Showing 132001 words to 135000 words out of 258256 words

Chapter 45 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

kaunar miji na tazo.
Nan naga mata na ta firfitowa daga sashen su suna zuwa yi min sannu da zuwa niko
sai faman washe baki nakeyi ina karba masu.
An shiga dani dakin su dan part ne mai kumshe da ciki da falo sai wani dan daki
karami da kicin a cikin part din dakin su aka kai min kayana.
Shiko yaya saadu ya rasa ina yaka saka dani don farin cikin shi baya boyuwa ranan
bayan na zauna falo .
Nan ta fara gabatar min da abinci da abinsha ban wani ciba sosai don banda yunwa
a tare dani aka kawo min baby a daidai lokacin da yaya ya shigo yana cewa kin ga
Safiya karama ko ?
Na dago kai da sauri nace yaya sunan da aka samata kenan yace Sunan ki taci
Safiya ko bai maki dadi ba na lumshe idona sai ga hawaye yazo min.
Yace kuka kuma kike yi har yanzu baki daina halin nan naki da na sanki dashi ba
na saurin kuka nace yaya bansan irin godiyan da zan maka bane.
Bayan taimako gashi kuma har sunana kasa wa yarka ta fari a duniya matar shine ta
fito ta samay mu zaune take cewa yaya naga kamar kina kuka.
Gaki ga yayan ki ga takwaran ki kin dauka kuma sai yaya yace wai duk farin cikin
yi mata takwara takewa kuka.
Tace ai dole ina haihuwa na dauka sunan mummy zai sa kona mama na sai naji yace
wai sunan yarinya safiya sai da nayi makin wanan irin shakuwa naku wallahi.
Bari kedai Samira ni duniya yaya ya gama min komai Allah dai yabar zumunci ya
raya min takwara na ta famnin addinin musulunci yasa mata albarka sukace amin.
Nan muka zauna muna hira yake ce min sai yaje gida ya samu baba ya samu lafiya
sosai sai dai su ummi ba kowa a gidan anata gyare gyaren gida.
Na nisa nace bari yaya nan na fara bashi labarin yadda abin ya faru da irin
taimakon da yake min shi da uwar dakina.
Sai da ya gama saurare na yace Alhamdullahi Allah maji rokon bawan sa Allah ya
amsa min addua na kullun ina rokon Allah akan kada rayuwan ki ya kare hakana baki
more ma rayuwa ba safiya.
Don ina ganin yadda rayuwan masu wanan matsalar yake karewa a lalace saboda
rashin gata da samun kulawa da basuyi.
Nacs haka abin Allah yake yaya sai dai muyi fatan dacewa da rahaman ubangijin mu
yanzu.
Amma yaya inda son samu ne asamu wanda zaiyi bincike kwakwara akan Sulaiman din
don kada ai abu cikin duhu a dawo ana da an sani kuma irin na farko.
Ya nisa yace insha Allahu kuwa zanyi kuma da yardan Allah sai Alheri don yadda
yake kulakin nan akwai alaman nasara ga abin.
Don da akwai matsala da tun yanzu zaki dan fahinci wani abu daga gare shi sai dai
zaki iya tara matsololin da ake fadi nasa ki auna ki gani .
Amma dai duk da haka zanyi kokari in bincike a kan shi don wani lokaci yin
binciken yana da kyau.
Na fara hamma yace naje na kwanta mu hadu da safe sai lokacin nace dashi yanzu
wani sana a yakeyi ne ?
Jeki ki huta da safe mayi magana naga kin fara hamma ni yanzu fita zanyi ya kwala
ma matarshi kira tazo ta kaini daki.
Naga ta nufi dakin su dani nace ai da kun barni in kwanta a falo ma nan ya yi
min yace haba dai ai kinzo taya ta aiki ne don haka ni na bar ki da ita ke nan.
Yai muna sallama cewa zai fita ya dawo na mike zuwa dakin inda na samu gadon
dakin yasha gyara dakin sai kamshi yakeyi .
Na yi shirin kwanciya dukkan mu a saman gado daya muka kwanta muka sa baby a
tsakiyan mu asuba ta gari yan uwa.



Idan zaki fitar min da novel na barki da raddin ubangijin mu je ki tayi tunda baki
san hakkin amana ba zaki fada ranan da baki baya magana sai hali.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,

4️⃣7️⃣4️⃣
4️⃣
🧕🏿 7️⃣7️⃣4️⃣

Ni safiya ace mutum bai tsoron Allah shi dole ne karatun nan ance ba a yafe ba an
hada ki/ka da Allah an hada ku da darajan annabi amma kuna wasa dashi ku sani fa
hada mutum da Allah ba karamar kalma bace akwai ranan haduwa dashi ranan nadama
ranan da baka da abin bayar sai ladan da ka tara ma kan ka.
Mutuna ko yanzu ko anjima koyau ko gobe ko ko ko ko zamu koma ga Allah koda ciwo
ko babu ciwo may zamu fada wa Allah.
Dabara ya rage ga mai shiga rami shi kadai ni dai tun da asuba na mike batare da
samira ta sani ba nayiwa gidan ta kwal ga ruwan zafi da na sa masu na wanka ya ya
tafasa na sauke na fara hada mata abin karyawa.
Sai da naje daukan baby dake barci a gefen tane ta bude idanun ta tana fadin
subbahanallahi gari ya waye ne ?
Murmushi nayi nace madam ki tashi ruwan zafin ki na jiran ki a bayi ban saurara
mata ba na fara cirewa baby kayan jikin ta na nufi bayin da ita inda maga kayan
wankan ta aje a gefe.
Wanka nayi mata na gasa mata jiki dama na iya tun ina gida idan ummina ta haihu
nakan taimaka mata da wankan yara.
Na fito na fara shirya baby sai lokacin Samira ta samu ta mike zuwa wanka tana
cewa yau wata rana zamuyi wanka da safe haka yadda ya dace.
Nikan naji dadin ziwan nan naki Safiya wannan kokari haka ta mike take bin dakin
da kallo tace wai ko kin yi barci safiya wanan irin aikin haka ?
Kafin ta fito na saka wa yarinyar kaya cikin kayan da nazo mata dasu uwar ta fito
wanka tana kallon mu da sha a wa tare da fadin aa lalai takwara tazo wanan kaya ai
da ki bari sai ranan suna ki saka mata.
Murmushi nayi kawai na goya yarinyar na na fita daga dakin sai gani na dawo da
cup cike da shayi mai kauri dana hado mata.
Na aje a gefen ta dago kai tayi ta kalle ni nace madam sai a sakai a shanye
kafin ya huce nace za a daukan maki kaya ne ki saka ?
Tace gaskiya Safiya zaki shagwaba ni da yawa ki wuce ki barni da kewan ki nace
kada ki damu madam dama shi nazo yi yanzu aiki na ne nakeyi.
Batai sanya ba ta kafa kai ta shanye shayin duka sai ga zufa ya karyo mata nan ta
mike ta dauko kayanta tana sawa.
Na fito falo naji ana bude karamin dakin nan dake rufe ashe yaya ne anan ya
shige ya kwana na juyo don ganin ko waye mukayi tozali dashi.
Nace yaya barka da kwana yace an tashi lafiya Safiya nace Alhamdu lillahi yaya
yace yau takwaranki ne ta samu goyo haka ?
Gaskiya banji kukanta ba yau da safe don kullun itace ke tayar damu da safe da
kukan ta nace yau tasan gwagon ta na gari batayi kuka ba tun da nai mata wanka
takoma barci.
Yace kai har wanka ta samu yau da wuri haka nace gwago tazo fa yaya zanbar diyana
takai wani lokaci bata gasa jikin ta ba.
Nan ya fara bin gidan da kallo yaga gyaran da ya sha yace keko kinyi barci kuwa
nace may ka gani yaya yace wanan irin aiki haka tun da farar safiya haka ?
Nace shiya kawo ni may zan kwata wa inyi ga aikin madam a gaba na yanzu lokaci
ne da take sin hutu a jikin ta don haka ta kwanta ta huta jikin ta ya watsake.
Na shige kitchen na barshi yana mamaki ya raya a ranshi da haka uwar shi ta rike
zumuncin da mahaifina yaso su kulla da abin yazo da sauki.
Ya shiga daki nan ya samu samira tana ninke kayan da ta cire ta juyo tana kallon
shi tace kaga aikin kanwaka ko sai yau na karkare yarda da abinda kake fadi nata.
Na shiga dakin na samay su suna magana nace yauwa bari ma in baku sakon ku tunda
gaka a dakin nan na jawo akwatin kayan da nazo dashi zuwa gaban shi na juya wirin
hand bag dina na ciro kudin da na ware mashi tun a gida na bashi.
Sai bina yake da kallo yana neman karin bayani nace yaya kana kallona mana yace
ban fahinta bane safiya nace to kaya da na takwara nane da uwar ta gashinan akwati
guda sai kudi kai kuma ka kara kai hidiman buki da su.
Tsaye yake dama zai shiga bayi sai naga ya kai zaune a wurin yayi shiru can ya
dago kai yace Safiya duka wanan dawainiyar ani kika yi shi bayan zuwan da kikayi
kuma ga wanan wahalar.
Ba wahala bane idan duk abinda nake dashi zanyi maka bazan taba yin da na sani
ba yaya kai kaja in maka hakan da nayi.
Samira kan kallo na take da mamaki da kyat ta samu bakin magana tace wai safiya
kin wanke ni ga bakin jamma a kin gama muna komai a duniyan nan.
Kin san yayan ki aikin company yake yi gashi wata uku ba a biya su jiya jiyan nan
muka gama magana dashi na yaya zaiyi ko zamu daga sunan nan har zuwa gaba.
Nayi saurin cewa a uzubillahi a daga suna kuma yaya Allah ya rufa muna asiri ashe
gwama da na daure nazo don da anty ta so hanani zuwa na nace nace sai nazo.
Tace Allah ne ya kawo ki yar uwa ta fara jawo kayan tana bude zip din jakkan don
na karshen ne babban duka duka nazo kasu dashi.
Shiko yayi mutuwar zaune ya kasa fadin komai har lokacin tana budewa ta sake
karamin ihu da fadin wai Safiya ?
Shago ke nan ta fara budan kayan tana azawa a saman gado karshe rufe akwatin tayi
tai tagumi kawai sai can ta nisa tace dear ka ga ikon Allah.
Sai lokacin ya nisa a sanyaye yace na gani samira ban san may zance bane kawai
imani da tsoron Allah sun cika min zuciya samira.
Kawar da zancen nayi da fadin ni kaga malam kai wanka ka shirya kazo ka karya in
ka gama ka fita ka sayo muna abinci azo a aje a gidan na ciro kudi ina mika mai.
Ido ya zaro yace na may ye kuma wannan kudin nace abinci zaka sayo mana dashi
wanan ba na hidimar suna na baka kayi ba sai naji yace haba kai safiya haba dai.
Tare shi nayi da fadin ka gode ma Allah adduan ku gareni ya karbu ga ubangiji shi
ya wadatani da wanan niimar idan ban gode nima na na rama maku ba may zanyi da
kudi.
Kudine ina samu alhamdullahi don sulaiman yana wadatar dani dasu kuma yana fada
min in yiwa yan uwana alheri daga niimar da Allah ya wadatar dani.
Yace Allahu akbar haka abun Allah yake safiya shiya sa idan kaga ubangiji ya yi
ikon shi akan mutum kai dai kabishi da addua don baka san hikimar ubangiji ba a
kansa.
Abinda nai maki a baya har ga Allah nayi maki ne a matsayin ki na yar uwata ta
jini da kuma matar yayana da hadi na musulunci banyi don zaton wata rana zaki zama
wani abu har ki rama min ba.
Nace na sani yaya nima kuma ba zan taba iya rama maka abunda kai min ba har abada
duk wanda yai maka abu a lokacin da kake bukatan taimako a kan shi ai baka da kamar
mai shi a duniya ba don kai ba da yanzu na wullakanta.
Yai saurin cewa Allah bai yoki wullakantata ba dama safiya ki godewa niimar da
Allah yai maki tun farko tunda kin samu kiyi karatun boko.
Nan dai mukai ta hira dasu har ya gaji ya mike zuwa wanka yafito ya karya ya fice
daga gidan baby Safiya ta tashi na kaita wurin uwarta na dawo na ci gaba da aiki
na.
Tuwo na tuka mata na Semon da na gani a kitchen din da miyar yauki ina gamawa
yaya ya dawo gidan da kaya niki niki tare da abokin shi.
Wai ya kirashi yazo yaga abinda na kawo masu abinci na gabatar masu bayan sun
gama gani yaya yace safiya sai kina sa ina ganin gidan yau kamar ba nawa bane.
Muna tsaka ga magana Samira ta fito daki da wayana a hannu tana mika min ana
kirana a lokacin.
Na karba naga Sulaiman ne da sallama na koma gefe daya ina amsa wayan yace gida
yai maki dadi kin manta da kowa ko ?
Murmushi nayi nace yallabai an tashi lafiya yaya aiki yace lafiya kalau watau ke
dai baki kiran mutum ko nace tsoro nakeji kada in kira ka kana cikin uzuri.
Yace don gani agogo sarkin aiki sai ba zan tsaya na saurari kiran mata na ba ko ?
Nace tuba nakeyi katse shi nayi da fadin ga yaya na ku gaisa yace af yana kusane
nace yana nan yanzu ya shigo namika ma yaya Saadu wayan.
Sun gaisa yake ma yaya barka da samun karu sai yaya yace Allah ya mayar gare ku
kuma da kunyi aure a sama mana tagwaye.
Murmushi yayi kawai yaya yake mashi godiya a bisa ga kokarin da yayi masu yace na
komai ai anzama daya yanzu.
Yake tambayan yaya din wani aiki yake yi sai yace mashi a wani company yake aiki
yanzu kuma company tai sanyi sai dai dan buga buga da suke yi sunyi hira sosai
kafin yaya ya bani wayan mu ci gaba da magana dashi har yake tambayana da yaushe ne
zan dawo ?
Nace jiya fa nazo har ake batun dawowa na yanzu sai nayi a kalla wata daya ko
biyu kafin in dawo sai takwara na tayi kwari zan dawo.
Yace kina hauka ne nifa in badon madam ta fada min yadda kuke dashi ba kuma yanzu
a wayan da mukayi na fahinci mutumin kwarai ne don gashi har yana min fatan samun
tagwaye da auren mu.
Da hankalina bai kwata da zuwan ki garin nan ba sam nace sace ni za a yi komay ?
Yace yana da wuya ne nace ni ko kofan daki ban taka ba tun zuwa ina ciki kumshe
ina za a gani har a dauke ni ?
Yace ki dai bi sannu don Allah ban son yawo please zan ma fada ma yaya don ya
saka maki ido sai nace ai ka hutar da kan ka ni din kifin rijiya ce fita a guna sai
ya kama dole nake fita.
Yace daya fi maki ashe ba zamu samu matsala ba ban son mace mai yawo a rayuwa na
ko gadan.

Yace kin san may ?
Na ce aa yallabai yace yau yayan ki ya fama min wani ciwo a zuciyata sai nayi sauri
cewa subbahanallahi.
Yace dakata mana kiji ai ba wani abu yace min ba illar cewar da yayi Allah ya
bamu tagwaye da munyi aure.
Sai nayi murmushi yace ban taba jin ina son haihuwa ba nima sai yau daya fada
min haka naji nima ina son in ga zuria na a duniya koda kuwa bazan rayu tare da su
ba.
Nace balle zamu rayu tare dasu insha Allahu ai Allah shi ya fimu sanin daidai ga
rayuwan mu ni dai mu bar wanan zancen ba yanzu ba tukun.
Yace saboda may ?
Ko ba kya son haihuwa ne ke nace wai kuwa kasan sunan yarinya Safiya ?
Kin kawar da zancen ke nan ko?
Safiya yaya yasa wa babyn namu nace wallahi ina zuwa yace ga takwara nan yayi
min ya ce Allah ya raya muna ita a tafarkin addinin musulunci nace amin.
Yanzu yaushe zaki dawo lagos ba wasa nake yi ba fa ina son in sani ne ?
Nace kaida baka ko kasan kake tambayana yaushe zan dawo bafa a gari daya muke
zaune ba balle kuma baka ma kasar baki daya.
Murmushi yayi yace ina son in san lokacin da zaki dawo idan yayi daidai da dawowa
na Nigeria don ta lagos zan sauka.
Nace gaskiya ban sani ba tukun sai dai idan anyi suna naga yadda yanayin ya ke
zan saka ranan dawowa na.
Munyi sallama dashi naci gaba da aikina na fito inda na samu su yaya sun gama cin
abinci sun cinye duka sai kwano.
Na kwashe zuwa kitchen tare da kokarin dora girkin yamma don inyi in gama da
wuri in huta ina aiki yan barka suna shigowa jefi jefi kamar yadda ake zaune a
bariki.
Na gama na gyara wurin na koma ciki nayi wanka sai lokacin na samu zama da samira
muka fara hira wanda hiran namu akan yanayin garin nasu take min da kuma bani
tarihin ta.
Da yadda suka hadu da yaya saadu yan uwanta suka so su hana auren su wai ba a san
asalin shi ba sai da kyat aka yarda ta aure shi don suna son junar su.
Nace ai yanzu aure babu inda bai kai mace gashi ban taba zuwa bauchi ba amma
aure yana shirin kaini can din.
Tace wanda zaki aura dan bauchi ne shi nace mata dan bauchi ne tace a can yake
zaune nace da ita a a .
Sai nayi dariya nace shi wanan ai baida takamaimai zurin zama dan kasuwa ne baya
zama sosai sai dai ina ganin abuja zai aje ni amma dai ban sani ba dai.
Waya na jawo na kira anty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login