Showing 108001 words to 111000 words out of 168506 words

Chapter 37 - luu luu Book1 by Huguma

kuma ta zare idonta daga
kanta tana jin bata da lokacin bawa shehnaz amsar komai.

Duk da cewa tare suke takawa suna kuma komawa zuwa cikin gidan amma ba
wanda yace da dan uwansa komai,daga qarshe suka rabu a mararraba,akhnan tana wucewa
sashenta gami da bawa buhaina saqon ta aikawa nannie tace mata zata shigo.

Kafin ta gama hutawa a rest room dinta tuni barratu ta hada mata
lafiyayyen ruwan wanka kaman yadda suka saba. Ruwan wankan da kullum ake shiryashi
hawa biyu. Na farko ruwan ganyan gwanda ne daya zame mata abokin rayuwa dana ganyen
lalle,wanda akayi packaging dinsa ake mata order dinsa tun daga qasar china.
Kowacce safiya ganyen gwanda shine abu na farko da ake dafa mata ta shashi a
matsayin tea(anti aging ne,indai bakison tsufa ki gwada shansa kullum da safe,yana
hana tsufa da gyara fata sosai).

Mayukanta na amfani dukkaninsu organic ne daga mayuka na asali irinsu
man kwakwa da sukanzo a mazubi me kyau da tsada,a kuma batar masa da kamannin da
zaka kasa tantance wanne irin mai take amfani dashi?.

Wani irin kyau na musamman fatarta take dashi,kaman yadda glowing din
skin dinta yasha banban dana mutane da yawa,zaka tara mutane sosai baka samu me
fata me sulbi da jan hankali irin nata ba,wannan yana daya daga cikin abubuwan da
yasa take alfahari da kanta,take kuma sake kula da jikinta tare da bashi wani irin
tattali da muhimmanci.

Mintuna talatin ta dauka kafin ta fito,ta zarce zuwa spa room
dinta,dakin da aka ware na musamman da dukkan wasu nau'ikan gyaran kayan jiki da
'ya mace zata buqata dan qarawa fuskarta da fatarta kyau dama jikinta gaba daya.

Idan ka kalli dakin zaka dauka an wareshi ne don yiwa hamshaqan mata
gyaran jiki,irin tsadajjen gyaran jikinnan me aji da kuma tsada da daraja saboda
yanayin kayan aikin da aka ajjiye a gurin.

Wani abu ne daya zame mata jiki duk qarshen kowanne wata,tana ware rana
irin wannan ta shiga body steamer machine ta tsuma jikinta sosai da sassanyan
turarukan da batasan daga ina aka samar dasu ba.
(Asalin turarukan INCENSE BY KABO DAUGHTER,masu tsananin kama jiki da muhalli da
wani irin tattausan qamshi,tasted and trusted,ba tallan molanka bane +234 803 211
9803).

Wasu awanni biyun ta sake batawa wajen maintaining jikinta da gyara,bayan
ta shafe kanta da kwababben lalle shima da wasu sinadarai na musamman.

Dukka wadannan din sun zame mata jiki,ta tashi dasu tun batasan darajar
abun ba a gurin mammina.......asali daga wajen morsa safiyya aka fara mata,saidai
rashin sakewarta da morsa safiyyan ya sanya ta miqa komai ga hadimanta da kusan
dukka rayuwarta da kulawarta ta lura a hannunsu take,su kuma suna rayuwa da ita ne
cikin sassan mammina din.

Sosai mammina ta riqi bada umarnin yi mata gyaran hannu bibbiyu,har ta
girma yazo ya zame mata jiki. Wannan ya sanya ta zama wata ta daban........koda
cikin mata dubu nawa zata shiga zaka hangeta ta fita daban a cikinsu.

Glowing dinta,qyallinta da kyan fatarta daya cakuda da wannan
sirritaccen kyan na asalin buzuwa ya sake zama wani abu na daban a
gurinta,kwarjinin data debo daga jinin sultane shima ya qara zama ado a komai nata.

Tsaf birra ta tayata ta shirya cikin wata sassauqar doguwar riga ta
wani irin nau'in material da aka saqashi daga auduga da zare me daraja da tsada. Ko
yaushe shirinta yakan zama me jan lokaci,tamkar shirin amaryar da ake kan hidimar
aurar da ita,ahi yasa har yau har gobe tafiyarsu office dasu aisa bai taba zama
daidai ba,har gwara ma lokacin dawowarsu.

Sha biyu saura na rana,don haka ta qarasa dining room,buhaina ta ja
mata kujera ta dora mata falin yanki ta zauna,sannan ta bara'atu ta matso tana dora
mata wani yankin na musamman saman jikinta don kada wani sashe na jikinta ya baci,a
lokacin tana duba kiran da yake shigowa wayarta.

Daya daga cikin directors dinta na kamfani ne,saidai a yanzun bata
cikin mode na wani magana daya shafi kamfanin,tana jiran ta gama settling wannan
issue din dake gabanta tukunna,don haka ta maida wayar ta kife tana miqa hannu ta
karbi spoon din da bara'atun keta miqo mata.

Sama sama ta taba breakfast din,so samu tayi zamanta a kebantaccen
balcony dinta,to amma kuma nannie ce.......tun jiya tasan da dawowarta,ta kuma aiko
still an shaida mata,amma ta gaza zuwa,wata fuskar ai tafi gaban mari.

Kawai dai bataso ta yiwa zuciyarta fami ne,tasan kuma halin nannie
qwarai,bata tsoron ta mutu balle tayi rai muddin akan gaskiya ne.

Sultane yana matuqar ji da ita,ita kadai ta rage masa cikin 'yan
uwanshi hudi da yake dasu,su kadai suka rage a raye a duniya......don haka
dukkaninsu da idanun matsayi irin na sultane suke kallonta.

Miqewarta kawai ya gayawa birra me take nufi,don haka da sassarfa ta
koma ciki,ta kuma dauko mata sassauqar alkyabbar da bata da wani nauyi ta daidaita
mata ita saman kafadunta,sai tafara takawa kawai idanunta akan wayarta ba tare da
tace komai kota dubi kowa ba.

Yau din a cikin jininta takejin izza da kuma miskilancinta yana
motsawa,don haka duk inda zata wuce,dukkan wanda Allah yayi yaga gilmawarta zubewa
yake yana kwasar gaisuwa,duk kuwa da cewa basa samun damar ganin fuskarta,bara'atu
da birra dake biye da ita suke amsa musu da sautin GODIYA TAKE.

Daidai lokacin da aisa ke cikin katafaren parlour din nannie din,wani
irin parlour da wanzuwarka ta farko a cikinsa zai gaya maka zallar sarautar da
mamallakiyarsa take da jibi dashi.

Bai cika kayan alatu ba,amma komai na cikinsa me daraja ne da janye
hankali




zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 55
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me
kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse
masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk
wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri
kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai
gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma
suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah


Dukkaninsu suna zaune a qasan tattausan carpet din saqar hannu dake
mamaye da parlour din,aisan na kashingide gefan nannie din,dankwalin kanta a
qasa,yayin da waya ke riqe a hannun nannie da alama amsa wayar takeyi.

Sallamarta ta sanya dukkaninsu suka daga kai suna dubanta,aisa ce ta
amsa tana tashi ta zauna sosai,suka hada idanu,sai akhnan din ta janye dubanta daga
kan aisa din.

Ko batayi magana ba ta gama fahimtar abinda akhnan ke nufi......fushin
takeyi da gaske,haushinta takeji,to amma a irin wannan lokacin da idan ta hau
wannan qadamin fahimtar da ita yake zama abu me wahala,sai itama ta share kaman
bata fahimci me take nufi ba.

A hankali ta tako zuwa gaban nannie a qasa kamar yadda ta samesu,ta
zauna sosai tana tattare rigarta yadda zataji dadin zama,ta jingina da daya daga
cikin kujerun alfarma da aka qawata parlour din,wanda sam sam basu ci guri ba.

Qamshin daya motsa daga jikinta bayan zamanta ya sanya aisa dubanta. Ko
bata tambayeta tasan daga gyaran jikinta na wata wata ta fito,duk kuwa da cewa ita
din gwanar qamshi ce,bata tunanin akwai wani company na turare da suka qware wajen
fidda nau'ikan turaruka masu tsada da kama jiki da basusan da zaman akhnan din
ba,amma wannan qamshin nasu khumras da lab lab din incense by kabo daughter daban
yake. Wani qamshi ne da zai dinga saukar miki da nishadi,kaji zuciyarka tana wani
irin sanyi da saukar da cikakken nutsuwa.

Har kullum kuma a koda yaushe,a duk kowanne wucewar daqiqa idan ta
kalli akhnan mamaki take qara bata.

Da gaske ne.....kamar yadda take fada,kamar kuma yadda ta saba
fadi.....bata rasa komai ba.......Allah ya bata dukkan wata cika da siffa da
kowacce diya mace zataso ta mallaka......Allah ya bata wasu irin qualities da
kebantattun abubuwa masu yawan gaske.....a zahiri a iya abinda idanu ke gani bata
da wani sauran naqasu ko buqata........amma ta kowace fuska da kowa ke iya hange
mata tana da buqatuwa zuwa AURE......abu dayan nan da har yanzu bata gamsu da cewa
haka yake ba.

Har yau har kwanan gobe,har jiya da yanzu babu wani dalili guda daya da
take basu ko zata basu kan haka,abinda kuma har a yanzun yake bawa aisa mamaki
kenan da daure mata kai.

Wannan dalilin guda daya bai kai mizani ba.....QASAITARTA DA IZZARTA da
kuma surki na GIRMAN KAI a wasu lokuta,basu gaya mata daidai din cewa......su kadai
sun isa su mallake su kuma mamaye gami da ci gaba da riqe mata rayuwa ba har izuwa
ga bigiren da ya dace da ita.

Hankalinta yana a kan waya,amma kunnuwanta na wajen nannie. Sai data
zauna din sosai sannan ta fuskanci da HAIRAAN take wayar.

Sau da dama takan manta da hairaan din shaf cikin mutanen dake
existing a rayuwarsu. Tana mantawa da ita kwata kwata cikin babin rayuwarsu. Duk da
kasancewar hairan din mutum me wani irin zuciyar zumunci......son duk mutumin daya
rabi rayuwarta,da kuma girmama babba,wannan yayi sanadin da ta maida nannie qanwar
mahaifinta kuma kaka a wajen ta ta halak malak.
Idan hairaan tana nan,ba zaka taba banbance wata haifa ba tsakanin
aisa da ita,idan hairaan tana nan,zaiyi wahala ka dauka morsa safiyya ce mamanta ba
nannie ba,idan kaga sabanin hakan,nannie din bata nan ko kuma tayi wani balaguro.

"To Allah ya kaimu......ya nuna mana cikin amincinsa da yardarsa......ma sha
Allah......ga biftu" Ta fada tana miqawa akhnan wayar kai tsaye.

Wani abu ne da batayi tsammaninsa ba,ba wani magana ko waya suke da
Tante ba(kamar yadda falaak ke kiranta dashi),duk da hairaan din tana da wani irin
kirki da jan 'yan uwanta a jikinta.

Ko yaushe fuskarta shimfide take da fara'a,kamar yadda lokaci lokaci
takan duban akhnan din koda ta watsapp ne,ita dince bata damu da duba hakan ba.
Idan ta nemeta shikenan,idan bata nemeta ba koda tsahon shekaru nawa ne ita din
bame damuwa ta nemeta bace.

"Biftu na" Hairaan din ta fadi da salon kirkinta da kulawarta kwatankwacin wadda
take nunawa falaak,saidai har yanzun ita din ta kasa jin haka har zuciyarta.
Kamanni da kuma murya na hairaan dukkaninsu ta debo na morsa safiyya ne,wannan
dalilin ya sanya kowanne qoqari na kawo kusanci tsakaninsu yake wargajewa a zuciyar
akhnan.

"Bonjour" Ta fada a taqaice da muryarta da tayi wani sanyi a yau da yake nuna
batason magana.

"Bonjour,comment ça va?" Ta maidata mata muryarta cike da nishadi.

"Alhamdulillah" Ta sake amsa mata bata wani jin armashi a gaisuwar.

"Fatan komai lafiya......ya sahel couture"

"Alhmdlh" Ta sake amsa mata,don tana jin bata da amsar data wuce wannan.

"Allah yayi jagora........muna kusa da zuwa gida in sha Allah,kafin qarshen
shekarar nan". Idanunta ta lumshe ta kuma budesu,tana jin bata da wani hadi sam da
wannan labarin.

"C'est bon" Ta sake fadi a taqaice.

"Ma sha Allah,Nous nous reparlerons bientôt in sha Allah(zamu sake magana nan kusa
in sha Allah).

Zare wayar tayi kawai daga kunnenta tana ajiyeta kuda Nannie.

A nutse nannie ta kalleta tana qoqarin karantarta,sai ta janye
idanunta,cikin nutsuwar nan dake cakude da qasaita tace.

"Barka da warhaka......" Sai da nannie din ta gyara zamanta,tana kuma karantar
yanayin boyayyar damuwa qasan ran akhnan din sannan ta amsa.

"Barkanki dai......."

"An dawo lafiya?,Allah ya karbi ibada"

"Ameen summa ameen" Nannie ta amsa can qasan ranta cike fal da maganganu,saidai
yanayin da take karanta tattare da akhnan din yana nuna mata abubuwa da yawa. Da
yawan yawan abubuwan da take karanta din mamaki suke bata. Wanne irin mugun tunani
ne a ranta har haka da fidda mijin aure yake zame mata babban abun tashin hankali
ko kuma damuwa a tattare da ita?.
"Abubuwa da yawa sun faru sanda bana nan biftu.......mene damuwarki ne?,akwai wani
abu ne daya kamata a sani wanda baki fadeshi ba a zahiri?" Ta furta da sigar
lallashi,tana tunanin ta wannan hanyar zata samu kamo bakin zaren damuwar akhnan
din.

Blue eyes din nan nata ta juya kadan tana janyesu cikin jin gajiya da
yi mata maganar kowanne d'a namiji. Tana ganin basu kai matsayin da rayuwarta zata
fuskanci takura irin wannan har haka ba......tana da 'yancin da zatayi rayuwarta
ita kadai,don bataga ta inda hakan ya sabawa addini ba muddin tana da qarfin zuciya
dana gwiwar rayuwa ita daya.

"Ina saurarenki" Nannie ta sake fada tana bata dukka hankalinta. Tsam aisa ta miqe
da zummar basu guri,amma sai Nannie din ta zube mata idanunta.

"Dawo ki zauna......kunfi kusa da ita akan kowa,qilan akwai wani abun da bamu san
dashi ba,ku zaku fimu sani......qilan akwai wani abun da ita ba zata iya fada ba,ku
zaku fada" Tayi maganar cikin maida hankalin nan nata akan komai.

Wuya ta karyar tana duban Nannie din,idanunta na nuna dukka
gajiyawarta.

"Nannie.......dama dai baki sani a wannan batun ba,don Allah kice na tafi" Ta fada
tana burin hakan,don daga ita har shehnaz bata tunanin akwai wanda ya yiwa akhnan
fahimta ta haqiqa akan wadannan tsare tsare nata.

"Aisa!.....zama nace kiyi" Nannie ta fada da yanayin daya tabbatarwa aisa bada wasa
take ba,don haka ta koma ta zauna a hankali.

"Ehmmn.......ina jinki biftu" Ta sake maida tambayarta kan akhnan tana tsareta da
kallonta. A nutse ta juya kanta,tana jin tuhumar Nannie takai mata ko ina. Koda ta
fada fadin baida wani amfani,don bata zaton akwai ranar da zatazo su fahimci juna
ita dasu.

"Nannie......bana buqata......ana aure ne idan ana buqatarsa,iya rayuwata a haka ta
gamsar dani Nannie ku fahimci haka......aure baya burgeni,koda nace zanyin zai
zamana tawaya ce kawai ga martabata da mutuncina........bada umarni da
karba........"

"Ungo nan" Nannie ta furta cikin tsananin mamakin maganganun bakin akhnan da
manufofinta da har yanzu basu canza ba.

"Biftu?......khadeeja?,hankalinki guda kuwa?" Manyan idanunta ta lumshe,cikin
ranta tana jin sassaucin da ba wani hadimi ko daya a gurin da Nannie tayi mata
haka,ta san kadan daga aikinta,yin hakan gaban hadimanta bazai zame mata wani abu
me wahala ba.

"Aure cikar kimar maca ce ko kinqi ko kinso,duk wata daraja da martabatar d'iya
mace ta ta'allaqa ne kan aurenta,shine mutuncinta,ko gawar me aure da maras shi sun
banbamta gun daraja......" A hankali aisa ta sanya fuskarta tsakanin siririn
mayafin kanta. Yau akhnan ta ja musu,bawai iya kanta kawai ba,harsu tasan yau
Nannie saita tayar da dukkan wani tsohon ballinta a kansu.
(08187255872 lu'u lu'u paying)

"Me yake daurarki ne biftu?......me kike tunani?" Ta sake maimaitawa tana dan fidda
idanunta akan akhnan nan. Kasa amsawa Nannie tayi,don zuwa yanzu maganganunta sun
fara juyewa suna mata kama da maganganun morsa safiyya,dukkan alamu kuma suna nuna
akwai wani qaqqarfan connection a tsakaninsu.
Hakan bazai bata mamaki ba,tasan cewa komai matar zata iyayi don
shiga tsakaninta da duk kowa da zai nuna so qauna ko kulawa a kanta.......takun me
martaba kaf ya isheta mizanin da zata dora girman qiyayyar da morsa safiyyan take
mata,da wannan mammina keson ta karbeta da irin karbar da ta yiwa mammina?......ta
bata matsayin data bawa mammina?.......ta dorata daidai da mizanin data dora
mammina akai?.....bata jin abune da zai yuwu sam.....har gaba da abada ba zata
daina lasaftata a mazaunin manyan abokan adawarta ba......har abada ba zata daina
irgata ba a mazaunin halittar da bata qaunar farincikinta ko walwalarta ba.

Idanunta kawai ta maida ta lumshe tana jin saukar maganganu da fada
daga bakin Nannie din irin wanda bai taba shiga tsakaninsu ba.

Nannie din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login