Showing 243001 words to 246000 words out of 258256 words

Chapter 82 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

kada ki hada kan ki da waccan don kila ita bata samun kulan da kike
samu.
Mun dade muna hira ta tafi ta kwanta nima na shige kwana daya sukayi muna suka
juya lagos don dama ganina kawai suka zo yi.
Yau na tashi da son gyara jikina don yanzu shagon matar nan yar uwar wacce tayi
min gyara a bauchi na karbi lambata can nake zuwa tayi min gyaran da nake so.
Tare da kanne na na tafi har da mummy amma tace kitso kawai take so nan samira
tazo ta samay mu tunda nace mata gamu wurin gyaran jiki tace gata nan zuwa itama
ayi da ita.
Angama ma mummy kitso ganin yaran zasu damay yasa sakina ta kaisu gidan ta su
zauna ta dawo mukaci gaba da hira.
Nan nake fada mata ina son zubar da cikin jiki na ido ta zaro min tace saboda may
madam niko a gani na da kibar abinki kwana nawa kin haife abinki safiya.
Wata mata da ta girmay muna tana jin mu tace mai zai sa ki zubar yar uwa idona
yayi kwalkwal ya kawo ruwa nace yanzu fa dana watan shi bakwai da haihuwa hajiya.
Shine suke son in bar cikin kuma inyi yaya da su su biyun don Allah tace ashe ba
a yaye shi ba ma lalai wata bakwai kan akwai wahala wallahi.
Yakai wata nawa cikin jikin naki nace yanzu wata biyu da kwanaki bai cika uku ba
cif tace ai mai sauki ne barin rubuta maki su kwaya sai ki saya ki sha mu gani idan
bai fita ba sai ki hada da alluran shi.
In haka yaki fitar dashi sai kin je an cire maki ke nan ta bude jakkata ta ciro
takarda da biro ta rubuta min nayi mata godiya na karba har mukayi musayan lamba da
ita a wurin.
Ban je gida ba sai dana biya na sayi maganin a wani babban chemist dake hanyan mu
na kwaso mummy da yaran gidan su samira muka dawo gida.
Kai aka wanke min sukayi min kitso sai dai ba kanana ba sai gyaran jiki da
sukayi min don jina nake na koma wata irin gaja dani rashin gyaran da ban samu
kwana biyu inyi.
Jin jikina nake yau kamar ba nawa ba sai dare Uncle ya dawo don suje site din
su dake sulaje yau a can store din su yake babba inda suke tara kaya indan an kawo
masu.
Idan yaje can ya dawo yakan gaji sosai don aikin wahala akeyi a wurin har shi
yakan taba aikin aje a dawo basu da hutu ranan.
Ko da yadawo ya gaji sosai wanka yayi yaci abinci ya kwanta nima ban dade ba na
samay shi a dakin har ya kwanta ko sai dai bayi barci ba.
Na shigo na rufe kofa ido ya tsura min daga inda yake kwance har na iso gare shi
yace yau wanan gyara haka sai ya mayar min dake wata irin yar yarinya under age.
Murmushi nayi na karasa hawa godan na kwanta nace under age haka kamar kumama
dani yace to be serious yau kin koma yarinya sosai murmushi nayi kawai ina gyara
kwanciya na.
Ranan bai barni ba sai da ya dan lalube ni muka gama muka sake wanka na kwanta
zuwa asuba sai zazzabi ya rufe ni kuma da kyat na tashi nayi sallah na kara
kwantawa.
Har ya gama shirin shi ban sani ba sai da zai fitane yake tayar dani zai fita
indan jikin ya matsa ki kirani mu koma asibiti tau kawai na iya ce mai na koma na
kwanta.
Yafita ya sauke yara makaranta ban fito ba sai kusan shabiyu koshi na fito in
samu dan ruwan liptop ne in sha.
Anan falo na zube na umarci Nura ta hado min ruwan liptop jin muryana yasa mummy
fitowa tana min yaya jikin , ?
Fuska a yamutse nace mummy da sauki take cewa ko jigilar gyaran jikin da nayi
jiya ne ya saukar min da zazzabi ciwon ne kawai ya dawo mummy.
Litop din ya taimaka min naji bakina ya koma min dan daidai har na sha lemu anebi
wanka na naje nayi dakina koda na fito wayana yana ruri a lokacin.
Na dauka da dan sauri kada ya katse uncle ne yake kirana a lokacin ina dauka
nace uncle yaya aiki shiku bai tsaya bani amsa ba sai tambayana yayi da yaya jikin
naki ?
Nace da sauki uncle kin ci abinci ya tambaya nace mai naci alhalin banci din ba
bani mummy yacd nace mommy tana dakin ta nima dakina nake kwance.
Ok sai ki sha magani kafin in dawo Allah ya sauka nace dashi amin ya kashe wayan
na wurga wayan saman godo naci gaba da shirina.
Bayan yadawo gida da yaran ya samu naji sauki sosai zaune ma nake da Aisha data
kwaso yara tabiyo tanan dubani da jiki mun da ita kafin ta wuce gidan ta.
A gida yayi magariba duk banda wani matsala komai zuwa tara kaina ta fara ciwo
kamar zai tsage min haka yasa dole ya fita ya samu min magani nasha.
Zazzabi sosai nayi da dare dole da safe muka nufi asibiti ban so zuwa ba amma ba
yanda zanyi dole naje aka dubani muka dawo gida.
A hanya ya matsa min may nake so ya saya min nace ban son komai sai masa mai zafi
idan zan samu dariya yayi yace aiki ko ya samay ni ni madam wani irin ciki kika
dauko wanan karon kuma ?
Haka mukayi ta yawo gidajen abincin hausawa ana muna kwantace sai da kyat muka
samu masa yayo min take away leda biyu muka juyu gida ina ji a mota yana ma hajitan
shi waya ta sa a turo muna da masa bana ya samu dan gargajiya a gidan shi.
Dariya tayi tace insha Allahu goben zata sa ai min za a samu wanda zai kawo min
in Allah ya yarda tace ya bani waya idan ina kusa muka gaisa tayi min yaya jiki har
muka iso ina magana dasu.
Ban tsaya falo ba dakina na nufa na aje jaka da maganin da aka bamu asibitin
irin ta masu lalurar mun ta masu ciki sai na saka a jakkana.
Ruwa na watsa ma jikina don in ji dadi nafito nayi sallah sai na dawo falo na
zauna masan naci shi sosai kusan na kusa cinye take away din.
Na sha ruwa nan muka zauna hira da mummy shiya dawo gida da yaran yau ma ya
zauna kusa dani yana wasa da Abba kamshin turare shi ya haddasa min wani irin
ciwon kai.
Gudu nayi na shige daki na kwanta sai kuma amai yazo min nan na amaye dan masan
danaci koda zai saura a cikina sai kadan.
Shine ya shigo yana tambayana a harasawan ya dawo ne kuma yanzu kai yace har ya
juya yace kin sha maganin ki kuwa nace ban kai gasha da na bari idan zan kwantane
tunda sunce yana da karfi.
Ina kika a je maganin yace min tare da kafe ni da idanuwan shi bako kiftawa nace
gayan nan cikin hand bag dina ina fadi ina mikewa zaune don nasan shan maganin
zanyi.
Sai damay yana cikin tona jakkan ya jawo wanan maganin da na sawo a chemist wanda
matar nan ta banj na zubar da ciki.
Jin shi shiru danayi yasani juyowa inga may yake yi a lokacin maganin na ganshi
rike dashi a hannun shi yana karanta wa.
Take naji gabana ya fadi a wurin juyowa yayi yana tambaya na wanan maganin may
Safiya ?
Magani na ne nace mashi yace ai nasan maganin ki ne na may ye na tambaya ?
Kaina na dukar kasa ban ce dashi uffan ba Safiya naji yace na dago kaina yace
cutana zaki yi komay ?
Shiru nayi na kasa magana sai naga ya fita da maganin a hannun shi take fuskan
shi ya juye ya koma wani irin zaki a gabana.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

8️⃣5️⃣8️⃣
🧕5️⃣8️⃣5️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


NOVEL DINA NA KUDI NE DON ALLAH DON ALLAH IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA DON
DON SHIGA HAKKIN WANKI DON GIRMAN ALLAH

Ke kuma mai fitar min da da novel nasan basai anje lahira ba ubangiji yazai daukan
min fasan akan ki don kin nuna baki da imani da tsoron Allah a fili.
Mai imani bai wanan halin ko yaya yana nuna tsoron Allah ba zance dake komai ba
amma zaki ga ni a rabon ki shi amana bibiya yake ta inda baki zata ba.
Jin dakin shiru bakajin komai sau karan nauran wutan dake aiki a dakin sai ko ni
da nake sauke numfashin wallah har wani zufa nake yi don tsoro da fargaba alokaci
daya.
Da kyat na yunkura na mike na sauke kafafuwa na daga saman gadona cikin karfin
hali na nufi dakin shi don babu kowa a falo gidan yayi wani tsit a lokacin.
Ganin kofan shi a bude ya tabbatar min yana gidan har wanan lokacin bai fita ba
ke nan da far gaba na tura kofan a hankali na shiga dakin.
Ya tsaye bakin window dakin dake kallon haraban gidan ya harde hannaye shi duka
biyu a saman kirjin shi kamar bai san na shigo dakin ba ya nuna min.
A hankali jikina a sanyaye na karasa inda yake tsaye har na iso gab dashi na sa
hannu na da nufin in rungumay shi ta baya ya juyo a zafafe cikin zafin rai ya
kwashe da wasu irin lafiyayun maru guda biyu masu kyau.
Sai da na kai kasa ban sani ba ya nuna ni da dan yatsan hannun shi yana fadin
ashe baki da mutunci baki da tausayi ban sani ba Safiya.
Ashe ke mutumiyar banzace nake zaune da ke ban sani ashe baki da tsoron Allah a
rayuwan ki ban taba zaton haka ba a gare ki ban taba ba Safiya.
Ashe daukan da nake maki ba hakana kika dauke ni ba ke may nayi maki da kike son
ki cuce ni haka da zafi may na rage ki dashi wanda na kasa baki kike son saka min
da wanan abin da kike shirin yi min.
Ni dai ina duke na rike kumci na sai hawayen da ba kuka nake fitar wa wani nabin
wani iri rike da kumatuna da yasha mahaukatan maru gare shi.
Kuma cikin maganan da yake fadi wani ma ban fahintar shi a lokacin wanda nake ji
kuma ta yaya zan fara bashi amsan su don suyi min yawa a lokacin.
Naji yace uban wa ya baki wanan magani a ina kika samo shi yau naji na tsane ki
nayi dana sanin auren ki dana nayi safiya tunda baki so na da karuwa banga dalilin
zama dake ba a rayuwa na.
Dago kai nayi na kalle shi karo na farko bayan marin da yayi min da hawaye na
shabe shabe a fuskana.
Mikewa nayi daga inda nake tsam ina shirin fita dakin wani tsawa ya daka min
yace dakata baki bani amsa na ba tukun .
Uban wa ya baki wanan maganin nace tare da nuno min maganin a hannu shi dan
kuturun yazo min nima a lokacin ban bashi amsa ba kawai na fice a dakin ba tare
dana kara juyowa gare shi ba.
Daki na koma na haye gado na dunkule a wuri daya take wani irin kuka yazo min a
lokaci daya mummy ne ta shigo dakin don taga fitowana daga dakin shi ita da Nura
suna magana a falo.
Hajiya lafiya may ke faruwa ko jikin naki ne ya matsa maki haka take tambayana a
jere lokaci daya sai kuka nake ban iya magana ba.
Banko kofar dakin da yayi da karfi shiya dakatar da mommy dake tsaye a kaina
tana jera min tambayoyin ta a lokacin.
Ganin mommy bai hanashi fadin abin da yazo fada min ba yace ni zaki mayar
mutumin banza ina magana ki wani fitowa ki barni yau sai kin fada min wanda ya baki
maganin nan ko ki fice ki bar min gida na don ba zan zauna da macen da zata haince
ni ba.
Da sauri mommy tace subbahanallahi Alhaji mai yayi zafi haka tsakanin ku har
kake fadin wanan maganan haka ?
Kallon mommy yayi cikin bacin rai kamar zai mata magana kuma ya fasa nasan
zuciya ce ta kawo mashi maiyi a banza balle yau ga dalili.
Ya juya gareni yace ke har kin isa baki san halina bane wallahi da bakiyi min
hakan ba ban cutan na tare da ni shi kuma Allah bai yarda ya cuce ni.
Don Allah Alhaji kayi hakkuri ku bi abin sannu niko ina saman gado na dunkule sai
kuka nake yi ya juya wirin mommy yana fadin mummy ashe duk ciwon da yarinyar nan
keyi ita taja wa kan ta.
Da sauri mommy ta mayar da han kalin ta gare shi tace ita taja wankanta garin
yaya haka ya faru kuma hajiya ?.
Gata nan shi nake tambayan ta tana son raina min wayau yanzu bayan Allah ya tona
mata asiri wai mummy kin san zubar da ciki take kokarin yi yanzu na kamata.
Innalillahi safiya baki da hankali ne may yayi zafi haka cikin da kowa ke farin
ciki da samun shi zaki ce kuma zaki fitar haba haka baiyi kyau ba wallahi.
Ni dai kukana nake ban saurare su ba don Allah Alhaji kayi hakkuri tunda ta gane
kuren ta ai mata afuwan kurciyane ya kai ta ga hakan da batayi ba idan ta sani.
Kurciya ina kurciyan yake anan tunda har tasan ta zubar da ciki ta cuce ni ga
abinda nake so don tana munafuka wawiya.
Zagin yayi min yawa uncle na iya furtawa da karfi a cikin kuka ya watsa min
harara yana fadin ok har ma kina da bakin magana zagi yayi maki yawa ko ?
Alhaji kayi hakkuri don Allah ka bar zancen nan haka na tunda ta gane kuren ta
yace sai fa ta fada min a inda ta samo wanan maganin zan barta mommy yace.
Zuwan yaya Saadu da ya kira ne ya katse shi ya fita falo wirin shi ya samay shi
nan yake fada mashi abinda ke faruwa a tsakanin cikin bacin rai.
Mommy ce ta fito dakina a lokacin goye da Abba bayan ta da yake barci ta karaso
inda suke tana gaisawa da yaya Saadu daya shigo.
Yaya saadu yace mummy abinda safiya take shirin yi ke nan ashe shiya tare da
fadin ina mommy zata san mugun nufita tunda batason kowa ya sani nima Allah ne ya
nuna min tun batayi min sawalwalin cikin ba.
Ka fada mata idan bata fada min wanda ya bata wanan maganin ba sai ta barmin gida
na yau don ban zama da mace da bata sona da karuwa .
Yi hakkuri yallabai ina Safiyan take yana tambayan mommy tace tana nan dakin ta
yace mommy ai min magana da ita don Allah.
Nan mommy ta juya ta shiga wurin ta fada min ga yaya Saadu yana magana dani
azuciyar ta kuma sai addua take Allah dai yasa ba samira bace don rawan kan samira
na da yawa.
Sai can na fito saye da hijjabin sallah na har kasa ina yiwa yaya saadu sannu da
zuwa cikin miryan na da ya dishe saboda kuka da ciwo da fargaba.
Ina zama Uncle yana bina da harara yaya saadu ne yace safiya yaya haka kuma ya
faru cikin lalama yake min magana wanda shi uncle din bai so haka ba a gare shi so
yayi ya balbala ni da bala,i a lokacin.
Sai kuma yaji yana min magana may kama da lalashi yace may ya kawo haka safiya
haihuwan ne baki so ko tsoro kike ji ne ?
Haushine ya kama uncle yace kaga malam ba lalashinta na kiraka kayi ba ta fada
muna inda ta samo maganin nan in ba haka ba bata zama min gida.
Na dago cikin zafin rai nace samay idan na bar maka gidan ina dai da gidan ubana
ko sai kuma idan ginan da kai muna zaka sa a rushe ka mayar muna da namu.
Tashi yayi kamar kububuwa yayo kaina yaya saadu ya tare shi yana fadin bari mubi
a hankali yallabai abin bai kai haka ai zata fadi nasan halin safiya.
Yace amma kana jin har ta samu bakin fada min bakar magana ko da mamaki yake
kallona ni kuma cikin zafin rai da hasala nace.
Dole in fada maka kana ta magana in bar maka gida, gida kan tunda ba anan aka
haife ni ba ai nasan ba gidan ubana bane sai in bari din sai may.
Safiya ashe haka kike inji yaya saadu nace yaya abin yayi min yawa ne wallahi
daga magana sai ya wanke ni da mari kawai.
Mari kinyi laife mai muni ne safiya dole ya mare ki ko nine abinda zanyi sai yafi
wanan da yayi maki ai don may ba zaki tsaya kuyi magana ta fahinta ba kin tsaya
garda yace ki fada mashi inda kika samo magani kin tsaya kina ja.
Wai may ma zai sa ki zubar da cikin ne safiya may cikin ya tare maki da kike son
zubarwa ne da baki iya hakkuri ki haife shi.
Yaya maganin nan ya dade a cikin jakkata wallahi ba yanzu na saye shi ba da yake
nufi ni kuma ba wanda ya bani dama na san shi tuntuni sai na sayo da nake ganin
kamar ciki ke gare ni a baya.
Ba yanzun na saye shi ba yaya karya take wallahi yanzu ta sayo shi take sha don
cikin ya bare to bari kiji ni ba dan rayuwa kawai na kawo ki gidana ba.
Don raya sunnan ma,aiki na kawo ki mu hayayafa mu cika sunna mai karfi ba a
haihuwa ke aka haife ki yana fadi kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login