Showing 72001 words to 75000 words out of 168506 words
kuma maida idonta ta rufe ruf ba tare da tace da
kowa komai ba,tana shaqar lallausan qamshin kabbasar a hankali tana tattaro
nutsuwarta.
Ganin haka ya sanya aisa qyarawa Shehinaz,sai kawai suka miqe a nutse
suna ficewa a dakin gami da ja mata qofar kowa baice komai da ita ba.
★★ *HAISAM*★★
Daga yadda shirunsa ya kasance tun bayan sallama da yayi dasu khadeem
bayan ya jagorancesu sallar magariba sannan sukayi sallama suka wuce filin sauka da
tashi jiragen sama na Niamey din omari ya gama sanin an samu matsala.
Daga yanayin idanunsa kadai omari ya fahimci ranshi a tsananin bace
yake,wani irin mutum ne shi da sam ba kasafai ya fiya magana ba koda ba cikin fushi
yake ba ballantana yana cikin fushi. Yayi riqo sosai da hadith dinnan na ma'aiki S
A W da yayi hani da magana cikin fushi,idan kana tsaye kuma ka zauna. Zai iya
qayyade sau nawa ya taba ganinsa yana magana alhalin cikin fushi yake?.
A karo na barkatai omari ya sake dubansa. Ya sauya kayansa zuwa wasu
Indonesian kurta farare tas masu laushi,wadanda aka yiwa ado da gray color din
zare. Kanshi ba hula sai tattausan gashinsa dake a gyare tsaf.....kai bakace shine
wannan da yayi tsere awa biyu baya da suka wuce ba.
Jikinsa da lallausan turaren nan nasa ya zaunawa qamshinsa ne yake
fita a hankali da wani irin sanyi me kwantar da rai. Dan qaramin littafi ne a
hannunsa da tunda suka zauna a motar shi yake dubawa shafi shafi.
Wannan din na cikin dabi'arsa ta biyu. Indai ranshi yana a bace ba
abinda yake bashi peace da relief sai karatu. Yana iya gamawa da littafi guda idan
yana cikin fushin da baison a matsa masa yayi magana duk yawan mas hafin littafin.
Yaso qwarai kada yace masa komai kamar yadda aikinsa ya nuna buqatarsa
kenan,to amma kuma ya gaji da canki cankin ganin sun dauki hanya d'od'ar,su da suke
da ticket na jirgin da zai sauka agadez qarfe bakwai da rabi na safiyar washegari.
Bugu da qari driver din dake tuqasu a yanzu dan qasar ne,ba baqo bane irinsu
ballantana yayi tunanin bace hanya yayi.
"Amma fa.....kamar awa guda kawai ya ragewa jirginmu ya tashi.....kuma naga mp din
yana nuna mun dauki hanyar barin Niamey ne". Omari ya furta a nutse kaman bashi ba.
Sau tari fushin haisam baya bayyana muraran,amma su suna kalla suke ganewa.
Dukkaninsu suna shiga wani sabon hankali da sabuwar nutsuwar idan ran haisam ya
baci,bawai don zai gaya musu maganganu marasa dadi,ko zaiyi fada da dayansu
ba....aah.....sai don nauyinsa da sukeji da wani irin kwarjini da nutsuwa da Allah
ya bashi. Zai qalubalanceka ne idan buqatar hakan ta kama da wani irin nutsuwa da
hikima a kalamansa......zai kuma dafaka da ruwan jikinka idan baikai yace komai da
kai ba.
Ba tare daya dauke littafin a fuskarsa ba ko ya dubi omari ba ya amsa
masa.
"Buqatar tafiya a motar tafi ta tafiya a flight muhimmanci" Ya amsa a taqaice yana
buda shafin gaba na littafinsa.
Shuru omari yayi yana sake zuba masa idanu. Wato halin zai gwada masa a
aikace?.....shikam baya jurar wannan,bazai bari bama su shiga garin mutane da
basusan komai nasu ba da wannan halin da haisam ya yanke nuna masa.
"Amma dukka wannan shariyar ta mece?,da magana a cikinka mafi kyau ka fito ka
fadeta" Omari ya fada cikin nashi kalar iya rigimar yana hade rai da bata fuska
kaman shi akawa laifin.
Bai kalleshi ba,amma yadda yayi maganar kadai haisam yasan me yake
shirin yi,don haka yayi kaman baiji me yake cewa ba.
Bai magantun ba kuwa har sai da omari ya fidda rai zaice wani abu
din,sannan ya rufe littafin a nutse bayan ya saka alama ya ajjiyeshi daga gefansa.
"Me kakeso nace maka omari?.......ince maka ka kyauta daka hadani tsere da wadda
take ba muharramata ba?......ko ince maka kyauta daga sakani hada jiki da matar da
take haramun nayi mata koda zuzzurfan kallo ballanta jikkunanmu su hadu?.....ko
kuma nace maka ka kyauta data sanadinka d'iyar mutane ta kusa ransa lafiyarta ko
ranta?". Idanu omari ya fidda yana duban haisam.
"Me kake cewa ne?....." Hannu haisam ya daga masa calmly yana lumshe idanunsa gami
da budesu akansa.
"Karka musa akan komai.....zanta istigar......nasan Allah da zuciya yake
amfani......amma zamuyi aiki dakai ne omari a bisa sharuddan da idan ba zaka iya
kiyayesu ba.......zaka fita daga cikin deal dinnan......ina magana ne a matsayin
boss dinka....a yanzu...a wannan lokacin.......not your friend?" Ya qarashe da
sigar tambaya yana kallon idanun omari.
Idon haisam kadai ya gaya masa muhimmancin daya dauki aikin dashi. A
komai haisam me sauqin fahimta ne,me kuma bada uzuri ne banda akan aikinsa. Zaiyiwa
haisam uzuri sau million times idan har yanason hakan.....don yasan wayeshi a waje
a kuma bayan aikinsa.
"Yes sir" Omari ya fada da dukka girmamawa da seriousness.
★Yadda ta farka a firgice shi ya sanya aisa dake daura dankwalinta gaban
madubi tsorata itama. Sosai ta maida dubanta ga akhnan da farkawarta kenan a
baccin.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Zama tayi sosai cikin kujerar tana saka fuskarta a tafin hannunta ba
tare data damu da gyaran hargitsatsen gashin kanta ba.
Ajiyar zuciya aisa ta sauke tana maida hankalinta ga abinda takeyi
cikin madubin. Tsakanin jiya da yau mafarkinta na uku kenan. Mafarkin data gama
fahimtar ba akan komai bane sai akan abinda ya faru jiyan.
"Ya kamata ki sassautawa kanki haka,abinda ya faru ya riga ya faru,saidai kuma a
kiyaye gaba" Aisa ta fadi hankalinta kwance. Ko kadan batajin zatayi tarayya da
akhnan wajen tayata jin ciwon abinda ya faru da ita,komai daya farun tana
dangantashi da zallar rashin jin magana da shawarar irin nasu ita da Shehinaz. Inda
ta dauka shawararta,inda taji abinda ta fada mata for the first place ma da ba'azo
nan din ba.
"Na wuce office......na bayar da sanarwar baki da lafiya don kada office dinki ya
zama ba wani motsi......yana da kyau ki qwarara jikinki ki koma office dinki" Aisa
ta fada tana yin gaba gami da ficewa daga dakin.
Da fari hawaye take zubarwa,amma maganganun aisa sai suka sake saka
mata dafi a ranta. Da gaske ya cuceta ya tsaida komai nata. Walwalarta,nishadinta
dama ayyukanta. Hakan kuma bai isa ba,har cikin baccin da take samun salama shima
bai barta ba?. Wanne irin mutum ne shi?,wanne irin azzalumi ne?,anya ruhinta zai
samu salama kuwa idan bata rama abinda yayi mata ba?.
Kuka me qaramin sauti ta saki ta jawo pillow tana kwantar da kanta gami
da maida gashinta baya. Daidai sanda aisa ta dawo don ta manta tabar wayarta cikin
dakin.
Wani mamaki ne ya sauko ya lullubeta ganin kukan da akhnan keyi,kuma
ganinta bai sanyata ta dakatar da kukan ta ba. Bawai bata yin kuka
bane.....a'ah.....hasalima ita din irin mutanen nan ne da abun kuka baya masu
kadan,don ko a quruciyarsu a rana tayi kuka kadan tayi biyar zuwa bakwai,to amma
tunda ta zama cikakkiyar mace waye ma zai bata ranta ballantana ya sakata
kuka?.....ko na quruciyar ma da tayi ta yishi ne saboda yarinta da kuma dabi'a.
Ta manta rabon da taga akhnan din tana kuka,abun sai ya zame mata wani
baqon abu. Cikin zuciyarta ta sake tabbatarwa,tunda har hawaye ya zuba daga idanun
akhnan din lallai abun babba ne a zuciyarta.
Ta rasa yadda zatayi controlling dinta dole ta kira Shehinaz,saidai
ko ita dinma akhnan bata saurara ba. Zafin da takeji a zuciyarta tana jin bashi da
hanyar samun sassauci na farko irin su barta tayi kukan.
Mamaki yaqi barin aisa. Princess dinnan ta agadez?.....CEO ta sahel
couture guda ta zauna tana kuka akan wani abu da a wajenta baida wannan girman?,to
wai quruciya ce har yanzu a jikin akhnan ko kuma zallar radadi da k'i fadin ne yake
taba zuciyarta?.
Duk yadda suka dauki abun da sauqi ita da Shehinaz sai suka lura sama
da haka akhnan ta daukeshi. Wunin guda tana qunci,tsakanin aisa da Shehinaz dinma
daga qarshe ba wanda ya fita office din.
*8:00 pm*
Yadda sultanate ya zubawa wayar idanu yana kallon abinda ke wakana haka
itama morsa safiyya ta kafeshi da kaifafan idanunta tana kallon kowanne reaction
nasa a duk gilmawar video din.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 36
___________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*
*Assalamualaikum*
*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*
*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*👘🥻
*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin
Aminci???*
*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*
*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana
✌🏽
goma KACAL! *
*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*
*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*🙌🏽
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*
*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*
*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT
da yardar Allah*
+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791
https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________
"Na shiga uku!" Ta furta a fili tana cusa yatsunta cikin gashin kanta
dake hargitse tana maidashi baya. Ita kanta a yanzun data kalli gurin,ta kuma
sakashi a mizanin hasashen gata ga sultane suke kalla......mene zai iya faruwa?".
"Biftu......Calme-toi! Uhmnn(ki kwantar da hankalinki uhmm)"
"Shehinaz......sultane ne fa da kanshi ya kirani......bana ji a jikina lafiya ko
dadi ne suka sa hakan......kira da kuma umarni dukka na kai tsaye?" Tayi maganar
idanunta na nuna tabata da abun yayi.
"Détends-toi!,(ki nutsu),Qu'est-ce qu'il a dit exactement?(me yace miki?)" Numfashi
taja sosai,tana son tsoron da takeji yana task masa ya narke da kansa,a nutse ta
motsa labbanta.
"Kome da nake na bari,alhamis tayimin a agadez,akwai abu me muhimmanci a ranar
juma'a". Shuru shehinaz tayi,ita kanta tasan lallai tabbas akwai wani magana a
qasa,banda hakan sultane bai taba yi musu ko yiwa akhnan zabin ranar zuwanta agadez
ko ranar barinta ba.
"Calme-toi,il ne va rien se passer,khairan in sha Allah(ki kwantar da
hankalinki......babu abinda zai faru,khairan in sha Allah". Shehinaz ta fada tana
sake son gamsar da akhnan din cewa ba wani abu din bane.
*_AGADEZ_*
Batayi ajiyar komai cikin ranta ba saboda samun tabbacin ta kafawa sultane
qusar da zai wahala akhnan ta cireta.....zai wahala wannan karon tarin soyayyar da
yake mata......tarin qauna da riritawar yayi tasirin kasa daukar matakin daya dace
cikin rayuwarta.
Don haka hankali kwance ta isa farfajiyar da takan zauna a duk yammaci
irin wannan. Kusan idan tayi irin wannan zaman,zama ne na musamman saboda al'ummar
agadez......takan zauna ne don sauraren koken al'umma,wanda asma'u mataimakiyarta
ta musamman data ajiye saboda sauraren koke da damuwar jama'ar masarautar dama na
wajenta.
Buqatu na mutane birjik da damuwoyinsu data maida nata. Cikin
kudinta,cikin arziqin da Allah ya hore mata. Sam bata taba gajiyawa ko kuma kasawa
ba koda sau daya.
Kunnuwanta suna kan asama'u dake lissafosu daki daki,yayin da take
matsa carbin hannunta a nutse zuciyarta kuma tayi nisa karanta "subhanallahi wabi
hamdihi,subhanallahil azeem" (Kalmomi ne da Allah yake sonsu,suke kuma nauyaya
ma'aunin aikin bayi ranar awon ayyuka).
Muryar aeera ta jiyo daga inda take ita da Aafreen,kafin daga bisani ta
hangi falaak na tahowa,hannunta dauke da qur'anin Aafreen.
Jikin momma aeera ta fada tana bata labarin ta haddace karatunta na jiya
har an qara mata wani. Murmushin momma ta saki,a duk sanda ta gansu suna tafiya ko
dawowa daga daukan karatun,tana jin wani nutsuwa gami da aminci har qasan
ranta,tana jin wani kwanciyar hankali yana saukar mata.
"Momma.....malam yace yana buqatar magana dake idan an masa izini". Aafreen ta fada
tana zama kan daya daga cikin tuntum din da aka qawata wajen dashi saboda hutawa.
Sai data kalli falaak ta gyada mata kai alamun haka ne,sannan ta dakatar da
asama'u.
"Ayi masa iso" Tace da asama'u tana gyara zamanta gami da sake lullube ilahirin
jikinta da kyau.
Cikin qasa da mintuna goma ya bayyana a wajen. Cikin shigar manyan kaya
na wani tattausan yadi babbar riga da 'yar ciki. Akwai kamala da nutsuwa sosai tare
dashi,shekarunsa na haihuwa zasu kai aqalla arba'in da biyar zuwa da takwas.
Cikin karramawa tasa aka tarbeshi,kafin su fara magana.
"Da dadewa na cike foam na ummul_quraa a madeena......shekara guda kenan sai wannan
satin Allah yayi na samu sanarwar samun gurbin karatu acan din,wannan dalilin ya
sanya nace bari na sanar miki.....ina me bada haquri mun fara karatu da yara kuma
zai yanke". Sosai momma taji zuwan maganar a wani abu na ba zata,har cikin ranta
taji sam labarin bai mata dadi ba,to amma ci gaba ne ya samu malam Ousmane haris
din,koda akan kanta ne ko yaranta kuma hakan zata kalleshi a abun alkhairi.
"Ma sha Allah malam.....na tayaka murna sosai.....ci gaba ne da qaruwa ai,ba kuma
akanmu kawai ba.....har qasarmu gaba daya,Allah yasa albarka".
"Ameen,godiya nake".
"Ma sha Allah.....in sha Allahu zan aika da tawa gudunmawar tafiyar". Murmushi ya
danyi
"To Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen ameen......saidai kuma wani hanzari ba gudu ba......karatun yaran nan,banaso
ya tsaya malam......don Allah idan ba damuwa.....ko zaka duban wani amintacce cikin
amintattunka?". Shuru kadan yayi na wasu daqiqu kafin ya nisa.
"Mutum daya ne na amince dashi,nasan kuma zai iya fiye ma da abinda zanyi,don
iliminsa ya zarga nawa nesa ba kusa ba.....saidai kuma shi din mutum ne me wuyar
sha'ani,hasalima bani da tabbas din zaiyi,kinga kuwa baima kamata na bada sunansa
ba". Tashin farko momma taji maganganun malam Ousmane haris ya zauna a ranta,karon
farko kuma hankalinta taji ya zauna daidai kan wanda taji yana yiwa yabon da kuma
tabbacin samun karatu sama da wanda shi yake bawa yaran.
"Don Allah malam.....ko za'a roqa mana ALFARMARSA?......ko nawa ne zan
biyashi......ya daure yaci gaba da dukan nauyin karatun yarannan". Shuru malam
Ousmane haris yayi,kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya.
" Abinda za'a biyashi ba shine damuwar ba,ku din da yaran,na tabbatar sai ya saka
ya kuma kafa musu wasu qa'idoji da dokoki muddin zai daukesu karatu,ban sani ba ko
zaku iya jure hakan Allah ya taimakeki". Qaramin murmushi momma ta saki tana
daidaita zamanta.
"Banda abun malam Ousmane......ai nafison irin wannan tsarin koyarwar......kuma ina
son mu'amala da irin wadannan mutanen,don nasan cewa komai nasu in sha Allah zai
zamana a nutse ne bisa tsari......wannan aikin za'a yimin malam.....ya fadi duka
tsare tsarensa.....in sha Allah zasu kiyaye". Qasa malam Ousmane haris yayi da
kansa. Yana jin nauyin matar qwarai,saboda tarin alkhairanta da sanin ya kamata da
take dashi.
"In sha Allah komai zai zo da sauqi".
"Momma" Falaak ta kirata sanda take shirin maida hankalinta ga asama'u bayan sun
kammala da Ousmane haris. Duban falaak din tayi,ta bata fuska sosai
"Gani nakeyi ba malamin da zaizo da yafi malam iya koyarwa.....na dauka zaki hana
mishi tafiyar ne saboda karatunmu". Murmushi kadan momma tayi,sai ta ajiye takardar
da asama'u ta miqa mata zata duba tana kallon falaak din.
"Bakisan duk me hankali yana mu'amalantar malami tamkar sarki ba saboda girman
qur'ani da tarin alfamar littatafan da suke kanshi ba......abune da bai dace ba
kayi karantsaye cikin al'umaransu ba........suna da daraja da martaba sama da wadda
sarakuna da masu mulki suke da ita......baka da hurumin amfani da qarfin iko ko na
mulkinka na sanyasu yin abinda basuji amincinsa a zuciyarsu ba.....tsakaninka dasu
biyayya girmamawa da tausasawa". Kai falaak ke gyadawa tana sake samum gamsuwa da
dukka bayanan momma din.
Ita din shaida ce,taga wasu irin mabanbantan dabi'u masu kyau da
nagarta gami da burgewa tattare da malam Ousmane haris da bata zaci akwai sauran
mutane dake da wannan dattakon da kamalar ba har haka. Mutum daya ta sani
haka....SULTANE dinsu.
(08187255862 luu luu paying)
★Cikin nutsuwar nan tasa wadda ta zame masa tambari yake takawa a hankali
zuwa saman stairs na gidan. Abdii omari da kuma addisaleem suke biye dashi a baya.
Omari ne a bayansa....abdii a bayan omari,sai addisaleem dake biye dasu a baya
cikin matuqar girmamawa.
A nutse yake duban saman,wanda ke dauke da wani irin qawataccen parlor
na zamani. Yalwatacce da aka yiwa wani irin tsarin gini aka kuma zuba masa
furniture masu wani irin mahaukacin tsada da daukan hankali. Kai ya jinjina a
hankali,komai na gidan yayi masa,tsarinsa da komai nasa. Idan iya qasan gidan ka
zauna ba zakayi tsammanin zaka taras da wani qawataccen upstairs da yakai kyau
tsari da haduwar wannan ba. Ba zakayi zaton samun aljanna duniya irin wannan a
upstairs din ba sam,haka ya tsara.....kuma haka yaso tsarin gidan ya kasance.
"Ta wanne bangare kuka ajiye library din gidan?" Yayi tambayar yana zubewa abdii
idanunshi. Qaramar dariya omari ya saki yana takawa gami da zubewa cikin lausasan
qawatattun sofas din da aka qawata parlorn dashi 'yan asalin qasar china hand
crafted da suka qawatu qwarai da gaske.
"Ka nuna masa