Showing 96001 words to 99000 words out of 168506 words

Chapter 33 - luu luu Book1 by Huguma

iya hangen mutumin da dukka jikinta da
zatonta yake bata tabbacin shine baqon nata.

Matashin saurayi ne,fari sol dashi,me wani irin haske da yake bata
tabbacin BUZU ne d'an qabilarsu,ko kuma wanda yake da alaqa ta asalin mutanen
Istanbul na daular turkiyya.

Kaman ragowar mutanensa,sanye yake shima da baqaqen kayan da suka
mugun shan banban da na jikin mutanensa. Saboda shi din trouser ne da shirt a
jikinsa da suke bayyana irin asalin tsadar da yadin da aka samar dashi yake dashi.

A tsaye yake yadan bada baya yana amsa waya,hannunsa daya soke a
aljihun wandonsa yana dan tattakawa daga hagunsa ya koma dama.

Idanunta taja ta lumshe tana jin wani baqinciki yana kamata. Ko na
qiftawar idanu......koda na qaramin taqi bata ga wani dacewa ko hadi ba ko guda
tsakaninta da shi ba.

Bata ma hangi wani kamala a tare dashi ba......baiyi zubi ko
komanceceniya da mutanen da sukasan meye ma'anar class ba a cikin dabi'unsa da
halayensa ba.

"Wow" Kalmar ta sauka a kunnenta sanda take dab da isa gurin,lokacin da bacin ranta
yake sake ninkuwa a duk sanda take qara taku zuwa gabansa.

Manyan blue eyes dinta ta daga tana dubansa,wani irin kallo yake qare
mata daga samanta har qasanta,fuskarsa shimfide da wadataccen murmushin dake nuna
zallar maqurar burgeshi da tayi. Duk kuwa da cewa baya iya ganin komai tattare da
ita banda kyakkyawar fuskarta. Baya iya ganin komai nata sai zara zara yatsun
hannunta data sanya ta dafe bayan kujerar data ja tunga kusa da ita tana kasa
qarasowa.

Wani irin abu ne yaji yana mamayarsa me girman gaske dangane da ita.
Iya tsahon rayuwarsa,idanunsu basu taba sauka akan wata mace da yaji ta burgeshi
haka irinta ba. Bai taba sauka akan wata mace da yaji ta sauke dukkan alfaharinsa
ba sai a kanta.

Ya lumshe idanunsa kana ya budesu yana imagination dinta a mazaunin
matarsa. Tabbas zai zarce sa'a,zai kuma sake zama na daban.

Tun daga samun damar ganawa da ita a karon farko ma ba abu bane me
sauqi,long process ne da baisan watanni nawa daddynsa ya dauka ba kafin ya samar
masa izinin.

An gaya masa,ya kuma ga alama......da gaske tana da izza,tana da
qasaita,akwai jinin sarauta sosai tattare da ita,ya gani kuma a yanzun.

Tsaiwarta kawai wani abu ne me burgewa a idanunshi,sai ya kasa riqe
kansa,ya kuma kasa controlling kansa,ya kasa jiranta har sai ta qaraso,duk da
warning dinsa da yayarsa tayi.

"Irinsu basason a fiya zaqe musu......irinsu suna son namiji ne me izza irin tasu
ko kuma wadda tafi tasu.....ka kame kanka ramadan......karkayi saurin bada
kanka.....duk da na sanka,kana da irin aji da quality din da kowacce mace ke
so,amma muddin kaci nasarar sato zuciyar the princess of agadez kingdom.......to
mun sake samun qarin wata martabar ne da daraja,koda a cikin family zamu sake
daukakuwa fiye da daukakar da muke da ita a yanzu".

Tazarar da ya bari a tsakaninsu bata da yawa,ya tsaya qyam a gabanta
yana ci gaba da kallonta. Yana jin kansa kamar zai narke a gaban nata,dukkan wani
surori na kyau,dukkan wani hasashe da yakeyi ashe nisa dake tsakaninsu ya rage
komai?. Wata irin ingantacciyar fata ce da ita dake tarwai kaman zaka hangi komai
dake yawo tsakanin bargo da tsokar jikinta,kamar batasan wani abu da ake kira da
qura ba sam sam.

Kyawawan idanunta da ba Kasafai aka fiya samunsu a nan ba......sunfi
yawa tsakanin mutanen Asia da sauran qasashe. Cikakkiyar girarta da kuma gashin
idanunta zara zara da suka qarawa fuskarta kyau da kwarjini.

Cikin mintunan da basu haura biyar ba taji wani irin bacin rai yana
saukar mata. Ta tsani yawan kallo,ta kuma tsanu kallon qurilla,koda daga gurin 'yar
uwarta mace ne ballantana a jinsin maza.

Zaro hannunsa yayi daga aljihun wandon nasa,yana jifanta da wani irin
murmushi da yasan yana da matuqar tasiri gurin 'yammata da yawa,ya miqa mata hannun
yana fadin.

"Sunana Aabood ramadan farree,ni d'ane ga ambassador ramadan farree,duk da nasan
zaki sani,mahaifina sanannen mutum ne ba boyayye ba,babban mutum ne a qasar
nan.........zamu iya......". Lallausan hannunta da babu d'igon komai ta daga masa
tana duban tsakiyar idanunsa. Cikin muryar nan tata dake cike da izza ts soma
magana.

"Ba filin sanin salsala da nasaba mukazo ba......a taqaitattun jimloli bakayimin
ba......" Ta qarashe maganar tana juyawa don barin gurin. Da hanzari ya tako ya
kuma sha gabanta yana qoqarin controlling tashin hankalin da yaji ya shiga.

"Ya da sauri haka?......ya kuma da gaggawar yanke hukunci haka?,ai kamar ya kamata
ki bamu dama da lokaci koda mintuna biyar ne mu gama sanin juna".

Wani irin kallo ta daga idanunta ta watsa masa. Qasan ranta takeji eh
lallai.......sultane yana dab da sarayar mata da daraja mutunci da dukka
kimarta,wannan ruhin me dimbin daraja da tsada sultane na dab da maidashi wani abu
maras kima ko qanqani.

"Mintuna biyar?,ka kuwa san da waye kake magana har kake neman mintuna biyar daga
cikin tsadaddun lokutanta?,banda darajar sultane kana tsammanin har ka mutu kana da
darajar ganin fuskar akhnan muhammad hammud ne?". Ta qarasa maganar tana jin ranta
yana sake dugunzuma.
Sak yayi yana kallonta,yana jinjina izzarta. Kalar izzar da tasa ya
raina dukkan wata izza tasa da ake batun yana da ita. Kalar izzar data sanya yaji
ya soma dulmiya a kogin sonta,tako ina yana jin tayi masa.

"Amma dai da zaki daure ayimin wannan alfarmar......beside ma bansan me zance da
daddy ba a kanki......"

"Ka fadi mishi dukkan abinda kaso wannna matsalarka ne.......amma dai karka canza
daga abinda akhnan ke akai yanxu......akhnan ba matarka bace.....don bakayi mata
ba" Ta fadi tana ci gaba da taku zata gotashi.

Bisa tsautsayi ya miqa hannu don dakatar da ita,ganin kalaman baki basu
isa su dakatar da ita ba,yayi nasarar riqo gefen mayafinta yana fadin.

"Silvouse plaît" Cak ta dakata,qirjinta yana wani irin luguden duka. A tsahon
tarihin rayuwarta,idan ka cire sultane......babu wani d'a namiji guda daya da taba
samun damar kama koda zaren da aka dinka tufafinta dashi,bare ya riqe mayafin dake
yane a jikinta.

Baisan girman kuskuren da ya tafka ba,shi ya sanya yaci gaba da tsara
mata kalaman da yake ganin zaisa ta fuskanceshi. Tsakanin buhaina birra da yalwa
basusan waye yafi wani gigita ba da ganin irin kalar kuskuren da abood ramadan ya
tafka ba,saidai dukkaninsu basu kai ga tantance abinda zai iya faruwa ba qarar
saukar marin ya isa ga kunnuwan mutane da dama......cikinsu kuwa harda haisam da
falaak wadda ta gaza motsi tun sanda akhnan ta fara magana da abood. Tun shigowar
akhnan din tajishi saboda gurin daya ne,wasu tsararrun shukoko ne masu tsaho da
kauri kawai suka banbamta gurin.

Cikin wani irin razana da tashin hankali falaak ta daga idanunta ta can
qasa tana satar kallonsa sanda yake ci gaba da sauraron karatun Aafreen.

Ba wani yanayi dake fuskarsa daya canza. Bataga alamun ma yaji komai
ba,abinda ya sanyata a dimbin dimauta da kuma kokwanto.

Babu ta yadda za'ayi yace baiji abinda ya faru ba,tun daga shigowar
biftu gurin baqinta har kawo yanzu ba. Tayi imanin koda kana nesa da inda su suke
karatun xaka ji komai ballanta a nan din inda suke zaune koda takun sauke qafafu
saman ganyayyakin da suke zube a qasa kana iya jinsa.

To amma me yasa yayi kamar baiji ba?,me yasa yanayinsa ya nuna baiji
komai ba?.

Qanqame hannuwanta da idanunta tayi sanda kalaman akhnan na qarshe cikin
tsananin fushi suke fita.

"Idan kai mahaukaci ne ya kamata kasan guraren da zaka dinga gwada
haukarka.........in bakayi wasa ba tabbas ba zaka fita daga masarautar agadez da
qafafunka ba,zan ganar dakai kuskurenka.......ka gaggauta kwashe karnukanka ku fice
mana a masarauta,domin nan din ba bariki bace"

"Me yasa yaa biftu?......me yasa?" Falaak ta fada can qasa tana jin jikinta yana
daukan rawa.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 47
__________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me
kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse
masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk
wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri
kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai
gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma
suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
____________________________



Ba ita aka mara ba amma tana jin saukar sautin marin har yanxu,tana jin
takun akhnan da yalwa ke faman sanyayawa rai

"Allah ya huci zuciyarki shelelen sultane,.......Allah shi baki haquri......ya
tafka kuskuren nan ne duk a rashin sanin wacece ke......ayi masa afuwa da gafara"
Har taji takun nasu ya mata nisa alamun sun fice a wajen.

Da qyar ya iya riqe numfashinsa zuwa sanda Aafreen takai qarshen surar.
Ya maida bangon qur'anin ya rufe yana qoqarin controlling hannunsa ya furta.

"Ma sha Allah" Yana miqa mata qur'anin.

"Yaaa falaak" Ta tsinci muryar Aafreen tana kiran sunanta,abinda ya dawo da ita
hayyacinta kenan. Ta daga kanta da sauri sai suka hada idanu,ba shiri ta maida
kanta qasa. Kusan sakanni goma bai sake cewa komai ba,kafin a nutse yace.

"Ki tabbatar kin ajiye komai daga bakin qofar nan kafin ki shigo aji,nafi buqatar
koya karatu ga wanda yasan girman abinda nake koya masa din........na biyu
jilbab,ki nema jilbab wadatattu da zaki dinga zuwa daukan karatu dashi......na
uku....." Sai yadan dakata kadan yana daidaita numfashinsa.

"Ki nemi wadda zaku dinga zuwa karatu tare da ita,bazai yi ajinki ya zama ke daya
bace" Ya fadi yana jin komai dole ya zama bisa tsari na shari'a. Baya taba yarda da
batun kebewa koda wane muddin macace don kiyaye hukuncin Allah da haqqin addini.

Kai ta jinjina a hankali tana sake yin qasa da kanta,mamaki kuma yana
sake kasheta. Dan siririn murmushi ya saki yana miqawa Aeera me shekaru hudu hannu.

"Ilallliqaaa" Ya furta da tataccen larabcinsa,sai yarinyar ta saki murmushi itama
tana maida masa amsa.

"Liqa'ana bi khair" Duk da qarancin shekarunta tana jin yana burgeta,tana jinsa
kamar wani abbanta ko yayanta.

"Yaa falaak.......an tashi fa" Aafreen ta fadi wadda ta miqawa ramma litattafanta
ta tsugunna tana qoqarin sanya takalman qafarta.

"Zan taho yanzu" Tace dasu tana miqawa ramma litattafanta. A girmame ta amsa,taja
hannun yaran suna wucewa.

Tsam ta miqe,ta zura lausasan takalmanta tana jin jikinta gaba daya
ya sake,zuciyarta kuma tana cakuduwa da wani irin yanayi guda biyu.

Takawa ta dinga yi a hankali,har ta zagaya ainihin masaukin baqin akhnan
din. Wasai yake babu kowa,alamun an gama,kuma kowa ya kama gabansa. Da wani irin
mutuwar jiki ta qarasa ta zauna saman daya daga cikin kujerun dake a wajen ta
zauna.

Wai meke damun yaa biftu ne?......mari?,marin ma a fuskar namiji me
cikakken hankali da kuma shekaru?. Ta yaya har take da zarra da qarfin halin d'a
namiji?. Yaushe zatayi aure?,yaushe zata fahimci aure yana zama wajibi akan mace
irinta?,sai yaushe zata daina raina maza har haka?.

Yadda qarar marin ya riskesu ya dawo mata,takai hannunta fuskarta tana
shafawa. Me yasa yayi kamar baiji komai ba?,me yasa yayi kamar baiji abinda yake
faruwa ba?. Ta tambayi kanta bugun zuciyarta na qara gudu da iya tunawar da tayi
kadai da fuskar sa.

"Saboda bai shafeshi ba,ba huruminsa bane" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa
nakai tsaye,amsar data sanya murmushi subucewa daga fuskarta duk da ba a yanayin
take ba.

Wannan shine kalar saurayin da yake burgeta,wanda ba ruwansa da
shishshigi.....kalar mutumin da sam baya shiga sabgar da ba tashi ba.....MISKILI NE
kenan da gaske?" Ta yiwa kanta tambayar tana rungume hannayenta a qirji.

Daga kanta tayi sama,duhu ya fara raguwa sosai,alamun dake nuna
magariba tana dab da qarasowa,saita miqe a nutse tana sake harde hannayenta a qirji
tana kuma takawa don ficewa a gurin.

Saidai har yanzu murmushi yaqi barin saman fuskarta,tana ta jimami
tanata kokwanton ba zasu samu kaman oustaz Ousmane ba........sai ga wani da yasha
banban dashi ta kowacce fuska. Ba karatu yayi mata ba yau din,yau din ta cika ne
kawai da tarin tambayoyi,amma yanayin tsarin da ya aza nasa karatun ya bata
gamsuwar dari bisa dari shi na musamman ne.

Amma ya cika izza da yawa,kaman akwai tasirin sarauta a jininsa,dukka
motsinsa da yanayinsa ya mata kama da wani basarake ko masarauci,saidai ba wata
qwaqwarar shaida daya nuna hakan,ta yaya karatun zai kasance?" Ajiyar zuciya ta
saki nannauya tana kai tafukan hannuwanta ta shafi fuskarta.

"A hankali falaak,wannan dogon tunanin duka na meye haka?" Ta tambayi kanta da
kanta,tambayar data sakata sakin murmushin dole.

"Tsarinsa ne da yanayinsa kawai yayimin" Ta bawa kanta da kanta amsa,batasan ko
tayi daidai ba ko batayi ba,iya amsar da takejin zata iya fita daga zuciyarta kenan
a daidai wannan lokacin.


*AKHNAN*

Ko sassan mammina batayi sha'awar komawa ba ta dakatar dasu yalwa tun
daga farfajiyar data raba sassan sannna ta wuce sashenta. Tun a falukan farko ta
dakatar da kowa,tace dukkan wani motsi bata sonshi,kowa yayi nesa da inda take ta
wuce kai tsaye zuwa dakinta.

Da kanta ta dinga zare kayan jikinta tana watsarwa,tana jin tsanar
suturar tana mamayarta.

Irin abinda take gudu sultane yake shirin jawo mata?,wannan din shine
mutum na goma sha biyu cif da sultane ya tilasta haduwarta dashi,yanzu har
yakai?,har yana da zarrar kama gefan mayafinta?.

Kuka take so tayi,amma sai takejin bashi da martaba da darajar da zata
zubda masa hawaye. Bashi da wannan alfarmar da hawaye zasu zuba a idanunta ta
dalilinsa,kawai abu daya takeji......kaman ya kamata hukuncinsa yafi marin da tayi
masa.

Toilet ta shiga,ta sake wanka gaba daya,tana jin kamar ya samu nasarar
taba jikinta ne ba mayafinta ba. Ta wanke jikinta sosai tana jin kamar ta sauya
fatar jikinta,ta fito daure da towel fuskar nan cike da wani irin fushi.

Ta jima zaune tana jira ruwan jikinta ya tsane da kansa,don ko samun
damar gogeshi batayi ba,zuwa sannan kuma har ta jiyo kiraye kirayen sallar
magariba,don haka ta miqe a kasalance ta shige closet dinta tana laluben kayan
sawa,abinda bata saba bata ma iya ba,wannan ya sanyata kafin ta kammala ciro wani
up and down skirt da blouse dinsa da dan madaidaicin scarfs dinsu taji ta gaji
tubus.

Gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta,har yanzu zafin abun takeji
har cikin fuskarta. Ba wanda zata nema,ba wanda zatayi magana dashi har sai sun
nemeta da kansu.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

Wani irin kyau kayan sukayi mata,sun fiddata kamar 'yar qasat turkiyya
din,ta aza abayar sallarta a sama ta tayar da sallah.


*MAMMINA*


Tunda suka fita da yalwa tana zaune daga bakin babban window din da
yafi kama da qofa,wanda ya bada wani irin yanayi me kyau da take iya hangen lambun
dake liqe da sassanta.

Wayarta na a hannunta tana duba fuskar wayar lokaci bayan lokaci,yayin
da gabanta ke shaqe da nau'ikan kayan ciye ciye na kayan marmari.

Idan tace hankalinta akan akhnan yafi rinjaye tayi qarya,a yau
hankalinta na saman wayarta fiye da kan akhnan din.

Takun da taji ya sanyata juyawa da wuri. Ayaana ce take takowa a
nutse,ta yarda qwarai da hankalin ayaana,wanda wannan yarda da hankalin bawai ta
sanya ayaana ta samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login