Showing 18001 words to 21000 words out of 168506 words

Chapter 7 - luu luu Book1 by Huguma

baya gakai dake cikin dakin" Ta furta cikin
wani irin yanayi da zai nuna alamu nason nuna mallaka da kuma isarta.

Dukka su ukun suka zuba mata idanu suna dubanta. Yanayin da tayi magana
kadai wani irin sauti ne dake tafe da izza da nuna taqama.

A Hankali mammina ta yunqura ta miqe tana furta.
"Bismillah". Tsam akhnan ta miqe itama tana gyara zaman yafen dake saman
kanta,wanda santsin gashinta ya hanashi zama dai dai.

"Ina zaki?,mommanki keson magana dake fa?" Mammina ta fada tana duban tsakiyar
idanun akhnan.

"Ba wata magana dake da muhimmanci idan babu ke a cikinta........babu wata magana
da zata bada ma'ana muddin akace an cire uwa daga rayuwar d'anta......".

"Khadeejatu" Sultane da ya miqe daga saman daddumarsa ya koma saman daya daga cikin
kujerun ya kira sunanta. Waiwayowa akhnan tayi tana duban sultane din ba tare data
iya amsa kiran da yayi mata ba.

"Ki koma kiyi magana da mommanki kamar yadda ta buqata".

"Rabu da ita......ka qyaleta,khadeejatu qaramar yarinya ce?......idan kin manta
irgen shekarunki ya kamata ki koma baya ki tariyosu da kyau!" Morsa safiyya tayi
maganar a zafafe da bayyanannen fushin da sultane da kansa zaice ya jima bai ganshi
haka ba.

"Zanyi maganar kamar yadda kika buqata a gabanta......bazan kuma fasa fadin duk
abinda nake da niyyar fada din ba...........ke diya macace gajeriyar rayuwa
gareki......damarmakinki gajeru ne......mafarkanki basu da tsaho......burikanku
kuma qayyadaddu ne.......kina da taqaitaccen lokacin da idan kikayi wasa dashi
saikinyi kuka da idanunki........a sanda kukan nan bazai amfana miki komai ba. Waye
UBANKI da kike ganin kowanne namiji ba tsaran aurenki bane AKHNAN?!!!" Ta qarashe
maganar da madaukakin zafin daya tokare mata dukkan wata mashaqar numfashi da kuma
iska data hada maqogaronta da hunhunta.

"Idan an kutsa cikind duk wani sassan dake daukan sauti zuwa kwanyarki......an miki
busar ke din d'iyar da tafi kowa ce to KIN CUCI kanki........idan a baya kedin
yarinya ce.....yanzu cikakkiyar mace kike da takai minzalin aure daidai da
daidai..........karki manta uwarki ba kowa bace tamkar BUZUWA kamar
kowa........hakanan mahaifin daya kasance shine taqamarki......zaki tsufa a sanda
mazan da kika raina sukayi miki nisan da baza suji kiranki ba harma su
waiwayeki..........zaki tsufa a sanda su suke tsaka da sharafinsu da kuma
ganiyarsu......" Saita juya inda mammina ke tsaye.

Wani irin fusatacce kuma wulaqantaccen kallo ta watsa mata.

"Naso ace zan iya bar miki akhnan kiyi yadda kikaga dama da rayuwarta.......saidai
kuma girman maganadisun jinin SAFEENA dake kewaya a jikinta bazai barni na iya
hakan ba.........bugu da qari UWA ake iya barwa D'A.......ba muna UWA
ba.......akwai da dama da basusan ciwon haihuwar ba.........amma suna da zarra irin
ta nagartattun uwaye........AMSA SUNA ta sigar da sunan yazo dashi wata baiwa ce da
ba kowa Allah yake baiwa ba......."

"Safiyya!......" Sultane ya kira sunanta da wani irin sauti daya sanya kalamanta
lanqwashewa ba tare da sun gama fita gaba daya ba.

Waiwayowa tayi tana dubansa da birkitacciyar fuskarta.

"A gabana kuke.......sassauci na da bayar da dama ga iyalina bawai yana nufin kowa
yayi irin maganar da yaga dama ba" Yayi maganar da irin harshen daya dawo mata da
hayyacinta,ya sake jadda kalmar SULTANE ne a gabanta har tsakiyar kwanyarta.

Sadda kanta tayi qasa a sanyaye tana tattalin hawayenta. Alqawari ne
wannan.......alwashine wannan na haramtawa kanta kuka a gaban zaitun HAR ABADA.
"Tuba nake.......amma dukkanku abun kiwo ne.....kuma zaa tambayeku game da abinda
aka baku kiwon". Lafazinta na qarshe kenan ta juya tana barin dakin da hanzarinta.

Tamkar suka haka yaji lafazinta na qarshe yana sauka saman tsokar
zuciyarsa,ya lumshe idanunsa yana saukesu saman fuskar mammina da hawaye suna fara
sauka daga ramin idanuwanta zuwa saman fuskarta.

"Bansan me zan yiwa safiyya na burgeta ba.......bansan me zan yiwa safiyya na
amintar da ita ba,dama nuna soyayya ga wani jinin yana iya zama qiyayya babba irin
haka?". Mammina ta fadi muryarta na wani irin rawa,ba muryarta kawai ba hatta da
hannuwanta.

Sosai akhnan ta kamo hannuwanta ta riqe cikin nata,wani irin
matsanancin fushi yana tasirantuwa tun daga cikin idanuwanta zuwa saman fuskarta.
Me yasa matar nan sam bata da kirki?,me yasa baa taba zaman lafiya da ita?,me yasa
kullum burinta ta wulaqanta ta kuma tozarta mammina?.....me yasa koda yaushe
idanunta a kulle suke bata ganin alkhairi?,wanne irin butulci ne wannan?......shin
bata jin kunya da nauyin yiwa mammina GORIN HAIHUWA a koda yaushe muddin magana me
shigen haka zata hadasu?

"Mammina......." Tayi maganar muryarta tana rawa.

"Ki daina kuka mammina s'il vouse plaît(please),ina tare dake koda cikin wanne irin
yanayi ne......ke din uwata ce,babu wani abu sa zai canza wannan" Ta qarasa maganar
tana jin zafi sosai cikin ranta. Tana jin wani mugun haushin morsa
safiyya......tana ji inama koda sau daya mammina din ko sultane zasu bata daman yin
wani abu......yin wani motsi me kama da hukunci akan morsa safiyya......tana jin
har ranta ta cancanci hukunci.......butulcinta kuma me girma ne.

"Barni nayi kuka biftu......qyaleni nayi kuka akhnan..."

"Saboda me mammina?!.....saboda me zakiyi kuka?,baki cancanci kiyi kuka
ba.....morsa safiyya ita ya kamata tayi kuka bake ba.....!!!" Tayi maganar a zafafe
fiye da dazu,tana kuma nuna qofar da morsa safiyya ta fita.

"Khadeejatu" Sultane ya furta da wani raraunan sauti da sam bai dace da yanayinsa
ba. Wani irin mutuwar jiki yakeji tana ratsashi da wani rashin karsashi sam,tun
daga sanda momma tayi maganan qarshe ta kuma fice......sai ya zamana kamar ta fice
da kuzarinsa ne da karsashinsa.

"Zo nan ki zauna". Ya fada yana nuna mata gefensa. Sai data zauna sannan ya dubi
mammina itama

" Zaitun ya isa haka......samu guri ki zauna" Kai ta soma girgizawa tana sake
sharce hawayen dake sake bulbulo mata.

"Kayi haquri......ba wai ina nufin nayi gardama da umarninka bane......amma ina jin
cewa bai cancanci na zauna ba alhalin na saka zuciyar safeera a cikin qunci
ba.......tabbas kome safeera ta fadi inajin kaman daidai ne.........tana da
iko,tana da puissance(power) akan akhnan sama da tawa........ina tsoron fushinta
kada yayi tasiri a kanmu......anya Allah bazai tambayemu ba?" Ta fadi da wata
narkakkiyar murya dake nuna zallar tsoro da kuma fargaba.

Sosai abinda ke takore a wuyan akhnan yake sake fadada.......tana jin
kamar zatayi aman zuciyarta. Ta kasa buda baki ta sake cewa da mammina komai,sai
lumsassun idanunta da taketa juya manyan qwayar idanunta a ciki. Me mammina tayi da
Allah zai tambayeta da haqqin morsa safeena?.
"Zoki zauna tukunna" Ya sake fadi yana nuna mata guri. A hankali take takowa harta
iso inda yake nuna matan,saidai kamar kowanne lokaci......bata taba hada mazauni
dashi ba,muddin yana tsaye ita tana tsugunne,idan yana tsugunne ita tana zaune,idan
yana saman kujera ita din bata da wajen zama sai qasa,daya daga cikin abubuwan dake
qara martabarta a idanunsa kenan.

"Akhnan.........kinfi kowa sanin morsa mommanki ce......don wani tsohon karatu ne
da na tabbatar tun bakisan me kalamaina ke nufi ba kika haddacesu.....zan sake
maimaita miki morsa mommanki ce......biyayya a gareta ya zama dole a kanki kamar
yadda zakiyimin......kamar yadda zakiwa mammina"

"Qwarai kuwa" Mammina din ta fada tana goge fuskarta da hancinta da gefen lallausan
mayafinta.

"Kije ki bawa morsa haquri........ki mata alqawari.......ki saka kuma a ranki zaki
maida hankalinki ki fidda mijin aure". Kai mammina ke jinjinawa,jin sultane ya
dakata ya sanya a nutse ta soma magana.

"Gaskiya ne.......a nan morsa ta fimu gaskiya ta kuma fiki gaskiya,kaman yadda naji
tasha fada miki mutuncin mace dakin mijinta......cikar mutuncin mace shine
aure,komai gatanta da martabarta........don Allah akhnan......ko don nayi haske a
idanun morsa,ta daina tuhumata,na daina shiga zarginta ki tsayar da wanda
kikeso......raina bayamin dadi......zuciyata bata min daidai" Ta qarasa maganar
tana hade hannayenta alamun roqo muryarta na rawa kamar wani kukan yana dab da
zuwan mata.

Kai kawai take jinjinawa don bata da abinyi sama da haka. Akwai tarin
maganganu da tarin ra'ayoyin da take buqatar furtasu ko qirjinta zai rage nauyin da
yayi......amma a yanzu ba abinda take buqata sama da kebe kanta ita kadai.

"Allah yayi miki albarka........ya baki abokin rayuwa na gari" Sultane ya fadi
idanunsa akan diyar tasa da wani irin qauna da kulawa me dimbin yawa.

"Ameen ya rahman ya Raheem" Mammina ta fada cikin tsantsar kulawa.


*Zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 08
______________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500
dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da
kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures
xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi
https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba
da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin
iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi
bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________


A nutse ta miqe tana takawa,tana kuma jin yadda bacin rai yake dawainiya
da ita,tana lissafa yadda zata iya zuwa wajen morsa safeera tace ta yafe
mata.........tana juya yiwuwar hakan,saidai kuma muddin umarnin sultane ne,ba wani
abu dake canza wannan umarnin,ba a gurinta kadai ba.......umarninsa TABBATACCEN ABU
ne da babu damar saba masa canza masa ko guje masa.

Har ta kusa da qofa ta dakata,ta waiwayo da wata irin kasala

"Papi"

"Na'am" Ya amsa mata yana dubanta,sai tayi qasa da kanta da salo na girmamawa.

"Inaso ayimin izini gobe na koma Niamey" Shuru ya danyi na wasu sakanni,wanda hakan
zai nuna maka nazari yakeyi kafin yace

"Allah ya nuna mana......Allah ya tsare"

"Godiya nake" Ta fada da lallausar muryarta sannan ta taka ta soma ficewa.

Sanda ta bacewa ganinsu mammina ta dauke idanunta daga bakin qofar
tana maidawa kan sultane,Shima ita yake kallo. Lokutta da dama tausayinta yana
tasiri a ransa fiye da qauna da kuma soyayya. Rashin haihuwa a duniya wani irin
ciwo ne da bashi da misali. Jarrabawar zaitun kenan.......yana daya daga cikin
abubuwan daya kawo kyautatawa me dimbin yawa tsakaninsa da ita......baya ga wata
irin tarin biyayya da take masa tamkar siyanta yayi a mazaunin baiwa bawai matar
aurensa ba. Yana da qwayaye biyu a duniya da zai nuna yace nashi ne.....mallakinsa
ne......mammina bata da ko guda daya,amma koshi da ya mallaki qwara biyun cikin
bege da kewar samun masu yawa yakeyi.

"Ranka ya dade......me yasa ka yarje mata?,me yasa ka aminta ta koma Niamey tun a
gobe gobe?,baka tunanin zata koma ne taje ta zauna ita kadai tayita tunani tana
sakawa kanta damuwa?". Idanu ya zuba mata na wani dan lokaci kafin ya janye
idanunsa. Irin wannan kulawar da qauna me yawan gaske yake gani a idanun mammina
akan akhnan tsahon shekaru ashirin cif kenan. Har yanzu kuma baiga abinda ya canza
wannan damuwar qaunar da kuma kulawar ba.

"Zuwa yanzu ya kamata ki rage sanya kanki a damuwar al'amuran akhnan.......ba
biftun ki ta shekaru ashirin baya bace......wannan wata biftu da muke sanya ran
aurar da ita nan gaba kadan,ta kuma bamu jikoki masu tarin yawa" Yayi maganar ta
qarshe yana jin kwadayin son aurar da ita yana taso masa.

Yana tsananin son yara.....yayi burin tara iyali masu fadi da
girma......saidai hakan bai samu ba......tashi rubutacciyar qaddarar kenan.

"Ita din wani sashe ce na zuciyata kamar yadda nasan sashe ce ta
rayuwarka.......bazan taba iya daina qaunar biftu ba har gaban abada,don Allah ka
tayani baiwa morsa haquri" Tayi maganar fuskarta na narkewa alamun zuciyarta ta
karye sosai.

Hannunsa ya miqa ya riqo nata a tausashe,cikin salon son kwantar mata da
hankali yake dubanta.

"Baki laifin komai ba zaitun.......kawai safiyya nada zafi.......tana da
fushi......wannan ne tazara da banbancin dake tsakaninku......amma bata da
riqo,bana tunanin abun zai dade". Kai mammina ke girgizawa,wani abu yana mat yawo
cikin zuciya.

"Ka tayani fahimtar da ita.......ya kamata ta sassauta fushinta a kaina......indai
akan qaunar biftu ne.......muddin kulawa da yawan adadin soyayyr da nake gwadawa
biftu zata iya zama laifi......ka fahimtar da ita zanyita dawwama a mazaunin me
laifi a wajenta" Tayi maganar tana riqe hannun sultane da kyau,wani hawaye me dumi
yana zarto mata.

Hannunsa ya miqa a hankali yana qoqarin kauda hawayen daga fuskarta.

"Ba zaki taba zamowa me laifi ba.....don ba inda qauna ke jawowa qiyayya.....ko
bata fuskanta yau ba.....koda bata fuskanta gobe ba tabbas wataran zata fahimta".
kawai matsawa mammina tayi ta dora fuskarta saman kafadarsa tana sakin wani
boyayyen kuka daya sake daga hankalinsa.

Gaba daya ranar zuciyarta a quntace take,a quntacen kuma cikin fushi da
bacin rai ta qarasa yinta. Don tunda ta isa sassanta raji wani abu me kama da ciwon
kai ya saukar mata,saita sallami kowa ciki harda cooks dinta dake hada hadar ganin
sun shirya abincin da zasu burge uwar dakin nasu dashi a wannan ranar. Duk da cewa
babu tabbacin fitowarta cin abincin a kowacce rana,amma hakan bai sanya sun gaji ko
sun daga qafa da tunanin girka abinda zai burgeta ba.

Sun sani yardarta da amincinta idan mutum ya samu cikin masarautar
agadez to ya taki babbar sa'a a rayuwa,wannan ya sanya basa wasa da duk wani abu
daya shafeta ko ya danganceta.

Lamo kawai tayi cikin duvet,tana jin kamar wani irin zazzabi zazzabi
yana son kamata,wanda ta tabbatar zallar bacin raine kawai dake sasaqar zuciyarta.

A gajiye ta zare jikinta daga cikin duvet din,ta zuro dogayen kuma
dogayen qafafunta qasa cikin jin kasalar miqewar kafin ta tattara dukka sauran
qarfin da ya rage ta yunqura a nutse cikin yauqinnan nata daya cakuda da yauqinta
na halitta

A hankali take takowa gaban balcony din sassanta wadda aka qawatata da wani irin
yanayi na lafiyayyun shukoki masu bada ni'imtaccen qamshe. Furanni ne masu yawa a
jikinsu da suka bada launin fari da pink,abinda ya sake qawata gurin kenan sosai ya
kuma bada wani launi da yanayi da musamman.

Wata gown ce a jikinta ta wani irin yadi na musamman da aka yiwa
sassauqan dinki,saidai gown din ta saukar mata sosai ta rufe har saman
qafafunta,duk da bata da wani hannu na kirki ko kuma hannun azo a gani.

Tsaye tayi jikin qawataccen qarfen balcony din,tana jin yadda sassanyar
iskar yammacin ke kadawa da wani yanayi dake saurin cire damuwa aran dan adam.
Sosai irin wannan iskar take mata dadi,wanda mafi yawan lokaci anfi samunta ne
tsakanin sallar bayan sallar asuba zuwa yammaci da farkon dare irin wannan,yammaci
zuwa daren da damina ta soma sauka a wasu maqwaftan qasashen da garuruwan,wanda
gari zai hada hadari ya kuma bada iska me kyau me cakude da qamshin qasa.

Sosai ta zuqi iskar tana kuna fesar da ita ta hanyar hancinta dake
zaune das saman fuskarta da wani irin zubi da tsari daya qarawa fuskartata matuqar
kyau. Hannu ta sanya ta janye gashinta dake yawo saman fuskarta sakamakon busawar
iskar data maida gashin nata kamar wani abun wasa,don babu ribbon ko band ko daya
data kama gashin dashi,hasalima tana jin kamar ciwon kai zai saukar mata ne,wannan
dalilin ya sanyata barinsa a haka kawai.

Tana samun view me kyau na masarautar agadez a irin yanayi irin
wannan.......tana samun damar kallon cikin masarautar da kyau dake qawace da wasu
irin qananun fitilu masu tsananin haske da suke sake qawata idanun me kallo,su kuma
sake qawata masarautar da qara mata kyau da kwarjini.

A karo na hudu ta sake maida gashinta gefan kunnenta saboda yadda yadda
iska ke sake kwasoshi kaman zai shiga mata idanu. Ta sauke ajiyar zuciya me nauyin
gaske tana jin yadda zuciyarta da kwanyarta gaba daya suka gaji da wannan tunanin.
Tana jin kamar daren yayi mata tsaho zuwa wayewar garin da zata bar agadez zuwa
Niamey.......tana jin masarautar duka ta mata zafi,sai ta dinga jin me yasa ta zabi
kwana a agadez ba Niamey ba?.

Ta soma jin gajiya sosai cikin dukka tunaninta,har yanzu kuma ta
gagara gano amsar nan guda daya dake wahal da tunaninta. Me zatayi da aure?,me
zatayi da wani d'a namiji?,bayan bata rasa komai ba?,ba abinda kuma take da
buqata?.......bata jin kuma akwai ranar da zata buqaci wani namiji a cikin
rayuwarta.

Ba komai cikin halittar d'a namiji face zallar sonkai.......
Mugunta,rashin imani ga mace da kuma tsananin son juya mutum da mulkarsa ta duk
hanyar da suka dama.

Ita dukka wadannan abubuwan bata shirya tunkararsu ba.......bata shirya
zama qarqashin umarnin wani ko hanin wani ba........bata shirya zama qasan juyawar
wani ba.......bata shirya karbar umarni ko hani daga hannun wani ba. Ita ke
umarni.......ita ke hani......ita ke alfarma......yardarwa wani ya zame mata miji
yana nufin dukka wadannan damarmakin sunbar hannunta.

Kai ta girgiza a hankali,tuna wannan kawai yana sanya ranta ya baci,ina
ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login