Showing 153001 words to 156000 words out of 168506 words

Chapter 52 - luu luu Book1 by Huguma

Babban abinda yake bashi mamaki shine,ta yadda kowacce qofa yazo zai
wuce da hanzari suke janye masa ya ratsa ya wuce abinsa,wanda a binciken da yayi
iyalin sarki ne kadai.ko 'ya'yan cikinsa ko wanda yake da mugun kusanci dashi ya
isa ya ratsa wadannan qofofin kansa tsaye,va tare da wata zazzafar tuhuma ba,har
kuma ya tsinci kansa kyakyawar harabar da yake takawa a yanxu,wanda tafi zubu da
makadeden tsakar gida na alfarma,wanda daga nan yake iya hango kyakyawar balcony
din dake lullube da shuke shuke,balcony din da ita zata sadaka kai tsaye da qofar
makadeden parlor din me martaba.

Guri ne da muddin ka iskoshi baka buqatar iso game martaba,dukka
shingen daka tsallaka ka wuce suka baka daman isowa ga nan din sun gama
tantanceka,don haka kai tsaye ya dinga takawa yana nufar balcony din.

Sanye yake da wata jubah me sulbi kalan gray color kalar data haska
ta kuma fidda tsananin kyan fatarsa na asalin qabilar oromo me hasken kala data
dara ta sauran asalin qabilar. Daga wuyan jubah jallabiyyar da hannuwanta wasu irin
maballai ne masu tsananin kyau da daukan hankali.

Kansa kuwa hiram ne me kyau daya masa wani irin nadi da mafi yawan
matasan larabawa 'yan birni keyi masa,shi ba yafashi yayi ba,amma yafi shigen kama
da daurin dankwali da aka saki jelarsa ta baya,wata kuma ya sauko da ita kafadar
hagunsa.

Tattausan unique scent dinnan nasa ke fita,iska tana kadashi gami da
kwasarsa tana watsashi sassanni daban daban na sashen me martaba dama
kewayensa,qamshin da yakan jimma manne a guri bar tafi ba,yakan dauki kwana uku ma
musamman idan har haisam ya zauna a gurin ne na wasu awanni.

Qafarsa wani lafiyayyen farin takalmin fata ne,wanda ya dace da
torches din jikin amama din kanshi(hirami) da kalarsa ta kasance gray da torches na
white. Koda sau daya ka aza idanu a kansa lallai zai burgeka,komai nasa yana nuna
tsantsar ilimin addini daya cakuda da wayewa ta fannin sanin duniya da abinda ke
cikinta. Wata irin wayayyar siffa ce dake kwance cikin duk wani motsinsa,wadda ta
cakuda da tasirin addini da wani iri kamala da kwarjini da alqur'ani yake zubawa
dan adam.

Can qasan maqoshinsa yayi bismillah a sanda yake dora qafarsa saman
step din farki na balcony din,bismillah din da adams apple dinsa ne kawai ya
motsa,wanda ya fito sosai daga saman maqoshinsa kaman idan ka sanya hannu zaka iya
ciroshi.

Manyan idanun nan nashi da shigowar dare ya sanya suka rusuna kadan
ya ware a hankali,yana duban mutumin da baya iya ganin fuskarsa sai faffadan
bayansa,yana maqale sosai da wani irin salon tsaiwa jikin tafkeken window din dake
kai iskar tsirrai me sanyi dake busawa a gurin zuwa cikin ainihin parlor din.

Kaman yadda ci gaba da takawan da yakeyi bai hanashi ci gaba da kallon
bayan mutumin ba......wanda da ganinsa basai an gaya maka ba qaqqarfa
ne......hakanan takunsa bai dauke hankalinsa ko na mutumin daga tsaiwar da yakeyi
ba. Qasan takalminsa yana da laushi kaman yadda saman takalmin keda laushi,wannan
ya sanya hankalinsa ya gaza daukowa don da alama bayajin kowanne irin sauti,sai
sake maqalewa da yakeyi jikin window din sosai,da alama akwai abinda yake tsananin
buqatar yaji,abun kuma daya kasance me muhimmanci qwarai da gaske a tare dashi.

Sannu a hankali mamaki ya soma wanzuwa qasan zuciyar haisam,ya kuma
katse duk wani nazari da yakewa katangun dake kewaye da sassan sultane din ya
maidashi kacokam kan mutumin.

Wani zuzzurfan kallo ya masa guda daya daya dasa masa wani qaqqarfan
zargi me girma a zuciyarsa game da mutumin da ko fuskarsa bai samu daman gani
ba,bai kuma yarda yayi wani motsin da zai alamta masa tahowarsa ba,har sai daya isa
saitin qofar parlor din,ya soma zame takalmin qafarsa ta hanyar yin amfani da
dunduniyar daya qafar sannan ya saki wata taqaitacciyar gyaran murya mara amon
sauti idanunsa kafe akan mutumin.

"Waaqa!(god!)" Ya fadi a razane sanda yake waiwayowa da hanzari cike da mamakin
wanzuwar wani dan adam a gurin bayanshi.

"OROMIA?" Haisam ya furta can qasan ransa cike da zallar mamakin jin fitar yaren
oromo daga bakin mutumin,mamakin da ya gaza boyuwa ya wanzu saman fuskarsa dama
idanunsa,ya kuma kafe TAMIM da kallo duk da a lokacin bai kamata cikin tsarin
aikinsa yayi hakan ba.
Idanunsa ya maida ga goshin tamim dake tsatstsafar da zufa,abinda ya
sanya tamim wanda shima ya zubawa haisam idanu kai hannunsa ga goshinsa,ya kuma
shafo gumin yana dubansa hannunsa.

Idanunsa ya sake maidawa kan fuskar haisam,zuciyarsa cike da wani irin
madaukakin mamaki da kuma tarin tambayoyin

"Waye wannan?......waye shi?,yaushe ya wanzu cikin masarautar agadez?,a wanne
lokaci ya samu matsayi irin wannan?,matsayin ketawa ta sassan sultane kanshi
tsaye?. Ba dan rakiya?,ba iso?,ba tsarewa daga gurin masu tsaron sassan?.

So yake yaci gaba da kallon idanun haisam ko zai iya karanta ko
sansano wani abu tattare dashi,amma wani irin kaifi da kwarjini dake fita daga
idanun haisam din sun danne nashi. Kasa jurar ci gaba da kallon fararen manyan
idanun haisam din yayi,sai ya janye nasa,yana maidasu wani sashen cikin Tsananin
mamakin jin wani baqon abu tattare dashi.

A hankali haisam ya janye dubansa daga kan tamim din,ya tura sliding
door din falon,abinda ya sanya tamim samun daman waiwayawa yana kallon haisam din a
sanda ya fara takawa yana barin farfajiyar cikin jin wannan nauyin yana zartawa
yana son murqushe zuciyarsa da duk wani karsashi nasa. Tashi guda kuma yana jin
wani irin nauyi da wani abu me kama da tsoro yana son lullubeshi.


"Bappi....." Akhnan ta kira sunan sultane din da wani irin rauni daya cika
muryarta,raunin da sultane din kadai ta yarda ya ganshi,raunin da bata taba yarda
ta bayyanashi gaban kowa idan ba sultane din ko mammina ba.

"Bappi.......kayi haquri,kayimin alfarma bappi,ka janye maganan nan,bazan iya auren
hakeem ba......ka yafemin bappi na roqeka" Ta fadi da sanyin da sai daya daki
zuciyar sultane din,saboda abune da ya jima shi kansa bai ganshi ba a tattare da
ita,saidai kuma tunawa da yayi cewa wani gatan zai sake yiwa rayuwarta,sai ya
gayyato wannan jarumtar tasa ya aza saman ranshi. Wani kallo ya aje mata me
nauyi,kallon daya soma ratsa duk wani jini dake yawo a jikinta da wani irin sarewa
da lamarin sultane,kallon daya bata tabbacin yin nasararta abune me matuqar wahalar
gaske.....hasashen daya kusa tarwatsa mata kwanya saboda razani,tayi qasa da kanta
cikin jiran tsammani,abinda ya sanya lullubin saman kanta ya hadu da sassalkar
sumar nan da tsananin kulawar da take samu ya maidata me sulbi,ya zame daga saman
kanta zuw kafadunta.

Saidai kafin shi ko akhnan wani a cikinsu ya sake cewa komai amon
muryarsa ya gauraya a parlor din.

Cikin muryar nan tasa dake da wani irin zurfi da kuma amo ya yi
cikakkiyar sallamar dake nuna yasan haqqinta yasan kuma cikakken ladan da ma'abota
cika sallama suke samu.

"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Sultane ya maida martanin sallamar fuskarsa tana
washewa da wata kwantacciyar fara'a,abinda ya d'arsa wani babban abu saman zuciyar
mammina,tana kuma jin nauyin sautin muryar haisam har saman zuciyarta.

Waye wannan daya samu nasarar gusar da fusata da bacin rai daga zuciyar
sultane da sallamarsa kadai?. Kaman sultane yasan me take tattaunawa da
zuciyarta,cikin nutsuwa da girmamawa yace.

"Bismillah sheikh muhammad........kai da falon mahaifinka?".

" Mahaifi?" Mammina ta maimaita kalmar can qasan zuciyarta,tana kuma jinjina girma
da nauyinta. Wannan kalmar da wannan furucin na sultane ya sanya zuciyarta cikin
zaquwa da son sanin waye wannan?,abinda yaja hankalinta kenan ta zubawa qofar
shigowa idanu don ganin bayyanarsa.

Cike da wannan cikakkiyar kamalar wadda ta cakuda da kaifin kwarjini
da haibar jinin sarautar OROMIA dake jininsa ya sanya qafafunsa cikin parlor da
cikakken nutsuwar nan tasa. Karon farko idanun mammina suka sauka a kansa,wata irin
matsananciyar faduwar gaba ta saukar mata ba tare da tasan dalilinta ba.

Dukka idanunta ta zuba masa sanda yake ketowa cikin gurin,tana jin
wani irin yanayi da batasan wanne iri bane yana ratsa jikinta har zuwa cikin
b'argonta a hankali,kamar wadda ake fifitawa iska tsakiyar sanyin hunturu.

Kallonta ta maida kan sultane wanda ya miqe yana fadada fara'arshi.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)


"Barka da zuwa sheikh......ga guri zauna na qarasa ganawa da me dakina" Ya fadi
yana yiwa haisam din nuni da mazaunin dake daura dashi.

Iska ta sake shaqa a karo na uku tana jin kamar kwanyarta ta fara
birkicewa,kaman komai ya soma dagule mata,kai kaman hauka ne ma yakeson kama ta?,ko
kuma depression ne yake mata sallama?. Banda haka ta yaya?.....ta yaya a irin
wannan lokacin?,a daidai lokacin da take tsaka da gwabza yaqin neman sauko da
sultane daga kujerar naqin da yahau,kuma sannan a lokacinne wai hancinta zai dinga
dauko wannan ajiyayyen qamshin yana kawo mata kusada hancinta?.....shin da wanne
zataji?,da qoqarin soke auren hakeem a kanta ko kuma case din wancan mutumin?.

Mutumin da tun daga wancan ranar zuwa yau bata sake lafiyayyen bacci ba
ita kadai?,mutumin da tun daga wancan ranar zuwa yau bata taba kwanciya ta tashi
lafiya qalau ba tare da taga gilmawar wadannan idanun masu wani irin magnet cikin
baccinta ba?,wannan idanun da take zargin ta sake ganinsu ko ganin irinsu a wancan
ranar,a ranar data kawo kanta wajen sultane.

Kamshin wani irin ajiyayyen abune da kwanyarta da zuciyarta ta yiwa
mugun ajiyar da koda cikin baccinta zata shaqeshi ta tabbatar saita farka,komai
nisa ko nauyin baccin,koda zata manta komai daya shafi wancan ranar,ba shakka ba
zata taba manta wadannan abubuwan biyu ne WADANNAN IDANUN da kuma WANNAN QAMSHIN da
har yanzu ta kasa samar da irinsa domin hujja.

To ta yaya ma zata mance dasu?,bayan yana cikin manyan burikanta?. Bata da
buri a yanzu days wuce zaqulo SHI. Wannan baqon da yaso tozartata ya tozarta
nasararta da ajiyayyen tarihinta name tabbatacciyar nasara?. Muddin ta barshi ko ta
haqura ko kuma ta manta ita din bata cika HALASTACCIYAR DIYAR SULTANE MUHAMMAD
HAMMUD BA.

Sam ko kusa ko alama bai lura da ita ba,har sai zuwa sanda ya tako da
zummar zama inda sultane din yayi masa tayin zaman.

Kanta yana qasa,abinda ya sanya wannan kyakkyawar sumar me kyau da
daukan hankali bayyana sosai fiye da fuskarta. A hankali kuma cikin ba zata
idanunsa sauka saman sumar tata,ya janye qwayoyin idon nasa da wani irin sauri yana
canza direction dinsa zuwa wata shiyyar ta daban. Wani irin abune ya tsarga masa
tun daga saman kansa zuwa tafin qafafunsa.

"Subhanallah" Ya fadi can qasan maqoshinsa,adams apples dinsa suna yin sama da qasa
duka lokaci daya.

Gashin mace yana daya daga cikin al'aura a jikin mace,zai iya cewa
tsahon girmansa bazaice ga randa yaga wani sashe na jikin mace haka ba,don hatta
dasu Anani suna da doka a kansu kai tsaye daga gareshi,bai yarda dayin kowacce
shiga da sukaga dama ba muddin ba'a cikin dakinsu bane,don haka zaiyi wuya ka
samesu kansu a waje ko wani sashen jikinsu muddin ba'a dakinsu suke ba.

"Bismillah muhammad.......nan dukka na gida ne,kaima kuma ka zama dan gida......ga
mamarka nan zaituna........ga qanwarka kuma babbar diyata khadeeja akhnan".

Sosai ta zuqi qamshin da qarshen harafin sunanta da sultane ya
furta. Sake cika gurin da qamshin da yakeyi da kuma yadda wani ya samu darajar da
zai shigo a sanda take ganawa da mahaifinta,har kuma sultane ya ajiye komai......ya
tsaidata ya kuma tsaida uzurinta da hanzarinta,ya tsaya saurarensa da dukka
girmamawarsa.......daga qarshe ya dinga hada dangantaka tsakaninta dashi,irin
dangantakar ma ta YAYA da QANWARSA.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*


PAGE 77
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________




Dukka wadannan tunane tunanen suka harzuqata,ta daga fusatattun idanunta
da taketa qoqarin controlling fushinta da bacin ranta da zummae saukewa koma waye
wulaqantaccen kallon da zai sanya ya fahimci iya darajarsa,saidai kuma a sanda
idanunta suka fada saman fuskarsa da take yau full opened......suka sauka kan
wadannan kewayayyun idanun da suka shiga rayuwarta,suka kuma shiga dukka mafarkanta
sukayi kane kane,sai dukkan komai ya kwance mata.

Wani irin lallausan murmushi ya sakewa sultane daya qara masa haiba,ya
canza gurin zaman daya tabbatar zai sake nesantashi da ganin wani sashe na surar
gashinta,yana qoqarin maida idanunsa kan wayarsa dake hannunsa wadda tayi blinking
har sau biyu,alamun shigowar saqonni a jere.

"Allah yasa buqatata bata takura ka ba". Miskilin murmushin nan daya qarawa
idanunsa wani irin sheqi ya saki,ya motsa labban nan nasa dake wani irin glowing su
kadai,saika zargi ma ya shafa musu lip gloss ne.

"Gayyata irin wannan girmamawa ce sultane........"

"Bappi......zanfi son ka kirani da sunan,don sunan da diyoyina ke kirana dashi
kenan" Ya qarasa fada yana maida dubansa kan akhnan.

Da qyar ta jefa hannunta baya ta jawo mayafinta,cike da tsammani da kuma
yaqinin haisam din zai maido dubansa kanta,saidai a maimakon hakan kai ya jinjinawa
sultane kawai ya maida wadannan idanun mash kaifi da nauyi saman wayarsa yana
qoqarin sanya ta a silent yana kuma furta

"Barka da dare".

"Barka kade yarona......ya qoqari?,Allah ya dafa ya saka da mafificin alkhairi"

"Ameen ameen" Ya sake fadi cikin girmamawa.

"Ammm.......mammina ga muhammad nan,sabon d'anmu,kuma malaminsu falaak dake
daukansu darasi duk yammaci" Sultane ya fada yana duba mammina din.

Wani irin numfashi ta fusgo,kafin kuma ta biya ta hado da aron murmushi
daga wani loko can na zuciyarta,kafin kuma a nutse ta saci kallon yanayin zamansa
da kuma saqar jubah din dake jikinsa,ta kuma dora da.

"Barka da warhaka sheikh,muna maka maraba da shigowa cikin da'irar ahalin
sultane,haqiqa lallai ka taki babbar sa'a da har ka samu matsayin D'A sukutum daga
sultane.......kinga daga yau biftu kin samu dan uwa ko?". Murmushin farinciki
sultane ya saki,yana jin haisam kamar da gaske d'ansa ne har cikin jininsa.
Ido haisam din ya lumshe tare da budesu lokaci guda yana dan jinjina
kai. Sautinta da yadda karin harshenta ke fita yake qoqarin harhadawa cikin kansa.
Wani irin accent yakeji daga bakinta daban,accent din da yake ji daga bakinta kamar
ya banbanta da sauran harsuna da yaji sunyi magana cikin agadez.

Idanunsa ya daga a hankali ya sauke kan mammina,wani kallo qwaya daya
amma da aka yishi da tarin manufofin dake dauke da harsashe me zurfi.

Idanunta ta lumshe tana qoqarin daidaita wancan qamshin a
hippodrome......wannan qamshin a ranar da ya saketa ta kusa faduwa kusa da dakin
hutawar sultane......da kuma wannan lokacin a yanzu da qamshin ya mamaye ko ina da
wani irin yanayi da taji yana harbawa har saman kanta yana kuna sake dawo mata da
ranarsu ta hippodrome data yiwa laqabi da BAQAR RANA. Ranar da har ta koma ga
mahaliccinta bata jin zata bace a kwanyarta.

A nutse mammina taci gaba da satar kallonsa qasa qasa,kowanne abu a
jikinta daka iya bata signal akan komai yana motsa mata gami da ajiye mata wasu
baqin yanayi a jikinta. Ba tambayar dake neman dakusar da nutsuwarta irin son sanin
WAYE SHI?. Duk da cewa kunnuwanta sun jiye mata kuma kwanyarta ta ajiye mata batun
MALAMINSU FALAAK ne. Sai takejin kamar sultane na zolayarsu ne......sai takejin
kamar sultane na son tsokanarsu ko gwada hankalinsu ne. Ta aminta zai iya zama
malaminne,saboda wani irin haske da ajiyayyen kwarjini da take hanga tattare
dashi,amma ko da malaminne bawai malaminsu falaak ba,yafi kama da qasaitaccen
malamin da gata da hutu suka huda jikinsa. Yaushe ma ya shigo masarautar amma bata
samu labari ba?,yaushe ya soma rayuwa cikin ta ita bata taba sani ba?......hakan
yana nufin tayi sakaci kenan?,hakan yana nuna akwai sauran qofofi data bari a bude
wanda bata toshesu ta hanyar zuba masu bata masaniya ta wannan qofar ba.

"Akwai sauran gyaran daya ragemin" Ta fadawa kanta,tana jin bata da sukuni har sai
tasan wayeshi. A tsarinta cikin lokaci me muhimmanci da tsada cikin rayuwarta irin
wannan,bata buqatar baqon abu cikin masarautar agadez,mace ko namiji,yaro ko
babba,don dukkan wani wanda yake rayuwa cikin masarautar tana da dukkan wani
bayanansa,na rayuwa hali dabi'u yanayin aiki da sauransu,samun qarin wasu baqin zai
zame mata kamar maida hannun agogonga baya ne.

Nutsuwa ko sau daya bata kusanceta ba,ta kwantar da wadannan idanun nata
sosai tana qoqarin karantarsa a duk wani motsi nasa,cikin salon da ba kowa bane zai
karanci haka kai tsaye. Saidai kuma cikin jikinsa yake jin akwai wani unusual kallo
dake fita daga wani bangaren na dakin zuwa jikinsa. Bai motsa ba amma jikinsa ya
gaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login