Showing 129001 words to 132000 words out of 168506 words

Chapter 44 - luu luu Book1 by Huguma

Miqewa tayi a matuqar fusace,saidai kafin ta samu daman cewa komai har
ya bada tazara daga inda take,sai wannan qamshin da har yanxu ba zata iya mantawa
dashi ba.......wannan qamshin da ta taba ji a wancan ranar......a hippodrome
Niamey....qamshin da taji a jikin wancan mutumin da a yanzun take sake jinsa.

Wannan qamshin da aqalla a sirrance ta sanya an kawo mata kalar
turaruka daga qasashe daban daban da manyan riders na dawakai na kowacce qasa
sukafi using nashi......a qalla sama da kwalba dari bakwai.......saidai ko me kama
da wannan qamshin bata samu ba........ya akayi shi wannan da bata san waye ba ya
samu qamshin?.

Daukuwa hankalinta yayi,ta sake shaqar iskar da kyau tana fesar da ita
gami da lumshe idanunta. Ganin sultane a yanxu yana da matuqar
muhimmanci......kamar yadda sanin waye wannan mutumin me tsananin tsaurin
ido........karbar kalar turaren da yake amfani dashi bayan tasa an ladabtar mata
dashi akan abinda ya aikata din a yanzu.

Maida dubanta tayi ga inda take tsaye.....ba guri bane na wasa,ba kuma
guri bane da kowa da kowa yake da damar takowa xuwa ciki ba,don koda masu tsaron
gurin suna ta wajen gurinne bata cikin gurin ba. Dukkan wanda ka gani yana kai kawo
a gurin tabbas yana cikin AHALI ko jinin sultane,kusanci kuma bana wasa ba. TO
WAYE?.......KO ALJANI NE?. Wani tsinkewa zuciyarta tayi,idanunsa irin idanun nan da
take gani a mafarki ne,irin wadanda ta gani a hippodrome ne sak!....wasu iri idanu
haduwarsu da nata a jikinta takejin ba gama garin idanu bane.....kamar su din an
cirosu daga cikin wani abu na dabanne bawai daga nau'inkan idanuwan mutane data
sani ba......qamshin sa.....dama abinda ya faru a yanzun,komai kamar ya maimaita
kansa ne.

Wani irin sanyi qafafunta taji sunyi,tsoro taji ya shigeta,ga yanayin
gurin daya soma lullumewa saboda gabatowar magariba. Me zai faru idan ya zamana
aljanu sun fara wasa da hankalinta ne da tunaninta?. Tafin hannunta takai saman
fuskarta da niyyar shafa don bawa kanta relief,saidai kuma wannan qamshin dai taji
fes cikin hannuwan nata kamar an diga mata turaren ne a cikin su.

Da sauri ta janye hannun tana duban tsakiyar tafin hannun. Hannun dai
nata ne,wannan lallausan tafin hannun da kowacce rana cikin wankeshi ake da
nau'ikan mayukan wanke hannu,ta kuma shafeshi da ajiyayyen cream na musamman saboda
hannun kawai,amma qamshin nasa ne......qamshinsa ne.

"Kina dab da rasa ganin sultane" Wata zuciyar ta yunquro mata da lamarin da ya
sanyata takowa ganin sultane kai tsaye ba neman izini ba iso. Damqe tafin hannun
nata tayi tana jin cewa wannan shine issue na gaba mafi muhimmanci a gareta. Ta
tsani wanzuwar qamshin a tare da ita......amma a yanzun tana buqatarsa a hannunta
zuwa awannin da zata kammala ganawa da sultane.

Tun a parlor din farko data hangi sultane din tsaye kowanne karsashi
nata ya soma sulalewa. Wannan kwarjinin dake lullube da fuskarsa dama gangar
jikinsa gaba daya suka soma dakushe nata kwarjinin dama jarumtarta,sai wani irin
rauni ya fara sauko mata,irin raunin da d'a kanji a sanda yake neman alfarmar da ba
wanda zaiyi masa shi sai iyaye,sai kuzarinta ya ragu,tayi qasa da kanta tana takowa
zuwa gabansa,ta iso dab dashi sannan ta sulale saman gwiwarta tana kafe gwiwoyinta
a qasa.

Wani abu qwaya daya da duk duniya sultane keda wannan girman da zatayi
masa shi......wani aiki da a duniya banda mahaliccinta babu wata halitta data taba
zubewa hakan a gabanta,sai ta saki siririn kukan da bata taba yarda ta yishi gaban
kowa sai gaban mutum biyu SULTANE DA MAMMINA. Don koda cikin addu'a da salla
batasan yadda ake kuka ba,bata zama doguwar addu'a saboda bata taba hasashen tana
da wata buqata ba. Rayuwarta ta cike mata tako ina cif cif a nata idanun,bata da
sauran abinda zata kuma roqa,rabbana Aatina fiddunya hasanatan wafil Aakhirati
hasanatan wa qina azabannar kadai take iya maimaitawa.

Yana tsaye kawai goye da hannuwansa a qirji. Baice mata ci kanki
ba,kaman yadda baice ta tafasa sauke ba. Indai akhnan ce......indai khadeejatu
ce,indai kuma shine ya haifeta yasan tabbas zatazo. Ya shiryawa zuwan nata kuwa da
kyau,ya kuma shiryawa ko meye zata ce,ya riga ya yanke hukuncin da ba abinda zai
sanyashi maida hannun agogo baya. Lokacin aurar da AKHNAN daga masarautar agadez
yana ji a jikinsa yayi,babu kuma abinda zai sauya wannan. To amma ta wani
Fannin.....idan har yace kukanta baya taba ranshi......ko kuma kukanta bata
mintsinin zuciyarsa yayi qarya. Kowanne iyaye akwai cikin 'ya'ya wanda Allah yake
jarrabarsu dashi,shi kam ya amince da akhnan din aka jarabceshi. Baya iya dauke
idanu daga dukkan wani ko wani abu da zai kusata da ita ya illatata ko ya cutar da
ita.....bashi da juriya jumuri ko jarumta game da ita.....ba kuma wai haka kawai ta
samu dukkan wadannan ba....Aah SAFEENA ce sila.

A duniyarsa ba wata halitta sama data safeena......ba wani mutum a jiya
ko a yau shekaran jiya ko gobe da zai iya wafce matsayin safeena a rayuwarsa,har
zuwa ranar da numfashinsa zaibar gangar jikinsa.

"Inda zaki sauqaqawa kanki khadeeja ki tashi hakanan,don babu abinda zai sauya
wannan hukuncin......ZARTACCEN ABU NE kuma tabbatacce da ikon Allah......ban taba
tunanin akwai lokaci da zaizo da zan iya zartar da haka ba a kanki......sai gashi
yanayi yazo da bayanan da suke gwada hakan shine gata na qarshe da zan gwadawa
rayuwarki......ki tafi ki fara shirye shirye......na baki watanni biyu kacal ki
horas da kanki yadda zaki zauna da HAKEEM a mazaunin mijin aurenki na dindindin".
Ya qarasa maganar yana soma barin wajen bayan ya dauki carbinsa da alkyabbarsa ya
maida saman plain jallabiyyar jikinsa.

Tafi kowa sanin sultane bawai don tafi kowa doguwar rayuwa dashi
ba......tafi kowa saninsa domin shi din jinin jikinta ne. Daga yadda ya nuna mata
ta sake karaya da samun tabbacin hukuncin sultane na wannan karon BABU GUDU BABU JA
DA BAYA!. Indai hakan ta kasance ta cika marar nasara.....tozartacciyar da zata
auri namijin da yafi kowanne nau'in mazaje rauni da kuma rashin NASARA.

Namiji me ilimin arabiyya kadai?......koda yana da ilimin nasaara ba
zabinta bane,hakeem da ire irensa dukka sun kasa .....namiji irin hakeem koda aisa
ko shehnaz bare falaak ba zata yiwa fata ba.

Koda tana ra'ayi muradi ko burin aure......tsayayyen namiji.....jan
zaki.....me budaddun idanun da suke iya hangen duniya a tafukan hannuwansa.......me
iya sarrafa tunani dama abinda duniya ke ciki.....me idanu a kowanne fanni na
rayuwa,gwarzo jarumin da ba abinda ke iya raunanar da zarrarsa......irin wannan ne
WATAQILA......WATAQIL ta iya bashi dama cikin kaso daya cikin dari ya gwada
sa'arsa.....sa'ar da idan ta tabbata wala'alla ta bashi daman ci gaba da nemanta
har zuwa sanda zata iya jin cewa ita KHADEEJA MUHAMMAD HAMMUD zata iyayin aure a
rayuwarta.

Sanda takai qarshen tunaninta sultane ya dade da bacewa ganinta. A
hankali yakai yatsarta kan fuskarta tana taba dumin da taji yana gangaro mata.
Duban yatsun ta sakeyi,hawaye ne......farare tas masu dumin da batasan sun sauko
mata ba.

Kuka ba dabi'arta bace......amma akan sultane da hukuncinsa zata iyayin
sama da kuka dinma.


★ "Me yasa ka nuna masa kana iya zama a gidan nan gaba?". Omari da ya zuba masa
idanu yayi tambayar ga haisam din kai tsaye.

A hankali ya bude idanuwansa,duk da cewa bai motsa ba ko kadan daga
yanayin yadda yayi relaxing cikin kujerar. A nutse yake duban omari,yana kuma son
hotonta ya bace bat daga idanunsa.

Muryarsa can qasa,cike da gajiyar da yake ji cikin sassan jikinsa yace.

"A wannan karon...cikin jikina nakeji akwai wani abu cikin masarautar,da akwai wani
abu cikin gidan,jikina ne kawai yake bani hakan,ba don ina da tabbaci
ba.....komawata bata lokaci daya bace.....komawata zata zama kadan kadan ne har
izuwa wani lokaci idan komawar ta tabbata gaba daya.......naji oromian language a
muhallin da naga gilmawar tufafin hadiman cikin gidan.....tabbas dole yana
kasancewa akwai alaqa ko sanayya ta juna tsakanin duk mutumin da kuke yare daya
dashi.... Qabila daya a sanda kuka tsinci kanku a wata baquwar qasar da ba taku
ba.... Tabbas akwai wannan zumuntar" Ya qarasa maganar yana jin tabbaci har cikin
ransa. Shuru omari yayi yana jinjina kai,hasashe da maganganun haisam a bisa layi
suke,baisan dalili ba,amma shima a jikinsa yake jin kamar nasara ce take tunkarosu.

"Meye sunan yarinyar da ka hadani race da ita?". Haisam yayi tambayar sanda yake
miqewa tsaye,sanye da wata fara qal din shirt cotton sosai me gajeran hannu da
round neck,abinda ya bayyana cikakkun muscles dinsa da suke gayawa duk wanda ya
kalla yanayin qarfi da yawan motsa jikin da yake dashi. Hannunsa zube a aljihun
wandonsa da bai sauka har qasa ba.


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*
PAGE 65


Daga kai omari yayi yana dubansa yana kuma d'an jin mamakin tambayar,don
ko a wancan karon haisam din baima tsaya sauraren kowanne bayani akan race din
ba,abinda yafi maida hankali kawai shine yadda wasan zai qare,su kuma samu daman
shigewa cikin agadez a sirrance.

"Princess akhnan muhammad hammud.......qasaitacciyar d'iyar sarki muhammad
hammud......bansan ya zata kasance ba duk ranar da tasan cewa kaine silar faduwar
nasararta" Omari yayi maganar yana sakin murmushi idanunsa akan haisam. Ya san
halin haisam din,yana da sauqin kai ta bangarori da dama.... Yana da bala'in bada
girma daraja da martabawa ga dukkan wanda yake sama da shekarunsa........amma fa
bashi da dadi a wasu lokutan......yana da wata irin zuciya da muddin aka
tabota......sauketa yana zama abu me wahala......ba kowanne irin hali da dabi'u
yake tolerating daga waninsa ba......akwai wasu halaye da dabi'u da muddin kana
dasu kada kayi kuskuren sha'awar yin rayuwa dashi. Yana da girmamawa don haka
bayason raini,bai fiya daukan kansa da girma ba......amma kuma baya daukan raini
wulaqanci ko qasqanci. Yana da dokoki......yana da iyakoki.......yana da layuka da
yakam shata akan kowanne mutum da zaiyi rayuwa dashi.

RESPECT wani abu ne muhimmanci a tare dashi........baya wasa dashi
baya yiwa wani wasa da mutuncinsa. Miskili ne irin miskilancin da idan ya motsa
masa zaka jima kana rayuwa dashi baka gama fahimtar ya sound na muryarsa yake ba.
Zai iya wuni guda kuna hira yana maqale da littafi abinsa,ko kunnensa ba zaku samu
ba ballantana hankalinsa. Murmushi yafi zame masa amsa akan ya furta da
bakinsa,dariyarsa tana da qaranci qwarai da ba kowa yasan launinta ba.......saidai
duk da wadannan yana da zuciya me taushi......yana da wani irin kyakyawar zuciya me
cike da dimbin alkhairi..... Irin alkhairin nan me sanyi da saka zuciya a mamakin
mallakin zuciya me tarin alkhairi irin wannan.

"Na fahimci abubuwa da dama a tattare da ita a fitata da nakeyi cikin mutanen ta"
Omari ya dora da fadi ganin ya samu daman hiran da yakeso yayi da haisam din. Taku
biyu haisam din ya qarayi gaba,abinda ya tabbatarwa omari idan bai hanzarta ba
haisam yana iya tafiya abinsa.

"Bata yana faduwa ba a dukkan komai.......itace gaba a kowanne abu da zai taso,ta
tsani faduwa.......tana da wata irin izza da take rayuwa sama da izzar da sultane
mahaifinta yake da ita. Ba kowa bane yasan fuskarta,ba kowa bane yasan muryarta,ba
kuma kowa bane yasan ainihin kamanninta koda kuwa wadanda suke rayuwa cikin
gidan.......a cewarsu har yanzu ba'a halicci mijinta.....su a karan kansu sunsan
babu wata halitta data dace da princess akhnan hammud..........kaima kuma tana
neman dukkan wata hanya da zata sake tsere da kai.....hakan kuma nasan baya rasa
nasaba da faduwarta daka zama sila" Omari yakai qarshe yana miqa masa wayarsa bayan
ya bude wani abu yana miqa masa.

Taku biyu haisam yayi ya dawo baya,ya kalli wayar da lumsassun manyan
idanunsa kafin ya miqa hannu ya karba yana dubawa. Har yanzu murmushi ne shimfide
saman fuskar omari,ya dade yana neman wannan damar da zaiwa haisam
magana........yanason yaga dambarwar ya zata kaya. Yana ganin yawan saqonni daga
hippodrome suna neman cikakken bayanai a kansa,da kuma yawan adadin request da suke
sake turawa na shirya sabon race da zai zama globally gaba daya.

Zayaso yaga yadda nasu prince din zai sake nunawa wannan qaramar
gimbiyar TAZARA da bambamcin dake tsakanin MAZAN ETHIOPIA da matan AGADEZ. Yayi
imanin cewa koda sau million nawa ne zata sake gwabza tsere da haisam,abune me
wahalan gaske taci nasara a kansa. Baisan gaibu ba......amma ta bangaren sarrafa
dawakai da raqumma baya tunanin har yau akwai mutumin da yakai haisam fasahar
sarrafasu. Bai manta dalilin hanashi wasan tseren da akan shiryawa 'ya'yan sarakai
da 'yan sarauta na cikin yankin jimma gaba daya ba....... Qwarewarsa da zarrarsa
tafi ta kowa,shi kadai yake zuwa na daya a dukka shekara ko watannin da za'a shirya
wasan,dole nanay ta sanya aka janyeshi daga komai gudan bakin al'umma.

Email din farko kawai ya karanta......tun sakannin da suka gilma
tsakaninsa da ita a jiya yaji a jikinsa itace. Yana da wani kaifin basira da
fikirar laqantar abu. Second biyar din kacal suka dawo masa da abinda ya faru a
wandancan mintunan na satittikan baya. Wannan abun da yaji ya tsarga jikinsa ya
gauraya da jininsa me kama da jan wutar lantarki still shi ya sake ji a dukka
jijiyoyin jikinsa dake aika jini.

Idan ka dauke mahaifiyarsa nanay......rumaisa noory da Anani da suke
shaqiqansa.......ba wata mace a kaf rayuwarsa da tafukan hannunsu suka taba gauraya
da juna. Ita ta fara kafa wannan tarihin da hakan ya faru a tsakaninsu har sau
biyu,wanda yakejin nauyin zunubin haka saman kowanne tafi na hannunsa har yanzu.

Sanda suke makaranta.......rayuwar makaranta rayuwa ce dake cakude da
tarin nau'ikan mutane mabanbanta. Duk kuwa da cewa sunyi karatu ne cikin
larabawa,sai suke ganin larabawan zamani,ba asalin balaraben mutum me tsananin
kamun kai da sanin addini ba. Shagalallu da har shagalarsu takan basu mamaki.

Yana da wani irin haiba da daukan hankali,wanda sassanyan kyau da wasu
kebantattun halitta da Allah ya bashi ya qara yawan adadin matan dake da muradi a
kansa. Daure fuskarsa......janye jikinsa daga shiga dukkan wasu huldodi da
mu'amaloli da suka shafi Mata a ciki basu sanya hakan matan sun janye jikinsu daga
neman alaqa dashi ba......saima qara neman shiga da sukeyi. Kamun kannasa sai ya
sake zame masa wani irin ado me fusgar hankuls,ba ga ashararan 'yammata ba,harda
kamammu masu kunya da kintsi......a lokacin da gaba daya baisan wani abun burgewa
tattare da d'iya mace ba,bai tantance wani abun jan hankali ba akan diya mace
ballantana yaja hankalinsa.

Abu daya ya sani.....mace me suturce jikinta,mace me kunya yana ganin
martabarta kima da mutuncinta fiye da me bayyana tsiraicinta. Karatu yayi masa wani
irin mugun kamun da bayajin zai iya hada space dinsa dana tunanin wata diya
mace......ya samu wani babban gurbi a rayuwarsa da baya tunanin akwai sauran gurbin
wata mace. Duk da cewa yana cikin shekarun da jini ke harbawa a jikinsa da
sauri,yake kuma aika saqo izuwa zuciya kwanya da ruhi.

Yana ganin yadda a hankali su mutallab wannan feeling din nason yin
budurwa.......wannan feeling din na nemewa zuciya abokiyar hadi kuma abokiyar
tarayya sannan abokiyar rayuwa ya fara tasiri a kansu. Ko kadan bai zargesu ba,don
yasan sunkai wadannan shekarun,don shi bai tasirantu da wannan ba ba lallai ma kowa
ya zama haka ba,bugu da qari dukkaninsu kamar guri daya aka musu tarbiyya. SARAUTA
sunan da aka bawa 'yan team dinsu cikin makarantar kenan da harshen hausa. Kyau
kwanya da gata dukkaninsu Allah ya musu baiwa,saidai wani yafi wani. Su biyu ne
'ya'yan da suka fita daga gidan sarauta cikin team din nasu,wannan ya sanya sukayi
representing sunan team din,don shi da maleek din yanayin gadon sarauta da sukayi
sai suka sake zama yanayinsu daban,ba kuma wai don sun qirqiri hakan bane a karan
kansu....a'ah,wani yanayi ne dake bibiyar jini.

Dukka bayanan omari yake saurara sanda yake qoqarin maida email din
kan nashi wayar,ya kuma saukeshi daga wayar omari din sannan ya miqa masa
wayarsa,bai kuma tsaya qarasa jin qarshen labarin ba ya soma takawa yana fita a
parlor din.

Wanka yakeso yayi da ruwa me zafi kafin ya kwanta,sannan kuma ya kira
nanay da yakejin kewarta. Kewarta dukka da kewar gida yakeji,kaman yadda yasan zuwa
yanzu qannensa dukkaninsu sunyi kewarsa,idan ma akwai wanda yakejin ko a jikinsa
hussam ne,zaima ji dadi me matsa mishi ya kauce ya bashi guri,zaici karensa babu
babbaka.

Sanda ruwan me dumi sosai ya soma ratsa gabbansa sai ya saki wata
ajiyar zuciya yana nutsewa cikin bathtub din sosai. Haka kawai komai nata yake dawo
masa,wanda duk yadda yakai ga ture tunanin sai daya mamaye ilahirin kwanyarsa.

Abinda ya faru akan kunnensa.......maganganun omari da
bayanansa.....email din da aketa turawa da komai da komai,take yaji wani bacin rai
yana sauka saman zuciyarsa a hankali.

Tana da izza tana kuma buqatarta.......tana son girmamawa daukaka da
martabawa amma bata iya aiwatar da ita akan kowanne d'an adam. Ta iya duban idanun
dukka wanda taso ta tozartashi da kalaman da dukka sukazo bakinta,batasan me ake
nufi da MUTUNTAWA da KARRAMA DAN ADAM ba.......

Masanan ilimi sune halittar da tafi RAINAWA tafi TSANA mafiya kuma
qasqanci a idanunta......while kuma sultane mahaifinta ya kasance mutum me karrama
wannan nau'in mutanen da ita kuma suka kasance wulaqa tattu a idanunta......garin
yaya RAYAYYE ya haifo MATACCE?. Daga ina ta samu dukkan wadannan baqaqen halayen da
suke kishiyoyin juna da halayen mahaifinta?.......mahaifiya?. Ya tambayi kansa
tunaninsa yana tsayawa cak!.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login