Showing 75001 words to 78000 words out of 168506 words

Chapter 26 - luu luu Book1 by Huguma

daidai inda ruhinsa zai dinga samun sakeena(nutsuwa?" Yana dan boye
dariyarsa. Murmushi abdii yayi shima yana shafa sassalkar sumarsa.

"Bayan ka sauka qasa,hannun hagu da qofar shigowa" Abdii ya fada yana kwatanta masa
da hannu. Kai haisan ya kada a nutse

"Yayi....." Hannunsa ya miqa yana cire jakarsa dake kafadar abdii din.

"Komai yayi....zan shiga na huta......ka fadawa musu kowa ya wuce
mazauninsa......sai gobe idan Allah ya kaimu zamu zauna gaba daya......."

"Amma Ousmane haris na buqatar ganinka obbo". Dakatawa yayi da tafiyar da yakeyi ya
waiwayo yana duban abdii,har ga Allah ya gaji tubus,tafiya ce ba 'yar kadan ba
tsakani Niamey da agadez. Tsananin yadda tafiye tafiye take cikin wasu abubuwa da
yake matuqar so ya sanya baiga nisa ba.....bai kuma gaji ba har sai yanzun daya
tabbatar ya kawo inda zai huta. Tafiyar awanni goma sha biyun nan a wajensa wani
sabon aji ne kuma mabudin ilimi.

"Kace ya bani zuwa goben injini" Ya furta a nutse tamkar ba wani gajiya a tare
dashi yana kallon yadda abdii din yadan diririce.

Zare kallonsa yayi daga kan abdii din.....wani lokaci can baya yana
gaza gamsuwa da maganganunsu amjad a kansa.

"Idanunka nada wani irin kaifi da nauyi......basan wacce budurwa ce nan gaba zata
iya dauke nauyinsu ba har ta tsaya ta fuskanceka da soyayya ko a mu'amala
ba......don Allah ka rage magana da idanunka da kake yawan yi........daukemin
idanunka haisam......bazan juresu ba". Kadan kenan daga muryoyi da kuma maganganun
mutallab game da idanunsa,bai kuma fahinta ba,hakanan bai qara gasgata maganarsu ba
sai da qara shekaru saman wadanda yake dasu,shekarun da suka fara fusgar hankulan
'yammata cikin rayuwarsa.

"Am.....obbo" Abdii ya sake kiransa sanda ya sanya hannu zai murda handle din
qawatacciyar qofar dakin.

"Kuma?" Ya fada yana juyawa kadan amma bai kalli abdii ba.

"Afwan obbo......saqo ne aka bani......kuma tamkar amana ce da bai kamata ce ban
idar da amanarta ba" Shuru parlor din yayi,don tuni omari ya wuce nashi
dakin,addisaleem kuma ya sauka yana komawa don tabbatar da shigowar kayansu ciki.

Ta baya ya miqawa abdii hannu,cikin farinciki ya matsa ya dora masa a
saman hannunsa ya juya da sauri sauri ya lalubi hanyar fita,tun kafin yakai ga duba
sunan me saqon,saidai cikin sa'a gajiyar dake taba jikinsa ta hanashi dubawa ya
wuce dakinsa da ita a ransa yana raya qila wani sabon shirmene na abdii din kawai.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*
πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 37
_________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*πŸ‘˜πŸ₯»

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin
Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana
✌🏽
goma KACAL! *

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*πŸ™ŒπŸ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT
da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________


"Rabbi anzilni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzileen" Ya furta da
nutsuwar nan tasa dake qara masa kwarjini,take kuma qarawa kyansa kyau,sannna ya
taka a hankali ya ajiye jakar tasa saman wani zagayayyar sofa ta hutawa dake wani
corner daban na dakin.

Da idanu shima dakin ya gama observing dinsa. Da gaske abdii yasan
komai a kansa.....da gaske abdii yasan abinda yakeso da wanda bayaso,yasan abinda
yake burgeshi dama wanda baya cikin tsarinsa,sai kawai ya furta.

"Bismillahillazi la'ilaha illa huu" Ya soma zare kayan jikinsa,don a yanzun wanka
kawai yake buqata ko zai warware gajiyar jikinsa.
(Ba'a cire kaya haka kai tsaye,saboda idanun shaidanun da suke a muhallinmu,idan
kikayi wannan addu'ar Allah xai sanya hijabi a tsakaninku ba zasu ga tsiraicinki
ba).
Sanda ya fito ya shirya tsaf cikin farar short sleeve shirt fara qal,ya
sanya joggers pant shima daya kasance fari. Shigar kaya farare da shigar kaya green
wani dabi'a ce tasa da kusan duk wanda ya sanshi ya sanshi da ita. Wayoyinsa ya
debo don sanya charge a parlor,yana fita akayi knocking. Daya tambaya sai yaji
muryar addisaleem.

"Nine obbo"

"Shigo" Ya bashi dama kai tsaye yana zama saman wata ottoman dake kusa da socket.

Rusunawa yayi kadan sannan yace.

"An kammala abinci......bansan ko kana buqata ba". Manyan zagayayyun idanunsa ya
daga ya kalli agogon bangon dake manne,dare ya soma yi,ba kasafai kuma yake cin
abinci me nauyi ya kwanta ba,don haka ya girgiza masa kai.

"Coffee kawai.....gahwa,kar kasa sugar,narkakken ruwan rake ya isa" Ya fada da
wani irin yanayi dake dake bayyana qasaitarsa da tabi jikinsa. Kai addisaleem ya
gyada sannna ya juya yana ficewa.

Kadan kadan sautin karatun hadisai da ake karantawa daga channel din
saudi sunnah daga littafin sahihul bukhari ke fita daga tafkekiyar TV din dake
zaune dafa'an cikin parlor din,yayin da hannunsa ke dauke da daddadan coffee
din,yana kurba yana ratsawa har cikin zuciyarsa. Ya yadda shan coffee da gahwa wani
rubutaccen abune cikin jikin oromia......uwa uba ma kuma cikin jinin sarauta,nanaya
yakeson kira,muryarta yakeson ji,amma koda ya kalli agogo yanzun goma na dare ne
cikin agadez,a jimma kuma yasan sha biyu na dare ne. Idan ya kirata zai tada ne
kawai,zai kuma lalata mata tsarin baccinta,don tana kwanciya ne akan lokaci don ta
samu ta riski sallar darenta ta kuma sukwane har asuba. Dole ya haqura da kiran
nata ya tattara ya wuce bedroom din nasa.

A daddade yayi shafa'i da wuturi,wanda komai tsanani baya taba bari su
wuceshi,ya cire kayan jikinsa ya saka pajamas,ya tsaya gaban mirror yana feshe
jikinsa da night scents dinsa masu lallausan qamshi.

Yana tsaka da feshe kyakkyawar qasumbarsa idanunsa ya sauka akan
envelope din. Har ya janyesu ya ajiye kwalban turaren ya juya,sai kuma ya dawo a
hankali ya dauki envelope din ya budeta ya zaro farar takardar ciki.

Rose flower ne qwara daya ta biyo bayan takardar ta fado,ya bita da kallo
ba tare daya tsugunna ya dauka ba,sai ya dawo da dubansa kan takardar ya farketa a
nutse,

Kwantaccen rubutune cikin yaren oromo,ya soma bin rubutun da idanu yana
karantawa.

_Sallama me cike da aminci da kuma fatan alkhairi,godiya a bisa amsa gayyatar abba
na zuwa cin abincin dare tun a wancan lokacin,a wannan karon ni da kaina nake roqon
wannan alfarmar don sada zumunci da kuma samun lada.......Menelik ce_

Sai number wayarta har guda biyu a rubuce daga qarshen takardar. Kansa
ya daga a nuts,ya cukuikuye takardar yayi cilli da ita a inda baisan inane ba,ya
daga qafarsa yana qarasawa bakin gadon. Hannu ya saka ya zuge net din dake kewaye
da gadon,sannan a hankali ya shige ciki yana yaba tsarin da aka yiwa gadon kansa.

"Allahumma innaka kalaqta nafsi,wa'anta tawaffaha,laka mamataha wa mahyaha,in
ahyaytaha fahfazha,wa in amattaha fagfir laha,allahumma inni as'alukal afwa
wal'afiyah" Lafuzzansa kuma addu'arsa ta qarshe kenan a kowanne dare idan ya
kwanta,yau dinma da ita ya rufe,ya lullube idanunsa yana fatan kasancewa cikin
wadanda Allah zaiwa alfarmar ganin washegari.


β˜…β˜…β˜…β˜…Sau uku tana duba tickets ko zata samu jirgin da zai tashi daga Niamey zuwa
agadez koda ranar laraba ne amma sam sam babu. Wani abu daya sake quntata ta,ya
kuma sake sanya ranta yayi matuqar baci.

Kamar yau dai,duk data kasance litinin ce,tana cikin ranakun da takan
jima a company ba tare data dawo gida ba,amma litinin din yau din ta zama ta daban.
Don tun break din da ake fita da azahar ta umarci driver dinta ya maidata gida.

A kebantaccen balcony dinta ta zauna bayan ta canza kayanta,tayi zaton
zata iya sake rage wasu ayyukan a system dinta amma saita kasa,ta koma laluben
ticket din da zai dace da ranakunta amma ta rasa.

Tsaye kawai tayi goye da hannayenta jikin qarfen balcony din,iskar dake
kadawa daga hagu zuwa dama suna wasa da gashin kanta da muddin tana gida basu fiya
shiri da dan kwali ba. Dogon wando ne a jikinta sakakke,sai shirt me gajeran hannu
rounded neck data fidda qirar qirjinta da kuma shafe din shafaffen cikinta da ya
bawa mazaunata suma damar fidda nasu shape din.

Banda lemo ba abinda yake dirkawa cikinta,duk wani hanya da zata samu
gutsiren dalilin da ya sanya sultane mata irin wannan kiran gaggawar ta kasa samun
kowanne labari,koda daga gurin mammina kuwa,don hatta mammina dinma bata da labarin
kiran saida akhnan din da kanta ta gaya mata.

Bacin ran taji yana neman mata yawa,don haka ta miqa hannunta ta dauki
headphone dinta dake maqale ta dora saman kanta,ta kuma lalubo waqar best artists
dinta cikin mawaqan dake waqa da French wato indila.....

Waqar love story ta kunna,ta qara volume din daidai yadda zai ratsata,ta
maida idanunta ta lumshe. Tanason waqar sosai,batasan kuma iya adadin sau nawa ta
taba saurarenta ba,har wasu baitukan sun zauna a kanta. Amma kuma duk da haka sau
daya tak ta taba kallon video din waqar.......tana against duk abinda ke cikin
waqar idan ka cire waqar kawai,sautin yana mata dadi sosai,ya kuma bata nutsuwa a
ranta.....amma sam video din bai mata ba. Bataga wani dalili bane......bataga kuma
wacce irin qaddara ce zata sakata dakon son wanda ya mutu ba.......ko rayayyen ma
bata fata qaddararta ta zana mata haka. Bata hangi komai ba cikin so sai qasqantar
da mutum......ta sanya duk qarfi da izzarka kayi qasa,itakam duk wani abu da zai
sanya kima da martabarta da kuma izza da ikonta su tabu to babu ita a cikinsa.

Yadda ta saka volume din ya sanya sam bataji sallamar da barratu ke yi
ba,har zuwa sanda waqar ta qare,ta zare headphone din a kunnenta. Haka kawai taji
yana sha'awar maimaita kallon film din the umbrella of Cherbourg.

Batayi zaton ganin barratu a gurin ba,wannan ya tsoratata sosai.

"Afuwa ranki ya dade.....inata sallama amma baki jini ba" Sosai ta shaqi iska ta
kuma fesar,ta lumshe idanunta ta budesu sosai a kanta.

"Shine me?.....shine zaki tsayamin a guri?.....da izinin wa?" Qasa ta sakeyi da
kanta,don ta fahimci cikin kwanakin izzar tata ce ta motsa

"Tuba nake" Ta fada a sanyaye.

"Karki kuskura ki sakemin wannan haukan.....bacemin da gani kafin raina ya qarasa
baci". Da hanzari barratu ta juya tana barin gurin. Ba wani baqon abu bane a
wajensu,dama kura ce tayi lafiya ai......lafiyar tata kuma sanadin dauki ba dadin
da suka dinga yo ne da morsa safiyya.
A duk sanda zatayi musu wani abu na rashin martabawa ko
girmamawa......muddin ya fada idanu ko kunnuwan morsa safiyyan saita dakatar da
akhnan din.....tun abun yana mata zafi,tana ganin yarfata take,wulaqantata take
gaban bayinta kuma hadimanta,har ta fahimci morsa safiyyan ba zata fasa mata gyara
ba ko a gaban waye,dole wasu abubuwan da yawa suka ragu.

Ta gama saita system din tayi playing film din kiran mammina ya shigo.
Iska sosai taja,ta yiwa birra dake tsugunne tana zuba mata lemon inibi sign na ta
bata wayar,ta dakatar da zuba lemon ta dauki wayar ta miqa mata da dukka hannuwanta
biyu.

Sai data janye qafafunta ta maida saman kujera sannan ta daga kiran tana
rungume pillow a qirjinta.
(08187255862 luu luu paying)

"Hi..." Ta furta da siririyar muryartannan maras hayaniya ko kadan.

"Sai yaushe zaki girma ne akhnan?" Mammina tayi maganar tana gyara zamanta hadi da
miqa hannu ta karbi yankakken apple daga hannun yalwa dake durqushe a gabanta.

"Mammina......indai ina dake......indai kina tare dani bazan taba girma ba" Ta fada
a narke tana jin kamar ta koma cikin mammina din ta sake haifarta a matsayin d'iyar
cikinta ta halali. Tabbas inda haka zata iya kasancewa lallai ba shakka da tafi
kowa sa'ar samun uwa.....irin uwar da zata lullubeka da soyayyar da ba zata baka
daman kokawa ba ko kadan.

"Gaskiya ne biftu na.......ina fatan kina lafiya ko?,baki sanya wannan damuwar a
ranki ba?". Sosai ta sake narkewa cikin pillow din kamar wata 'yar
mage.....muryarta a karye tace.

" Dole na damu mammina......banason na bata da sultane......banaso nayi masa abinda
ranshi bayaso". Shuru kadan mammina tayi tana jujjuya dukka maganganunta a ranta.
Akwai abubuwan da ya kamata tayi magana da akhnan akai......amma ba zatace mata
komai ba,zata jira har zuwa lokacin da ta yanke gaya mata.

"Bana jin akwai wani abu da zakiwa sultane da zaiyi muni har irin yadda kike zato
ko zargi ba biftu.....na jima banga soyayya tsakanin uba da 'yarsa ba irin
taku.....soyayyarki da sultane daban take a zuciyarsa" Sosai maganganun mammina
suka bata wani irin relief data gaza samu tunda sukayi magana da sultane. Ta sauke
ajiyar zuciya me nauyi,yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya take matuqar son
mammina din,take kuma ji da ita a rayuwarta sama da kowa da ya rabeta ko ya
jibanceta.

Tana bata relief qwarin gwiwa da kuma tabbaci akan duk wani abu da
zai tunkareta. Tana nuna dukkanin damuwarta da kulawarta akan kome da zai
shafeta...... Wannan shine cikakken banbanci da tazara me nisan gaske data yiwa
morsa safiyya.......kuma irin wannan tazarar ko mafiyiyarta ta yiwa morsa safiyyan
a cikin rayuwarta.

"Me yake faruwa a sahel couture?" Mammina tayi furucin cikin tausa murya.

Kiran sahel couture din da tayi ya sanya akhnan bude zara zaran idanunta
gaba daya da suka rusuna a dazu.

"A sahel.......bazan iya tunawa ba mammina". Wani ajiyar zuciya me nauyi mammina ta
sauke da tazarar sakanni sannan tayi magana.

" Tabbacin ba cikin nutsuwarki kike ba biftu......shin kin manta muhimmancin da
kamfanin yake dashi a tare dake?.....me yasa zaki bari damuwa ta shiga cikin
muhimmam al'amuranki?". Numfashi ta jawo tana gyara zamanta sosai cikin sofa din.
Da jiya da shekaran jiya dama yau duka dai sunan ta shiga company dinne
kawai......amma ba wani aiki da tayi daya shafeshi,ba kuma wanda ta bawa daman
ganinta idan ka dauke aisa da Shehinaz,suma kuma bata bari sun mata maganar komai
ba.

"Mammina.......Je ne suis pas dans le ton(bana cikin yanayin)" Tayi maganar kamar
qanqanuwar yarinyar data rasa mafita.

Wani murmushi ne ya subuce mata,wanda daga ita sai zuciyarta ne kawai
sukasan da fitarsa.....koda yalwa dake zaune gabanta ba zatace ta ganshi ba bare
akhnan da bata tare dasu.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*


πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž
*H U G U M A*


PAGE 38
_________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*πŸ‘˜πŸ₯»

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin
Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana
✌🏽
goma KACAL! *

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*πŸ™ŒπŸ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT
da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________




"Har yanzu baki gama fuskantar matsayinki ba akhnan.......kinsan girman
matsayinki da martabarki a qasar agadez?.......ina kikai jarumtarki?.....me yasa
zaki bar qaramar damuwa ta mamayeki har haka?.....ba haka na sanki ba.....ba kuma
haka nakeso naci gaba da ganinki ba" Ta furta cikin kambamata da kuma motsa mata
matsayinta.

Idanunta ta lumshe ta kuma budesu a sarauce.

"Ina nan yadda nake mammina.....ban canza ba,bana jin kuma zan canza din.....saidai
sultane daban yake a raina....dole damuwarsa dama komai nasa ya zama daban a
raina......koda sahel couture a bayanshi take.......da girman qarfinki na amince
kiyi abinda ya kamata na dan lokaci kafin komai ya daidaita". Shuru sukayi
dukkaninsu,wani abu yana bugawa a tsakiyar qirji da zuciyar mammina.......ta tsuke
idanunta daga inda take zaune,tunaninta kuma yana harbawa da nisa fiye da nisan
dake tsakaninta da akhnan.

"Indai kina da uwa irina har abada ba zakiyi kuka ba.......ki dauki
lokacinki.....kiyi amfani dashi har iya yadda kikeso.....mammina dinki zata kula
miki da komai.....zata kuma ji miki da komai".

" Na gode" Ta furta da wata lanqwasashiyar murya,kuma bata qara cewa mammina din
komai ba ta yanke kiran,ta ajiye wayar a gefanta ta zame tana kwanciya.

Da sauri yalwa ta miqa hannu ta karbi wayar daga hannunta tana duban
yanayin fuskar uwar dakin nata. A nutse ta maida dubanta kan yalwa.

"A jikina ina jin akwai wani baqon abu......akwai wani abu na daban ba irin abu ba
yau da kullum ba.......bansan me yake faruwa tsakanin sultane da akhnan
ba......banga alamun komai tattare dashi ba,kamar yadda baiyi niyyar gayamin
ba.....daren jiya mun kasance tsahon daren tare dashi muna hira......amma baicemin
komai ba a kanta,bana buqatar tambayarsa komai,kaman yadda baiyi niyyar na sani
ba......amma ina buqatar sanin komai din.....yalwa" Ta sake kiranta a karo na biyu.

"Allah ya taimakeki" Ta furta cikin girmamawa.

"Inason nasan meye wannan?......wanne laifi ne akhnan ke zaton ta yiwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login