Showing 9001 words to 12000 words out of 168506 words

Chapter 4 - luu luu Book1 by Huguma

kunnen
akhnan. Da gaske take,tsarin da yanayin ya burgeta,yanayin da ya sanya cikin
jikinta takejin kamar akhnan tayi miji........kamar altaab din zai dace zaiyi kuma
daidai da tsarin akhnan.

Baki kadan akhnan ta tabe,saidai bata ko motsa labbanta ba ballanta
tace komai da aisa. Bata jinta cikin yanayin magana,koda kuwa tana da jin cewa wani
abu tasan wannan banbancin dake a tsakanin tunaninta hangenta dana sauran al'umma
ya zama babbar katanga kuma hijabi daga fahimtar ma'anoninta motsinta da
maganganunta.

Kamar a cikin jikinsa yake jin tahowarta......kamar a cikin jikinsa
yake jin alamun fuskantowarta zuwa muhallin da akayi masa mazauni,saiya daga kansa
a hankali daga duban Mac book din da yakeyi,yayi kyakkyawan gani kuwa ta hanyar
zube idanunsa a kanta lokacin da take takowa d'ai d'ai da qasaitaccen takunnan
nata.

Wani irin abu ne me qarfin gaske ya harba daga tsakiyar qirjinsa zuwa
zuciyarsa........wata mummunar faduwa gabansa yayi,sai ya lumshe idanunsa can qasan
zuciyarsa yana gayawa kansa.

"Ka nutsu altaab". Tsahon second biyar sannan ya sake bude idanunsa yana maidawa
kanta da wani irin qwarin gwiwar daya samu ya arota da qarfin cin tuwo.

Ba sau daya ba,ba kuma sau biyu ba yakejin labarin kwarjinin da take
dashi. Sau da dama......sau tari kuma siririyar dariya yake saki,shine fa
altaab........altaab nu'uman sirreen?,har akwai dama wata halittar diya mace da
zatayi masa tasiri da girma?,har akwai wata qwayar halittar KWARJINI da zata
sanyashi ya gaza fuskantar diya mace ko wacece ita?,komai girma da
izzarta......komai qarfin ikon masarautarsu?......kai koda hurul'eeni ce.

Daga sanda girma ya ruskeshi.......shekaru suka cillashi zuwa matakin
samartaka baisan adadin matan da suka soshi ba.......baisan adadin matan da yayi
soyayya dasu ba.........baisan adadin matan da ya sanya kuka a kansa ba.......sai a
yanzun 'yar sarkin AGADEZ zata gagareshi?.

Bai santa ba,......bai kuma taba katarin ganin koda gilmawarta ba
bare akai ga ganin hotonta.....wani abu daya fuskanci yana wahala shine.......sanin
ainihin fuskarta da kuma kamanninta,duk kuwa da cewa SHUGABA ce kuma CEO ta babban
kamfanin da kaf nijer babu na biyunsa. Babban kamfanin da ida kace baka taba sanin
sunansa ba ko bakasan da zamansa ba kayi gawurtacciyar qarya.

Tana da wani irin dogon tsinkaye.......iya nazari da kuma karantar
komai da wani irin kaifin basira dana idanu. A yanzun da take takowa tana sake
fuskantarsa kwata kwata hankalinta bai tare da aisa dake fasalta mata altaab din da
yadda take tsammanin samun dukka wani quality da take buqata tattare dashi.

Inda a yanayin nishadi take tabbas zata yiwa aisa murmushi ne,a yau ta
yarda ta kuma sake yarda da gasken gaske ita din tasha bamban da kowa.......kamar
yadda take diyar MUHAMMAD HAMMUD tallin tal! Haka dabi'unta dama zabubbukan
rayuwarta sukayi nesa dana kowacce mace dama kowanne mutum.

A abinda baifi taku goma ta riskeshi ba ta gama tantance
altaab.......ta kuma tabbatar cewa YA FADI bazaici ba ba kuma zai tsallake
sharuddan da take neman ya cikesu kafin ya samu nasarar mallakarta ba.

Duk da cewa tana qare masa kallo ne amma koshi da ake kalla din bai
fahimci shi take kalla ba......tsaiwarta a gabansa ya sanya wani abu tsarga masa
tun daga qasan tafin qafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Hakanan ya samu kansa da
miqewa da dan hanzari,ya miqa hannu yana jifanta da murmushi,ya dawo da daya daga
cikin kujerun dake wajen daura da tasa yana fadin.

"Barka da fitowa......marhab". Har yanzu idanunsa na a kanta yana jifanta da wani
irin murmushi hadi da sanya hannunsa ya sauke nadin rawanin daya rage bayyanar
fuskarsa gaba daya zuwa qasan habarsa......murmushi da ya jima da sanin cewa,yana
daya daga cikin abinda yake narkar da zuciyar 'yammata.......yana daya daga cikin
abinda yake qara masa kyau tare da fidda zatinsa.

Wani irin abu na daban yakeji a kanta,wani irin yanayi da bai taba
tsintar kansa a ciki ba game da kowacce d'iya mace ba.......tabbas inda yasan yadda
AKHANAN take.......da ya jima da nemawa kansa ita. Sai yakejin kamar daya daga
cikin matan dake aljanna ce aka sauko da ita gidan duniya.

"Na tsani yawan kallo" Kalamanta suka shiga kunnensa da wani irin kaifi da sautin
muryar da yanayin amonta ya tilasta masa kubcewar ajiyar zuciya.

A nutse ta taka zuwa wata kujerar ta daban da wadda ya ajiye mata,har
qasan ranta tana jin tambayoyinsa shikam masu sauqi ne idan har zai iya amsasun,don
bata jin kwata kwata zai iya shallake sharuddanta. Inda zata iya,zata zabi tsaiwa
akan zama harta sallameshi,saidai bata jin hakan ya dace da darajarta da
ikonta.......baqo ya shigo cikin masarautarta ya kuma zama dalilin tsaiwarta saman
qafafunta.

"Waye kai?" Ta jefa masa tambayar bayan ta zauna sosai cikin kujerar,ta kuma aza
qafarta daya saman daya da wani irin salon zama dake sake tabbatar da izza da
qasaitarta.
Sauke idanunsa ya somayi akan qafafun nata,duk da ko farcenta bai
samu daman gani ba amma salon zaman nata sai yaji gaba daya ya tafi dashi. Karon
farko da yaji ya soma d'ari d'ari,ya kuma soma raina qarfin nasu ikon da a baya
yakejin ba wata masarauta ko sultane da yakai mahaifinsa,ballantana azo Maganar
'yan'yan iko irin na nasu masarautar.

Tambayar tata ta bashi mamaki sosai,ya maida dubansa saman fuskarta
yana son karantar gaskiyar tambayar tata. Abu na farko da yayi tsammanin fara ji
daga bakinta shine tarba........ban gajiya sannu da hanya bisa tattakin da yayi har
zuwa gareta,koda ace babu gaisuwa cikin tsarinta. To amma duka ba wannan
ba........shi ALTAAB ne bata sani ba?.

"Da gaske bakisan waye altaab ba?.......altaab nu'......" Daga masa hannu tayi tana
alamta dakatar dashi.

"Ka fadi matakin farko........waye kai?" Ta sake jefa masa tambayar tana ware
manyan idanunta saman fuskarsa,idanun da suka sanya gabansa sake tsananta faduwa.

Yasha ganin blue eyes iri daban daban amma ba irin nata
ba........yasha ganin idanuwa masu shape da launi daban daban amma banda irin
nata.....natanne da gaske ko itama tana amfani da qwayar canza launin idanu?.

"Na tsani kallon qurilla" Ta furta a hankali tana ware yatsunta suka zama guda
biyu.......

Motsin da tayi da yatsunta guda biyu kadai suka baiwa birra dake
zaune daga qasa a gefanta alamar mataki daya ya ragewa altaab ya rasa damar ganawa
da akhnan din.

Wani abu ya hadiye fargabarsa taba qaruwa,fargabar rasata,fargabar rasa
damarsa. A baya bai zurfafa da yawa haka a kanta ba,don baisan yanayinta ba baisan
kuma yadda take ba,amma a yanzun da idanunshi suka gauraya a kanta sai yakejin
dukka burinsa na duniya ya ta'allaqa a kanta,duk burinsa na duniya ya rataya ne
akan son ta zama MALLAKINSA,don haka ya hadiye dukka mamakin da take bashi hade da
wani yawu daya zarce zuwa maqogoronsa ya fara magana.

"Sunana altaab dan sarkin tahoa sarki nu'uman......nine d'ansa na farko daya haifa
kuma magajinsa da zai maye gurbinsa nan ba da jimawa ba in sha Allah........"
Yatsunta na hagu ta kada masa,abinda ya fahimtar dashi dakatar dashi takeyi.

"Ba wannan nake nema ba.......waye kai A DUNIYA........wacce daraja gareka bayan
SARAUTA?.......da wanne abu kake jin zaka iya mallakar AKHNAN?" Cak komai yaso
tsaya masa,saboda tambayar tazo masa a sanda bai shirya mata ba,tazo masa ne a
sanda baiyi zaton akwaita ba.

Dukka jarumatar da yakeji yana da ita ya tattaro guri guda,wani sashe na
zuciyarsa na qarfafashi ta hanyar tuna masa.

"Kaine fa wannan altaab din da mata ke kuka a kanshi.....kada ka bada maza mana
altaab......kada ka bari 'yar sarkin AGADEZ tayi nasara a kanka......ka kafa
tarihi.......a kuma kafa tarihi a kanka,kayi nasarar da maza da yawa da suka nemi
mallakarta suka kasa kafashi.

Wannan qwarin gwiwar daya samu ya sakashi sakin murmushi.

"Wannan ai tambaya ce me sauqi........ko waye kuma kika tambaya koda bani ba zaki
samu amsarta.........sanin kowa ne mahaifinmu babban attajiri ne daya tara mana
dukiyar da bana tunanin ko dan jika a zuri'armu zaiyi wahala a rayuwa.......komai
da muke da buqata an tanadeshi tun kafin haihuwarmu.......bama buqatar karatu me
zurfi don mun mallaki abinda takardar zata bamu tun kafin samuwarta..........idan
kika auri altaab zaki san cewa kin samu kalar mijin da yakewa mata
wahala........kin taki babbar sa'ar da ba kowacce mace keda irinta ba.....".
Yatsunta ta sake motsa masa,tana jin kalamansa gaba daya sun mata banbarakwai.

Ita akhnan ce zata taki sa'ar mallakar altaab?.......ba altaab za'a
yiwa murna ba idan har tsananin rabo ya ratso da sa'arsa cikin rayuwarta?.

A iya wannan gabar taji ta kowanne fanni altaab ya gama rikitowa.....

"Zaki nake nema ba kura ba.......me fita yayi farauta ba wanda ake farutowa
ba.......ILIMI ina buqatar mijin da iliminsa ya kasance shine matakin qarshe na
ilimi a DUNIYA......SA'A kuma tana ga wanda yayi nasarar mallakar diyar sarkin
agadez.......bazan wahalar da lafuzza na ba wajen yi maka sauran tambayoyi
ba.....don ka fadi tun a nan......abu na qarshe....." Ta furta da kalaman dake fita
a jejjere kamar wadda ke irga adadin haruffan da zatayi amfani dasu a
wajen...........

Abu na qarshen da bata fadeshi ba kenan saita miqe a qasaice,tana jin
kamar iya haka ya kamata ya gama jin sautinta,kamar tayi masa alfarma me yawa idan
ta qara bari yaci gaba da jin sautin nata........abu na qarshen data qi gaya masa
ta kuma kalmashe magananta a cikinta ta fara takawa dashi,ya bita da wani irin
razanannen kallo me cike da mamaki,saidai ita dinma tana jin ya kamata maganar ta
fits a cikinta.........yadda aka halicceta kenan......yadda ta dabi'anci kanta
kenan.....muddin tana ji a zuciyarta ya kamata magana ta fita tana barinta ta
fita,bata ajiyar maganganun da takeji sun cancanci su fita din.

"Bakayimin ba......baka dace da irin tsarina ba".

"Wanne tsarinne irin naki?,a shirye nake na dabi'anci kaina zuwa ga wannan yanayi
da tsarin" Altaab da ya kasa zama ya miqe da wani irin sauri ya furta yana duban
akhnan da bayanta kawai yake iya gani wanda ke lullube da babban mayafin dake
sharar qasa wanda yazo hade da rigar.

"Ka makara........kafin ka shigo da'irata ya kamata kasan wannan" Abinda ta fada
kenan a taqaice,sai taci gaba da takawa tana motsa yatsarta,abinda ya bawa birra
daman matsowa dab da bayanta a rusune tana biye da ita.

"A fitar da kyauta mafi girma da nauyi wadda zata taba zuciyar masarutar tahou a
hadashi da ita........akwai abota tsakanin mahaifinsa da sultane........ina buqatar
tarin karamcin agadasawa yayi masa rakiya zuwa gida". Ta fada tana jin kamar a yau
lambun yayi mata tsaho da yawa,don bata da burin da ya wuce ta kammala ficewa daga
cikinsa.

"An gama Allah shi taya miki" Birran ta furta cikin tsananin girmamawa.

Haka kawai takejin wani nishadi yana ratsata sanda take takawa tana
komawa zuwa cikin gida.......tunda ta samu ta kori altaab sai taji kamar ta zare
wata qaya. Wannan nishadin nata ne ita kadai,kuma wani yanayi ne da bazai boyu a
fuskarta ba,bata kuma buqatar tayi wani abu da zai sanya hadimai na gidan da nata
hadiman sassauta matsayinta da izzarta,don haka ta sallami kowa ta soma takawa ita
kadai zuwa nata sassan ta wata sirrintacciyar hanya data haramta kowa ya bita idan
ba sultane ita ko su mammina ba.

Shukokine suka lullube hanyar suka zame mata tamkar sune rufin
gurin,wasu irin shukoki dake sarqafe da junansu,wannan ya bawa tsintsaye da yawa
daman baje kolin samar da guraren zama gurin. Wasu irin tsintsaye da dare da rana
basa gajiya da raira waqoqi da wani irin kuka me sanyi. Duk da cewa nishadi ne
qasan ranta amma sam bai nuna saman fuskarta ba. Tsaki taja karo na hudu
kenan,tanaso ta kawo dakatar da zuwan da maza sukeyi neman aure gurinta. Ta fara
gajiya,tana kuma hangen raguwar martaba ne kawai a gurinta. Batasan rana ko lokacin
da wani namiji zai samu yarjewarta a aure ba......to meye duka na batawa kai lokaci
irin haka?. Sam ita bata shirya rabo kowa cikin rayuwarta ba,bata sha'awar hakan
sam,don bataga abinda zasu bata ba.

Hankalinta kwance ta isa ga qofar data sadata da sassanta,bata kuma
tsaya ako ina ba ta zarce zuwa bedroom dinta.



*_Uhmmmm........tofa😊_*



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*

*LAST FREE PAGE 05*
_____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500
dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da
kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi
https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba
da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin
iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi
bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________




★Yadda Armelle da take zaune a gabanta ta sadda kai cikin wani irin
taushi da rashin son su hada idanu kadai ya darsa qaqqarfan zargi a ranta. Tun
kafin Armelle ta bude bakinta tace komai ta soma hasashe iri daban daban,hasashen
daya soma haifar da motsuwar zuciyarta da kuma soma taruwar gangamin tawagar fushi
a qasan zuciyarta.

Ta sani......wannan din dabi'arta ce,tana da zafi,tana da fada tana
kuma fushi,saidai dukka wadannan dabi'un nata akan gaskiyar ta suke faruwa. Ba ita
ta yiwa kanta wannan shaidar ba......kusan shaida ce data sameta daga wajen kowa.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ta furta tana kuma sake zama sosai ta zauna cikin
Kujerar,sannna ta ajiye carbin hannunta a glass table din dake kusa da ita.

"Armelle"

"Ranki shi dade" Ta amsa mata tana gaza dubanta.

"Ki gayamin komai kada kice zaki boyemin". Kai sosai Armelle ta jinjina,sannan ta
daga kanta a hankali ba tare data iya duban momma ba.

"Shima taqi amsarsa.......taqi karbar tayinsa na aurenta".

"Allahumma la sahla illa maja'altahu sahla.......la haula wala quwwata illa
billahil aliyyul azeem" Ta fada tana qoqarin danne fushin dake taso mata.

Maida kanta qasa Armelle kawai tayi ba tare data sake cewa komai da ita
ba. Kowanne motsi na uwar dakinta sananne ne a wajenta da abinda yake nufi,koda
bata fada ba tasan cewa fushi ne sosai yake taso mata shi yasa take maimaita
addu'ar. Da alama tana qoqarin danne fushinne da nauyin addu'ar don gudun aikata
abinda zai jawo musu dana sani.

"Armelle.......idan na lissafa daidai wannan shine karo na goma sha daya da biftu
ke aikata haka?". Kai armelle ta jinjina,tana jin tausayin momma din yana ratsata
da yadda take sake dulmiya cikin damuwa cikin kowanne wucewar rana kwanaki da kuma
watanni dukka akan AKHNAN din ita kadai.

"Haka ne ranki shi dade.......amma dole abi abun a sannu....don......" Hannu momma
ta daga mata tana dakatar da ita.

"Jeki abinki armelle......kiyi haquri......nan gaba kadan zan nemeki". Tsam armelle
ta miqe,tasan halin dattakonta,tasan kuma halin karamcinta,da gaske tana buqatar
space dinne kamar yadda ta buqata.

"Allah shi huci zuciyarki" Bata iya amsawa armelle ba,don tana jin kamar zuciyarta
zata balle daga qirjinta ne ta fito.

"Ki saka buhaina ta dubamin yiwuwar gabawa da sultane". Maganar tadan bawa armelle
mamaki sosai. Baqon abune a wajenta ganin sultane ko kebanta dashi,musamman a irin
wannan lokacin na yammaci......a kuma ranakun da yake samun yawaitar baqi qwarai
fiye da kullum,amma sanin yanayin da ake ciki ya sanya bata tunasar da ita akan
komai ba ta saka kai tana ficewa zuciyarta ita kanta cike da alhini da kuma dogon
nazarin da taso ace momma ta tambayeta wani HASKE Ko ta shigo da ita ciki,to amma
ita dimma tana tsaiwa ne kawai inda aka buqata,duk da dadewa da kuma tarin amincin
dake tsakaninta da MORSA SAFIYYA(momma).

Cikin kowanne bugawa da jini da kuma zuciyarta sukeyi ba abinda takeji a
cikin ruhinta sai wani irin tashin hankali. Khadeeja ce?,khadeejan
juhaifanta......jinin JUHAIFA ne.....jinin juhaifa ne ake waannan wasan kuran
dashi?......idan ta zuba idanu gudan jinin juhaifa qwaya data tallin tal data bari
a duniya ya wulaqanta haka shin TAYI ADALCI?.......anya bata zama BUTULU ba?,anya
batayi cin amana ba?. Jinin juhaifa ya zarcewa duk wata kima da martaba a gurinta
da idanunta......zatayi dukkan wani yaqi......zatayi kuma duk me yuwuwa na ganin
bai wofanta ba.

Ko sau daya ko kuma daidai da qiftawar idanu..........bata taba daukan
iqirarin MAMMINA da wasa ba. Wani irin kalamai ne da suka yiwa zuciyarta kyakkyawan
dashe,irin dashen da girgizarsa ko tabuwarsa ba abu bane mai sauqi. Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login