Showing 129001 words to 132000 words out of 258256 words
Chapter 44 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
zuwa ba tare zaku zauna.
Koma tare ne fa anty nace mata ?
Tace ai shi na gani.
Wai ma yaya akayi tazo maki da zancen ne sai na dukar da kai tace lah bazaki fada
min ba ?
Ko dai ke kika fito mata da zancen ?
Nai saurin cewa a a wallahi ita dai ta samay ni da maganan wai tazo fada min
gaskiya taga kamar yana sona to shine take son ta fissheni .
Don taji ana rade radin kamar baya da lafiya a jikin shi.
Salati ta saka nai sairin cewa anty tace kada in fada ma kowa don Allah abar
zancen a rufe don ba zata ji dadin fada min wani ba gaba tace hakane.
Na dai kwashe yadda mukayi amma ban fada mata zaginta da tayi ba na boye wanan
sai na sulaiman din na fada mata.
Tace wa yan nan yaran gulman su yayi yawa wallahi ni duk nagaji da zaman su anan
don ma zuwan ki ne da duk sun koma gida.
Nace a raina don ma baki ji sauran ba aida kin rage su gaba daya sai naji tace
dani gulmana fa suke yi sosai harda sakaran nan Fati da bata san ciwon kanta ba.
Naiyi saurin kawar da zancen da cewa ayyawa anty kin san ko abinda uncle yayi
tace may yayi safiya ban san komai ba.
Nace dazun muke waya da ummi take fada min cewa wai ya tura a gyara gidan mu nan
da wata daya a gama komai.
Ummi tace aiki akeyi ba dare ba rana sai naga ta kwashe da dariya tace namijin
duniya ai tun ranan da ya tafi mukai waya dashi.
Tausaya maku yayi ya damu da yanayin da ya samu gidan ku a ciki ai ke ki godewa
Allah don Allah ya kashe ya baki.
Sulaiman ban sanshi da halin banza ba sai dai mutane ne da basu fahince shi ba
kawai suke gani bai son mutane ne.
Tace aiko zan kirashi in shamce shi don yasan mun sani nace anty da ki kyale shi
maga gudun shi tace ai shine.
Ke har kin ma fara fahintar halin shi tun yanzu zai ce wani dan gulma ya fada min
kiko ga bazan iya ce mai ummi ce ba.
Dariya na kwashe dashi nace ai sai ko ki fada tace wane ni wallahi safiya idan
kin fahinci waye sulaiman shike nan kin huta.
Sai dai kinyi hakkuri da shirun shi don shi mutum ne wanda bai son magana sosai
haka yasa mutane suke mashi kallon miskili.
San nan kuma dole ne in kaiki ki koya wasu abubuwa don ko shi din ba karamin dan
gaye bane in dai zaki daure gaskiya kin huta safiya.
Ta tambaye ni labarin inna da za a rushe gidan yaya tayi na fada mata nan tai ta
kwasan dariya tana mamakin karfin hali irin na inna.
Taci gaba da min bayani kan halin sulaiman din dana yan uwanshi da kuma halayen
shi da damuwan da yake ciki.
Kaina na dukar ban iya magana ba tana ta fada min halin shi ina kara fahinta
komai sai goma nabar dakin ta koda na sauko ba kowa a falon har funke ta rufe gida
ko don daddy yayi tafiya kwatonu.
Har na kwanta ina tunanen maganganun da ta fada min a kanshi nace Allah ka bani
ikon yin biyyyan aure
Ina tunanen ko yaya zama zamu yi dashi har mada yan uwan shi don na fahinci sudin
masu haline zurian su niko gashi iyauye na ba kowan kowa ba.
Ai so ya na hana komai idan dai shi ya kamani da mutunci ai dole yan uwan nashi
su soni ko don shi tun da dai dan uwan su ne na aura
ZAINAB IDRI MAKAWA
SEENABU
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 09017242889
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , ,
4️⃣6️⃣4️⃣
4️⃣
🧕🏿 6️⃣6️⃣4️⃣
AMANA YAR UWA KADA KI FITAR MIN DA NOVEL IDAN KI BA WATA BAN YAFE MAKI
BA, , , , , ,
Tun karfe shida na safe na samu wayan yaya Saadu cewa matar shi ta haihu nayi murna
sosai tare da kwararo mata addua yana cewa amin cikin jin dadi da adduan da
nakeyiwa yarinya.
Na gama yace yaya alkawari nace yana nan daram nace so ace daya daga cikin su
ummi zata zo mu tafi tare amma yanzu babu hali don gyaran gidan da ake masu yace ai
ya sani.
Nace ka sani yaya yace to baki fada min ba Safiya yays zanyi ido kawai na saka
maki ai nace wallahi yaya nima sai last week na sani ummi ta kirani take fada min.
Yace you are free don da har na kullace ki don yanzu bakiyi dani nace da sauri
wanne ni yaya ai kaine nafarko a zuciyana.
Yace to mu bar zancen sai kinzo muyi don baiyi a waya yace zai kira su gwago ya
fadamasu do nice ta farko daya fara fada mawa.
Mukai sallama ma kashe wayan ina mai farin ciki a zuciya na ranan duk wanda ya
ganni yasan na tashi a cikin farin ciki.
Anty tayo shirin zuwa office bayan mun gaisa nake fada mata zamcen haihuwan matar
yaya Saadu itama ta tayani farin ciki.
Nace zan tafi banda gobe don nayi mashi alkawarin zuwa sai naga antu batai farin
ciki da hakan ba, bata bani amsa ba, ta dai fita tana muna sallama.
Hakan bai min dadi ba amma zanyi hakkuri in ga tafiyan ta akan zancen don ba zan
saba ma yaya Saadu alkawari ba gaskiya.
Bayan na gama aiki na shiga daki na buga ma anty waya ina fada mata zancen
haihuwan na matar yaya saadu.
Itama tayi murna sosai tayi ma yarinyar adduan sosai nace mata ina son zuwa kamar
yadda nayi masa alkawari don wanan kawai zan mashi in iya rama mai halarcin da ya
gwada man.
Tace dako kin kyauta yar nan nace sai dai ina ganin kamar anty bazata yarda da
zuwa na ba tace sai ki lalashe ta kada kiyi gaban kan ki.
Nikan shiri na fara yi sai dai ban fada ma kowa ba kamar yadda ya saba kirana a
ko wani rana safe da yamma yauma ya kirani da dare bayan na kwanta nan nake fada
mai cewa matar yaya na ta haihu ina son zuwa Carlaba wurin suna ya taya ni murna
tare da tambaya na yaushe ne suna na fada mai tare da cewa ina son in tafi suna.
Sai naji ya danyi jim sai yace yaushe ke nan kike son zuwa nace banda gobe don
haka nayi ma yayana alkwari don yace yana son inzo da wuri.
Don banda kamar shi a cikin yan uwa ya taimakeni a lokacin da nake neman taimako
banda wanda zai taimaka min.
Yace lallai kina ji da wanan yayan naki sai ki turo min da layin sa in mashi
godiya nace angama yallabai.
Da jirgi zaki tafiya ko da mota sai nayi saurin cewa jirgi kuma zan dai bi mota
in tafi yace ban faye amincewa da batun motar nan ba.
Ki dai bi jirgi ki tafi yafi tafiyan a mota sai ki kai da wuri yace zanyi magana
da madam sai a san yadda za a shirya maki tafiyan dan ni bani kasan yanzu haka.
Nayi saurin duba lanban wayan nashi naga daga kasar South African yake magana
tirkashi nace a raina.
Mukai sallama na kashewayan tare da kwantawa naja bargo na rufe ina mai ci gaba
da tunane a zuciya na.
Anty ta fita aiki da safe bai kirani ba sai nayi tsamani aikin da yaje yi ya
dauke mashi hankali ne a can.
Da ta dawo ne take ce min munyi waya da sulaiman nace a a sai tayi shiru can
tace ashe kina ga zuwa Calabar din ne don naji sulaiman na fadin a sayo maki ticket
din jirgi.
Nace a dake eh anty gobe nake son zuwa don hakane kawai zan iya rama ma yaya
Saadu halarcin da yai min a baya.
Ta gyada kai tace shike nan da amma ni naga da kifita hanyan duk kansu baki daya
har saadu din zai fi tunda sabon aure zakiyi yanzu.
Da sauri nace anty kina ganin zan iya yanke zumuncin da ke garemu da yaya Saadu
shine fa dan uwa na farko da yai min tsaye na samu lafiya.
Kuma ana haihuwanan bai kira kowa ba nice ya fara kira ya fadawa idan nai haka na
zama butulun a duniya har da wurin Allah.
Sai tayi shiru bata kara yi min magana ba hiran ma sama sama muke yin shi da ita
taje sallah azahar nima na tashi na idar na fito bata falo.
Na samay ta a dakin ta sama nace anty ina son in dan fita in sayo wa baby tsara
ba don kada naje hannu sake.
Ok ai yanzu muka gama magana da sulaiman bance da ita komai ba nace zan wuce sai
naji tace dan dakata min in zo.
Na samu wuri na tsaya daga kofan daki ta mike zuwa safe din ta ta bude ta fito
da kudi kashi biyu tace ga wanan sulaiman din ne yace a baki ki yi sayayya sai kuma
wanan nawane asaya wa baby kaya.
Nace Lah anty ai da ku barshi ina da dan kudi hannuna da na dawo gida dasu tace
kin raina kenan ko da sauri na isa wurin ta ina karban kudin.
Sai naji tace Safiya kamar maganan danayi akan saadu bai maki dadi ba ko nace ba
haka bane anty ai gaskiya kika fada min.
Sai dai shi yaya Saadun ne banga laifin shi aciki ba don bai min komai ba tsakani
na dashi sai alheri har gobe don ko dawowanan da yayi sai da yaje gida duba jikin
baba.
Tace ai nayi tunane daga baya naga kina da gaskiya tace ki dai zabo abin kwarai
don Allah kada ki kwaso shirmay.
Nace to anty na gode na juya zan wuce tace dani zan kira driver sai ya kai ki
godiya na kara yi mata na fita.
Faiza tana ganina take tambayana inda zan tafi na fada mata sai tace zata rakani
ta dan mike kafan ta.
Na jirata ta shirya ta tafi ta fada ma anty muka fita tare nan muka samu driver
yana jiran mu a waje muka fada mota ya fice daga gidan.
Kaya na kwaso na baby da na uwa sai da na cika akwati dashi muka nufo gida Faiza
take ce min tana son mu tafi tare nace sai mu fada ma anty idan zata yarda.
Bayan ta gama ganin kayan ta sauke ajiyan zuciya tace wai Safiya kaya haka kamar
mai shirin bude shago ai kin fanshi uban diya.
Nake cewa anty dama ai fannin uba muke sai lokacin ne Faiza take gabatar mata da
son zuwanta tayi saurin cewa da jirgi fa zatayi tafiyan.
Ba zai yuyu kuje tare ba da dai a mota zakuyi tafiyan zan barki ki tafi Faiza
bataji dadin haka ba kuma gashi taji ance a jirgi zan tafi wai.
Sai yake ta mamaki wani irin asiri nayi ma anty ne haka da basu jin wuyan kashe
min kudi har yaushe na dawo gida akaje airport dauko ni.
Yanzu kuma ace a jirgi zan kara tafiya kodai maganan Fati gaskiya ne da take
fadin tana turani karuwanci ne wurin maza.
To amma kuma wanan uban kayan da muka sayo fa namay ye shi gashi kuma taji nace
fannin uban jegon nake bukin dai zan tafi amma akwai dai daurin gindi wani wuri.
Yadda tasan anty da kudi bazata iya biya min kudin jirgi ba har Calabar in je in
dawo na kwashi kayan zuwa dakina ina shiga daki kiran shi ya shigo wayana.
Ban dauka da wuri ba sai da nayi halin mata jan rai na dauka tare da sallama sai
naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin.
Ke idan ba a kiraki ba baki kiran mutum watau nace na dauka kana uzuri ne tunda
banji ka ba yace ban uzurin komai fushi dai nake yi dake.
Nace ni kuma may nayi yallabai ?
Sai yace ashe bukin dangin mijin ki na da zaki tafi ban sani ba nace kwarai
dangin shi ne nima kuma dangi na ne ba gaiyan sodi zan tafi ba sai na fara bashi
labaron irin halarcin da yaya Saadu yai min a lokacin.
Yace kin fini gaskiya daga baya madam ta fahintar dani ai daga baya yanzu na
fahinta Allah yakai lafiya.
Nace amin yace tace girgin karfe hudu zaki bi sai ki sanar dasu can azo a dauke
ki nace nagode yace ban son tsaron lafiyar matata nakeyi.
Ya kashe wayan nabi wayan da kallo tare da tunanen watau anty ta fada mashi
abinda ta fada min ke nan da farko.
Idan haka ne bata kyauta min ba kuwa zuciyana ta nasa min cewa kodai abinda su
Faiza ke fadi gamay da ita gaskiya ne ?
To inma gaskiya ne ni dai batai min komai ba don bazan manta da halarci ba kuma
ban iya matawa da mafari.
Da dare na kira yaya nake sheda mai karfe shidda azo dauka na a airport yace
bazaki zo ba kenan amma safiya baki kyauta min ba.
Gashi na sa rai kece zan gani cikin yan uwa da zaki zo ki zama min garkuwa don
suna fadin ba a san yan uwana ba.
Nace yaya karfe hudu nace azo airport a dauke ni ba wasa nakeyi ba in Allah ya
yarda gobe zan shigo yaya yace masu gari don Allah da gaske nace Allah yaya.
Koda gari ya waye na shirya tsab sai dai yan gyare gyaren daki da na tsaya yi don
kada in dawo in samay shi ba gyara.
Wayan shi ne ya shigo min muka gaisa yace an shirya ko nayi murmushi nace kamar
ka sani komai na hada tafiya kawai ya rage min yanzu yace nasan dari biyu zai ishe
ki yin komai su nace ma madam ta baki jiya.
Nace ta bani na gode ubangiji ya kara rufa asiri amma dai kai baka gajiya da yi
mani dawainiya haka ?
Yace idan banyi wa matata dawainiya ba in yiwa ai ke da hajiya baaba kune dole na
yanzu ba zan taba dana sanin yi maku ba a rayuwa na.
Mun dan taba hira mukai sallama yake cewa idan na isa zai kirani yaji sauka na
nace nagode.
Mun kashe wayan ya barni da tunanen maganan anty watau kudin da ta bani dubu
goma cikin kudin da ya bani ne don dubu sittin ta bani tace inji shi.
Amma kada in zargeta zan bari in gani ko idan zan wuce zata ban sauran inma bata
bani ba taci halas ai albarkacin ta nake ci da badon itaba ina zan samu wanan
gatan.
Karfe uku ta dawo gidan don tafiyan nawa take cewa nayi na shirya kafin hudu
driver zai kaini airport.
Nace mata tau.
Uku da ashirin na fito tafiya tana dakin ta naje mata sallama fuskan ta da fara a
take ce min tau safiya Allah ya kiyayye haya agaida su ina masu barka.
Yaushe zaki dawo nayi murmushi nace sai dai idan na je can anty zamuyi waya sai
in sanar dake tace to Allah ya kiyayye hanya na ce amin na fita da kayana Faiza tai
min rakiya har waje sai da muka daga ta dawo ciki.
Mun fara hanya na nisa tare da fadin mutum kasan shi baka san halin shi ba yanzu
ba don Allah yasa ya fada min ba ba zan taba sanin komai ba akan anty.
Bamu dade da isa airport din ba jirgi ya tashi dan wani lokaci naji ana sanarwa
jirgi zai sauka mu shirya .
Mun sauka na fito tare da kaya na ina faman rabon ido ko ta ina zan ga yaya
Saadu sai gashi tare da abokin shi.
Yayi murna kwarai da ganina yana ta faman washe baki yana fadin safiya ashe da
gaske kike yi kin san Allah karfin hali nayi nazo airport kawai ba don na yarda ba
na dauka kin fara wasan cousi ne dani.
Nayi murmushi ina gyara gyalen kaina dake kokarin walwalewa a kaina nace haba
yaya ai bamu yar haka dakai.
Suka dauki kayana zuwa motar da suka zo da ita nan muka kama hanyan zuwa unguwar
su sai faman zolaya na yakeyi yana fadin waiko Safiya kece nake gani a gabana ko
mafarki nakeyi kin koma haka ?
Ni dai murmushi nake mashi ina bin gari da kallon mamaki abubuwan zamani irin
nasu na arna da kallo.
A can wani ungwa mai kama dana hausawa muka shiga don akasarin mazau na ungwan
hausawa ne amma na gari daban daban sai hausan su ya juye kamar yare.
Mun tsaya a kofan wani gida nan yace min tau Safiya yau kin zo gidana muna maki
maraba da zuwa murmushi nayi nace na gode.
Mun fito suka bude bayan motar suna fito min da kayana daga ciki a tare muka
shiga gidan dasu sai ga matar shi Samira ta fito da gudun ta tana min oyoyo .
Muka run gumay juna da ita tace ashe gidan gidan yawa ne mai apartment da yawa
ban luraba sai naji tana fadin ku fito ga