Showing 120001 words to 123000 words out of 168506 words
daren jiya bai kammala ba,ya bude ya fara dubawa a nutse,wannna ya sanya
kusan duka abinda ke faruwa cikin masallacin bai sani ba.
Rufe littafin yayi a hankali sanda yaji alamun fara daidaita sahun
sallah,ya miqe a nutse yana gyara cloak robe dinsa.
Satar kallonshu Maher yayi,har qasan zuciyarsa burgeshi haisam yake
sakeyi. Yayi imanin inda wani ne Allah ya bashi mulki kudi da qarfin iko irin
haka,bazai taba aiki da hukumar national intelligence ba,saidai su suyi masa aiki.
Inda wani ne....bazai taba yarda a jashi ko a jagoranceshi sallah ba......saidai
shi yaja. Yana da tarin ilimin da iya zamansu na kwanakin nan Maher ya fahimta.
Baya daukan kansa da nisa,shi yasa da yawa wadanda ke tare dashi basusan irin
ilimin da Allah ya hore masa ba.
Ranar daya fahimci yarukan da yakeji ya jima yana juya abun. Tabbas
rayuwa kowa da irin nashi nasibin. Ya iya French ya iya English,ga amheric ga oromo
ga larabci,sai hausa da bata kama bakinsa sosai ba,don bashi da sabga me yawa da
ita. Bai bari ya gane yasan ya iya duka yarukan ba,don ya fahimci kamar yana
sirranta hakanne.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 60
"Salamu alaikum" Yaji sautin sallama daga gefan damansa. Idanunsa da suka
rusuna kadan ya daga yana dubansa na wasu sakanni sanda yake sakar masa
murmushi,shima sanye cikin cloak robe da zaunennan rawanin da kana dubanshi kasan
qwararru ne suka zauna suka masa wani nadin burgewa saman kansa.
"HAKEEM" Sunan yazo kansa lokaci guda,sai yayi qoqarin daidaita fuskarsa yana rage
mata daurewar da take dashi tun a dazun,daidai sanda hakeem din ke qoqarin masa
bayanin yana tunanin bai ganeshi bane,don ya fahimci kadan daga halayensa na rashin
son shiga sabgogin da basu shafeshi ba,saidai shikam ya jima yana burgeshi,tun daga
wancan ranar a Riyad har yau ya kasa mancewa da fuskar sheikh din.
Musabaha sukayi da juna,haisam ya zame hannunsa,don babu dogon magana
kasancewar an fara tayar da iqama.
Cikin mintuna bakwai suka kammala sallar. Hakeem na gefansa bai
tashi ba yana nashi azkar din na bayan sallah.
Ya gane hakeem,a wata musabaqa da suka gabatar a Riyad akan wasu
kebantattun litattafan addini daga dukkan qasashen duniya. Kwanaki uku sukayi a
wani kebantaccen hotel,wanda kusan duka haisam dinne ya dauki nauyin komai,amma
kasancewarsa mutum wanda baison asan yayi wani aiki na alkhairi gudun shigar riya
ayyukansa,sai bai bada dama ga kowa yasan shi ya dauki nauyin komai ba.
Hakeem yana daya daga cikin wadanda suka tsaya takara......a lokacin
haisam ya shiga sahun alqalai na gasar. Tabbas a lokacin yaga matuqar qoqarin
hakeem,ya kuma yaba sosai da irin hazaqarsa da yadda ya iya fadin kowacce amsar
tambaya daga masu tambayar,duk da daga qarshe ya samu zuwa na biyu ne maimakon na
daya,saidai a wajen yin jawabinsa abun ya qayatar da haisam,har ya sanyashi yadan
murmusa kadan. Yadda Hakeem din ya bayyana shigarsa qasar kawai nasara ce basai an
ayyanashi ba,ya kuma miqa kyautarsa da girmamawarsa dukka ga mahaifinsa,ya kuma
ware guda daya yana sake karbar abun magana.
"Inaso a bani dama na miqa wannan kyautar guda daya data rage,zuwa ga wani mutum
daya da daga yau nakejin ya zamemin wani abun kwaikwayo koda daga nan ba zamu sake
haduwa ba SHEIKH MUHAMMAD HAISAM" Iya sunan da haisam din yayi amfani kawai dashi
kenan,gudun bayyanuwar identity dinsa. Yana jin dadi idan ya shiga guri yayi
mu'amalolinsa da rayuwarsa cikin privacy ba tare da an fahimci waye shi ba. A
rayuwa yana jin ba kowanne lokaci bane......ba kuma a kowanne guri bane ya kamata
asan wayeshi ba. Wannan kyautar ta Hakeem taxo masa a bazata,saidai abinda yayi
masan bazai manta dashi ba.
Sosai Hakeem yaso karbar number haisam,saidai hadimansa basu bawa
hakeem wannan damar ba,sun rabu yana yawan tuna haisam din,har yau daya ganshi
cikin ba zata.
Sanda haisam ya kammala addu'o'insa ya shafa a nutse,hakeem ya sake
miqa masa hannu cikin sakakkiyar fuskar nan tasa,cikin tataccen larabci ya soma
magana da haisam din,don bazai iya tantance wanne yare yakeji ba,kasancewar ko a
wancan lokacin da larabci sukayi dukka kwanakinsu da mu'amalolinsu.
"Naji dadin sake ganinka sheikh.......ban tsammaci ganinka a agadez qasarmu ba,da
nasan kana kusa damu da na jima da nemanka" Murmushi yadan saki masa,baisan me ya
hada jininsu haka da hakeem din ba.
"Nazo ne ganawa da d'iyar sultane,amma ban sani ba ko zan iya samun damar sake
ganinka?" A nutse haisam ya daga kanshi.
"Indai baiyi sama da mintuna arba'in ba"
"In sha Allah zan qoqarta na kammala a qasa da hakan"
*AKHNAN*
A zaune take daga gaban dressing mirror din saman stool cikin shigar
atamfa embellished holland golden sea blue da ratsin blue black. Wani irin colors
ne a jikin atamfda masu wani irin daukan hankali da suka dace da kalar fatarta na
cikakkiyar buzuwa. Wannan fatar dake da wani irin glowing da sparkle masu daukan
hankali dake nuna zallar kulawa da hutu gami da jin dadi da cikakken sukunin rayuwa
da take samu.
Wani irin dinki ne na buba akayi mata,kusan zata iya cewa karon farko
da zata iya tuna ta sanya atamfa a rayuwarta,don itakam tafi ganewa ready made gown
da exclusive abayas,sai designers materials da take bada umarnin zaba mata dinkuna
ta hannun LAARA dake kula da closet dinta tana bincika me ya kamata a zuba mata,me
kuma ya kamata a cire. Dinkuna dari uku da sittin da biyar duka shekara,domin kuwa
sau daya tak take sanya kaya,bata kuma sake maimaita sakasu saidai a sakasu a kayan
bayarwa. Shadda kam tana dasu,su dimma bawai sakasu takeyi ba,don kwata kwata iya
adadin sanyawarta da shadda zata iya qididdige lokutan.
Ko wannan atamfar ma laara ce ta dinkota,ta kuma bawa birra ta gabatar
mata da ita,tana ganin zata dace da shigar ta ta yau.
Ba wannan bane a kanta a yau,don tana kallon lamarin baqonta na yau
shine zai zame mata matsalar qarshe,kuma namiji na qarshe da zata sake bari ya samu
daman ganin xagayen fuskarta da furucin bakinta da tsadarsa yafi qarfin kowanne
namiji ya jishi.
Dinkin ya zauna mata a jiki sosai,ya kuma sake fidda sigar
kyanta,qirar jikinta da kuma qara mata wani irin zaunennan kwarjini. Shehnaz na
kallonta tana sake gasgata da gaske suturar bahaushe na daya daga cikin suturu da
tufafin dake qarawa mutum kyau da kuma kwarjini.
Birra ke taje mata doguwar sumarta tana kuma shafeta da tsadaddun mayukan
da take kula dasu,saidai duk wannan abun da yake faruwa hankalinta ba'a nan yake
ba.
Idanu hankali tunaninta dama nutsuwarta gaba daya ta azasu saman ipad
din data kafeta saman dressing table din da yake gabanta. Wannan wasan
dai......wannan tseren na Hippodrome Niamey shi take bi da kallo cikin kowanne
gilmawar second.
Har a yau har kuma a kwanan gobe bata da nutsuwa akan faruwar abun.
Tunda abun ya faru har zuwa yanxun yana jin sunan MARASA NASARA yana bibiyarta a
duk harbawar daqiqa,bata jin kuma zata samu nutsuwar har sai ranar data lalubo WAYE
SHI?....Har sai ranar data san meye manufarsa?,me yasa ya zabi ya shirya wasan,ya
qirqireshi,ya kuma gabatar dashi?.
Meye dalilin bata mata LAMBARTA da ita kadai keda mallakinta tsahon
shekaru?,me ya yiwa thunder data kasa controlling dinsa?,har dai shine yayi
controlling dokin da kaf cikin dawakanta tafi ji dashi?,dokin da suke communicating
ita dashi da tsananin sabo tamkar dan adam?.
A hankali aisa ta tura qofar tana shigowa da sallama,saidai shehnaz
kadai dake kwance rub da ciki saman gado ce ta amsa,don akhnan din ko motsawa
batayi ba bare tayi yunqurin amsawar. Abinda ya ja hankalin aisa din,ta taka a
nutse zuwa inda take,sai tayi tsaye a bayanta tana duban abinda take kalla,wanda
clip din yazo daidai inda take fadowa ya kuma tallafeta da hannunsa guda daya.
Ita da aisa din lokaci guda hannuwansu yakai kan ipad din,kaman aisan
tasan niyyar akhnan nayin wurgi da ipad din ta samu nasarar rigata dauketa tana
kasheta ta wurgawa shehnaz ita.
Idanunta ta aza kan akhnan,duk wani mode nata yana nuna fushi da
bacin rai,wanda aisa din takejin sam baima dace ta doshi baqonta a haka ba. Muddin
haka zata kasance komai zai iya faruwa.....kunyar da dukka aka tattaru ana fatan
kada yau a jita zai wahala ba'a shata ba.
"Meye amfanin kallon abinda ya riga ya faru......banda yiwa kai tanadin bacin rai?"
Aisa ta furta tana duban akhnan da fuskarta tayi wani irin kyau tsakanin surfanin
dake wuyan atamfar bayan gama daure mata gashin da birra tayi.
Hannu ta sanya tana ture dankwalin da birra ta aza mata a kai da nufin
daura mata,ta dubi aisa din tana juyo da kujerar gaba daya tana fuskantarta.
"Kina zaton wannan tarihin zai tafi ne a banza?......kina tsammanin xan qyaleshi
ne?,yayimin abinda,ya kuma bace ba tare da yabar wani alama ko guda da zata bayyana
wayeshi din ba......kina zaton duka hakan ya faru ne bada wani shiri ko manufa
ba?......na rantse saina laluboshi a duk inda ya shiga......na kuma rantse sai na
sanyashi ya kwashi kashinsa a hannu......diyar SULTANE MUHAMMAD HAMMUD NAKE FA".
Idanu aisa ta janye a hankali tana sauke ajiyar zuciya. A yau ne ta sake yadda da
akhnan din baudadden halinta na halitta ne......kafiyarta kuma a jininta take,bata
tunanin akwai wani yanayi ko wani dan adam da zai iya canzata
"Est-ce que c'est la seule chose qui vous dΓ©range?(wannan ce kadai damuwarki?" Ta
tambayeta tana riqe da qugunta tana dubanta.
Sai data daga fararen idanunta masu surkin blue ta watsawa aisa,sannan
a nutse itama tace
"Est-ce qu'il y a autre chose?(akwai wani abunne daban?)" Idanu aisa ta bita
dashi,ta fuskanci da gaske idan ta biye mata zasuyi rigima ne,sai taja tsaki kawai
tana matsawa inda shehnaz ke kwance.
Harara ta watsawa shehnaz din tana dubanta.
"Ba wani sauran abinda zakiyi ne?" Ta furta cikin gatse,don ta fuskanci wani lokaci
plan din akhnan yana zuwa daidai dana shehnaz.
"Ques veux-tu que je fasse?(me kikeso nayi?)" Ta fada cikin rashin ko in kula. Ta
sani,ita ko aisa basu isa canza ra'ayin akhnan ba.
Mayafinta ta zara wanda birra ta ajiyeshi daga gefe da nufin idan ta
kammala shiryata ta bata tayi amfani dashi. Lullubawa tayi kawai saman kanta ba
tare data damu da d'aura dankwali ba ta soma takawa tana fita a dakin,sai su dukka
suka bita da kallo cike da mamaki.
*FALAAK*
Wata baquwar dabi'a ce a tare da ita,damuwa da duba kowanne lungu da saqo
na fuskarta tanason tantancewa ko akwai wani abu daban da bai kamata ta fita dashi
ba?. Ko akwai wani abu da baiyi a fuska ko kuma jikinta ba?.
Ita kanta batasan hakan yana faruwa da ita ba,har sai da taji
dariyar badee'a.
Cak ta tsaya daga goga lipstick din da takeyi tana duban badi'a din.
"Lafiya?" Ta fadi a mamakance. Kai badee'a ta girgiza tana dubanta.
"Bansanki da irin wadannan sanaben ba uwar dakina......yau din da kikeyi sai abun
yake bani dariya da mamaki". A hankali ta maida dubanta ga lipstick din
hannunta,wanda ba wani color gareshi ba,sai ta maidashi saman madubin a hankali
tana ajiyeshi.
"Dama kin qarasa,yayi miki kyau sosai" Badee'a ta fada tana duban ta. Kai falaak ta
girgiza tana daukar wayarta dake gefe.
"Muje badee'a" Ta fadi tana jin wani fargaba da bugun zuciya yana qaruwar mata. Tun
daga safiyar yau take lissafin adadin awannin da ya rage su shiga karatu,a duk
sanda daqiqa daya ta ragu kuma sai ta samu kanta cikin wani matsanancin harbawar
gudun zuciya.
Sai takejin kamar me tsoron haduwa dashi,tsoron kuma daya cakuda da
zumudin zuwan awannin haduwar. Ta sani,zallar kwarjininsa ne yake dukan idanu da
zuciyarta,wanda batasan dalilin hakan ba,kwarjinin da har a jiya data kwanta tana
wassafashi ne cikin idanunta.
Tayi karatun addini daidai gwargwado hannun malamai kala kala a
france sanda take hannun hairaan. Kusan kuma dukkaninsu babu dan africa,amma
yanayin da takeji a yanxu bata taba jin makamancinsa ba.
Bata samu morsa ba,an shaida mata tana ganawa da baqi,wannan ya sanya
kai tsaye suka wuce ita da badee'a wadda ke dauke da wasu daga cikin litattafan da
yace zasu sauya,duk da ba duka aka samo ba. Wasu babu su a kasuwa,har sawa morsa
tayi aje a duba amma an tabbatar mata babu su,sai nan gaba za'a shigo dasu daga
misra.
A nutse yake takowa cikin gurin bayan Maher ya juya tun daga shingen
qarshe. Wanda hakan umarni ne daga haisam din,bawai don ba za'a bar maher din ya
shigo ba.
Wannan qasaitaccen qamshin da a jiya ya sanyata laluben kalar turaruka
da dama ko zata samu wanda qamshinsa yayi daidai dashi shi ya fara marabtarta,shine
kuma ya shaida mata wanzuwarsa a gurin,sai ta daga kai tana jin wata irin fargaba
qwayar idanunta qasa qasa tana dubansa,kafin ta zame idanun nata can qasa daga
barin kallonsa gudun kada ya ganta,sai takalman da suke qafarsa kawai take iya
kalla.
Idanu ta zubawa takalmin tana son tuna wani abu. Tsahon wasu sakanni
sannan ta tuna. Irin takalmin sak da morsa ta taba siyawa me martaba cikin kayan
gift da takan hada masa a duk shekara na barka da sallah. Kudi ne masu nauyi da har
falaak ta dinga cewa.
"Sultane dan gatan morsa,Allah sarki ni auta falaak,morsa nan na kawo na dubu dari
biyar kikace yayi tsada da yawa,ni din macace da zanje gidan wani,ba lallai komai
na samu a gidanmu ba na sameshi a gidan mijina......amma ga sultane da
takalmin......" Daquwa morsa ta watsa mata tana jifanta da harara,saita saki
dariya,ta dauki takalmin kawai tana juyashi,don sosai ya tafi da ita.
Idanunta ta janye a hankali tana laluben fuskarsa,kallon fuskar daya sake
tsananta bugun zuciyarta. Wani washewa fuskar tasa tayi sosai cikin lullubin da
yakanyi ya suturta habatsa har zuwa karan hancinsa,wanda hakan ba kasafai yake bada
daman ganin fuskarsa gaba daya ba. Fuskarsa ta yalwata da sakewar da ba zaka kirata
murmushi ba,yana riqe hannun Aeeda sarkin saurin sabo da mutane,wadda kuma ko sau
daya mutum yayi mata me rabata dashi dai Allah. Aeeda irin yaran nan ne masu shiga
rai,ba ruwanta da baka yinta ko kana yinta,itadai indai kayi mata shikenan,sauran
matsalar taka ce.
Tana ankare dashi,da salon takunsa dinnan dake nuna lallai akwai digo
na jinin sarauta a jikinsa ya qaraso section din su Aeeda,ya zare takalman socks
yayi saura a qafarsa,yahau saman tattausar kujerar da tafi zubi da ni'imtacciyar
shimfida me tudu,ba kuma tare daya daga ido ko sau daya ya kalli sashen da suke
zaune ita da badee'a ba
Yanayin zamansa kawai sultane mahaifinta ya haska mata,ire iren
xamansa kenan a fada ko a cikin gida. Wani zama ne na musamman dake sake fidda
kwarjini sosai ga sarakuna,sai ta zuqi wani irin numfashi,kafin kuma ta ajiye
badee'a ta rigata magana.
"Hodijam.......yanzun wannan malami ne me koyarwa?" Ta jefawa falaak tambayar tana
me mantawa da girman tazarar dake tsakaninsu. Tun dawowarta jininsu yazo daya da
badee'a,kuma morsa ta sanyata cikin hadimanta na kusa,don ta yarda da hankali
tarbiyya da kamun kan badee'a din. Bugu da qari falaak tana buqatar wani a kusa da
yayi rayuwa sosai cikin agadez......cikin masarautar agadez da zai dinga kwatanta
mata yadda abubuwan gidan suke,don ta jima rabonta da qasar,tun batafi shekaru
bakwai kacal a duniya ba.
"Me kika gani?" Falaak ta tamabayi badee'a tana dubanta a hankali.
"Allah ya huci ranki idan har nayi maganan da ya sabawa tarbiyya da kamata.
Kwarjininsa da kyansa ba na irin gama garin mutane bane,zamansa uwar dakina kadai
yana alamta ba mutum bane irin kowa......baiyi kama sam da jinsinmu ba.......duk da
yana zubi da kamanni da buzaye.......amma akwai banbancin launi a tattare dashi"
Tayi maganar qasa qasa,saboda yadda jikinta yake bata kaman zaiyi kaifin jin
magana.
"Amma da French yake magana......saidai bayan wannan bansan ko yana magana da wani
yaren ba na daban". Falaak ta fada tana neman qarin haske daga gurin badee'a.
Kamar ruwa ya cisu haka sauran kalaman dake bakin kowannensu ya
dauke tsaf saboda daga idonsa da yayi ya kallesu sau daya,cikin qasa da second biyu
kuma ya sauke kansa qasa yana duba ayyukan Aafreen.
Dukka suka rufe babin maganar,don daga ita har badee'a ba