Showing 15001 words to 18000 words out of 168506 words
ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da
kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi
https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba
da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin
iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi
bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________
*_MORSA SAFIYYA_*
Tun a parlor din qarshe da yake mazaunin shinge na qarshe da zai
kaika ga turakar sultane morsa safiyya ta samu tabbacin sultane yana ciki. Sai a
sannan ta tuna wannan lokacin wani kebantaccen lokaci ne a gareshi kowacce rana ta
duniya,wani kebantaccen lokaci da yakan zauna yayi wasu addu'o'i har zuwa wasu
awanni kafin ya tashi.
Ba bata lokaci ta murda handle na qofar dakin tana tura kanta ciki gami
da sallama.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ya amsa sallamar cikin wata nutsuwa da tarin
kwarjinin daya kasa tsaida morsa safiyya ko ya hana bayyanuwar bacin ran daya riga
yayi tasiri saman fuskarta.
Cikakken ba'abzine ma'abocin tsaho da qibar da za'a iya kiranta da
sunan murjewar jiki kawai. Sanye da jallabiyya 'yar qasar Morocco wadda tadansha
banbam da sauran jallabiyya da aka saba gani,saboda bayan zubin dinkin morocco da
akayi mata,kana dubanta zakasan farashinta na musamman ne saboda qasaitattun mutane
irin me martana sultane muhammad hammud din.
Shigowarta bai sanyashi ya fasa shimfida lausassar fara dardumarshi
ba,duk da hakan bai hanashi ganin tasirin fushin data shigo dashi ba.
Wani lokacin yana ganin SAFEENA a tare da ita........saidai ba
safeenan bace. Akwai tarin abubuwa da banbamce bambance daya saka tazara ya kuma
shata layi tsakaninta da safeena din. Yayin da wasu gamayyar halaye da jini kar
d'arsa tsakanin mutanen da JINI ya zama sanadiyyar amsa sunan DAN UWA yake
haifarwa. A qasaice ta samu kanta da takawa,tana kuma sake tsuke fuskarta wajen
qoqarin bayyanar da dukka fushinta. A wannan lokacin a wannan karon bata jin zata
iya......bata jin zata iya kauda fuska tayi kamar komai faru ba......batajin zata
qaryata feelings dinta da abinda ke tasowa tun daga qasan maqoshint har zuwa saman
harshenta.
"Barka da yammaci" Ta furta muryarta a cushe guri daya.
Da zuzzurfan kallon nan nasa ya bita,kallon da tabbas ta jishi har
cikin jininta,to amma ba zata yarda ta kallo kwarjantattun qwayar idanun nan nasa
dake hana mutum duk wani motsi da yayi niyya ko ya kamata yayi ba.
Muryar safeena ce..........amma safiyya ce tayi magana.......kamannin
safeena ne amma kuma dabi'un na safiyya ne........safiyyan ce dai,da wannan sautin
da wannan fusataccen yanayin nata daya tabbatar ba zaa kwashe lafiya ba a duk sanda
ta shigo dashi. A nutse yake qare mata kallo,yana son tuna kwanakin daya dauka bai
sanyata cikin idanunshi ba.
"Barkanki......kina lafiya?".
"Magana nazo muyi dakai" Ta fadi kanta tsaye ba tare data tsaya damuwa da amsa
tambayar lafiyarta da yayi ba,hannuwanta kuma goye a qirjinta,yayin data kauda
kanta wani sashe na daban ba tare data yarda ta kalleshi ba.
Kai ya jinjina,ta iya rigima da gasken gaske,irin rigimar da idan ta
farata sai abinda hali yayi. Wata irin birkitacciya ce ita idan bataso
ba,birkicewar da shi kansa a wasu lokutan yake kasa gaza shawo kanta.
"Allah yasa maganarki bata shafi khadeejatu ba?" Ya furta maganae da qwarin gwiwar
da fushinta bai karya shi ko kassarashi ba ko kadan.
Har batasan sanda ta sauke hannayenta da sauri ba ta kuma maida
fuskarta zuwa sashen da yake........yanayin sautinsa kawai ya tabbatar mata da
gaske indai akan khadeejatu ne ba wani magana da zata tasirantu a ransa?.....kamar
ma launin sautin nasa yana gaya mata tabar batun kan khadeeja karta sakoshi.
"Saboda idan a kanta ne baka da lokacin da zaka saurari safiyya?......saboda idan a
kanta ne baka da sauran wani qwarin gwiwar jagoranci?" Tayi masa tambayoyin a jere
tana zube masa kyawawan idanuwan nan nata da shekaru basuyi nasarar jirkitasu ba
sam,idanun da yake hango tsantsar kamanninsu dana biftu dinsa(akhnan),idanun da sau
tari kallon cikinsu suke sanyashi dagewa morsa safiyya qafa,saboda akwai wasu tarin
kamanni masu daraja a cikinsu.
Qaramar cushion chair dake daura dashi me wani irin yanayi dake nuna
alfarmarta ya jawo ya zauna akai cike da wani irin tarin nutsuwa,ya sake zuba mata
dukka idanunsa yana kallon ta na wasu daqiqu kafin yace.
"Ba duka abinda kika lissafa bane.........ina nufin hakanne kawai don har yanzu ba
wani abu guda daya da khadeejatu tayi wanda ya sabawa addini".
"Al'ada fa?" Ta sake tambayarsa a zafafe,duk da yadda idanunsa ke mata kwarjini
sukeson dakusar da kaifin fushinta.
Sake tsareta yayi da kallo kafin ya dage kafadunsa biyu.
"Har a al'adar ma banajin ba daidai bane"
"Koda gudun aure ne?,da kore duk namijin da yazo da buqatar aurenta komai
cancantarsa?" Tayi maganar a karo na biyu cike da qwarin gwiwar jin ta riqi hujjar
da a yau zata dankwafar da duk wani dalili da sultane ke iya bayarwa don samarwa da
akhnan din kariya.
Dif din da yayi da yadda yaci gaba da kallonta kawai ba tare da yace
komai ba ya soma bata hope........ya soma bata fata akan sultane,ya kuma soma bata
yaqinin a wannan karon saita balla wannan shingen.......wannan iyakar don gano
ainihin meye a shirye a bayanta?.
Ga mamakinta murmushi sultane ya saki yana dan lumshe manyan
idanunshi da akhnan tayi gado,ya dora hannunsa ya shafi tattausar sumarsa ta asalin
abzinawa sannan ya maida bayansa ya jinginar da kujerar.
"Shin musulunci ya haramta bawa diya mace daman zabar miji ne?.......ko ya haramta
zabar mijin da zaiyi daidai da daraja da martabar mace?".
Sak tayi kawai tana dubanshi.......wani bacin rai sabo yana sake taso
mata gami da qara ninkuwa a ranta.
To ta ina sultane muhammad hammud ya cika sarki.......gwarzo kuma jarumi
me wata irin madaukakiyar daraja a suna kawai bare akai ga nagarta........amma
tabbas a nan FADUWARSA take........tarannan da akace dan adam yake bai cika goma
ba.......anan tashi rashin cikar take.
Zuciya dama gangar jikinta gaba daya sukayi rauni. Yana kima ta miji a
gurinta......yana da martaba ta shugaba a cikin qasarsa......yana da daraja ta
shekaru daya bata. Dukka wadannan suna bidar gurbinsu a gurinta......dukkansu suna
bidar muhallinsu a dukka kalamai da aikinta......amma kuma hakan yana nufin tayi
shuru ta bari ayita yin abinda take jin ba daidai bane?. Hakan na nufin ta zuba
idanu BAKI yana yawa akan abinda tayi imani shi kadai zai fita kusa dashi?,hakan
yana nufin ta bada dama komai yaci gaba da wanzuwa a bahaguwar hanya?. Kowa ma
yasan ba daidai bane ga WANDA yasan daidai.....wake da qarfin gyarawa cikin wadanda
ke hangen rashin daidai din SAMA DA ITA?.
"Wannan shine alqawarin?......wannan shine tabbacin.....wannan shine
alwashin......wannan shine cika buri wa gawar SAFEENA?" ta fada da wata irin murya
data daki sultane a tsakiyar kansa.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel" Ya furta yana watsa yatsuntsa saman fuskarsa kamar
wanda ke gudun ganin wani abu.
"Safiyya!" Ya kira sunanta da wani irin yanayi yana sauke hannunsa daga saman
fuskarsa. Duban da yayi mata daya ta karanci launin idanunsa dana fuskarsa ya
sauya........hakan takeso,ta taba wani guri dake zuciyarsa........ko hakan zai
sanya yayi abinda ya dace?.
"Me kikeso?" Ya sake tambayarta kai tsaye.
"Ka kira biftu.......kayi mata fada irin fadan da kowanne uba zai yiwa
'yarsa.......ka datse wannan halayyar.........ka kawo qarshen wannan wasan,Coupe le
jeu.......ka tsaida wasan da takeyi da rayuwarta dama dukka
damarmakinta.......wasan da nayi imani da yaqinin wulwulata akayi a tsakiyarsa ba
tare data ankare ba.......ban yarda da zaitun ba......bazan taba kuma amint......."
Da sauri ya daga mata hannu
"Ça suffit!(ya isa!)" Tsaf ta tsareshi da kallonta......ba abinda ya kawo wannan
dakatarwar ta gaggawa sai kiran sunan mammina a ciki da tayi.
"Kada ki dauki zunubi......kada ki dauki alhaki akan abinda baki da hujja......me
kikeso?" Yayi maganar muryarsa na sanyaya,sam ba zakace sarki muhammad hammud
dinnan bane me yawa kwarjini.
*_AKHNAN_*
A hankali mammina ta bude baki da zummar sake magana,amma taba qofar
parlor din data kasance ta glass ta katseta. Dukkaninsu suka maida dubansu ga
qofar,kafin muryar barra'u ta ratso ta tsakanin curtains din.
"Ayimin afuwa ranki ya dade keda gimbiya......" Duk da barra'u ta katse musu
magangunu masu muhimmanci da sukeyi,amma saita saita muryar ta da yanayinta tace
mata.
"Fadi abinda yake tafe dake".
"Me martaba sultane ne yake son Gimbiya yanzu yanzu a shiyyarsa". Ba mammina
ba.....hatta da akhnan maganar ta bata mamaki.
Abune me wahala sultane yayi aike takanas a irin wannan lokacin......ya
buqaci ganin akhnan,ganin ma kuma ita kadai?,duk da suna kebewa sosai a lokutta da
dama suyi hira irin na tsakanin 'ya da uba,amma yanayin wannan kiran yasha banban
da kowanne. Kai mammina ta gyada.
"Saqonsa ya iso,tana tafe" Ta amsawa barra'u wadda amsar mammina ta sakata matsawa
tabar gurin.
Dubanta ta maido kan akhnan,wadda ta jima tana kallon mammina kamar tana
neman sanin dalilin kiran da sultane din yake musu ta saman fuskarta.
"Anya ba wani abu matar can taje ta gayawa sultane ba?" Akhnan tayi maganar da wani
yanayi da zai tabbatar maka jikinta ya bata akwai wani abu daya faru.
"Ita din uwa take a wajenki.....kada ki munana mata zato.....tashi ki amsa kiran
sultane". Kai akhnan ta shiga girgizawa.
"Babu inda zani saida ke mammina........banajin qwarin gwiwar tunkarar sultane a
yau ni kadai".
Duk yadda taso ta kwatantawa akhnan bata fahimta din ba,har sai data
aminta suka miqe tare akhnan din na riqe da yatsun mammina cikin nata.
Cikin qasa da second biyu yanayin fuskarta ya sauya yana sake gauraya da
wani irin bacin rai. A kowanne motsi kuma a kowanne taku mammina ba zata taba qyale
biftu ba?.....a kowanne taqi na rayuwa ba zata taba barin komai nata ya wanzu shi
kadai ba?. Wannan kawai ya isa ya bata amsar cewa.......rayuwar biftu din tana
cikin wata da'ira ne da ake sarrafa mata ita ga zaton ita ke sarrafa kayarta.
Morsa safiyya itace mutum ta farko da idanun akhnan suka sauka a kanta.
Ta janye blue eyes dinta da bacin rai ya sanya suka sake shanyewa tana maida
dubanta ga sultane dake zaune saman lallausar dardumarsa yana jan carbi.
Tasha kwatanta inama ace morsa safiyyan wata mutum ce ta daban,ba irin
mutanen da ko yaushe mammina da sultane ke jaddada mata girman kowanne lamari daya
shafeta bane?......ba shakka da hakan zata kasance sunanta shine a sahun farko
cikin jerin sunayen mutanen da zata furzar dasu daga rayuwarta.
Daidai da bugawar daqiqa guda......wannan dangantakar ta UWA da
aketa kiranta tsakaninta da morsa safiyya bata taba jinta ba,hasalima inda zatace
wani qin jininta takeji sosai yana disa saman zuciyarta a kowanne motsi to batayi
qarya ba.
Tamkar bata ganta zaune a wajen ba,ta taka cikin wata irin nutsuwa da
izzar sarautar dake yawo a jininta ta sanya ta zauna mata,take kuma qara mata kyau
da haiba matuqa,ta qarasa gaban sultane a nutse ta sulale tana duqawa saman
qafafunta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
✍🏽
*HUGUMANKU CE*
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 07
__________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500
dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da
kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi
https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba
da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin
iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi
bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________
Duk da kasancewarsa mahaifinta.......mahaifin da tafi kusa dashi akan
kowanne d'a namiji.......akan kowacce halitta ma dake duniya,to amma ita dinma bai
fasa yi mata kwarjini ba. Wannan kwarjinin da kowanne talaka dake rayuwa
qarqashinsa yake ganinsa......yake dukansa itama takanji haka game dashi lokuta da
dama.
"Barka da warhaka sultane" Ta fadi har yanzu kanta yana qasa
"Barkanki dai biftu.....ina fatan kin wuni lafiya?" Ya fada cikin tsananin nuna
kulawa da kuma tausasa harshe. Yanayin daya sanya wani abu ya tsayawa morsa safiyya
dake duban akhnan a wuya......duba na bacib ran yadda ta dauketa. A lokuta da
dama,a yanayi irin wannan.......tanayin abubuwan da a kullum take sake sauke
darajarta ne daga idanun mammina. Daya daga cikin wasu abubuwa data
tsana.......bata da matsayin da har yau akhnan zata gaidata sai bisa umarnin
sultane ko ita kanta mammina.
Bata jin zafi idan sultane ne ya sanyata.......amma tana jin tsananin
quna idan umarnin gaidata ya zama ya fito ne daga bakin mammina.
"Ranka ya dade barka da yammaci" Mammina data qaraso ciki ta fada a hankali tana me
zamewa saman lallausar dardumar dake shimfide a dakin,da wani irin zama dake nuna
zallar ban girma,tamkar irin zaman da bayinsa keyi a gabansa. Idanunshi ya dago
yana dubanta
"Barkanki zaituna.......fatan kin yini lafiya?" Wani murmushi ta aje tana gyara
zamanta sosai sannan a ladabce ta sake magana.
"Lpy alhmdlh......hakan kuma ya sake tabbatuwa a kanmu sakamakon naka wunin cikin
aminci da qoshin lafiya" Kai ya jinjina a hankali,qaramin murmushi yana subuce
masa wanda ya bayyana har saman labbansa.
"Ma sha Allah......ya kacaniyar jama'a".
"Har mun kaika ne ma Allah shi tayawa mulkinka?,kai ya kamata a yiwa wannan
tambayar" Ta qarashe maganar tana sakin murmushi. Dole Shima ya maida mata sannan
ya amsa.
"Alhamdulillahi bisa taimako da jagorancin ubangiji".
" Ma sha Allah,Allah ya qara lafiya ya qara taya maka"
"Allahumma ameen" Ya amsa a taqaice yana aza idanunsa akan akhnan
"Ga mommanki nan" Sultane ya fadi yana dan duban morsa safiyya sannna ya maida
dubansa ga akhnan.
"Barka da yammaci" Akhnan din ta fadi ba tare data daga idanunta ko tayi wani abu
da zai nuna morsa safiyya take gaidawa ba. Cikin tsananin juriya da shanye abubuwa
kaman yadda ta saba ta hadiye wani abu,muryarta can qasa kuma a shaqe ta amsa mata
"Barka" Daga hakan sai wani irin kakkaifan shuru ya gifta,kafin sautin muryar
akhanan ta sake motsasu
"Papi(kamar yadda wasu lokuta take kiransa idan tana buqatar UBA da zasuyi
magana),na samu saqon kira daga gareka,ina fata ya kasance lafiya?" Murmushi kadan
ya saki,ya ajiye tasbahar hannunsa yana sake bada hankalinsa a kanta.
"Khadeejatu"
"Na'am papi" Ta amsa tana sake yin qasa sosai da kanta.
"Altaab yazo dan sarki nu'uman haka ne?" Kai ta jinjina
"Yazo papi"
"Kun gama ganawa?" Ya jefa tambayar kai tsaye.
"Mun gama,har ma ina tunanin zuwa yanzu yayi nesa da masarautar AGADEZ".
"Ma sha Allah.....yayi miki?,kina jin zaki iya zama dashi kiyi masa biyayya a
matsayin mijin da zai kaiki aljanna?". Sultane muhammad hammud ya fada yana ci gaba
da nazartarta.
Shuru ya ratsa na daqiqa daya zuwa biyun da basu haura biyar
ba......daqiqar data wuce da bugun zukatan morsa da mammina........zukatan dake
kwance qirazan da suke da mabanbantan burika da hasashe dukka akan AKHNAN din.
"Baiyimin ba papi......na kuma bayyana masa sannan na sallameshi" Ta fadi kanta
tsaye cikin gwada daya daga cikin dabi'unta na fadin gaskiya kai tsaye ba tare da
wani qumbiya qumbiya ko ado ba.
Shuru ya danyi yana wani nazari. Nazarin da yafi karkata kan rashin
haramci cikin abinda ta aikata. Aure zama ne na mutum biyu da dukkaninsu suka
aminta zasu rayu da juna har zuwa mutuwa.......ba wata yarjejeniya bace ta
taqaitaccen lokaci.....ko kuma taron da zaa yishi tsakanin wasu awanni a gama a
watse ba.
"Shikenan.......Allah ya tabbatar da abinda yafi alkhairi". Maganarsa ta qarshe da
tayi daidai da saukar wani nannauyan abu a kunnuwa da zuciyar morsa
safiyya......kalaman
"Ameen ameen" Da suka fito daga bakin mammina kuma suka sake gwamutsa tunaninta
daga wani yanayi zuwa wani bigire na daban.
"Zan iya tafiya idan an yarjemin?" Akhnan ta furta cikin neman izini.
"Mommanki nason yin magana dake itama" Ya fadi yana mata nuni da morsa safiyya.
"Da d'iyata kadai nakeson nayi magana