Showing 42001 words to 45000 words out of 168506 words
da suke juyawa a hankali cikin
screen din,har zuwa sanda ya kammala duba saqon. Bayansa ya jinginar jikin kujerar
yana yin relaxing sosai,still bai dauke fararen idanunsa daha kan allon computer
din ba. Yatuntsa guda uku cikin sumar dake kwance saman habarsa yana dan yamutsasu
a hankali.
Paragraph din qarshe na saqon da bobbo ya rubauta masa da kalmar turanci
ya motsa labbansa a hankali ya karanta *_operation into AGADEZ_*
Ya kafe kalmomin da idanu yana maido tunaninsa baya. Duk tsahon
wadannan lokutan?,duka tsahon shekarun?,me yasa tunaninsu da bincikensu baikai can
ba sai yanzu?.
Idan zai iya tunawa shine ya fara kawo wannan idea na baza komarsu
zuwa ga qasashen dake cikin fadin africa gaba daya. Bai manta osama yana daya daga
cikin mutanen da sukayi Challenging nasa a lokacin......saboda dalilai na ganin
cewa duka duka yaushe ya shigo hukumar tsaro ta sirri?......bai wuce watanni da
fara aiki dasu ba amma ya samu nasarar shigowa babban team irin nasu na goggaggun
ma'aikatan sirri.......ya tsinci kuma case din kisan gillar Abban ajani
Ahmed......duk da akwai abota me qarfi da girma tsakaninsa da mahaifinsa me martaba
abba jifar,amma osama yana ganin wannan daban da wannan. Ya raina tunaninsa a
wancan lokacin,yana kallonsa a wanda baisan komai ba akan aikin........taka haye ne
shi. Ran osama yayi fari qal a sanda aka soma fadada binciken zuwa wasu qasashen
Africa din.......kuma basu samo komai a kai ba.......sai matsala ma da yaso jawowa
ta alaqar diplomacy tsakanin Ethiopia din da maqwabtanta.
Daga qarshe bobbo yace a haqura a ajjiye binciken......aci gaba da taba
case din lokaci bayan lokaci. Yana da wani abu guda daya a rayuwarsa daya zame masa
silar nasararsa.........JAJIRCEWA DA TSAIWA akan dukkan abinda yasa a gaba,ya kuma
samu gamsuwa cewa eh zaiyi. Baya tunkarar komai da ka,sai ya gabatar da ISTIKHARA
irin wadda ma'aiki ya koyar da sahabbansa......sannan ya dora da addu'o'i. Wasu
lokutan harda azumi,muddin ya gama wadannan ya samu nutsuwa da gamsuwa akan
komai.....to ko meye wannan abun,komai girman hatsarinsa baya jin fargaba ko digo
akai,domin yasan Allah ya bawa zabi......kuma ya gama zabar masa koma
meye..........so bashi da wani sauran haufi tsoro shayi ko shakka.
Tun daga wancan shekarun bai qara bari zuciyarsa da jikinsa sun huta
ba akan case din ajani Ahmed.......musamman daya zama aboki sosai ga mooti abba
jifar........wannan sai yake sake motsa zuciyarsa a duk sanda hira ta hadashi da me
martaba zancan ajani Ahmed ya fado ciki.
Komai yayi farko yana da qarshe.......kamar yadda akace komai nisan
jifa qasa zai fado......komai girman gona kuma akwai kunyar qarshe.........cikin
watan daya wuce yana tsaka da bincikensa game da wanda dukkan hukumarsu ke qarfafa
zato a kansa.
Ya samu wani irin haske daya sanyashi jimawa yana duba bayanan gami
da hadesu da wasu bayanai dake ajiye a kwanyarsa. Ya ajiye bayanan yana musu
kyakkyawar ajiya......sannan ya miqe ya daura alwala yayi sallah,a sujjadar qarshe
kuma ya jima yana ganawa da ubangijinsa ta hanyar karanta la'ilaha illa anta
subhanaka inni kuntu minazzalimin. A wunin ranar duka ya lazumci istigfari da ya
hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis.
Aiki ne me hadarin gaske daya tabbatar samuwar nasararsa wata samuwar
nasara ce me zaman kanta ga gwamnatin Ethiopia. Mutuwar abba ajani Ahmed ta kusan
zamewa gwamnatin Ethiopia gaba daya barazana......kasancewar abba ajani Ahmed
mahaifinsa dan asalin qasar America ne......kuma shi kansa acan aka haifeshi,don
haka halalin qasar ne.......kasuwanci ya dawo da mahaifansa qasar Ethiopia shekaru
masu yawan gaske a baya,har suka rasu suka barshi da tarin nashi iyalin har zuwa
sanda ajalinsa ya riskeshi shima. Bashi da kokwanto akan bobbo game da case
din......amma addu'ar da yayin ta sake saka masa nutsuwar bobbo ya sani.
Ya jima shuru yana duban haisam bayan gabatar masa da dukkan bayanan. Ya
rasa me zaya fada a kanshi?. Tabbas yana ji a ransa irin haisam din duk bayan qarni
guda ake haifar mutum daya irinsa. Jajirtacce dan kishin qasarsa al'ummarsa dama
iyayensa. Kafadarsa ya dafa yana jin zuciyarsa tana narkewa.
"Ina sake taya mooti murnar samun d'a kamarka haisam.......kaidin wata kadara ce me
tsadar gaske.......ko yau ko kuma a iya nan ka ajjiye aikinka tabbas qasarmu zatayi
alfahari dakai".
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 20
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
"Ya rahman......ka sanyi na kasance mafi alkhairin abinda suke
zato(wannan din addu'a ce me kyau daya kamata ka dinga yi a duk sanda aka yabeka
game da wani abu,ita annabi ya koyar)"
"Zanso na aiwatar da aikin nan qwarai bobbo" Haisam ya furta a sanda muhammad
dawud(bobbo) ya bashi tabbacin sahalewa aiwatar da aikin.
Idanu muhammad dawud ya zuba masa,yana yawaita mamaki sosai akan yadda
haisam keson aikinsa da yawa. Tabbas ba shakka national intelligence and security
service sun bashi wani girman matsayi......sun bashi albashi me kyau da yawan daya
kusa daidai dana shugana qasarsu.......yana da masu tsaron lafiyarsa.......to amma
dukka wadannan ya samesu dama tun daga gidansu,ya samesu tun kafin ya shigo
NISS......gata da soyayyar daya samu daga gida ta ninka wannan. YARIMA ne da
kowanne lokaci zai iya zama sarkin jimma.......mallakin hamshaqiyar fadar ABBA
JIFAR amma duka ya watsar da wannan ya rungumi aikin da matsayinsa ya haura wannan
inda yazo cikin masu wannan dabi'ar.
Eh......tabbas,duk wanda ya kalli haisam a ganin farko zaisan cewa
wannan jinin na SARAUTA yana harbawa a kowanne sassa na jikinsa.......akwai wannan
QASAITAR da IZZAR a tare dashi,don sarauta ba qarya bace......duk qanqantarta saika
samu tasirinta cikin jinin ahalinta.....ballantana babbbar masarauta me dimbin
dukiya da arziqi irin ta JIMMA. Yana da wani irin kwarjini da akan samu akasarin
ahalin sarauta dashi.......yana da irin nasa jin kan wanda nature dinsa ne bawai
yana yi bane don gwada shi wani bane.....don ya karanta yasan kuma illar
hakan.......amma kuma kyakkyawar mu'amalarsa da dukka wanda yake sama
dashi.......tausayinsa da jin qansa ga masu rauni ko wanda yake qasa dashi na
dabanne.
"An baka dama haisam.......amma wannan tafiyar tafiya ce me hatsari.......don hatta
da gwamnatin qasar NIJER da hukumominsu bamu yarda susan da shigowarka qasar
ba......zamu dan take wasu dokoki na qasa da qasa saboda mu samu cikakken
sirri......don haka yana da kyau ka shaidawa mooti........har nanay itama". Ya
gamsu da batun gayawa me martaba.......amma nanay fa?,baisan ta ina zai fara
fahimtar da ita ba.
Zuqe numfashinsa yayi ya fesar yana maimaita sunan garin......bazaice
bai taba jinsa ko jin sunansa ba.......amma basa cikin garuruwan daya dauka suna
existing suna kuma da wani manyan abubuwa da bincike ko wani aikinsu zai iya rabawa
ta wajen. Shi duka bincikensa NIJER ya gani.......baisan ya akayi cikin NIJER din
ba kuma ya fada wani gari wai agadez ba.
Cikin qwarewa da iya sarrafa na'ura ya koma kan system din,ya tura
bobbo komai yana shaida masa yau din zuwa azahar zasu sauka a addis ababa in sha
Allah shida omari,ya qarasa tura masa komai,sannan ya fita daga system din ya
kasheta gaba daya.
Kowanne qwan lantarki sai daya kasheshi,ya maida dakin yadda yake
sannan ya dawo bakin wannan qofar me siddabaru ya fito ya dawo ainihin parlor din
da ya fita cikinsa a dazu. Kusa da littafinsa ya koma ya daukeshi hade da
wayarsa,ya taka zuwa wata ma'ajiyar litattafai dake parlor din wadda yakan dubasu a
iya parlor din ya sakasu a ciki yana duba fuskar wayarsa.
Fararen idanunshi ya zaro waje.......kiran da bai samu daman dagawa ba
na nanay ya gani har uku,sai ya kalli lokaci sannan ya juya ya dauki wayarsa ya
maida saman kansa yana dosar qofar fita daga parlor din.
Wani courtyard ya bulla me ban shaawa da aka cikashi da tsirrai bisa
tsari me burgewa,sannu a hankali ya sake fadawa wani balcony sannan ya bulla wani
setting room din kafin ya tadda doguwar veranda da zata sadashi da ainihin sassan
nanay.
Wani irin gini ne musamman da yafi kama da gine ginen mutanen sin wato
CHINA fadar abba jifar ke dashi......shigen gine ginensu sak da sak da sai kayi
tunanin a qasar sin din kake. Yana takawa da cikakkiyar nutsuwa da dadin da iskar
safiyar tayi masa......zuciyarsa na shirya masa yadda zai fahimtar da nanay tafiyar
ba tare data daga hankalinta ba. Tun a jiya suka raba dare suna magana da me
martaba.......ya gama fahimtarsa,ya bashi goyon baya kuma d'ari bisa d'ari,saidai
ya jadda masa yaci gaba da riqe addu'a.......ya kula sosai.......ya kuma rage jefa
kansa cikin abubuwa masu hadari har haka.
Cikin girmamawa dukkan wani hadimi da suka hadu saman hanyar yake
gaidashi da wani matsanancin martabawa. Baya gajiya haka yake amsa musu cikin
kulawa shima,mata a cikinsu ne kadai yake dagawa hannu ya wuce.
Sannu a hankali ya cimma farfajiyar sassan farko na nanay........,tun
bai kai ga qarasawa ciki ba daddadan sautinta ya soma sauka a kunnensa da irin
qir'arsa sak. Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu yana jin wani yanayi yana ratsashi.
A duniya babu wani sauti mafi girma.......sauti mafi saukar masa da dukkan nutsuwa
irin sautin karatun qur'ani. Ba wani abu dake sauke fushinsa.......yake dawo da
nutsuwarsa gangar jikinsa irin sautin qur'ani. Ba wani labari dake masa dadi a
kunnuwa idanuwa da zuciya irin ya bude qur'ani......surorin da Allah madaukakin
sarki ya saukar dake bada labarai na al'ummar da suka wuce.....labarai na annabawa
da sauran abubuwa na rayuwa.
Cikin tsari daliban nata da suka kasance hadimai ne na sassan nanay
suke zaune a gabanta. Kowaccensu sanye da yalwataccen hijabin daya sauka har
qasa,wanda da kudinsa ya bada kwangilari dinkin kyawawan hijaban har guda dari da
suka kasance launin Sacramento green me kyau.
Samee din data kasance malamarsu a kowanne ranakun mako irin wadannan
guda biyu tana zaune saman wata gajerar cushion chair maras tudu,tana sanye da
farin hijabi qal kamar hannu bai taba sauka a kansa ba. Baka ganin komai nata sai
kewayayyar fuskarta da manyan idanunta dake yawo tsakanin ayoyin qur'ani.
Wannan din wani ginannen burinsa ne daya taba furtawa nanay......burin
ilimantar da duk wasu hadimai da bayi dake sassanta dama gidan gaba daya da
ingantaccen ilimi daga qur'ani cikin sanin fassararsa da kuma tarin ma'anonin da
yake dauke dashi. Yayi maganar ne a sanda samee ke shigo cikin parlor din wajen
nanay.......ashe kuma taji,kafin yakai ga zabar malamar da zata kasance malamarsu
sai zuwa yayi wani hutun qarshen mako ya samu samee din ta fara gabatar da karatun.
Idan yace baiji dadi ba yayi qarya......idan yace girmanta da kimarta
basu dadu a idanunsa ba yayi qarya,don haka sai ya bada kwangilar dukka hijaban da
zasu sanya harda malamar tasu. Yaransu yasa an tashi makarantar islamiyya gagaruma
cikin gidan,wadda ta zama kyauta kuma sadaqatul jariya ga kowa,har yaran dake wajen
masarautar. Mazajen gidan kuma ya kawo malami namiji da zasu dinga nasu karatun
juma'a da asabar........yawanci asabar din shi yake zama yake musu litattafai guda
biyu na fiqhu da hadith saboda inganta ibadarsu bayan qur'anin,wannan ya sanya
itama samee ta saka ma matan littafin qwaya daya na fiqhu.....bayan sun saukeshi
kuma take sanya ran saka musu hadith koda me hadisai darinnan ne.
A cikin jikinta taji akwai wai baqon abu me kaifi a wajen........a
cikin jikinta taji wata baquwar halitta ta wanzu a wajen,don haka tana kaiwa
qarshen ayar suka kama suna maimaitawa,saita daga idonta a hankali take suka fada
cikin nasa.
Wannan qaqqarfan maganadisun ne taji ya fusgeta da wani irin
qarfi,wannan kwarjinin nasa daya sanya gumi tsatsatsafo mata ta cikin
hijabinta......wannan kyan nasa daya zame mata tamkar wata jarrabawa ya ratsa
idanunta,duk sai taji wani abu yana tsumata,musamman a yau data samu damar ganin
Fuakarsa gaba dayanta ba tare da suturtaccen mayanin nan nasa ba.......a kuma
safiyar da dakusashen hasken rana ya bayyana fuskarsa tarwai.
"Subhanallah" Ta furta qasan ranta sanda ya sake mata dan siririn murmushin da iya
labbansa ne kawai suka motsa,yana alamta mata jinjinawarsa,sannan ya juya a nutse
yana bin qofar da zata sadashi da nanay din.
Sai data rasa numfashinta na wasu daqiqu kafin ta samu kamoshi,inda
ta godewa Allah ta gaya biya musu suna maimaitawa ne tana musu gyaran inda suke da
kuskure. Can qasan ranta tana tuhumar kanta da kalar tuhumar da har yau bata daina
yiwa kanta ita ba. Me yasa ta jarabtu da kyansa?,me yasa ta jarabtu dashi?,daidai
ne ta sakarwa zuciyarta linzamin kyau ado da qawa kuwa?.
Ta sani yana da wasu qualities da ba ita kadai ba.......mata da yawa
dake kewaye dashi sunsan yana dasu.......ya mallakesu ya kuma samu baiwa
dasu......to amma a karan kanta me yasa kyansa yake zama barazana a gareta?.
Akwai wani ra'ayinta guda daya da take dashi,bataso ta cusawa haisam
kanta.......bataso a mishi tayinta......bataso kuma ya sota saboda wani abu na
daban,tanaso ya sota da kansa......tanaso ya sota don ta cancanci ya sota din.
Tana karantarsa sosai,duk da cewa yawa yawan zamansa ba a jimma
bane.....a addis ababa ne,zuwansa sai weekend,amma duk da haka ta karanci abubuwa
da yawa a kansa.
Har yanzu bataga alamun da takeso take kuma sanya ran ganinsu a tare
dashi a kanta ba,saidai ta sanya a ranta zataci gaba ta dukka hanyar data dace.
A nutse ya sake jaddada sallamarsa a parlor din kaman yadda ya saba
a duk wani guri da zai shiga.
"Wa'alaikumussalam" Matashiyar budurwar dake zaune saman doguwar sofa ta amsa tana
daga kanta. Qaramin murmushi ya subuce mata,ta miqe daga zaunen da take tana duban
haisam da yake shigowa da kyawawan idanuwanta da suke kama dana haisam din. Wanda
banda su ba abinda ta dauko na kammaninsa,saidai ko tsaho da nata yafi bayyana
saboda jikinta baikai nashi murjewa ba.
"Akkam bulte(barka da safiya)" Ta fada murmushin nan yaqi barin fuskarta
"Akkam jirta rumaisa(kina lafiya rumaisa?"
"Alhamdulillah captain sheik" Rumaisa ta fadi tana murmushin daya sanya haisam
yasan lallai akwai wani abu a qasa,musamman data kirashi da wadannan sunayen a jere
haka guda biyu.
"Ehheeenn" Ya fada yana dage dukka girarsa biyun sama,abinda ya qara masa kwarjini
kenan har a idanun rumaisa. Kai ta girgiza tana rage kaifin murmushin ta. Ganin
data sama a ya zun da yadda Moroccan abayar jikinsa ta dace da zubi da tsarinsa,sai
maganar daya daga cikin qawayenta me suna anniisa ya fado mata. Kusan sallar isha'i
ta daren ranar da akayi irreecha festival yabar baya da qura......don qira'arsa ta
tayar da sirrin boyayyun zukatan dake cike da boyayyar soyayyarsa cikin qawayenta.
Ganin kamar bata shirya gaya masa ba sai ya kauda zancen yana tambayarta
"Nanay eessa jira?(ina nanay?)" Da hannu ta nuna masa bangaren dakunanta na
musamman da banda iyalinta ba wanda yake da hurumin tsallakewa har nan.
"Tana ciki bata jima da shiga ba" Baice komai ba ya fara takawa,sai muryar rumaisa
ta dakatar dashi.
"Obbo captain(sir captain)". Sunan da sukafi kiransa dashi. Dakatawa yayi daga
tafiyar da yakeyi wadda rumaisa ka qarewa kallo tana kuma sake gasgata zancan
anniisa
"Yana da wani irin taku na daban.......qasaitarsa tafi taku.....kuda kuke mata amma
shine yake da jan ajin da izzar". Hararta kawai tayi a sannan,don itakam obbo
haisam ba zata iya cewa ga wani sanda ta tsaya qarewa takunsa kallo ba.
Eh har gwara maganansa,ita kanta wasu lokutan idan yana magana burgeta
yanayin tsarin maganarsa takeyi cike da ginshira......amma tafiya kam a yau itama
ta shaida hakan.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 23
____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500
dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce π₯°ππΌ
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da
kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa niβima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi
https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata