Showing 138001 words to 141000 words out of 168506 words
CEO ta rattaba hannun amincewa da
hannunta". Shigar mammina maganar tayi da wani sauti da tajishi ba'a daidai ba,amma
saita tsaurara kallonta akan fuskar aisa din tana sake fadada fara'arta.
"Ina kyautata zaton baku samu kunyi kowacce magana da akhnan din ba?......banda
abun aisa,ai ba akhnan ba,ko ke ina da ikon zartarwa ina da ta cewa a rayuwarki
ballantana akhnan......" Yadda tayi maganan sai aisa taji kaman tayi maganana
muhallin da bai dace tayi maganan ba,kaman tayi rashin kyautawa a ciki,kamar kuma
mammina taso fahimtarta baibai.
"Ayimin afuwa......tambayata bawai tana nufin wani abu na daban bane,inaso ki
fahimceni da kyau,da akhnan da sahel couture dukkaninsu amanarki ne dana sultane a
hannunmu,bazan manta wannan maganan naki ba,gata nan na baku amanarta.....ku
kulamin da ita kowanne qarshen sati idan baki gayawa shehnaz hakan ba ni zaki
gayamin,amana ba abar wasa bace......sahel couture shine zuciyar dukiyar
akhnan,zuciyar dukiyar masarautar agadez,dukkaninmu mun aminta zamuyi aiki cikinsa
ne bawai don bamu da tamu dukiyar ba......muna aiki cikinsa ne don kawai
sadaukarwar da zamu iya yiwa kowa a cikinmu idan buqatar hakan ya taso.....yin
wasarere da irin wadannan abubuwan zai iya zama cin amana ne,zai kuma iya haifar da
matsalar da bamusan qarshenta ba a gaba".
"Well done" Mammina ta fada cikin salon burgewa tana dan tafa hannuwanta.
"Ashe muna da talented girl har haka ban sani ba......ma sha Allah aisa" Mammina ta
fadi tana sauke qafafunta qasa cike da tsananin nuna jin dadin dukkan bayanan aisa
din.
"Na sake samun nutsuwa,na kuma sake samun tabbacin akhnan tana tare da sisters din
da babu irinsu.......yanzu gayamin kanki tsaye me kike buqatar ayi?". Ta fada tana
miqawa aisa takarda da abun rubutu.
Kadan aisa taji zuciyarta ta saki daga tarin saqe saqen da takeyi,tadan
rusunawa mammina din
"Basai na fadi ba,kaman zaki fimu sanin abinda ya dace mammina". Kai mammina ta
girgiza.
" Yadda kika gano dukka wadannan abunuwan na tabbatar idan nabar kwanyarki tayi
aiki yadda ya dace za'a samu result me kyau". Kai aisa ta jinjina,tabbas daga
farkon wancan watan zuwa yanxu tana ganin abubuwa da yawa a kamfanin da bata gane
musu ba,take kuma ganinsu kamar ba'a daidai suke ba,tunda har mammina din ta bata
cikakkiyar damar yin magana zatayi maganan.
"Ina ganin a dakatar da daukan ma'aikata da kuma rarraba muqamai da ake tayi a
yanzu,ayi limiting fitar kudi da siyo wasu kayayyaki da kamfani ke da
buqata.....wadanda aka Riga aka dauka kuma yana da kyau a auna amanarsu da
ingancinsu kafin a sakar musu komai......saina qarshe,ina ganin a rufe office din
biftu......a barshi a rufe,a dakatar da dukka ayyukan da suka shafi office din har
sai bayan ta dawo".
"Ke zaki karbi office din ciki gaba da gudanar dashi" Mammina ta fadi kai tsaye
hankali kwance cikin confidence idanunta cikin na aisa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
PAGE 69
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
Dubanta itama aisa din takeyi,haka kawai cikin kanta takejin wani abu
daban yana amsa kuwwa da maganar mammina.
Wani abu ne da bata taba tunani ba,wani abu ne da bata taba kawoshi kanta
ba,kuma wani abu ne da ita din bata taba sha'awarsa ba. Jagorancin office din
akhnan wani abu ne daban da tayi imani ba kowanne mutum bane zai iyashi. Dari bisa
dari dukkaninsu sun aminta da akhnan din ta musamman ce,tana da wani irin fikira da
hazaqar tsara abubuwa da sanyasu a guraben da suka dace,lissafinta daban yake kaman
yadda kwanyarta take daban......baya ga haka ma kuma tana ganin babu tsaro sam sam
gurin bude office din CEO guda aci gaba kuma da tafi dashi,tana ganin akwai hatsari
cikin hakan,ba kuma tsari akai.
Wadannan lissafin ya sanya aisa din sakin murmushi,ta kuma girgiza kai.
"Mammina......tu n'as aucune Γ quel point ta fille est incroyable(bakisan wacce
irin d'iya gareki me ban mamaki ba).....ba wanda zai iya tafi da l'enterprise sai
akhnan din". Yanayin fuskar mammina ne ya sauya,tadan tsuke fuska tana duban aisa.
"Aisa?.....yanzun ace akhnan babu ita,ko dalili ya sanya ba zata iya ci gaba da
gudanar da aikin ba,shikenan komai ya tsaya?." Kai aisa ta girgiza a hankali.
"Hakan bazai faru ba......"
"Daga yau na hukunta kece a mazaunin CEO.....ina fatan zaki riqe amana da jajircewa
har akai lokacin da 'yar uwarku zata dawo daidai". Tayi magana tana yin rubutu
saman wata takarda,sannan ta turata gaban aisa,da alama tana buqatar sanya
hannunta.
Kai aisa ta daga tana duban shehnaz,itama shehnaz din ita take
kalla,sai tayi mata sign da idanu na ta karba din,amma sai aisan ta zare dubanta
daga kan shehnaz,ta maida kan mammina tana dan sakin murmushi.
"Zanje da takardan tukunna kafin saka hannu,idan na saka din zan dawo miki da ita".
Kai ta gyada a nutse.
"Baki da damuwa,Allah yayi muku albarka ya qara hada kanku" Ta fadi tana nuna
tsananin kulawa da taushinta.
Da idanu take bin bayansu da kallo sanda suke ficewa suna barin
gurin,har sai da suka kammala ficewa sannan ta dauke dubanta tana sakin wani
murmushi. Gyaran murya yalwa tayi wadda ke zaune a gefanta,abinda yaja hankalin
mammina kenan ta maida dubanta ga yalwa,sai yalwa din ta sakar mata murmushi.
"Akwai wani sabon karatun hala uwar dakina?". Jinjina kai sosai mammina tayi tana
dauke idonta daga kan yalwa.
"Wani lokaci kina da son jin gulma yalwa" Dariya yalwa ta saki tana sake yin qasa
da kanta.
"Ba son gulma bane Allah ya baki dogon kwana....kawai dai na sani,a dukkanin
motsinki.......a dukka wani abu da zaki aiwatar.....dukkan wani second qwaya tak na
rayuwarki darasi ne ga duk wanda ya rabeki......tabbas a wannan motsin akwai wata
maganar......akwai wata hikimar,akwai kuma sabon aiki....sabuwar kwangilar da na
tabbatar ta sake shigowa da sabbin jerin sahun sunayen da babu su asali a cikin
aikin" Murmushi sosai da yafi kama da dariya mammina tayi tana dunqule hannunta
guri guda kaman wadda ta kama wani abu.
"Daya daga cikin abinda ya sanya na zabeki kenan,daya daga cikin abinda ya ya sanya
nake kuma sonki kenan yalwa......kina da saurin kama abu da zaquloshi" Ta furta
tana miqewa tsaye.
"Tabbas......wasu sun shigo tsarin......wasu kuma sunayensu sun fice.....akwai
yuwuwar shigar wasu kuma a nan gaba,don suna tsakanin gaba ne......saidai ki sani
yalwa,ita matsala daga sanda ta qunshi ciki kake rainonta.....kake kula da
ita......daga sanda ka fahimci tana yunqurin haife wannan abinda yake cikin
nata,hakan yana alamta maka sabbin rassa take shirin zubawa.......sai kayi dukkan
me yuwuwa wajen murqushe wannan naqudar......" Saita waiwaya tana duban yalwa
"Idanma fa har kayi saken da matsalar taka ta qunso wani abu kenan" Ta qarashe
maganar da wani yanayi a idanunta da kuma muryarta.
Kai yalwa ta jijjiga alamun fahimta ganewa da kuma gamsuwa. Tana kuma
sake juya girman iya tsari iya yaku da iya tafi da komai cikin wani madaukakiyar
basaja da bad da kamanni.
β
β
Magazine na qarshe ya rufe ya kuma dorata a hankali saman sauran magazines din
da suke gefansa yana furzar da siririyar iska daga tsakiyar tausasan labbansa dake
da wani irin launi da yanayi me jan hankali.
Tun sanda yazo agadez ya zame masa dabi'an duba jaridunsu. Da farko me
kawowar ya tsaya mamakin me zaiyi da jaridu?,bayan a iya abinda ya sani bai iya
yaren French ba ballantana ya fahimci abinda suke rubuta ba,saidai abdii ya datse
wannan mamakin ta hanyar fadi masa.
"Abinda akace kayi kenan". Cikin ran abdii yana masa kyakkyawan uzuri.
Ko shi yasha mamakin yadda captain obbo ke iya sarrafa yaren English da
French a harshensa,kai kace yana yara yaren oromo ne,hankali kwance da wani irin
qwarewa da accent din da ko cikin mafarki zai qaryata cewa captain obbo dinne. A
hankali yake karantar cewa aikinsa ya dace dashi,hakanan aikinsa ya dace da
yanayinsa.....komai nasa yana da wani irin sirri,yana kuma da wani irin tsaro. Ba
komai daya shafeshi yake bari a sani ba,sai abinda shi din ya aminta ko ya yarje
maka ka gani ko kuma ka sani.
Sau da dama dabi'unsa na bala'in burge abdii din,harma yakan zauna ya
dinga imagination na kanshi a matsayin muhammad haisam din.
A nutse ya miqa dogon hannunsa ya jawo wani dan littafi dake dauke da
calendar din shekarar da muke ciki gaba daya. Watanni goma sha biyu ne a ciki,ba
kaman calendar qasarsu Ethiopia ba,da su suke da watanni goma sha uku a shekara.
Duba kwanan watan yau yayi,wanda a kansa yayi cycling dinsa da
maka,wannan ya tuna masa schedule dinsa na yau,sai ya maida calendar ya ajiye,ya
zaro wayarsa ya soma kiran hussam.
Bugu daya ya dauka,cikin girmamawa da barkwancin nan nasa ya soma
gaidashi.
"Barka da rana captain obbo". Numfashi yaja kadan yana lumshe idanunsa,ya rasa me
yasa duk yadda yakai ga tsare gidansa sai hussam yayi wasa dashi?. Nanay kanyi
dariya,duk da kasancewarta bame yawan magana ba,takance.
"Yana kallonka a matsayin sakonsa,ya manta cewa inda Allah ya qaddara amud yana
raye shine sakonka". Zuwa yanzun ya soma sabawa da halin hussam,ba komai bane yake
bashi muhimmanci ba......a haka yaci nasarar soma sauya masa halaye na maida
abubuwa serious daga kasu ashirin zuwa kaso tamanin.
"Barka......ina fatan kowa yana lafiya?".
"Alhamdulillah......se kewarka da kowa keyi,nanay nata boyewa.....amma ni nasan
hakan koda zata boye din kuwa" Boyayyen numfashi haisam ya sauke,ya sani nanay
zatayi kewarsa akan kowa,daga ita kuma sai noorah daya tabbatar ita zata biyo bayan
nanay din. Akwai shaquwa da qauna sosai tsakaninsa da 'yan uwansa.....hakanan ko a
tsakanin junansu akwai wata soyayya me yawan gaske.
"Nan kusa in sha Allah.......yau nawa ga wata?" Haisam ya dora kai tsaye akan
dalilin kiran.
"Sha takwas obbo" Kai ya jinjina a nutse.
"Dukka security din bangaren motii,dana bangaren nanay zasu bar bakin aiki a
yau.......inaso su koma bakin babbar qofa,na babbar qofa dana kewayen gidan gaba
daya aikinsu zai dakata.....za'a kawo wasu yau,bana buqatar ka sanar da kowa,zanyi
magana daga headquarter,zasu zo su kwashesu su kuma kawo wasu" Yayi magana da
calmness dinnan nasa dake nuna adadin rashin son hayaniyarsa.
Shuru hussam yayi,yanason tuna watannin da kwata kwata mutanen
sukayi. Wannan wanne irin aiki ne da yake sanya obbo din rashin yarda da
kowa,musamman akan motii da nanay?,idan zai iya tunawa cikin shekara biyu kacal an
canza masu tsaron wadannan gurare sau uku kenan.
Yana ji a jikinsa akwai wani dalili daya sanya yake irin hakan. Wani
irin tsaro yake bayarwa a dukka wani gilmawa tsakanin sassan motii dana nanay dama
fadarsa da muhalli da guraben zamansu.
Irin wannan abun ya sanya masarautar jimma ta zama ta daya,kuma ta
daban da sauran kowacce masarauta dake cikin Ethiopia,masarauta mafi girman izza da
fadin mulki,tsananin tsaro da wani irin tsari daya sanya idanu da yawa suke kanta.
"Amma obbo......."
"Karka tambaya.....umarni nake baka,ba labari bane ko shawara".
(08187255862 lu'u lu'u paying)
" An gama" Ya fadi cikin girmamawar nan dake a tsakaninsu tun asali. Sai haisam ya
zare wayar daya kunnensa kawai ya kasheta,sannan ya dorata a hankali saman table
din dake kusa dashi.
Lallausan farin tafin hannunsa ya miqa me dauke da zara zata yatsu yana
kalla. Wani irin abu yaji ya tsarga masa tun daga cikin tafin hannun nasa zuwa
sassan jikinsa,wanda sai daya tilasta masa lumshe idonsa kana ya budesu yana jin
wani abu na bin jikinsa.
"Astgafirullah" Ya maimaita har sau biyu. Besan me yasa abun yaqi bacewa daga
jikinsa dama idanunsa ba,tun daga ranar shudewar awannin da kwanakin basu sauya
komai ba. A duk bayan wucewar wasu lokuta sai yaji komai ya dawo masa kaman a
sannan hakan ta faru. Tafin hannunsa tsakiyar nata tafin hannun me wani irin dumi
da laushi. Hannun nasa ya maida ya dunqule yana mutstsukashi a hankali wai ko zai
daina jin abinda yakeji din,ranshi na baci a hankali,siririn tsaki yana kubce masa.
Itace mace ta farko da hakan ya fara faruwa a tsakaninsu. A hankali
tunaninsa ya koma baya,yana tuna wancan ranar a hippodrome,kalamanta cikin gidansu
na ranar juma'a dana washegari asabar. Wani tsakin yasake fusga daga harshensa yana
jin wani bacin ran yana sake d'iga saman zuciyarsa. Yana jin nauyin zunubin data
jawo masa ya dauka,girman zunubin taba jikin macen da ba taka ba,wadda annabi
muhammad S A W yace ya fiwa mumini sauqi ya zauna a samu qusa a kafa a saman kansa
bugata da guduma ya lume tsakiyar kansa.
Numfashi yaja me wani irin nauyi yana sake ambatar
astagfirullah,daidai lokacin da yake bude idanunsa a hankali sai suka sauka kan
fuskar omari dake tsaye cikin gurin wanda sam baisan sadda ya shigo ba.
"Kada kacemin banyi sallama ba......don bansan jazabar daka shiga ba data hanaka
jin kyawawan sallamata har guda uku" Ya fada yana daukan apple guda daya dake saman
tray sannan ya koma ya zauna saman kujera gami da yin bismillah ya gatsa ya fara
ci.
Idanunsan nan ya zubewa omari yana maimaita abinda omari din ya
fada. Banda babu 'yar qarya a tsakaninsu da kai tsaye zai qaryata omari din. Baiji
wani sound ko daya na sallama ba ballantana motsinsa,kuma bayajin tunanin da yakeyi
din yakai nisan da zai hanashi jin hakan.
"Kana da baqo......na dakatar dashi ne akan saina shaida maka zuwansa in kana da
interest na ganawa dashi" Omari ya fadi yana sake kai apple din bakinsa.
Idanun nasa kawai ya watsawa omari da body language dinnan nasa
dake nuna tambaya ga omari din.
"Kaaiii" Omari ya fadi yana gotar da nasa idanun daga cikin na haisam.
"Am telling you ka daina tsare mutum da wannan idanun naka idan ba qarya yayi maka
ba,idan ba haka ba one day zaka saka mutum ma yayi qaryar,abdii yasha gaya maka
hakan". Sassauta kallon nasa yayi kadan,can qasan ransa yana mamakin meye haka a
idanunsa da suke yawan complain?. Shi kam zai iya cewa bai ganin komai koda ya
tsaya ya kalla cikin mirror,abu daya ya sani,suna da girma,girman kuma daba me yawa
bane can can,sannan wani lokaci sukan koma su rusuna kamar name jin bacci,musamman
idan ranshi na bace ko kuma ya gaji sosai ko da gaske baccin yakeji.
Bai cewa omari komai ba,ya miqe tsam yana ware hannun long sleeve black
shirt din jikinsa dake nade tun dazun. Da kallo omari ya bishi sannan ya sake
magantuwa.
"Bansan a ciki wanne kaya bane sukafi maka kyau.....jubah?.....shirts da
trousers?.....ko suit?" Yayi maganar da dukkan gaskiyarsa yana tallafe kanshi da
tafin hannunsa guda daya.
Kaman baijishi ba haka yayi,sai ya duqa kadan kaman yana dauko
wayarsa,ya faki idon omari din ya hado da wata babbar apple guda daya,ya dago cikin
hanzari ya jefi omari din da ita yana cewa.
"Ban sani ba......wannan ta baka amsa dan neman rashin zaman lafiya,zan gayawa
nanay,duk ranar da akace mayu sun kamani to tabbas cikinku ne kai da su amjad" Sosa
qirjinsa inda apple din ta sauka omari keyi yana dariya bayan ya dauketa daga saman
cinyoyinsa inda ta fado.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
βπ½
*HUGUMANKU CE*
π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
Page 70
____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________
"Ka tunamin da masoya......yau ya kamata mu hadu mu sada zumunci koda ta
video call ne........amma dai gaskiya ce ba zamu daina fadi ba,ka rufa mana asiri
ka fidda mata ko za'a samu kaifin kyan nan da abinda ke diban mutane ya ragu".
"Saika aurar dani din ai" Ya amsa masa qasa qasa yana sauka da stairs din cike da
karsashin nan nasa da cikakken kuzari irin ta lafiyayyen namiji.
"Saura qiris.....menelik na nan,ga kuma saamee,auren gata,mata biyu a rana
daya.....motii yafi daukan jikokinsa da yawa kuma da wurwuri.......don wallahi a
idanunka naga duk matar daka aura zai wahala ta cika shekara daya babu d'a". Wannan
maganar ta omari ta qarshe ta sakashi sakin murmushin da baiyi niyya ba. Omari yafi
kowa shige masa hanci da qudundune,bai sani ba tsananin shaquwarsu ne ya kawo
haka?. Yafi kowa gaya masa maganganu ire iren wannan gaba gadi,ba kunya ba shayi ko
nauyin abinda zai fito daga bakinsa. Tabbas banda yanzun yana da abunyi me
muhimmanci sai ya koma ya samu omari ya gaya masa wanne irin kalar sharri ne yayi
masa haka?,amma ya saka maganan a mala,tabbas sai omari yayi bayaninta.
Bedroom dinsa ya koma ya daura alwala,sannan ya tsane ruwan da
towel,don yasan zai wahala kafin su gama ganawa lokacin sallah bai shigo ba. Babban
minister ne harkokin tsaro na cikin gida,yasan da zuwansa,amma bai bashi daman zuwa
din ba,bai kuma zaci zaizo koda bai samu izini daga gurin haisam din ba. Tunda ya
riga yazo bazai qi ganinsa ba,don mutuntawa da martabawa suna daya daga cikin
kyawawan halayen haisam din.
Kafin ya fita ya dauki personal waya ya kira security kan su bashi
masauki gashinan fitowa.