Showing 99001 words to 102000 words out of 168506 words
daman sanin komai daya shafeta bane. Ta tsaidata iya
matsayinta na babbar jakadiyar dake da ruwa da tsaki akan dukkan al'amuran da suka
shafi bangaren sassanin matan sarki.
"Allah ya baki yawan rai" Ta fada tana rusunawa.
"Tamim ne iso......nace bari na shaida miki kamar yadda kika buqaci hakan" Kai
mammina ta girgiza,tana sauke qafafunta qasa.
"Ki masa iso......yalwa kadai na yarda a sake bari ta qaraso nan". Jinjina kai
ayaana tayi tana furta.
" An gama" Can qasan ranta yana cika da mamakin irin wannan zuzzurfan kusancin da
ba kowa ke iya karantoshi ba. Ita kanta ba zata tuna lokacin da tamim ya shigo
gidan ba......ba zata iya tantance sanda ya fara wanzuwa a gidan ba......amma zuwa
yanzu,mutane kadanne suka fishi daraja da kuma matsayi gami da kusanci da manyan
gidan.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 48
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me
kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse
masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk
wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri
kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai
gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma
suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
_____________________________
Kafin tamim ya shigo,sai ta dinga jin kamar lokacin yayi mata tsaho. Ta
miqe tsaye,ta taka a hankali zuwa bakin qofar shigowa gurin tayi tsaye goye da
hannayenta tana jiran qarasowarsa.
Bata cika mintuna biyu ba cikakku tamim ya bayyana a gurin,da wannan
suffar tasa dake nuna qarfi da lafiyar da yake da ita. Zubewa yayi a
gabanta,kwatankwacin bawa da uban gidansa,kansa a maqasqancin qasa yake magana.
"Barka da wannan lokaci,barkanki da warhaka uwar gijiyata". Sauke hannayenta tayi
tana fesar da iska daga bakinta,ta kuma koma da baya ta zauna tana fadin.
"Ba lokaci bane na gaisuwa yanzu.......lokaci ne na aiki,aiki kuma tuquru,lokaci ne
na cimma muradai.......banaso lokaci ya quremin,banaso ya kasance komai ya kasance
cikin qurataccen lokaci......har yanxu banji kalar labarin da nakeso ba" Ta qarshe
maganar cikin girma tana zama saman daya daga cikin kujerun dake zagaye da gurin,ta
ware tafukan hannayensa tana miqa masa.
Murmushi ya fidda me sauti,sannan ya miqe tsaye. Babbar riga ce a
jikinsa wadda aka fi sani da malum malum,wadda aka yiwa aikin hannu dake dauke da
zanen tambarin gidan sarautar agadez manya manya,abinda zai gaya maka ya narkar da
kansa,ya kuma maida kansa mallakin gidan sarautar halak malak.
Hannunsa ya zura daga cikin babbar rigar,wadda kafin ita akwai riga da
wando har iri biyu a jikinsa. Rigar farko daga wajen cikinsa ya zura hannu ya zuge
wani zip,ya cusa hannun nasa,ya kuma ciro wasu takardu a nannade,abinda ya sanya
tumbinsa komawa,ya kuma rage tudun da yake dashi.
Zubewa yayi a qasa yana miqa mata takardun da dukka hannayensa guda
biyu,ta saka hannunta guda daya ta karba zuciyarta na wani motsi da fatan ganin
abinda takeso ta gani din,sannan ta soma warwaresu cikin dauki tana dubasu daya
bayan daya.
Wani irin murmushi ne ya subuce mata,wanda kana kallon fuskarta zakasan
yayi nisa da zurfin da ya taba zuciyarta sosai. Tsaf ta kammala dubasu,sannan ta
daga kanta tana duban tamim.
"Na jima banga mutum me hatsarinka.......na jima kuma ina tunanin kalar sadaukarwar
da zanyi maka.......saidai nan gaba kadan.......lokaci taqaitacce kawai nake jira
na baka zabin abinda kake so na sadaukar maka dashi.....domin kuwa ka cancanci
komai tamim" Wani irin murmushi yake yana gyada kai.
"Ina nan ina jiran wannan ranar.........ina kuma me baki tabbacin daga randa na
zabi abun sadaukarwa......kuma kika sadaukarmin din......na rantse miki harga Allah
daga ranar zan damqa rayuwata da numfashina dukka a hannunki" Ya fadi yana dunqule
hannunsa gami da dukan qirjinsa.
Wani amintaccen murmushi ta saki. Alwashinsa kadai ya sake rura mata
wutar son akai gabar da zata tambayeshi ta kuma bashi dukkan abinda takeso. Tamim
nata ne zata iya cewa,tsahon shekaru masu yawa yana bauta a qarqashinta,bai kuma
taba bijirewa umarninta ba. Batasan iyakar adadin umarninta da tamim ya cika
ba,daga randa ya zame mata bawa zuwa yau,bata da wannan lissafin.
Batakai ga cewa komai ba muryar yalwa ta ratso gurin.
"Anyimin izinin shigowa?".
"Anyi miki" Mammina ta fadi tana nannade takardun da kyau gami da maida dubanta ga
bakin qofar.
A ladabce yalwa ta qaraso,ta kuma zube gaban mammina wadda ta kafeta
da ido.
"Komai ya lalace Allah shi dafa miki,komai bai tafi yadda ya kamata ba" Dubanta
sosai mammina keyi,saidai izzarta ta hanata tambayar yalwa komai,tana ganin ita din
ba sa'arta bace.
"Allah ya baki yawan rai.......shima tayi watsi dashi yadda ta saba......wannan
karon ya samu tsaraba mafi girma da ba wanda ya taba samun irinta......tsarabar
mari". Waje mammina ta fidda idanunta,cikin matsanancin mamaki. Yayin da tamim ya
runtse idanunsa dukka biyun da kyau yana hasashen wani abu.
"Garin yaya haka ta faru yalwa?,kina ina?" Mammina ta sake tambayar yalwa din.
Qasa yalwa tayi da kanta,a sanyaye ta furta.
"Gefan mayafinta ya riqe ranki ya dade". Da sauri ita da tamim suka zube mata
idanuwansu,shuru ya baqunci gurin,kafin mammina ta gyada kanta.
"Yayi kuskure ba qarami ba,amma kuma hakan ma yayi......ki kiramin laraba,taje ta
duban halin da take ciki a sassanta,ina buqatar fara zuwa ganinta,ina buqatar fara
ganinta kafin kowa,don nasa nan da awanni kadan tabbas sultane zai buqacu ganinta".
Kai yalwa ta girgiza sannan ta miqe ta juya tana fita.
"Tamim" Ta kira sunansa,abinda ya sanyashi daga kansa daga sunkuyon da yayi.
"Ina buqatar wanzuwarsa a wannan duniyar tamu kaman kowanne dan adam,ina buqatar
rayuwarsa tahau saiti.......kwanaki satittika ko kuma watanni kadan masu zuwa zamu
samu buqatuwa da wannan wanzuwar......da wannan sabuwar rayuwar". Kai ya jinjina
sannan ya miqe cikin ban girma,ba tare da ya sake cewa komai ba ya juya yana
ficewa.
Guri daya ta zubawa idanu tana wani gajeran nazari,daga bisani kuma sai
ta fara gyada kanta a hankali qaramin kwantaccen murmushi yana subucewa daga
fuskarta.
*SHEIKH HAISAM*
Tun a cikin motar da hambal ya dawo da kansa ya daukeshi bayan
tattakin da yayi daga cikin masarautar agadez din har zuwa inda yace su jirashi
baice da kowa komai ba.
Tsakanin maher da hambal din suke hira kadan kadan kan yanayin garin da
kuma al'adunsu. Fiye da rabin hankalin hambal din yana kan haisam,kamar yadda maher
shima hankalinsa ya karkata ga haisam din. Wannan mode din ba dashi ya shiga agadez
palace ba,to amma sunsan halinsa. Idan ba yaso bane fadi maka abu,bai fiya son a
tambayeshi ba,wannan ya sanya suka ja bakinsu sukayi shuru.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Mintuna kadan suka iso gidan,wanda da sauri daya daga cikin hadiman
gidan ya matso ya bude masa qofar. Qafafunsa ya zuro waje yana cewa.
"Kuyi alwala,zan fito yanzu mu wuce masallaci" Ya sauke qafafunsa yana takawa a
nutse zuwa cikin gidan.
Har ya isa bedroom dinsa bai hadu da kowa ba,tunda dama sassan
mallakinsa ne,sai omari da suke zaune tare kowa da shiyyar dakunansa. Baiga omari
ba,kuma baya cikin mode din tsaiwa tambayar inda yake,sai ya rage cloak robe din
jikinsa ya ajiye,ya zare rawanin kansa a hankali ya ajiye saman dressing
table,abinda ya bawa sumarsa me santsi damar bayyana wadda ke kwance saman kansa
cikin wani irin tsari.
Fadawa idanunsa sukayi kan fuskarsa,fuskar da tayi wani fresh tayi
tarwai saboda tsananin hutu da kuma kulawa,kawai sai ya samu kunnuwansa da dawo
masa da sautin marin kamar a sannan aka yishi.
Almond eyes dinsa ya bude sosai cikin madubin,yana son ya gano wannan
sautin dama shine abinda yayi masa tsaye a rai tun dazu?,ashe shine abinda ya
dunqule masa a wuya yaqi kuma wucewa?. Ta yaya d'iya mace zata daga hannu ta mari
namiji?,namiji ma baligi Aaqili?. Imagine ace noory ko rumaisa ne zasu aikatawa
wani haka?,waninma da yazo ganinsu da shirin auren sunnah.
Wani mahaukacin tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa. Ta yaya ma hakan
zata faru a masarautar oromo?. Ta yaya suma zasu fara aikata hakan?. Ya tabbatar
daga shi har nanay sun musu wani irin horo da babu yarinyar da zata iya soma
kwatanta hakan,sai yaja da baya yana jin yadda ranshi ke motsawa,irin abinda a
dazun baijishi ba sai yanzu,ya fara tattare hannun jubah dinsa yana tafiya a nutse
zuwa toilet.
Alwalar daya daura ne kawai ta bashi relief,dama kuma yana cikin
dabi'unsa,duk yadda yakejin fushi cikin ransa muddin zaiyi alwala to zai samu
sassauci cikin ransa( a duk sanda kike jin fushi kije kiyi alwala,in sha Allah
zakiji sanyin ruwan yana ratsa har zuciyarki).
Suna takawa zuwa masallacin dake layin,wanda qananun taku ne kawai zai
sadaka dashi zuciyarsa na sake yi masa tariyar yadda al'amarin ya wakana. A lokacin
ya gayawa kansa ne ba wannan ne ya kawoshi cikin masarautar ba.......ko meye zasuyi
daidai da tsarinsu ne da rayuwarsu,aiki ya shigo yi,shi ya dameshi,kuma shi ya
kamata ace ya kula dashi,amma baida jib'i da komai na rayuwarsu,sai gashi a yanzun
yana jin kamar ba haka ba,abun yana neman tsaye masa a rai.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 49
___________________________
*_INA MASU BUQATAR QAWATA GIDAJENSU DA KALAR TSUNTSAYE DON ADO DA DEBE KEWA?_*
*_INA MASU BUQATAR FARA SANA'AR SAIDA TSINTSAYE.....SANA'A ME TARIN RIBA DA ALBARKA
DA KUMA SIRRI A CIKINTA?_*
*HALY JASHERU VENTURES.*
munada tsuntsaye na kasashen waje masu kyau da daukar hankali kmn haka.
TATTABARU
French modain(Argentina)
Indian faintail (3in1)
indigo,opal,Andalu,Lahore,busa,Bukhara, indomie,Jacobin dasauransu.
KAJI.
Brahma,silkie,silver lace,coshine,dawisu, parrot (aku)dasauransu.
,
Munada kayan Islamic center.habbatus saudah,hulba,zaitun,qusdul Hindi,minannas,Rose
water dasauransu,dangin garinsu ,mansu yayansu ,ganyensu. munada original Zuma,yar
chad da mombila.
Munada kayan gwanjo masu kyau daga jariri zuwa babba,
Overall,Rumpers, bodysuit, sweaters,wanduna, tracksuit dasauransu,munada kaya masu
kyau na bacchi na gwanjo.
Munada Ethiopian magic hair oil πͺ Wanda yake Kara gashi,yayi tsaho laushi,yayi Baki
drct daga Ethiopian muke kaisa ko Ina afadiin duniya.
Don Neman Karin bayani number waya
07046665338.
____________________________
*AKHNAN*
Ko kafin takai ga idar da sallar taji an mata knocking ya kusa sau
biyar. Tana sallan amman ranta yana baci. Ba wanda take buqata yanxu haka a kusa da
ita,ba wanda take buqatar tayi magana dashi,kebewa kawai take so,sai kuma jiran
kiran sultane. Kiran da inda tana da dama tabbas da zata tsere masa ne,amma kuma
tasan bata da damar hakan,hakan kuma bame yiwuwa bane. Dole ne ta amsa tambayoyin
sultane,dole ta tsaya ta fuskanci sultane muddin tana neman 'yancinta,dole ta masa
bayani ta yakice kowanne irin tsoro dake a ranta.
A hankali ya fado mata a rai sanda take zauke daidai saman
daddumar,tafukan hannayenta akan saman fuskarta. Wancan lokacin da kalmar.
"Subhanallah" Ta fita a bakinsa,sanda take dab da shan qasa daga saman thunder
dinta. Har yanxu wannan sautin yaqi barin kunnenta,har yanzu wannan sautin ya sha
tashinta daga baccinta a darare masu yawa. Tasha sake ganin wannan abun daya faru
yana sake maimaituwa a cikin baccinta.
Qamshinsa da har yanzu bata sake jin makamancinsa ba,har kwanan gobe
tana iya hakaitoshi,saidai kuma da tarin wata irin matsananciyar tsana da kuma jin
haushi.
Inda tana da hali,tana kuma da dama lallai da sai ta laluboshi a dukka
inda yake a fadin duniya. Tana da wannan qudurin,amma kiran sultane da maganar da
sukayi a jiya kawai ta warware duk wani karsashi da take dashi.
A yau kawai tsanarsa ta ninka a zuciyarta ninkin baninkin. Shine
silar duka wani hukunci da sultane ya dauka a kanta. Shine sila,ta tabbatar wannan
video clip din ya gani........ya kuma zame mata dalilin wannan horon da sultane
yake shirin yi mata.
Ta sake yadda abun shiryayye ne,dama ya shirya ne kawai don yaci
mutuncinta ya kuma ci zarafinta. Tunda ga shaida da alamu dukka ta gani,ta tura
musu request tana son a sake shirya wasan,amma sun maido mata amsar wannan dan
wasan isn't available.......amma idan tana da sha'awar sake yin wasa,akwai tarin
'yan wasa available da zata iya karawa dasu.
Bata da buqatar ko daya a cikinsu,tana buqatar karawa da shine don cire
masa dukkan wani abu da yakeji a kanta......don cire masa tunaninsa na yayi nasara
akan akhnan muhammad hammud..........da wannan tunanin ta wayi gari,saidai a yanzu
sultane na shirin dakushe wannan shirin,ya kuma maida akalar tunaninta kan wani abu
na daban.
A karo na uku da aka buga qofar saita miqe a fusace ta isa qofan da
kanta maimakon tayi amfani da remote ta bude. Cikin ranta tana me cin alwashin ko
waye saita wanke masa fuska da zafafan mari tukunna,ko waye.....koda falaak
ce,saidai kuma tana bude qofar sai taci karo da fuskar da tafi qarfin mari a
gurinta.
Mammina ce a tsaye yana fuskantar qofar dakin. Dukka wani yanayi na
alhini rashin jin dadi da kuma damuwa gashinan kwance saman fuskarta. Jiki a
sanyaye ta saki qofar tana komawa ciki,mammina ta biyo bayanta.
"Don meye zaki kulle kanki akhnan?,bakya tsoron lafiyarki?,ko bakya tsoron wani
abun ya sameki?" Ta fada tana riqo dukka hannayenta cikin tsantsar kulawa.
Blue eyes dinta da suka rusuna ta waiwayo yana zubewa mammina su,tana ji
a ranta har tsakiyar zuciyarta.......bata da wani sauran gata daya rage mata a
duniya bisa dukkan alamu idan ba mammina din ba......sultane ne taqamarta na
farko,to amma kuma alamu sun nuna kamar sultane din ya fara yi mata nisa,ya fara
nisa da muradinta. Ba zatace ga a abinda yake faruwa ba kai tsaye,amma tana da
yaqinin zai wahala idan ba MORSA bace ke shirin rusa wannan kyakkyawar alaqar ba.
Duk wasu halaye da sultane ke gwada mata a yanzun baqi ne a tare da
ita,tunda ta mallaki hankalin kanta bata taba ganinsa da wadannan dabi'un ba.
Ci gaba tayi da kallon mammina kawai,abinda ya bawa mammina damar
karantar abinda yake kai kawo a zuciyarta.
"Tsoron me kike biftu?,kin manta alqawari na?......kina zaton idan sultane zai iya
manta alqawarin dake tsakaninku ni zaituna zan iya mantawa?......duk runtsi duk
tsanani ina tare dake akhnan" Sosai maganganun mammina suka karya mata zuciya.
Bataso tayi kuka,don batajin ya kamata zuwa yanzu ta fara samun rauni har haka a
zuciyarta,amma kuma tana buqatar kafadar da zata jingina da ita don samun sassaucin
abinda takeji,don haka ta qara taku biyu,ta aza kanta saman kafadar mammina din.
Hannunta ta dora saman sassalkar sumar akhnan dake da tsaho santsi da
kuma sheqin baqi tana shafawa a hankali,kaman yadda uwa keyi ga qaramin yaronta da
sigar lallashi.
"Indai ina raye ba wanda zan bari ya aurar dake ga mijin da baki aminta dashi
ba......ko baki fada ba yalwa ta gayamin.......sultane mahaifinki ne......indai ba
zugashi akayi ba,bazai taba aurar dake ga mijin da baiyi miki ba......" Saita daga
kan akhnan daga kafadarta tana riqe hannayenta dukka biyun.
"Ki sa a ranki da mahaifinki kike magana.......ki bude bakinki ki gaya masa bai
miki ba!". Ta qarasa maganar da wani sauti dake nuna akwai wani abu daban daya taba
zuciyarta.
Shuru akhnan tayi tana duban tsakiyar qwayar idanunta,irin duban da a
yawan lokuta da dama yake qarfafa mata gwiwa tun daga yarintarta. Kallon idanun
mammina din na bata wani irin qwarin zuciya tare da bata qarfin gwiwar aikata
abinda take ganin bame yuwuwa bane ko ba zata iya ba.
"Shirya muje.....ya aiko a kiraki,ni zan tsaya miki koda hakan yana nufin yin baqin
jini,baqin jini a idanun sultane.......baqin jini a idanun morsa safiyyah".
Zame hannunta tayi daga na mammina,iya Kiran sunan morsa safiyyah kadai
ya sake harzuqa zuciyarta,sai ta juya da baya da sauri,ta kai hannunta kawai kan
dogayen rigunan dake zube saman gadonta,wadanda dukkaninsu sabbi ne,birra ta soma
gyarasu zata zuba mata a closet dinta tace ta barsu ta fice ta bata guri.
Duk yadda take jin zuciyarta ta tsayu amma sai