Showing 255001 words to 258000 words out of 258256 words

Chapter 86 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

mai girma sosai ba kamar yadda suka bar gida
ba.
Da murna muka tare su sai fadin lalai Safiya ba lafiya jiki duk ya zube haka a
lokaci daya murmushi nayi ina fadin ai naji sauki mama yanzun gashi ina iya mikewa
kai tsaye ban taba komai ba.
Waya na dauka bayan mun gama gabatar masu da abinsha na kira uncle da bai dade da
fita ba a lokacin ganin kirana yasa gaban shi faduwa sosai ya dauka cikin murya na
yanayin mai ciwo nace su ummi na sun zo uncle har da baba.
Nan Abuja suka zo ko ina nace nan suka zo uncle yanzu suka iso garin da sauri
yace gani nan tafe na kashe wayan na dago kai na kalli mummyn su Amina nace.
Mommy yaya hanya yaya wajen su Amina da yaranta tace suna lafiya naji tana fadin
ai zats zo idan an kwana biyu tace yaya jikin naki yanzu ?
Naji sauki sosai mommy yanzu tace amma dai kan kinji jiki wallahi duk kin zube
haka kamar kin dade kina jinya.
Mama tace yanzun kin ji sauki ke nan a haka gaskiya hankalin yan uwan ki ya kasa
kwance sun koma suna fada muna ba dadi wallahi.
Sai da uncle ya iso ya matsa ma baba su shigo da dan uwan mommy daya jawo mota
da yaya sani matan suka mike suka bi mommy zuwa ciki.
Har kasa muka zube muna gaida baba sai yaya jikin yake mun tare da jajantawa sun
dade suna magana da uncle bai yarda yasha ko ruwa a gidan ba munyi munyi dashi yaki
shan komai .
Gab da magariba yaya Saadu ya iso suka fice tare baba na fadin gidan dan shi zai
tafi sai gobe idan sun shigo.
Mukai mai sallama ya tafi Allah ya taimake ni nura bata tafi ba a lokacin ta
dora girki da sauri saboda bakin da tagani a gidan sun zo.
Gaskiya ina jin dadin zama da ita don tasan ya kamata sosai koda nace mummy taje
asan abinda za a ayi masu sai ta samu har ta kusa gamawa a lokacin .
Ranan ban san irin farin cikin da nake ciki ba yau ummi ce da kanta a gidan aure
na wani abu sai ciwo wallahi da ban san ranan zuwa mommy gidana ba.
Muna dakina dasu tunda akayi sallah suka shigo dakin lokacin ina ciki na dan
kwanta anan suka samay ni mommy ce tayo masu jagora zuwa dakin.
A nan aka kawo masu abinci mama sai bin su maimu sukeyi da kallo wai yaran sun
girma sosai yanzu..
Ranan dai kwanan farin ciki mukayi ga iyayye na a gidan uncle ya rasa ina zai
saka su ya kwaso wanan ya sayo wanan yace a ba baki su ci.
Da safe suka tashi da shirin haraman komawa don wai kwana daya zasuyi muna anan
uncle ya dago da maki da na samay shi a daki ina fada mai shirin tafiya sukeyi.
Take ya kira yaya Saadu yace mai yayi magana da baba ba zancen tafiya yau gare
su sai gobe ko jibi idan an duba masu motar su.
Dole badon baba ya so ba ya hakkuri suka kara kwana yaya Saadu yazo ya dauke su
suka tafi gidan shi ya kaisu kuma gidan Aisha.
Uncle ya shigo ya samay ni da rana yana fada min cewa ummi fa ba zata koma ba
dasu don zata kwana muna biyu ina son muyi tafiyan nan da ita.
Yaya Saadu nace yayi wa magana don nasan ko baba ya yarda ita tana iya kin yarda
tace bata zama gidan suruki komawa zatayi gida.
Hakan ko akayi shima baba bai so yarda ba da farko sai da yaya saadu yayi mai
magana akan yara yake son a tafi da ita ya yarda.
Ita ko da aikai mata magana kafewa tayi bazata zauna ba su mommy suka ke be da
ita a idon mama suka ce kada tayi haka.
Ko wace uwa tana fatan haka a wanan zamani Allah yayi mata baiwa don may zata
guje ma haka dole bataso ba ta yarda ta zauna tana kallon washe gari suka kama
hanya zuwa gida.
Kwana biyar muka kara wani yammaci sai gashi ya shigo har dakina yace an gama
komai a shirin tafiyan mu don haka ranan monday zamu tashi har da yara zamu tafi
don zamu kwana biyu a can.
Ban dauka har mommy su samira zamu tafi ba don ganin dawainiyar yayi yawa sai
gashi da yaba pasphot na ga har da ita a tafiyan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/25/20, 5:46 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , ,


8️⃣9️⃣8️⃣
🧕9️⃣8️⃣9️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


Mun sauka lafiya gidane da mai kyau irin ginan kasashen waje akwai da kuna sama da
kasa da katon falo a cikin gidan.
Komai akwai na rayuwa a gidan kwana daya mukayi a kaini asibiti kusan bayanin su
daya da likitan da ya dubani a Nigeria sai dai su, sun bada maganin da zai yi
saurin shawo min matsala ta.
Sannu a hankali jikina ya fara dawowa normal har na fara dan kumatu a fuskana
komai mai gina jiki da yananyin garin suka taimakamin wurin saurin cike wa da samun
lafiya.
Ga mama da mommy dake kula da yaran da ni kaina a can ma bai bar kanne na hakana
ba sai da ya somo masu makaranta suna zuwa.
Bai faye zama a guri daya ba ko yaushe yana wurin neman halak din shi zama wuri
daya ya ishi ummi sai dai babu yadda zatayi ne kawai yasa tayi shiru.
Daga ita har mommy sun canza jikin su yayi kyau sosai dan samun hutu da sukayi a
can ga kula da muke samu daga wurin uncle .
Baifi yayi kwana hudu ba ko biyar ya kama idan yazo har Nigeria yake zuwa ya
dawo ya samay mu a nan dadi da daula mun samay shi a wurin uncle sosai watan mu
takwas cur muka dunkulo maka dawo gida cike da abin arziki a tare damu.
Tun baba na fada a dawo mai da matar shi har yasa ido ya daina tambaya yaushe
zamu dawo ne wai.
Niko banki muyi ta zama dasu haka ba har abada don ummi na kula min da yara sosai
tana kuma basu tarbiyan daya dace a basu.
Wani irin kiba nayi ga haske dana kara da wayewa a lokaci daya mun zo mun samu
komai na gidan an sauya muna anyi gyare gyare an canza ma gidan fasali sosai.
Saukan dare mukayi duk da haka su yaya Saadu sun zo taron mu da wasu ma, aikatan
su gaba daya sai naga gidan ya sauya min gaba daya kamar ba gidan da muka bari ba a
baya.
Mun shiga gidan kowa na mamakin sauyawan gida don uncle bai taba fada min cewa
ana gyaran gidan sai da muka dawo kawai na gani yayi surprise din mu ga hakan.
Gaba daya komai ya sake dole muka tsaya a falo kafin yazo ya fada muna inda part
din kowa yake mu shiga bayan ya gama sallaman mutane yace muyi hakkuri ya barmu a
falo dakin su mommy ya fara nuna masu sai na su maimu kowa ya tashi da zumudi zuwa
dakin sai lokacin ya nuna min part dina dake wani bangare nashi ma a dayan bangaren
yake.
Duniya tayi min dadi yanzu sosai har nakan manta cewa ina da cuta a jikina a
baya saboda yadda nake jin jikina a lafiye.
Ummi sati daya ta kara a tare damu muka kaita gida kwana biyu kawai nayi wanan
karon na juyo ban samu tsayawa ba don zamu bauchi muga baaba da yan uwa.
Yarana sun girma don ko karamin da mommy tasa mashi suna azahabi yana tafiya
yanzu da kafan shi ko ina yayi saurin girma sosai don ba jikin Abba da mahaifin shi
ya debo ba shima Abba din ya girma sosai dan har ya fara karatu a can .
Ranan da muka dawo gida da yamma yaya Saadu yazo gidan yake fada min an bugo mai
waya jikin gwago ya tsanan ta sosai don haka gobe zai tafi.
Na jajanta mashi tare da fatan Allah ya bata lafiya yadan dade wurin uncle suna
fira ya tafi don dare yayi a lokacin .
Yaran ke rikice a gaban mu akan remote din tv nace wa Abba ya bar ma Azahabi
kallo na uncle yayi cikin tsawa yace ma yaron ya kawo mashi remote din ya kora su
zuwa dakin mommy wai suje ai masu shirin barci su kwanta dare yayi.
Bayan sun wuce ne don suna matukar tsoron shi ta juyo gare ni dama nasan ba zai
barni ba sai na samu rabona a gurin kan hukuncin da na yanke din ga yaran.
Yace yanzu kinga kinyi wa Abba adalci ke nan a hakan shine babba fa ama kika ce
karami ya rike remote din yanzu ne kike son sulaiman din fiye da Abba.
Uncle ba hakana bane nace gani nayi shine ya fara dauka shiyasa nace ya bar mai
kai ya girgiza min yace ina lura dake kin fison shi akan Abba din don kirikiri
yanzu a gabana kuka zalunce shi.
Nace cikin dago kaina ina kallon shi Zalunci uncle akan may zamu zalunce shi
kuma wai ke baki san hakan da kike yi ba zalunci ne maimakon ki karbe duk a hannun
su sai kice yabarwa kanin shi.
Shiru nayi kada zancen yayi nisa a tsakanin mu ya mike yana fadin irin haka sai
ya kawo raini a tsakanin su balle yana ganin ya cin mashi da girma yanzu uncle har
wanan yasan wanj abu raini a yanzu.
Yace a haka ake tasowa dashi ki taimake ni ki hada kan yayan nan don Allah kada
ko bayan mu su samu matsala idan kan su yana hade babu wanda zai iya shiga tsakanin
ko gaba.
Nasan inda maganan shi ya nufa yadda ya taso da yan uwan shi ne baison hakan ya
faru da diyan shi daki ya wuce ni kuma na mike na shiga dakin nasu don in ga
kwanciyan su.
Na samu mommy har ta shirya su ana rikici wurin kwanciya nace su kwanta su rike
junan su sai suyi barcin a tare ba tare da sun rungumi mommy ba da suke ma fada.
Kwana biyu muka shirya muka tafi bauchi ganin hajiya taji dadin wannan ziyaran
don mun dade bamu zo gida ba irin haka.
Banzo da kanne na badon makaranta da suke zuwa nan na barsu da mommy Abuja da
yaran kawai nazo garin.
Mun dan zaga wurin dagi da sauran yan uwa mun gai dasu muna bauchi kwana hudu da
zuwa bauchi sai ga sakon daddy sun yi nutsu a cikin ruwa inda suke aiki.
A ranan uncle da wasu yan uwa suka wuce lagas sun barmu hankali a tashe a gida
sai zuwa safe muka samu labarin rashin dadddy din da akayi.
Hankali ya tashi sosai dole uncle yace mu biyo jirgi mu dawo Abuja in gari ya
waye mu nufi lagos din don har wasu sun tafi ko.
Yadda yace haka mukayi hankali a tashe muka iso gida nike fadawa mommy abinda ke
faruwa hankalinta ya tashi matuka da jin labari mara dadi daya dawo damu ba shiri.
Mun isa Abuja washe gari har lokacin ba a kawo gawan shi gida ba suna abinsu na
yan kaki da gawan .
Mun shigo anty suna falo zaune gani na yasa ta sake wani kuka mai tsuma rai nima
rungumay ta nayi ina kukan rashin da mukayi na daddy mutumin arziki.
Sai yamma suka bada gawan su nan aka shirya masu bi harda mu don zamu dafa ma
anty baya.
Mun kwasa mun koma bauchi da gawan a jirgi guda da yan uwa isar mu da gawan ya
tayar da hankalin yan uwa da abokan arziki.
Zuwa safe aka kaishi gidan shi na gaskiya har rana ban samu ganin uncle ba mu
zaune a dakin anty cikin tashin hankali don ni na zamay mata kamar yar uwarta na
jini a wurin duk da ga yan uwan nata a kusa da ita.
Shigowan yan uwan daddy maza a cikin su har da uncle sukayi gaisiwa tare da addua
ga mamacin nan sukai dan bayani akan gobe zasu koma lagos dan ana son ganin su acan
akan komai na daddy din.
Suna fita nabi bayan shi dole ya dan tsaya min na iso kallo daya nayi mai naga a
lokaci daya duk ya sauya min a idona uncle kako ci wani abu na iya fadi.
Kai ya girgiza min yace yanzun dai nake son in karya magani fa nace dashi da
sauri yace ban sha ba safiya ji nayi ina son in kebe dashi don ya samu ya karya
yasha maganin shi kada ai biyu babu.
Su hajiya baaba ma suna gidan don haka na karbi makulli a hannun ta na fito muka
wuce gida a sai da na zuba mai abinci na dauko mai maganin mu na bashi.
Yana zaune ya dafe kan shi a hankali na iso gare shi na zauna a gefen shi kuka
yake yi nace uncle kayi hakkuri kowa yayi rashi amma ansan kai da anty akafi yi ma
wanan rashin .
Yace safiya daddy mutumin kirki ne ya tafi ya barni a lokacin da nafi bukatan
shi a tare dani rugumay shi nayi don maganan kara mashi bakin ciki yakeyi.
Sai da naga ya natsu sosai naji yace kinyi waya da mommy yaran na lafiya nace
lafiya suke sai dai Abba ne tace yau ya tashi da mura ta bashi maganin shi.
Gobe zamu tafi lagos kuma da madam zamu tafi ina ga gida zaki koma don yaran sai
ke tsaya Abuja ya kamata ki huta yanzu jigilan yayi maki yawa hakana.
Nace uncle ai kai keda jigila ga rashi ga ba hutu a tare da kai yace yaya za a yi
dole nine zan bi komai nashi yanzu har komai ya daidaita.
Hari aka kawo masu na bazata shine ya zama ajalinsu haka su goma sha bakwai suka
rasu a lokacin .
Allah dai ya jikan daddy nace yace amin yanzu ban san plain din madam ba nasan
dai a can lagos din zata zauna saboda aikin ta ko kuma ta dawo arewa da aikin ina
ganin zaifi mata sauki kusa da gida.
Haka dai sukai ta jigilan akan alamuran daddy har komai ya kammala ya dawo gida
bayan wasu watanni aka nenawa anty trasfer ta dawo Abuja da aiki tare da yaranta.
Jikin gwago ya kiya baba yace a dawo da ita gida ayi na gargajiya a gani gashi
basu jittuwa da Samira duk kokarin da take mata gwago bata gani sai zagi kawai ke
shiga tsakanin su.
Haka yasa hankalin yaya Saadu yafi kwantawa da akaita gida don yawan fitinan da
ake samu da samira duk da kokarin samira din.
An kaita gida ba afi wata biyu ba Allah ya amshi ranta muka je gida gaisuwa nan
na samu zance aure yaya Sani ya tashi sai gina yake tayi inda zai saka matan shi.
Don yace bai son zama ko kusa da gida don gudun samun matsala da inna duk da
inna yanzun tayi laushi sosai da fitina har in nazo takan dauki su Abba tayi masu
wanka da sauran su.
Uncle yazo da ma, aikatasu sai dai basu kwana ba suka juya ranan mu sai da mukai
kwana biyu muka dawo gwago ba karamin dukiya ta bari ba wa yayan ta.
Yaya Saadu yace yabarwa kannen shi mata idan sun samu mazan aure ai masu aure
dashi sadiya ta dawo da zama wurin yaya Saadu.
Tare da mama da inna muka sauke farali inna ta saka hakora uku a bakin ta inda
mama ta saka biyu sunyi dani in saka nace uncle yace baya so sai suka kyale ni.
A wurin jefa inna ta tashi mutuwa da kyat muka cetota wanan abin ya kara tsorata
inna duk inda na jefa kafana tana biye dani.
Mu dawo lafiya saida suka kwana biyu a wurin mu suka wuce gida don ta Abuja suka
tafi sai da muka dawo muka je gida bukin yaya Sani da yar wurin mai unguwar mu.
Abubuwa da yawa suna faruwa inda girma kuma ke kara shiga uncle da nauyi na yan
uwa da abokan arziki idan aka kwana biyu kuma ya debe mo zuwa waje mu huta.
Bayan shekara hudu na sake haihuwa yar budurwa taci sunan hajiya baaba muna
kiranta da baaba din sai na dakatar da haihuwan jikin kan dan motsa muna wani
lokaci wani lokaci kuma sai ka gan mu kamar ba mu ba.
Yanzu nasan cuta baya kashi sai kwana ya kare do ga daddy mai lafiya ya tafi ya
barmu gwago na ta tafi ta barmu muna rayuwan mu a cikin salama.
Yarana suna nan duk lafiyayun su basu da wata matsala a tare da su sun girma sun
zama kyawawa dasu gwanin ban sha awa.
Ina kula da yan uwana da yan uwan miji nice na zama jigo a gidan mu inda ake
girmama ni kamar wata babba a cikin zurian mu komai za ayi sai da shawarana.
Yanzu inna taba kai bori ya hau sai bi da lalami a tsakanin har in wani yaron ta
yayi wani abin tana kawo min kara in yi mashi fada.
Rayuwan mu sosai yaci gaba don uncle ya bunkasa sosai ni da anty mun dinke sosai
dawowan ta Abuja mun zama kamar uwa daya da ita.
Uncle ya dawo daga dubai bamu san da zuwan shi ba sai ganin shi mukayi ya sagalo
jaket din shi a kafada Azahabi ya fara ganin shi .
Lokacin ina zaune dasu a dining suna cin abincin safe daddy daya ce yasamu duban
kofa da gudu yaran suka nufe shi ya rugumay su duka ukun a jikin shi sai da ya gama
sun batan su ya dago yana kallo na ina tsaye na taso taron shi na harde

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login