Showing 189001 words to 192000 words out of 258256 words

Chapter 64 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

kwana da mummy a dakina don haka muke kawa wani lokaci mu dan
hira da ita sai mun gaji mu kwanta.
Washe gari su samira suka zo gidan nan muka wuni da ita da yar uwar ta anan nake
jin wai yar uwar nata ta samu miji aure a inda suke.
A cikin hiran mu ne nake fada ma Samira abinda ke faruwa tsakanina da anty
zancen in tura mata kudi tace.
Amma dai wanan matar ta fadi kasa wallahi ita duk kudin ta sai tayi zari haka
mummy tasa muna baki a maganan mu tace hakan da Safiya keyi yayi kyau su dai rabu
lafiya da ita ba shike nan ba.
Kudin may mutuncin da tayi mata yafi kudi ai tunda halin ta ke nan ba sai ai mata
yadda take so ba a rabu lafiya rashin yin zai haifar da wani rikici a tsakanin su
ne kuma.
Tunda yanzu mutane ba tsoron Allah ne da su ba kun sani ko har yanzu suna ga
bakan su na son mijin ta ya auri yar wanan dayar matan.
Nace mummy in dai ma auren zasu yi su barni da lafiya suje suyi tayi kowa ya
tsaya a matsayin shi mummy tayi saurin cewa dani.
Umm umm yar nan kada ki soma fadin haka kishiya idan ba dace ba babu wanda ke son
ayi mashi sai dai in ya kama dole shine ba mafita.
Ai da zaran ya kara aure yanzu duk wanan mutuncin da kikaga yana maki sai ya ragu
namiji ai ki barshi kawai.
Idanuwa na na lumshe ina tunanen maganan ta idan uncle yayi min kishi ni ai na
shiga uku ko a gidan mu ba balle gun bakin jama,a.
Samira ne ke fadin jifa kishirya Aishan ku sai da mijin ya bata saki kwanan don
ta ishe shi akan zancen gida da motar da aka sai wa Aisha din ji da muka je take
fada muna.
Nace ai kaji matsalar duk da ba mijin nasu ya saya masu ba amma bata bari an
zauna kalau ba kuma ?
Tace wai har nan gidan Aisha ta biyo shi da masifa anan ya dankara ma yar iska
saki sai gata kuma ta zube tana kuka a gidan.
Mummy tace shine ai matsalar matan yanzu dan abu ba abu ba su mayar dashi fitina
su hana kan su shaka da abokan zaman su.
Nace ai wanan zaman namu mummy sai mu, mace ta samu gidan aure amma kishi sai ya
rufe muna ido mukasa koyi da halin iyayyen mu na baya.
Kuma mafi yawan mata haka muke yanzu da bakin kishi bamu natsuwa muyi kishin
hankali sai na hauka wanda idan mutum yaji sai ya rena masu hankali.
Mun wuni cikin dadin rai dasu Samira a gidan sai yamma lis yaya yazo ya dauke
suka tafi daga gidan.
A gaskiya ina jin dadin zama da mummy don ba karamin debe min kewa take a gidan
ba bata bari taga na shiga damuwa ko kadan.
Mahajjata sun tashi lafiya har sun sauka kasa mai tsarki inda suka bugo min waya
na samu layin da zan dinga kiran su a can .
Yaya sani ne ke rike da wayan a hannun shi don haka idan zan kira ummina ko baba
sai nakirashi yake mika masu waya muyi maganan da zanyi dasu wanda duk wayan namu
gaisuwa ne.
Har yanzu uncle yana gurin tafiya bai dawo ba a wani dare ya bugo muna hira yake
fada min ba zai samu dawowa ba daga can zai wuce saudiya ya sauke fari a can.
Nace Uncle kayi min wayo ke nan ka tafi saudiya au na manta fa ki shirya gobe
kema zaki biyo jirgin safe ki samay ni anan.
Kai daddy kana son a koroni tun filin jirgin Nageria ke nan a yadda nake nan na
tun kare su ai sai suce ban da hankali yace.
Ki fada masu ke fa matar uncle ne ai zasu bari ki wuce kawai nace uncle abin ya
koma yar haka ne kuma tsakanin kai dai kawai ka yarda kayi min wayo yace to na
yarda madam ai min afuwan ko nace ayi ma Uncle.
Munyi hiran sosai dashi kwana biyu aka hau arfat nan mahajata na jirgin yawo suka
fara shirin dawowa gida acikin su harda uncle.
Sallah da kwana biyar na tashi da matsanacin ciwon mara cikin dare mummy ta rude
duk da tasan cewa haihuwa ne yaya saadu ta kira baizo gidan ba sai tare da likitan
uncle da wata nurse.
Don haka agida Allah ya saukeni lafiya da taimakon Allah da tasu na likitoci na
samu na haihu karfe biyar na asuba.
Nurse din ce ta taimaka min har wankan yaro da komai da itace tayi nan a gaban
mummy bayan yan aune aunen da sukayi min sukace kada aba yaron nono wai ina da
matsalan kaikayi a jikina wanda ni san suyi hakane don kawai batar da sawu.
Likitan ya kara dacewa mummy ba kowa za a bari yasan yaron bai shan nono ba don
yawan surutun mutane amma zan dan iya bashi lokaci lokaci kafin yayi wayo.
Don sun diba zan iya shayarwa na dan wani lokaci yaya yace tunda akwai abinda zai
sha kawai kada ma na bashi nonon ita mummy tace hakan ma yafi.
Tace ta fahinta yaya Saadu ma ya gara gargadin ta kada ta bari kowa yasan zancen
mummy tace ai ko samira baza taji ba don bama zata bari aga yaron ba.
Nan ya kwashe su ya mayar gida don lokacin har gari ya haska ko an fara fitowa
shaanin yau da kullun.
Mummy ne ta miko min yaron bayan sun wuce na kalli yadda ya kwaso uban shi da
kama wai jinin uban shi yafi kadfin nawa a cewar ta.
Murmushi nace mummy ke nan daga inda nake zaune ba tare da na karbe shi ba nake
kwararo mai addua.
Barcin gajiya ne ya dauke mu a gidan dagani har mummy din sai tara na safe su
yaya saadu suka shigo da su samira gidan.
Shigowan su ne yasa muka tashi basu jima ba sai ga Aisha ta iso kowa sai yaba
kyau yaron yake yi don ya gado kyau ta ko ina daga iyayyen shi.
Aisha sai cewa tayi dasu yaron yafi kama dan ya dauko fuskan yan gidan su ne ni
dai sai murmushi nake masu karshe ma barci nayi na barsu nan.
Ganin na sake komawa barci mummy tace su dawo falo su bar ni in huta yaya Saadune
ya shigo dauke da madaran da za a ba yaron da ruwan zamzam .
Nan dai yadan bata lokaci yana buga ma mutanen su matar oga ta haihu yau na tashi
mummy tace na danje na gasa kaina a bayi.
Naje na taba ruwa na dawo dai dai lokacin da Uncle ya sake buga waya akace dashi
na falka daga barcin.
Wayan yaya saadu ya miko min yace madam barkan mu da arziki ashe an sauka bayana
dariya nayi nace Allah ya sauke ni uncle Allah ya rufa min asiri baka garin na
haihu baki alaikum.
Yace kudai kunyi min wayau naso ace nine zanyi karban haihuwan ai naga kalar
rakin ki har video zan yi maki a lokacin.
Murmushi nayi nace wanan dai ya wuce ka yayi saurin cewa saura wani uncle rufa
min asiri nace dashi da sauri tare da kashe wayan



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/29/20, 11:42 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,

6️⃣7️⃣6️⃣
6️⃣
🧕🏿 7️⃣7️⃣6️⃣


Ranan duk da gajiya ban samu hutawa da amsan wayan daga yan uwa da abokan arziki ba
masu bugowa su na min barka da arziki.
Sai da dare samira suka bar gidan amma yar uwarta ta zauna a wurina zata taya
mummy aikin jego nima naji dadin zaman nata.
Nafito bayi don yin tsarki dare saboda zan kwata a lokacin ina tsaye ina
shiryawa wayana yayi kara mummy ke fadin wa kuma yakiraki yanzu kina shirin
kwanciya ?
Daukan wayan nayi amma sai gabana ya fadi mummy tana ganin yadda na firgita da
ganin mai kira na din a lokacin.
Waye mummy ta tambaya cikin son ji nace mata anty lagos ne bata san ina da ciki
ba nassan taji zancen haihuwan ne take kirana anty tace dauka mana sai ki fada mata
kin dauka ta sani ne ai.
Kiran ya katse sai ni na kirata kira biyu gana uku ta dauka nace mata anty ina
bayi ne da kika kira tace yanzu nake jin wai kin haihu sulaiman yakira yana fada
min.
Nace eh anty kin kyauta tace min lalai Safiya yanzu nasan yadda kika dauke ni har
kiyi ciki ban sani ba sai dai inji haihuwa kawai daga sama.
Ko shekaran jiya fa kin kira ni mun gaisa dake amma baki fada min cikin ki ya
tsufa ba haka sai dai inji haihuwa kawai.
Nace anty kiyi hakkuri na bansan yadda zan fada maki bane da baki na na dauka ai
ya fada makine da dadewa.
Ya fada min may shine zai fada min ko ke to bari kiji kada kiyi tsamanin kiyi
min kan ki kikayiwa sai ta kashe wayan kit.
Wayan nabi da kallon mamaki a hannuwan kamar ita ke gabana sai kuma na sake wani
murmushi kawai.
Don nasan inda maganan ta ya dosa alokacin bai wuce zancen kudi ba ne don ko
gabanin sallah na tura mata da kudi ta account din da ta turo min.
Mummy takatse da tambayan cewa may take nufi da kinyi wa kanki ko da ban san ta
ba nadai san a yanzu babu abinda zata gwada maki na rayuwan duniya.
Tana miko min tea mai kauri take fadin haka nace mummy anty tayi abinda bazan
iya mantawa da ita ba rayuwana .
Ta katseni da fadin don kaiwa mutun alheri ba saboda Allah kayi sai kuma mutum ya
zama bawan ka saboda Allah haka Allah yace ayi taimako duniya?
Tea din na karba na shaye sai ga zufa na karyowa a jikina na aje cup din ina
shirin kwanciya yaron mummy ta miko min tana fadin taba yaron ga tunda yazo duniya
baiji dumin uwar shi ba.
Karban yaron nayi na rugumay shi a jikina kamar wani babba da yasan may ake nufi
da haka sai naji ya sauke ajiyan zuciya a hankali a jikina.
A hankali hawaye ke zubuwa daga idanuwa na wanda ban san ina yin su ba alokacin
tausayin kan mu dana yaron ne ya kamani a lokaci guda.
Mummy tace a a yaya haka kuma daga karban yaro ki kama hawaye haka don Allah
kibar irin wanan dabiar mana ta mika hannu ta karbi yaron daga hannu na.
Har lokacin ban daina kuka ba wiwi badai ce min komai ba da kukan ya isheta sai
kuma ta koma lalashi na tana fadin.
Haba Safiya ke da zakiwa Allah godiya sai kuma ki gode mai da kuka kamar baki
gode mai da kyautar da yayi maki ba.
Tadai samu nayi shiru tare da nadewa saman godo ni kadai nasan abinda ke damun
zuciyana a lokacin wanda ita mummy ba ta sani ba.
A haka barci mai nauyi ya dauke ni sai da asuba naji motsin mummy ta tashi zuwa
ban dakin ta wanda acan take kewayawa bata shiga nawa har wankan yaron acan take yi
mashi.
Yau da yake ikilima yar ta na gidan sai ta dan jima bata dawo ba haka yasa na
samu daman komawa batcin dake idona.
Sai wani lokaci naji tana ta dani wai in tashi inyi wanka tun rana bai yiba sosai
haka na tashi na shiga na gasa jikina a ban dakin.
Na fito na shirya cikin wasu super masu launi ja da fari dinkin shi mai daukan
ido don an tsara shi dakyau da fasahan teloli na zamani.
Wayan Uncle ne ya shigo a lokacin da na gama saka sutura a jikina mun gaisa yake
tambayana babu matsakan komai a tare dani ko ?
Nace lafiya kalau muke Uncle sai dai kewan ka daya cika muna zuciya baka gidan
gidan babu dadi yace muyi hakkuri zamu ganshi nan da sati uku mai zuwa.
Nace haba uncle har sati uku baka zo kaga kyautan da ubagiji yayi maka ba yace
karki damu ina nan ina gode ma Allah ki san a gaban shi nake ma yanzu don ina
dawfin bankwana ne yanzu haka ina fitowa daga cikin kaaba ne.
Allah ya tsare nayi mashi yake tambayana mummy nace tana dakin ta da baby suna
karyawa ya sake tambaya idan muna da matsala in fadawa yaya saadu nace uncle bamu
da matsakan komai a tare damu.
Mukayi sallama naci gaba da shirina zuciyata cike da kewar miji na da bai kusa
damu a lokaxin da muke bukatan shi a tare damu din.
Goma da rabi ma,iakatan wurin su yaya saadu suka shigo min barka bisa jagorancin
yaya saadu din sun kai su goma duk kan su sun sha corth a jikin su bakake.
Wanda nake gani haka yanayin shigar wurin aikin nasu yake a falo suka girshe ni
zaune dasu mummy ba hijjab a jikina kafin a dauko min hajjib duk sun kare min
kallon da yaba hallitana a zukatan su.
Yaron mummy ta dauko masu nan suka shiga yaba kyawon yaron wasu na fadin wai ni
ya biyo wasu kuma suna fadin ogan su yaron ya biyo.
Basu dade ba suka aje muna kyatutukan da suka zo muna dashi sukayi muna sallama
suka tafi yaya saadu ne yadan tsaya fada muna samira na tafe ta tsaya gyaran gida
ne yanzu zai koma ya dauko ta.
Basu zo tare ba sai gata wai wani driver yasa ya dauko ta shi ya shiga kasuwa
muna zaune sai hira ake faman zubawa irin na mata idan an hadu.
Sai ga matan maikatan su Uncle sun shi su da yawa muka zauna ana gaisawa wanda
duk basu sanni ba sai a wanan lokacin.
Wata daga cikin su ce ke tambayan waye mai haihuwan sai samira ta nuna na
turancin yan Nigeari suka fara yi suna cewa ayyah.
Very young Lady nan hira ya kaure a tsakanin su suma dai yaba kyawon jaririn
suke ta faman yi zasu tafi suka aje muna kyautan da suka zo muna dashi.
Sun fice muna masu godiya naji Samira tace shegu muna fukai kawai ina ruwansu da
kurciyan ki dama sun zata ke tsohuwace ko may ?
Na da sauri nace kai Samira daga abin arziki sai zagi haka kuma tace ke baki san
komai ba ina wanan maidan jan gyale wai ita mijin ki take mutuwar so kamar ta mutu.
Nace wa uncle tace shifa wallahi kyale wahalaliya wai kuma a wurin dan uwan ki
take kamun kafa wai ya shawo mata kan shi.
Dariya nayi nace ashe aiki ja yagan ta kuwa sai kuma ita bakar nan mai kama da
zubin arnan daji itace ta lakewa yayan ki sai da na kirata ranan naci mata mutunci
sosai.
Dariya ta bamu dukan mu mummy tace ashe kina da aiki wanan zamanin idan kince
zaki dinga kiran yan mata a wayan miji kina zagin su.
Don haka zasu samu damar shige mai su nuna ai su na kwarai ne sai tafiya yayi
nisa su fitar da halin su na boye.
Nace ni yanzu mata sun baci mummy tace bari ke dai mace fa yanzu ba abin kunya
bane ta tunkari na miji da kalman son shi takeyi .
Nace ni mummy ba abinda keci mun rai da matan yanzu sai kiga mace na tafi taga
mota tafe ta kasa kawar da idon ta ga mai motar.
Har ba da matan aure dabi an su ne yanzu bin namiji da kallo cikin mota ba birnin
ba ba kauye ba.
Samira tace ai sai kiyi ai wanan yanzu ya zama ruwan dare a ko ina mata da sunji
rurin mota basu da kwanciyan hankali sai mai motar ya wuce su.
Yaya Saadu ne ya shigo gidan yana neman Nura akace tana kitchen kiranta ikilima
tayi sai gata da saurin ta ta fito yake ce mata tazo ta duba kayan kitchen abinda
babu ta fadi a sawo zata koma kitchen din yace mata a a tafito suje waje suka fice
tare dashi samira ta tashi ta bisu wajen.
Dariya muka kwashe mata dashi tace kuka ga abin dariya tsaron kaya yafi cigiyan
shi ai nace ke dai baayi niyya ba mai zaki iya hanawa samira.
Mummy tace rabu da mahaukaciya sun dade a waje sai gasu suna shigowa da kayan
abinci cikin gidan katon katon komai an sawo.
Zai fita nace haba dan uwa zauna na mana kaci abinci nasan wanan zirga zirgan da
kakeyi baka tsaya kaci wani abu ba.
Mummy tace ga matar shi sai kishin hauka takeyi bata san ta tambayi lafiyan mijin
ta ba.
Tace ai nasan ko nayi mai tayi bai zama yaci yana wanan zirga zigan haka mummy
tace haka ake son aminin kwarai yayi maka tsaye da gidan ka idan bukatan haka ya
taso bai kusa.
Abincin yaci yana ci muna hira yake fada min sunyi waya da baba yaya sani ya
fada mashi kila jirgi na biyu zasu biyu don da shi suka tashi.
Mummy tace kafin su dawo ai mu mun sha bukin mu sai dai suji labari a bakin mu .
Wai yaushe shi maigidan zai dawo take tambayan yaya saadun yace basu yi waya ba
don ko yabar saudiya Dubai zai tafi daga can sai dai ranan da muka gane shi.
Banji dadi ba a raina har hakan ya baiyana a fuskana yaya saadu ne yake mun
sheri dan murmushi nayi kawai ban iya bashi amsa ba.
Jego ya karbe ni sai dai ina makin yadda nono na basuyi min ambaliyan ruwa ba sai
na fahinci kila maganin da likita ya bani ne ya kawo hakan.
Suna saura kwana ukku muna daki da dare mu uku muna shirin kwanciya ikilima tana
muna hira a dakin mu mukaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login