Showing 6001 words to 9000 words out of 258256 words

Chapter 3 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

hannun shi mukai dakin su.
Shima idan yar dahuwar shi ya samo ni zai nema na dafa mai kuma ko ya bani bana
karba nace ya bar shi, sai idan ya zare min ido zan karba naci ko na bawa kan ne
na suci.
Tun wanan fadan da akayi gidsn mu ummin mu ta dan samu baki idan ana mata wanin
abin cin fuska zata zage ta mayar da martani kamar yadda akai mata ba dadi din
itama.
Abin dake ci mun rai shine irin yadda gamu da yawa a gidan mu amma kowa a ware
yake ba mai hurda da wanin shi dan dama tsakanin yaran dakin mama dana Inna akwai
dan shiri a tsakanin su.
Nice dai babu halin idan suna zaune ko suna wanin abin da ya shafe yara mata nace
zanzo wurin yanzu zakaji sun fara hattarana.
Suna fadin ke kuma may kika zo yi nan munafuka kawai sai wata tace muguwa mai
irin halin uwar ta kawai in ba gulma ba may kika zo saurare nan.
Dole zan bar wurin don zagi da hattara irin haka yasa ko suna abin su bana shiga
shirgin su ina daki da ummi na ko ina wani aikin a waje sai dai abinka da yaro
inayi ina sauraren su sai na manta na saka baki wata rana su kyale ni wata rana
kuma nasha ba dadi garesu.
In kaji dariya na ko farin cikina muna tare da kanne na ko kuma na fita zuwa
makaranta ne.
Idan baba ya shigo yaga bana cikin su yanzu zai fara fada dani wai ina tsabbare
kaina a cikin yan uwana.
Sai kaji Inna tace mugun hali ya ci may idan batai hakan ba ko uwarta baka ganin
komai nata a makidance takeyi shi don dai kawai duniya ta zage mu.
Ace muna gallaza mata ita da uwarta a gidan kasan mutum baida gadon ka amma yana
da na maganan ka yanzu.
Sai kaji baba ya amsa da naga alama ai an koya mata halin tsiya ta iya itama.
To ba dole ba kullun suna daki ana mata hudubar tsiya a kai dabiar da ba zai
amfane ka ba ko yau tana tsabbare sun hada kai da uwar ta a daki suna wance tayi
min abu kaza don may bazata tashi da mugun hali ba kuwa ?
Abin yana ban mamaki don sai inga ai komai a baiyyane yake ai a gidan ni dai a
iya sani wani fitina bai tasowa ace da Safiya a cikin sa.
Ko wani ya kawo kara daga waje yace ai Safiya tai mun wani abin suko ko yaushe
cikin sallama mashi ake ana kawo karan su gun shi.
Sai dai abin mamaki wanan bai sa yayyena maza su kini ba a gidan namu don su
basu matsa min kuma ba su yarda ai min sheri a gaban su yanzu zasu ce zasu daki
yarinya idan tai masu tsiya tun dai yaya sani.
Kuma duk wanan abin idan sun dan samo kudin su gun Ummina zasu nufo dashi ta
baye masu har ya kare.
Da haka har ummi ke dan samu tana basu shawaran abinda zasu yi wanda zai amfane
su a rayuwan su, sai kuma iyayyen nasu suka koma cewa.
Wani sallon yaudara ne don ta raba su da yayan su ummi ta dauko sukai mata ahir
da yaran su shikan yaya sani da ya samu labari tun a nan yau zaune tsakar gida yana
fadin.
Oho wai ni za aiwa yau don a raba ni da mai taimaka min a dinga kwace min kudi
to ban yarda ba babu wanda zai hanani bawa maman safiya a jiyan kudi na a gidan
nan.
Ke mama da kike fadin haka ba nan Nura ya sayo akuya ba ku kai masa sheri aka
sayar da akuyan akace mai ya bata.
Cikin tsawa mama tace dashi kai kada ka kawo min diban albarka idan kaje kayo
shaye shayen kane kake son saukewa a kaina bazaka sha da dadi ba yanzu na saka yara
na suyi maka tsinanen duka a gidan nan.
Wuf daya yayi ya yanko reshen darbejiyan dake baya gidan mu yana fadin yau naga
shegen dan ki daya isa ya tabani a gidan nan idan ba a kwashi gawan shi ba shege
nake.
Yau kuwa zan gwada maki halin mashayan da kika kira min aiko yai cikin su a kofan
dakin ta da take tsaye da diyan ta a take suka watse.
Suna rige rigen shiga daki wani na ture wani daga kofan dakin wurin shiga dakin
don yai masu mai ka uwa da wabi baki daya.
Ashe fadan bai kare ba sai ga Inna ta na cewa idan har yaron na yana shaye shaye
ke ko diyan ki barayin kororo ne da karuwai, waye bai san abin da suke a gari ba
har akuyan da kike fadin an sace dake da diyan ki kuka sace shi ai.
Nan fada ya kaure tsakanin ranan dai gidan mu babu dadi tonon asiri zalla suka
dinga yiwa junan su har abin dake a boye saida kowa yaji shi gare su.
Baba na kasuwa dole aka kirashi shi yazo ya kashe wanan wutar fitinar da ya ruru
a gidan don gaba daya yaya Sani ya haukace masu a gidan.
Iyakarmu kallo da saure sai washe gari da baba ya kira sulhu da safe kuma suka so
su dora laifin gun ummi na mai farin jini a gare su.
A nan ma yaya Sani baiyi shiru ba yace may ye laifin ta a ciki kudi dai ne har
gobe ko kaya ita zanbawa a jiya ni babu ruwa na da zancen kishin ku.
Dole inna tana ji tana gani suka saka mashi ido don ya riga da ya kangare ba mai
iya lankwasa shi a halin yanzu.
Idan ya shigo gida har da gaiyya yake jan ummi na da hira a cewan shi haushin
mama yake ji don itace ke kulla duk wani makirci a gidan.
Ita ko Inna bata tsayawa saurare sai ta hau ta zauna a kai daga baya kuma mama ta
zamay jikin ta ta nuna bada ita akayi zancen ba ta bar Inna a ciki.
Mu dai a gun mu har gobe gaba dayan su a yan uwa muka dauke su ba mu banbanta a
tsakanin mu dukkan su a yan uwa muke daukan su.
Sai dai su a gun su ba wani canji a gare mu dasu har gobe halin yana nan na yan
ubanci da suke nuna muna a gidan.
Mun zama su shanun ware ko bare da suke kyankyamin mu daga cikin su suna bakin
ciki su bude ido su ga dan dakin mu na wani abin ci gaban rayuwa yanzu sheri zai
tashi a tsakani sai anga bayan abin an durkusa.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON, , , , , , , ,


3️⃣🧕🏿


FREE PAGE, , ,


SEENABU MAKAWA, , ,

NA ROKE KI DAN ALLAH DON SON MANZON RAHAMA IDAN DA ZUCIYA BIYU ZAKI SHIGO GROUP
DIN KADA KI SHIGA DON ALLAH DON BAZAN YAFE MAKI BA WANDA KIKA TURAWA HAKKIN YANA
AKAN KI YAR UWA DON ALLAH KI HAKKURI DA DAUKAN HAKKI AKAN NOVEL DON BA A YAFE BA
ONLINE NOVEL NE KIN SANI BA PUBLISH NOVEL BANE DA KI KE FADI KIN BIYA NE DON ALLAH
MU SAHIRCE WA JUNA AKAN HAKA YAR UWA KAN ABINDUNIYA DAFATAN ZAKI KU FAHINCE NI.


Yau alhamis bamu shiga islamiya don haka na ke son zuwa ziyara gidan yan uwan
mahaifiyar mu dake a cikin gari.
Zaune nake ina kwaliya a kofan dakin mu yayin da mutane gidan mu ke ta aiyu kan
su na yau da kullu a cikin su har da ummi na wacce ke wanke kofi.
Sallama aka shigo dashi gidan dashi shi ne ya dauki hankalin kowa a gidan baki
daya tare da amsawa.
A, a mutanen lagos yau she agarin abinda su maman mu ke fada ke nan mu yara muka
shiga sannu da zuwa.
Ta dan tsaya a tsakar gida suna gaisawa sama sama da mutanen gidan da ga nan ta
kwasa tai dakin mama,
Daya bayan daya ake shiga gaida ita tana amsawa don sanin muhinmanci ta ga
iyayye mu baki daya.
Gwago kulu ke nan kauna ne ga mama kuma yar uwa ga mahaifin mu don mama da
mahaifin mu yan uwane dukkan su auren gida ne sukayi irin matar fari zabin iyayye
din nan.
Haka yasa mama ke shimfida mulkin ta yadda taso a cikin gidan daga ita har yaran
ta ko magana ake a gidan wanda ya shafi gida zakiji mama tace mu din kujera ne dole
a bi mu.
Don da mijina aka samay ni ko anki ko an so dole ne a gan mu a gidan babu yadda
za yi damu dan mu yandagi ne.
Watarana idan tana irin wannan habaicin Inna takan biye mata suyi tayi sai sun
gaji har ta kan ce ban ga macen da zato tace zata shifida min doka ba a gida na.
Sai dai duk wannan haukan ga may wayau da hankali yasan Inna ce ke shimfida
mulkin ta a gidan don baba a can hankalin shi yafi karkata.
Ni dai nakan ce tsoro ne don wani lokaci zaka ga ya juya gun wata da zaran inna
taga haka yau zata birkice mashi da masifan dare daban na rana daban saiya dawo a
kan ta.
Duk wani dan uwan mahaifin mu da zai za gidan wirin mama zai yadda zangon shi ba
zai tafi wani daki ba sai in wani dalili ya kawo mai shi.
Wannan abin yana kona wa inna rai don ita mace ce mai son taga komai ita ne a
kan gaba a gidan namu.
Saida na kanmala kwaliyana na saka hijjab dina na karasa kofan mama ina fadin
sannu da zuwa gwago alokacin sun hade kai da mama suna magana a hankali kasancewan
su biyu ne a dakin ki.
Cikin dan hanzari ta amsa min da yawwa na juya zan tafi sai take cewa wa nake
gani kamar sai tai shiru can tace ba yar wurin Rabi bane ?
Mama tace itace tace, mana tace ikon Allah girman dan mutum baida wuya har yaushe
yaushe aka haifi yarinya nan diba yanzu yadda takai da girma.
Sai naji mama tace ta biyo tsawon kafan uwar tane kisan Rabi ba baya ba wurin
tsawo shine suka kwaso ai duk haka yaran suke in kin gansu.
Nidai na tafi ba abina ban tsaya jin sauran abinda zasu fada ba don dai zancen
bai kare ba na bar su akai.
Dariya naji sun kwashe dashi wanda nasan wani sheri aka fada wanda yai dadi har
sukayi hakan .
Mu Huda muka fita da kannena gidan gwagon mahaifiyar mu muka fara zuwa inda muka
samu taro na arziki ta rasa ida zata saka mu.
Haka mu ke gani idan munje gun ta muna samun taro yadda ya kamata sabanin dagin
mahaifin mu, wanda basu ma san da zaman mu ba nake gani.
A binci ta shiga girka wa don idan muje wuni muke a gidan ta, nafito na kama mata
aiki yadda ya kama ta har muka kan mala yin komai.
Abinda bamu saba ba gidan mu an cika muna kwano da shinkfa da mai da yaji sai ci
muke yi hannu baka hannu akushi.
Ga zobo mai sayi data sayo muna mu sha dashi mun kai kat na kwashe kayan da
mukai aiki da amfani dasu da wanda mukaci abin ci akin sa.
Na gyara mata gida sai nace da ita zamu mu gaida su mama watau diyan ta ke nan
dake aure a cikin uguwa.
Tace kada mu dade don mu koma gida da wuri mun tafi inda can ma muka samu taro
yadda ya kama ta sun bamu alheri su man shafi da sabulu da omo da dan kudi muna ta
murna mun samu kyau ta .
Gwago ma tai muna abin arziki muka dawo gida bayan sallah la, asar cike da zudin
kyautan bajin ta da muka samu.
Muna tajin dadi muka nuna wa ummi alherin da tan uwanta suka kai muna ta sani
tare da fadin shine abin dayasa bani son kuna zuwa gidan su don dawai niya kuke kai
masu.
Kani yai caraf yace ummi cewa sukayi fa mu dinga zuwa ko yaushe kuma kikece
damu kada mu koma abamu .
Gaba daya dariya muka sa mai ummi tace damu tare da dubana nida nake da wayo a
cikin su yawan zuwa zai sa su gaji daku ne ku zauna matsayin da Allah aje ku Allah
zai dube mu.
Jikina yai sanyi don na fahinci may ummi take nufi din a sanyaye na ce in sha
Allahu ummi baza kara zuwa mu kai masu nauyi ba haka.
Dan abinda muka samu ummi ta ware min wani abu acikin sa waina kara jari dashi na
sana, a na da nakeyi kada mu kashe a baki daya.
Wanan kudin shine sillar da har takai mun da samun sauki a dakin mu don a
hankali na fara sarrafa kudin biyar na kamowa goma gama na zama ashirin ashirin ya
koma wazo har zuwa sama.
Idan baka raina sana, a tau watarana sai ya koma maka babba don tun ina dan
madara har na koma ina soya ruwa ana saye a gida.
Sai gashi har nawaje suna shigowa saye na hada da aya da sauran makulasa sai
sanaa ya koma na ummi na.
Sannu sannu ina sana,ar har muka koma mangyada da sauran abin amfani kudi na
shigo muna.
Sai hassada da kyashi ya shigo a cikin wa yan gidan mu nan kuma bamu da sauran
shakat gare su zasu ce damu ganin muna dan sana,an dake kawo mu kudi ya muke son yi
masu gani gani.
Sai suka da habaici ya tashi har zance yakai gun baba na magana kadan yanzu zai
yo cikin ummi da zagi yace wai mutane suna shigo mai gida don su din ga lekan may
asirin gida suna fita waje suna fadi.
Nan mama ta turza don kan taki yarda da zancen baba na wanga karon ta ko hankace
mashi da fitina tana cewa ai da takoma in irin halin da ta fito gara ta hankura
dashi ta tafi inda ake son cigaban ta yafi mata don ta ganne cigaban ta akewa
hassada bakomai ba.
Inda watane ke wanan sana, ar aiba za hana ba amma don anga tana samu za ai mata
bakin ciki ga sana,an ta, kowa na dan sana,an shi cikin gida bai yi magana ba,
sai nata ne za ia wa bakin ciki.
Da haka zancen ya mutu karshe mama ta ce ya kyale ta taita sana an ta tunda
kowa na saman sanaar ashi badon aina tasa ba dole ta kyale ummi ta ci gaba da sana,
an ta tana na kallo ba yarda zata yi a gidan.
Wanan ke nan ya wuce saura wani kama don ummi ta kyatare wanan karon daga kaidin
ta.
Wanan abin da akeyi ina yar shekara goma sha uku da haihuwa amma duk idon gidan
mu na ga kaina gaba dayan su kamai yan yazu ace safiya ce.
Koban ji ban gani ba don dai kawai ai min fada suji dadi yanzo zasu jawo abinda
za ai min fadi din .
Duk wani aiki aike yi mai dadi da akasin sa duk ni zan yi amma duk wanan ban
tsira akan shi ba don cewa suke wai lalaci da raggaci yai min yawa.
A haka jebawan mu shiga secondary yafito inda naci makarantan kwana aiko take yan
gidan mu suka nuna bakin cikin su ka zancen.
Suke cewa makaratan kwana ko lalacewa may zaki koyo banda lalacewa a makarantan
kwana bokon diya mace ko lalacewa.
Kai komai sun fada akan wanan zuwa karatun nawa karshe dai baba sha zuga sai cewa
yayi abar zancen karatu don shi bai ga amfanin yin karatu ga ya mace ba.
Ina ji ina gani aka watsar da zancen karatu na ganin da gaske baba keyi na
sulale jiki na tafi wurin gwago na fada mata komai.
Batai sanyi ga gwiwa ba ta sami babana a kasuwa don magana bai yi a gida nan dai
gwago ta shawo kan shi har ya yarda amma da sharadin .
Baba hannun shi a ciki ko kwadalan shi ciki gwago tace taji ta dauka akwai Allah
zakawo mafita.
Amma yace ba zai yarda da batun zuwa makarantan kwana ba gwago tace taji zasu
samo jeka ka dawo na tafi.
Wannan shine dalilin zuwa na makaranta da nayi mutane gidan mu dai sun ga ina
shirin ba su san komai ba.
Ranan da zan fara zuwa hankalin kowa a gidan ya tashi don sai suke zargin
mahaifin mu ne yai min ko mai.
Nan ko ina ta saka shi a gaba da cewa munafucin banza da wofi idan an tanbaye
shi kudin yace bai dashi amma ya dau ki yar gwal ya saka a makaranta don ran uwar
ta yai dadi.
Ba dole ba yana gudun bacin ran uwar ta kada ta hana shi kwana da ita ya rasa
jin dadin shi.
Da abin ya ishi baba yai ratsuwa har ya gaji shi ba dasanin shi bane baiba ma
san wanda yai samo min makaranta ba amma nasu yarda ba.
Sai cewa yayi ya biya min din suda yake wa dayan su lalurori fa saiko fada dashi
da inna har takai ga yin ya ji a gidan.
Yaya sani yace safiya ki shirya da kaina zan kaiki in ga wanda ya isa ya hana ki
zuwa na gane yan bakin ciki ne mutanen gidan nan.
Da yaya sani muka tafi makaranta sai da yaga komai ya kamala ya dawo gida.
Tun wanan lokacin aiki ya rage man agidan namu saboda ban da lokacin zama a gida
har su ganni suce in ma su aikin.
Sannu a hankali girma ya shi gana yanzu na fara ganewa bawai son ummi ne
mahaifin mu ba yayi ba kawai dai shakun matan shine yake ji.
Na gane hakane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login