Showing 117001 words to 120000 words out of 168506 words

Chapter 40 - luu luu Book1 by Huguma

wata juriyarta ta qare,koda ta cikin allon computer
din tana muradin ganin fuskarsa.

"Nagaan waaree booda obbo(barka da yamma obbo)" Ta fada a hankali tana sauke
idanunta akan fuskarsa.

"Barka kade saamee......ya dalibai?" Yayi maganar yana qoqarin jawo wayarsa dake
bada haske,abinda ya sanya sam idanunsa da hankalinsa basa kan system din kenan.

"Alhamdulillah" Ta fada a hankali tana jin wasu abubuwa biyu suna saukar mata.

Na farko wani yanayi da kai tsaye zata iya kiransa da qarfin izzar so irin
tashi,wata qauna da ta cakuda da kewar abinda zuciya keso din. Ya mata wani
fresh,ya mata wani irin kyau me daukan hankali,irin kyan da a kowacce rana ta daga
idanunta take sake ganin sabuntarsa a idanunta.

Na biyu tayi burin ya kalleta......ko yaya itama ya kalleta kaman yadda
ta kalleshi,sai kuma akayi rashin sa'a sam idanunsa basa kanta.

"Zamu sake magana anjima hussam,of eeggadhu(ka kula)" Ya qarasa fada yana aza
idanunsa akan saamee da tuni ta maida kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta kana
ya katse kiran gaba daya.

System dinma gaba daya ya soma kashewa yana dan aza idanunsa akan
agogon dake jikin system din kafin takai ga yin shutting down. Siririn tsaki yaja
yana jin kamar kada yau ya sake fita ko ina. Saidai cikin qasa da second guda
abinda ya faru jiya ya gilma a idanunsa.

Yaren oromo da ya fita da wani irin harshe da accent da yafi kama da
irin nasu sak!. Irin karin harshen dake nuna duk wanda yayi yaren idan ba
haifefaffen jimma bane yankin oromia,to lallai akwai wani dogon zama da kuma
doguwar rayuwa da yayi a qasar.

Gilmawar kayan da ya gani dake bashi tabbacin na gidan sarautar agadez
ne......sai ya miqa hannu ya dauki daya wayar tasa.

Notepad dinsa ya bude,yana sake duba documents din da yayi saving plate
number din jiya yana sake duban numbers din da idanu,sai yayi minimizing ya koma
contact nashi yana laluben wata number.

Bugu daya tak aka daga. Daga daya sashen ya soma gaidashi cikin
girmamawa da yaren oromo irin na bakinsa sak.

"Aiki nakeso ayimin,amma bana buqatar gaggawa......take your time,inason respond
din da zan samu ya zama me ma'ana....."

"In sha Allah sir" Ya kirashi da laqabin girmamawa na yaren turanci. Bai katse
kiran ba yayi copying numbers din ya tura masa sannan a nutse yace.

"Have you seen it?".

"Yes sir" Ya fada da qwarin gwiwa.

"Fingers crossed" Ya fadi a taqaice.

"Thanks" Shima ya amsa masa,sai ya zame wayar daga kunnensa yana miqewa riqe da
dukka wayoyin saboda knocking da yaji an masa kadan,yasan kuma zai wahala idan bai
kasance maher bane.

Ya canka daidai,maher dinne rungume da litattafai a hannunsa.

"Minti arba'in yayi saura lokaci ya cika".

" Ka jirani" Kawai yace dashi yana takawa a nutse gami da nufar hanyar da zata
sadashi da sassan dakunansa yana karbar towel daga hannun salaana,abinda ke alamta
masa ya kammala hada masa ruwan wanka kenan.

Baisan me yake faruwa dashi ba,ba kuma zaice gashi ba......amma haka
kawai yake loosing interest akan aikin. Aikin da shi ya nema gudanar dashi,amma
haka kawai yakejin yana barin kansa,wanda baisan dalili ba.

Dukkanin yaransa da suke aiwatar da aikin tare sun fishi zama serious.
Baisani ba ko saboda sanin da sukayi masa shi din bame wasa da ayyuka bane yasa
kowannensu yake cikin hayyacinsa akan aikin ba tare da sunsan shi din ya rasa
interest ba.

Ya dan jima gaban closet dinsa yana duban kayansa dake tsare a saqale
jikin hanger. Mafi akasarinsu jubah ne masu tsananin kyau sulbi da kuma daukan
hankalin dake bayyana tsadarsu da darajar zaren da aka samar dasu. Kusan yawancinsu
qasar qasar saudiyya ne....qatar oman da morocco. Sai kuma cloak robe da suma
bangarensu yake daban,nau'ika da kaloli mabanbanta da suka dace sosai da kowacce
jubah da jallabiyya dake cikin closet din. Akwai kurta da kuftas masu kyau,wanda ba
kasafau ya fiya sanya kufta ba,yazo ya samesu ne an jeresu cikin closet din,wanda
ya tabbatar aikin abdii ne,kuma tafiyayyu ne daga qasar nigeria,bayan wani dare da
abdii din ya kashe yana searching qasa da kuma yankin da yafi ko ina iya
dinkasu,bincikensa ya sauka a garin kano dake qasaf nigeria din. Sun burgeshi,sun
bashi sha'awa sosai,kowacce kusan da hularta 'yar Maiduguri me daukan idanu,amma
har yau bai sanya ba,yana ganin kamar bazai zama comfortable ba idan yayi shigar.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki
kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

✍🏽
*HUGUMANKU CE*

πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 59
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me
kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse
masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk
wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri
kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai
gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma
suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
_____________________________
Sake bin kayan yayi da kallo,a qalla sun kusa set d'ari. A hakan kuma
kadan aka tsakura daga suturunsa dake tsakanin addis ababa da kuma jimma,don idan
yace yasan adadin suturarshi tabbas yayi qaryar da baisan ta inda zaiyi kaffararta
ba.

Wani irin ni'imtaccen qamshi cikin closet din kanshi yake
bayarwa,ballantana kuma suturun dake ciki,masu abu da abunsu....... Gidan turare ne
shi din.....sai ya zamana kuma masoyin turaren,kyautuka guda biyu mafiya girma da
tsada da daraja da zaka masa shine. Turare da littafi,sai kuma dabino daya zame
masa kusan abincinsa. A kowacce shekara qwararrun masu sarrafa turare daga dukkan
kamfaninsa ne suke zama su fidda masa qamshinsa na musamman,irin qamshin da komai
kudi dukiya ko mulkinka basa taba fiddashi ko su saidashi,wani unique qamshi ne da
babu inda zaka sameshi sai jikin SHEIK HAISAM din.

Sun fara haka ne da zummar tukuicin kyautatawa da yakewa dukkan wani
ma'aikaci dake qarqashinsa,basusan dame zasu saka masa ba,shi yasa suka maida hakan
a mazaunin hanyar rama alkhairansa a kansu. Hakan yana masa dadi,dukkan wani turare
da zasu fidda masa yana jin kamar yafi na baya dadi,da wannan ya
kasance.......yadda komai na sheik HAISAM yake na daban.......na musamman,haka ma
qamshinsa. Wannan qamshin ya nasaka zukatan 'yan mata da yawa......qamshin da
muddin kika jishi sau daya ba zaki sake jin makamancinsa ba har abada.

Masu kudi da masu mulki da dama daga sassan duniya,sun saka kudade
masu nauyi saboda samun irin wannan scent din,amma dukka ma'aikatan,duk da ya basu
dama sunqi aminta su bawa kowa wannan TAMBARIN wannan TAG din,wannan alamar ta
SHEIK MUHAMMAD HAISAM ce.

Wata dark grey colour jubah hannunsa yakai kai. Lafiyayyen dinki aka
mata da wani irin yadi me yauqi. Hannu da wuyanta dukka na musamman ne da wani irin
button na musamman.

Cloak robe ya zaro me hasken kala da zata dace da rigar ya taka yana
matsawa a gurin. Tsaf ya kammala shiryawa,yayi tsaye gaban mirror yana daura agogo
a tsintsiyar hannunsa. Tun daga nesa idan ka kalleshi zaka ga wani irin kwantaccen
kwarjini saman fuskarsa,duk da yau fuskar haisam din adan dinke take,wanda yake da
nasaba da yanayin da yakejin zuciyarsa. Haka kawai yakejin ranshi ba dadi,kaman an
masa wani abu daya taba ranshi. Ya sani,ba wani wanda ya bata masa rai,hakan
wataqila yana da nasaba da shaidan,wanda a kullum burinsa shine ya zunguri zuciyar
dan adam,don haka ya daga idanunsa a hankali ya sauke akan fuskarsa data fita sosai
da wani irin annuri. Kwantacciyar sumar kansa data habarsa zuwa kuncinsa tayi luf
da wani irin baqi me qyalli da daukan hankali,ya lumshe almond eyes dinsa yana
furta.

"A'uzubillahi minashshaidanir rajeem.....subhanallahi wabi
hamdih......subhanallahil azeem". Ya maida qwayar idanunsa akan agogonsa.

Tsaiwa yayi cak yana karanta brand din agogon. Yayi kudi da yawa,yayi
tsadar da duk wanda yasan kudin agogo yana kalla zai dora zargi a kansa,ya jawo
jewelry organizer din dake saman dressing mirror din yana neman me sassauqan
kudi,saidai har ya gama lalubensa bai samu daidai da wanda yakeso ba,dole ya dauki
qaramin ciki ya daura ya koma neman takalmi.

Shima still kaman agogon dai,duk ciki ba wani me qaramin kudi,ya gama
lalubensa shima dole hakanan ya dauka ya saka,a ransa yana mita akan abdii.

Baisan me ya samu abdii ba,shi ya shirya masa komai na amfaninsa,me yasa
yake manta dalilan shigowarsu agadez ne?. Dole komai nasa ya zama moderate,idan ba
haka ba da taqi kadan zamansu zai kasa tsaho,duk da yace baisan inda zai sama masa
sutura masu qaramin kudi ba sama da wadannan,amma dole ya canza masa wasu abubuwan
nashi.

Cikin girmamawa drive dinsa ya bude masa BMW din. Yana shirin shiga
muryar omari ta tsaidashi.

"Captain sheikh" Ya fadi yana takowa a nutse. Baice komai ba sai daya shiga ya
zauna,ya daga idonsa yana duban Omari. Gira kawai ya dagewa Omari din,a karon farki
kuma Omari ya fahimci yau 'yan miskilancinne a kusa.

Maganan da zasuyin me muhimmanci ce,banda hakan zai qyaleshi ne ya
tafi,yasan idan 'yan mode din nasa suka sauka zaya nemeshi da kansa.

Screen din system dinsa dake hannunsa ya juya ya nuna masa,sai baice
masa komai ba bayan ya kalla ya masa nuni da hannu yana matsawa ciki omari din ya
samu gurbin shiga.

Ba wanda yace da kowa komai,omari na qoqarin qarasa saita bayanan da
zaiwa haisam din,yayin da haisam din ya maida hankalinsa ga qari'ar dake fita can
qasa cikin motar. Sanda Omari ya yunqura zaiyi magana sai ya dauki remote din dake
gefansa ya kashe karatun.

"Captain sheikh.......mr Ilaalcha gadi buusuun" Ya fadi yana murmushi ba tare daya
kalli haisam din ba.

"No more oromo dialogue here mr man......ka kiyaye" Ya fadi yana maida mode dinsa
na senior oga kaman yadda yakeyi wani lokacin.

Murmushi me kama da dariya sosai Omari ya saki,yayi saluting nasa yana
cewa.

"Yes sir......but am sorry,Allah saina fadi,mr lowering gaze.......amma komai naka
ya zama me daukan hankali.......ta yaya su matan zasu iya kame idanunsa daga
kanka?......ka kalli kanka yau kuwa?,kasan Allah?......am very serious,duk yarinyar
da tayi falling a kanka saina tayata yaqin samunka?". Ido kawai haisam ya zubawa
omari,ganin yadda yake maganar da dukka gaskiyarsa. Sai ya janye idanun ganin Omari
shima ya dauke dubansa ya mayar ga system dinsa yana qananun mitoci qasa qasa.

"Haka kawai,rashin adalci ne ka dinga tunanin 'yammata ba zasu soka ba,......suma
da laifinsu.......mu su somu su gani mana".

Bai shirya yin dariya ba sam,duk da dama ba al'adarsa bace,amma duk da
haka sai da omari yayi sanadin fitar murmushi a fuskarsa,ya kuma kaiwa Omari dind
duka,sai shima ya saki dariya yana wani mazewa.

"Allah,da gaske......inajin akwai wani laqanin da kake karantawa a kansu"

"Inda akwai Omari saika riga kowa sani......inda kuma akwai da tuni na dade da baka
omari,kaje kayi kaji yadda nakeji......banaso omari,sau da dama yawaitar mata a
rayuwa mutum irin haka idan baiyi takatsantsan ba,idan kuma baiyi da gaske ba
sharri suke zame masa......amma kaima kaji tsoron Allah,ka manta ma'eesha?.....ka
manta khansaa?,ka manta batul......"

"Qyaleni haka" Omari ya fada da sauri yana boye dariyarsa,sai kawai haisam din ya
dauke kai yana qyale Omari din kamar yadda ya buqata.

Ba wai shi kadai ba,ba kuma Omari kadai ba,kusan dukkaninsu su bakwai
dinnan wani baiwa garesu na musamman. Sun hada wani irin qualities ne da ba kowa
Allah yake baiwa shi ba,wannan dalilin ya sanya suka zama masu nuna godiyarsu ga
Allah ta hanyar kame kansu da kuma kare mutuncinsu da mutuncin iyayensu dama na
addininsu gaba daya.

"Duba nan" Omari ya fada yana jiye system din a tsakiyarsu.

A hankali haisam ke duban bayanan daya fitar masa din yana saurarensa.

"Wadannan guraren,suna daya daga cikin guraren da na samu information gurine na
haduwar jama'a masu yawa kuma mabanbanta a qasar nan da garin nan,sannan a nan ne
kadai a bincike na za'a iya samun wani da yasan yaren oromo,ko yake yarawa ko kuma
ya taba jinsa. Koda taba jinsa yayi zai samar mana haske gurin kusantar samun inda
TURAAD ya boye a qasar nan". Shuru haisam yayi yana ci gaba da duban bayanan,kafin
a hankali ya janye idanunsa.

"Ka hada dukka bayanan ka turamin ta e-mail,sannna ka turawa abba muhammad
dawud.......amma ban gamsu da hakan ba". Ido omari yadan zuba masa. Ya iya magana a
dunququne da qananun jimloli,mai hankali yana iya faffasata yayi dogon sharhi a
cikinta. Duk abinda ya fadi yana da hujja,kuma akwai dalilin da yasa ya fadi haka.

"Me yasa kace baka gamsu ba?".

" A nan unguwa ko nan garin da muke tabbas akwai yaren oromo" Ya fadi cikin harshen
turanci. Idanu Omari ya fidda sanda motar ke gangarawa don tsaiwa a gurin da haisam
din yace duka satinnan a nan zasu dinga tsaiwa su jirashi,idan akwai yuwuwar sauya
guri cikin satin zai fadi musu.

"Ka bari na dawo......ka jira abeer.......ka gaya masa yau su sauya unguwa,su matso
maqotan unguwannin da suke kusa da nan,a yau dinnan basai gobe ba......idan na dawo
zamu qarasa magana" Ya qarasa fada yana bude murfin motar gami da sanyo qafafunsa
waje bayan ya tabbatar ba gilmawar kowa.

Da kallo Omari da yayi zaune cikin motar yake binsa dashi. Qaramin
murmushi ya subuce masa a hankali.
(08187255862 lu'u lu'u)

Komai nasa yana nuna sarautar dake zagayawa a jininsa,tsananin nutsuwarsa
da kamun kansa,takunsa kadai yasha banban dana maza da yawa,gashi kuma cikin gidan
sarautar wasu. Muddin akwai mutane irinsa cikin gidan,muddin akwai mutane masu
kaifin hange da dogon nazari irinsa,to babu abinda zai hana su kasa gasgata
zukatansu akan cewa shi din malami ne kawai......malamin da zai koyar da yara kawai
a biyashi.

A nutse yake karantar kowanne sauyawar motsi da yanayi na gidan. Yana
wuce kowacce qofa....kowanne shinge yana fahimtar kamanceceniyar yanayin jiya dana
yau.

"Shalelen sultane.......akhnan yau zata sake baqon da zai zama final choice dinta
dana mahaifinta". Maher ya furta qasa qasa wanda yake biye da haisam a nutse. A
qofar shiga gidan suka hade da Maher din.

Sarai yaji abinda Maher din yake fada amma kuma baiko waiwayo ba bare
ya alamta ya jishin.

Abinda ya faru jiya sai yaji ya dawo masa fes cikin kanshi. Baya ko
shakka yarinyar jiya ce,baya kokwanto ita din ce wani mara sanin ciwo da darajar
kan zai sake taka qafarshi muhallinta. Tsaki yakeso yaja,amma yana ganin ba wani
dalili na yin hakan,matsalar wasu ce.....matsalar cikin gidan.....matsalar mutanen
dake zuwa gurinta.

A iya saninshi,babban abu guda daya dake janye hankalin nutsatsen namiji
zuwa ga mace shine nutsuwa da kuma tarbiyyarta. Bai ganta a ido ba ballantana yasan
nutsuwarta,amma kuma duk inda nutsuwa take tana damfare da tarbiyya.......tarbiyya
da bayajin akwai sauran b'urbushinta a gurin.

Har qasan ransa yakejin idan ya fadi hakan baiyi laifi ba,don ba
tarbiyya a muhallin da d'iya mace zata iya daga hannunta ta mari d'a
namiji.....baligi. Ya jima baiga wani abu da bai shafeshi ba wanda yazo yayi masa
tsaye a rai irin wannan ba. Besan dalilin da yasa wannan din ya zame masa karan
tsaye ba,ya tsaye masa a rai,ya kasa cireshi.

"Ya isa" Ya tsawatarwa da zuciyarsa cikin don zare abinda bai shafeshi ba daga
ransa. Ya dinga takawa a nutse cikin kebantaccen masallacin da zummar bada faralin
sallar la'asar kamar kullum,kafin yakai ga qarasawa cikin makarantar.

Ya lura da yadda shiga ainihin cikin masallacin yau ya zama wani
kebantaccen abu ga wasu kebantattun mutane,amma hakan bai hanashi takawa a nutse ba
yana wucewa ciki abinsa,ba tare da jiran izini ko dama daga bakin kowa ba.

Su kansu basusan dalilin da ya sanya suketa dage masa kowanne shinge
yana shigewa ba. A cikin jikinsu ba wani me zarrar dakatar dashi ko masa bayanin
yau dinma sultane zaiyi sallah ne cikin masallacin tare da surukinsa.

Akwai ragowar mintuna da suka rage,wannna ya sanya ya zauna cikin
sahu a nutse,ya sanya hannunsa yana fidda wani dan qaramin littafin daya soma
dubawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login