawa don barin
gurin.
A yadda takejin zuciyarta a sannan kuka kawai take da buqatar yi,banda
kukan ba wani abu daya kamaceta........saboda zafin da takeji a ranta ya zarta ta
iya cinyeshi kota hadiyeshi. Saidai kuma babbar faduwa ce a tare da ita wani daban
yaga hawayenta......wanin da ba sultane ko mammina ba......koda morsa sai ya zamana
dole ne take bari ta hangi fitar hawaye a fuskarta.
Tana ji a ranta a wannan karon itama a shirye take ta bijirewa umarnin
sultane,a shirye take tayi fito na fito da umarninsa....... Gwaraba tariyo mata
dukkan mazan da suka taba takowa domin nemanta......sultane ya zaba mata koma waye
a cikinsu akan hakeem .
Hakeem fa?,hakeem din da rana ta farko data fara saninsa a rayuwa tayi
masa laqabi da lusarin namiji.......hakeem din da bata tunanin ko digo qwara daya
yahau cikin kaso dari na kalar zabin da take dashi idan har ya zama dole ma sai ta
rayu da d'a namiji......hakeem din daya kasance malami,wanda baida kowanne irin
experience na rayuwa........baida kowacce irin gogewa a rayuwa,baisan ma me duniya
take ciki ba. Banda littafi rawani da zaman karantarwa ba wani abu daya sani.
Kai tsaye taji ba inda ya dace ta nufa sai gurin mammina.......ita
daya ce ita kadaice kuma fatanta,ta tabbatar zata cika mata alqawarin data dauka na
tsaiwa a gefanta da kuma tsaiwa a bayanta a duk sadda irin hakan ta faru.
*MAMMINA*
Ci gaba tayi da irgen mintuna daqiqu da kuma sakanni,tana jin ba wata
kujera cikin parlor din da zata iya dauke nauyin abinda ke saman ruhi da zuciyarta
ballantana ta zauna a kai. Wannan jiran ya zame mata wani irin jira na daban,irin
jiran da yake da tsaho da kuma tsauri duk da fata da take dashi cikakke da kuma
tarin yaqini.
Ta riga ta d'ana ta kuma dasa gami da harba komai......wanda abune me
wahalan gaske wadannan shingunan.....wadannan turakun dukkaninsu ace an shuresu.
Bakin window ta qarasa,ta saka hannu ta bude labule kamar wadda iskar
dakin ta sassanyar A.c ta yiwa kadan,batakai ga ajiye hannunta ba lafuzzan da take
faman jira suka sauka mata a kunnenta.
"Yalwa ce"
"Qaraso" Ta bata umarni kai tsaye ba tare da taji qarshen maganar tata ba.
Da hanzari ta baro bakin window din,ta kuma tako da dan hanzarin tana
zama hannun kujera,yayin da yalwa ta zube a qasa fuskarta da murmushi.
Iya murmushin fuskar yalwa ya isa ya gaya mata kalar
nasararta.......iya wannan murmushin kadai ya gama bata dukkanin amsar da
takeso,amma saidai tana buqatar taji ta kuma sake samun tabbaci daga bakin yalwa
din.
"Allah ya tayawa ayyukanki......komai ya tafi daidai......kamar dai kullum,kamar
kuma ko yaushe,shima dai ta tankwabar da tayinsa,ta kuma watsawa sultane qasa a
ido,don tozarcinsa yafi kowanne kalar tozarci da ta taba yiwa wani". Wata ajiyar
zuciya me nauyin gaske ta sauke wanda take