Showing 180001 words to 183000 words out of 258256 words

Chapter 61 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

rayuwan mutun sai
mutane sun gane halin shi na banza mutum dai dan tara yake bai cika goma ba
wallahi.
Nan dai muka isa masaukin mu kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi a lokacin
bayan munyi sallah mukaci abinci bamu dade ba muka shiga barci.
Tashin asuba zamuyi don hakane muka kwanta da wuri shiya tadamu mukayi wanka
karfe biyar a airport yayi muna mun gama komai kafin shidda muna cikin jirgin da
zai daga.
Na dauka zuwa Canada wasa ne ashe ba karamin tafiya bane nan na jinjina ma uncle
da bai jin wutan tafiye tafiyen da yake yawan yi ko yaushe sai da muka kwana washe
gari muka sauka canada din.
Inda abokin shi yazo ta tare mu wani dan gida madaidaici ya kaimu nikan ban boye
kauyancina sai kallon abin mamaki nakeyi a garin. .
Wanka mukayi da sallah sai abincin da mukaci nan muka kwanta ranan duk kwakwan
uncle sai da ya barni shima barci yake yi sosai.
Sai wani lokaci muka tashi ko shi zuwan wanan abokin nashi da iyalinshi yasa mu
tashi barci don sun kawo muna abinci irin namu na bakaken fata.
Matar shi tana gani na tashiga yaba tana fadin lalai Uncle bakayi ruwan idon
banza ba wirin zaben mace haka maikyau ga tsari ga hankali.
Mijin yace na gaya maki ai mutumin nawa ruwan idon shi da dalili ya tsaya yin
shi nan dai sukayi muna fatan alheri basu wani dade ba sukayi muna sallama suka
tafi.
Kwana biyu uncle baya fita ko ina muna gida acewan shi yanzu ne yake more
amatcin shi dariya nayi nace wani amarci ya saura amarya wata shidda a dakin ta
kuma.
Yace ai wuyan aiki ba a fara ba don ni so nake kafin mu bar nan din sai kin samo
ma hajiya baaba dan jikan da tace tana son dauka nawa.
Daya fara fita ko saida na raina kaina naji dama ya barni a gida ne yafi don ko
yaya muna dan hira da zara ko Nuratu mai aikin mu.
Amma nan haka zan wuni sai kallo sai ko kwanciya ban tsinana komai a rayuwa tunda
safe in yafita sai dare sosai yake dawowa gidan.
Haka kuma idan gari ya waye zai sa kafa ya fice gidan sai kuma dare kwana zai
dawo duk suna wurin harkan kasuwancin su.
A kasan muka fara azumi duk da ba musulmi a kasan sai jefi jefi wani lokaci zai
dawo gida da wuri tunda azumi ya fara.
Mukan dan fita idan ya dawo da wuri yadan nuna min garin mu dan yi sayayya mu
dawo gida bai kara fita sai kuma gobe.
Ranan ya dawo gida da wuri ya shigo da sallaman shi da gani a gajiye ya shigo
gidan don yanayin shi kawai zai nuna hakan.
Kwance nake saman carpet ban ko iya daga kai in mashi sannu da dawo ba a lokacin
don tun cikin dare nake jin jiki kuma ga azumi a bakina.
Ya cire takalmanshi akofa kamar yadda mukeyi acan tare da rataye rigar sanyin da
ya dora saman kayan jikin shi.
Ya tako har inda nake tare da sunkuyowa gaba yana fadin madam yau lafiya kike
kuwa da kyat na iya dago kai na dan dube shi da idanuwa na da sukayi min ja saboda
wahala.
Na mayar dakai na kasa ina wani irin numfashin wahala nace da kyat uncle sannu
da dawowa.
Kasa yakai zaune a inda nake don ya tabbatar da ba lafiya nake ba a lokacin zama
yayi saman carpet din tare da dan tallabo kaina yana fadin may ke damun ki ne haka
?
Na runtse idanuwa tare da cije baki na nace uncle banda lafiya ne tun da dare
nake jin zazzabi yana damuna sai kuma amai ya biyo baya bayan fitar ka gidan.
Dan taba jikina ya shiga yi yazo daidai wuyana yaji yadda jikina yayi zafi ya
gashe sosai a lokacin yace shine baki kirani ba ana wasa da ciwo ne komai karantar
shi akace maki.
Ya ce ki tashi muje asibiti yanzu a duba ki ansan abinda za a baki na cije baki
nace uncle bari in ansha ruwa mu tafi don yanzu ina dauke da azumi.
Ya katse ni da cewa wani azumi kina haraswa haka sai ya mike tea mai zafi ya
shiga ya hado min ya dawo inda nake yana min sannu ya mikar dani ya matsa min sai
da na sha ina runtse idanuwa don ba dadin tea din nakeji ba.
Ina sha yana min sannu da fadin dan kara dai ko kadan ne na cije baki na kara
amsar cup din ina kurbawa da gudu na mike zuwa bandaki sai da na amaye shi kaf na
samu saida a raina.
Yana tsaye a bayana yana min sannu na dago cikin cije baki ina maida numfashina
dakyat ya rungumoni muka dawo falo daki ya shiga ya dauko min hajjab dina na sa.
Sai faman cije baki nake yi haka ya kamani zuwa waje inda muka shiga motar da
yake amfani dashi a kasar wani asibiti mukaje.
Nan ya yaki kati inda babu dadewa suka shiga yimin gwaje gwajen su na likitoci
tare da yan tambayoyi.
A karshe da result ya fito likitan yayi mashi albishir ina dauke da juna biyu na
wata biyu a jikina hakan ya nuna tun a gida nageria nike dauke da cikin a jikina
bamu sani ba.
Tun fitowan mu yake faman washe baki shi yana jin wani irin dadi a ranshi yana yi
yana dan kamoni tare da fadin Allah ya karba adduan mu dana hajiya baaba.
Ni dai ban iya ce mashi komai ba har muka shigo gida har na haye kujera na kara
lafewa kafin ya shigo yakkule ko ina na gidan haka yasa na fahinci bai kara fita ko
ina ke nan ranan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/23/20, 5:39 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,


6️⃣2️⃣6️⃣
🧕🏿 2️⃣


NOVEL DIN NAN NA KUDI NE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA IDAN
KUMA KIN FITAR MIN DASHI UBANGIJI ZAI SAKA MIN A KANKI KAN NOVEL.

Ina kwance na saman kujera na dunkule a ciki naji ya sauke min kiss a goshina yana
fadin Alhamdullahi kinga Allah ya amsa muna adduan mu yanzu ni na gama aikina saura
naki.
Da sauri na bude idanuwa na dake lumshe na sauke su gareshi acikin sanyayyar
murya nace dashi.
Uncle kada ka zamo mara tausayi mana kana nufin yanzu aikin nawa ne ni kadai kai
ka gama naka ke nan ?
Ya mike ya samu wuri ya zauna yana fadin eh to ai gaskiya na fada don nayi yadda
duk wani kosashen namiji ya kamata yayi dasa ciki a jikin mace.
Kin ga yanzu ke kuma sai kiji da amai da daukan nauyin ciki amma kada ki damu
zandan rika taya daukan shi ta hanyan rage maki jin nauyin shi a jikin ki.
Sai idan haihuwan yazo kuma ai tare zamuyi labour dake ba inda zan fita ranan
hararan shi nayi sai muka kwashe da dariya kuma.
Nace ashe kai har wahala kayi wurin dasa vikin a jikina yace ba kadan ba ai nayi
kokari sosai wallahi yanzu jina nake wasai don na fara sauke nauyi na.
Murmushi nayi mai ina gyara kwanciya ban san lokacin da barci mai nauyi ya dauke
ni ina dan tunane daga inda nake kwance.
Ban falka daga barcin ba shikuma bai tadani ba sai karfe takwas na dare lokavin
yana zaune yana buda baki a falon kusa dani.
Jin motsin da nayi yasa shi dago idanuwan shi ya dube ni ganin shi nayi zaune
yana yana buda baki da sauri na mike ina fadin anyi sallah ne Uncle ?
Yayi murmushi yana fadin kin falka yays jikin nace da sauki tare da sauko da
kafafuwana kasan kujera da nake sama.
Yun kurawa nayi don in tashi zuwa sallah sai na gaza tashi wani irin jiri ya
dauke ni da sauri ya mike ya taso zuwa inda nake yana fadin yi a hankali fa.
Kin san ba ke saya kike ba yanzu dole kibi sannu don Allah zama yayi saman
kujeran tare da riko min hanaye na ya mayar dani ya kwantar yana fadin sannu bari
ya dan sake ki sai ki tashi.
Na dan dade kwance a wurin sai da naji jirin ya sake ni na mike na shiga dakin
kwanan mu wanka nayi don nauyin da jikina yayi a lokacin ko zai sake.
Na fito na tada sallah bayan na idar na dade a wurin zaune ina mika godiyana ga
Allah tare da fatan Allah ya bani mai albarka.
Ina nike abin sallah nawa sai gashi ya shigo dakin dauke da abinci a hannun shi
wanda noddle ne ya dafa a lokacin yake shan ruwa dashi kallo daya nayiwa abincin
naji wani amai yazo min a bakina.
Da sauri na juya tare da boye fuskana ga ganin abincin dake gaba na tashi na
shiga ban daki banyi komai ba na fito.
Yana zaune bakin gado yake fadin abincin bai maki bane kuma na cewa ban dai jin
cin shi ne a raina kawai.
To may zaki ci ya tambaye ni nace zan dai ci fruits in na samu falo ya koma ya
debo min fruits mai yawa zai juya sai gani na fito falon na karbi plate din a
hannun shi da sauri na koma saman kujera na zauna.
A hankali nake taunan apple dana fara dauka naji yayi min dadi a baki na muna
hira ina cin abina sai gashi na cin fruits din sosai.
Naji yace a lissafi na cikin nan tun kan mu tafi bauchi gaida hajiya kika samay
shi idanuwa na na lumshe kawai tare da daukan dan annibi in jefa a bakina.
Tun wanan lokacin na ke samun wani kula na mussanman daga wurin uncle din nawa
ciki kuma na bunkasa acikin koshin lafiya da samun kulawa a jikina.
Don ban damu da cin abinci ba saidai bani wasa da cin diyan itatuwa dama gashi
akwaishi kasan da muke kamar banza.
Tun Uncle na fadan rashin cin abinci ya gaji ya kyale ni tunda yaga diyan iccen
kawai zanci ya zauna lafiya a cikina abincin da raina ke so babu shi a kasan.
Alhdullahi uncle ya gama abinda ya kawo shi kasan kai ya kammala sunyi nasaran
shiga da kayan su daga nageria sun kuma juya su sun zama kudi sun saro abinda suke
so a can sun tura nigeria din.
Saura sati daya mu bar kasan zuwa kasa mai tsarki ya dauke ni mukaje shopping din
kayan baby acewar shi yana da wuya ya samu dawowa kasan kafin in haihu.
Mun dawo a gajiye gida ba abinda nake so kamar indan watsa ruwa lokacin sai
in dan kwanta kuma don in huta saboda naci gaba da azumi da na samu sauki.
Bayan na fito daga wanka falo na dawo inda yake zaune yana wani lissafi a cikin
laptop din shi a lokacin.
Kujera na samu na zauna ina kokarin kwanta a lokacin sai ga kiran Faiza ya shigo
min na dauka da sauri muka shiga gaisawa da ita din.
Yana zaune yana jin hiran mu take fada min wai ashe haka mukayi ma anty bana na
hana uncle ya bata rabon kaya wa yan uwa sai ni na raba.
Nan dai take fada min irin zagin da nake sha gun anty yana jin mu sai murmushi
yake yi kawai yana ci gaba da aikin shi mukayi sallama na dago ina sauke ajiyan
zuciya.
Tare da fadin nikan na shigesu ga anty wai sai yaushe ne wanan abin zai kare a
tsakanin mu ne wai ?
Bata tare da ya kalli inda nake yana aikin shi yace sai ranan da zaki bar mata
mijin ki ta aura ma wacce take son ta aura min din.
Nace zan dai bita a hankali in gani ko zamu kawo karshen matsalan amma zancen in
bar mata mijina ai ko a mafalki bata raya haka gare ni yanzu.
Ina wurin kwance har lokacin shan ruwa yayi na mike jiki a sabule na har hada
muna komai anan mukayi buda baki shine yake bamu sallah kullun dani da shi.
Mun idar muka zauna cin abinci kowa yayi shiru sai cin diyan icce na nakeyi
hankali kwance naji yace dani zanso kafin mu bar kasan nan mu koma asibiti su baki
don kin san asibitin irin ta masu lalurar mune zallah a wurin.
Da sauri na dago kai na dan kalle shi nace uncle kana nufin duk mutanen da na
gani a wurin suna da cutar dake karya garkuwan jiki a tare dasu.
Yace ai kin san kasan nan mafiyawan su kasan baki ne don haka kowa ke abinda ya
ga dama a kasan shiyasa har suka kai ga bude asibiti irin haka.
A hankali na shiga tunane a raina don zama da uncle yasa yanzu har sai in manta
cewa muna dauke da matsala a jikin.
Tuno abinda zan haifa nayi ko in haifi mai lafiya ko kuma kasin hakan Allah
kadai ya sani banyi aune ba naji idona yana fitar da hawaye tausayin kan mu da
abinda zamu haifa din ya kamani a lokaci guda.
Dago kai yayi ya dan kalle ko ban fada ba yasan abinda nakewa kuka a lokacin don
yasan tunane na idan ya nufa.
Ji nayi yace dani kiyi hakkuri madam ni kaina wanan tunanen kanzo min a rai har a
baya nikan raya ba zan yi aure ba balle har in haihu in mutu in bar yara a cikin
maraicin iyayyen su.
Amma da na natsu sai naga ai Allah mai kashewa kima shine mai rayawa ga masu
lafiya suna mutuwa subar marasa lafiyan abin daga hannun Allah yake don haka sai na
barwa ubangiji sanin sa.
Haduwa ta dake kuma sai kika kara mantar dani daga damuwan da nake ciki a baya
don haka yanzu na ragumi kaddaran da ubangiji ya jarabi rayuwan mu dashi a duniya.
Ga komai na rayuwa ubangiji ya hore ma rayuwan mu dashi amma sai dai muna
rayuwan ne cikin BAHAGON RAYUWA.
Domin bamu san yadda abin zai kasance damu ba a karshe sai dai muyi fatan gamawa
da duniya lafiya don wanan rayuwan yishi kawai ake a bahagon yanayi.
Nado kai a hankali muka kalli juna sai naji so da kaunar shi da tausayin mu ya
dira min a zuciyana.
Nace Uncle mu namu kaddaran ke nan yazo muna a haka sai muyi fatan samun mai
lafiya mutaima mu bashi tarbiya mai inganci koda bayan mu bazai samu matsalan
rayuwa ba.
Naji ya riko min hannuwana da na sake fruit din da nake sha a hankali yana dan
murzawa yace Safiya har kullun addua na shine mu samu zurian da zamu bari a duniya
ko bayan mu zamu samu masu muna addua da tunamu a matsayin iyayye a gare su.
Addua na yanzu shine Allah ya sauke ki lafiya ina mai tabbatar maki bayan
haihuwan ki zaku samu kullan yadda ya dace a gare ni.
Don a lokacin zan tabbatar maku dani din zsn zamay muna jigon rayuwa da ko bayan
raina zakuyi alfari da samu na a tare daku.
Nayi murmushi tare da fadin insha Allahu a tare zamu raka da junan mu har diyan
da zamu haifa din yace tau Allah ya bamu rai da lafiya din nace amin da sauri don
yadda ya karasa maganan shi akwai tarin damuwa a zuciyar shi sosai.
Nayi ajiyan zuciya tare da kokarin hada kayan da mukaci abinci ina gyara wurin
ina gamawa na shiga wanka don a gajiye nake lokacin.
Bayan shima ya fito wankan ne ina zaune bakin gado na mayar da hankalina sosoi a
wayana ina duban sakon nin dana samu ranan.
Yafito daga wankan yake cewa dani ya kamata dai tunda anji sauki kuma sai in samu
tukwaici haka horon yayi yawa mana madam ya iso gare ni yana kokarin taba min , , ,
.
Da sauri na manna mashi cizo daidai kunnen shi cikin rashin damuwa sai dai
kokuwan da muka fara yana sai ya rama a lokacin na shiga rokon shi sai kirjina yake
hari wai anan zai rama cizon shi na fara tsala mai ihu bai sa ya sake ni ba.
Sai dariya da yake kwasa yana fadin sai ya rama cizon shi anan din saman kirji
dole na kyaleshi yayi abinda yake so din.
Washe gari muka tafi asibitin kamar yadda yace munga likita yakuma dora mu a
maganin da zanyi amfani dashi da kuma yadda zan kare lafiyana dana jariri har reno
da komai sai da yayi muna bayani yadda ya dace.
Yaje ya sayo maganin masu inganci da amfani wanda bazamu samu a gida nigeria ba
sai a nan din ko wata kasa da taci gaba sosai a duniya.
Mun hada komai na ranan thursday muka tashi da dare zuwa saudiya inda zamu yadda
zango a wata kasa kafin mu isa can din.
Sai dai duk wani sayaya da mukayi a canada ya tura gida Nigeria za a tafi muna
dashi a cikin sabin kayan da zasu tura can.
Mun sauka a birnin madina direct inda already an sama muna masauki inda zamu
zauna wanka kawai mukayi muka isa masallacin fiyayyen halita muka mika gaisuwan mu
gare shi bamu dawo masaukin mu ba sai da mukayi sallah ishai acan muna ta rokon
Allah saukin alamura.
Kwanan mu takwas a madina muka wuce birnin makka mukayi umurah sai mu muka shiga
zama ko yaushe a massalaci barci ne kawai ke kaimu masaukin mu.
Ban taba sanin haka uncle keda yawan ibada ba sai wanan tafiyan namu don duk da
yasan ina cikin lalura hakan bai sa mun dan huta ba sai dai ko yaushe yana kara min
karfin gwiwa da fadin in dai jajirce in matsa mu samu wanan falalan.
Cikin ikon Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login