Showing 120001 words to 123000 words out of 258256 words

Chapter 41 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

kut na kirasu gefe muka kebe dasu.
Nan na fara jero masu bukata na suna saurare na karshe dai yaya Sani ya nuna
baruwan shi ga maganan sai da abokin ya kwantar mashi da hankali ya yarda.
Akan zasu je su samu mutumin nan da yai mata ciki aji hadin ta dashi sai dai
zasu biya wirin kanin mahaifin mu don a samu wani babba ya tsaya muna ga maganan.
Sun yarda da hakan na shiga gida suka wuce wurin dan uwan baba sun mai bayani sai
yace wanan maganan fa maganan kudi ne.
Abokin yaya sani yace adai tun kare shi aji don aiwa abinda zata haifa din gata
baba baiki ta nasu ba ya tashi suka samay shi a shagon shi na kasuwa ya na tsaka da
kasuwancin shi.
Sun kira shigefe da suka fito mai da maganan sai cewa yayi shi sam bai san
maganan ba suka ce to za a zauna gaban hukuma.
Sai cewa yayi aje mana abu na kudi haka suka dawo da labari babu dadi daga gare
su bayan sun gama magana nace haka yace suka ce eh.
Nace a hadu din babu komai nasan dai dan kudin da suke hannuna suna isana kashe
maganan kauye.
Don haka washe gari muka maka shi kotu tare da ganin mai shari a saadatun tai
mashi bayanin komai da zamu tafi na kawo hamsi na bashi nace ga goro.
Haba abin nema ya samu aiko take ya aika yana neman shi washe gari za a zauna
kotu bai ji wani tsoro ba don yasan dubu ashirin na raba su da alkali.
Ya rigamu isa kotun don yaga alkali nan ya cin na mai dubu ashirin din ya karbe
da farko sulhu ya kiramu yi don dani aka je amma nace ban san hakaba nan na dan
turza har ina cewa idan sharian baiyi anan zamu tafi abuja.
Kajini fa sai alkalin ya rude nace idan mun tafi can ai akwai awon da za a yi a
tabbatar idan na shi ne koba nashi ba.
Sai ga Isah mai mangyada na share gumi a fuskan shi yana cewa ai maganan bai kai
can ba ciki dai nawane amma kuma ai ba wurina kadai take zuwa ba.
Saadatu tai saurin rantsewa akan bata taba zuwa wurin wani ba in ba shi ba nace
tun da bai yarda ba abari kawai aje birni a hadu a can .
Daga alkali har mutumin suka fara cewa haba ki kwantar da hankali abi maganan
sannu a hankali a fahinci juna.
Kowan su na gudun zuwa gaba don ba zasu ji dadi ba sai suka ce mu fito waje suyi
shara muka fito wajen muka basu wuri.
Kiran abikin yaya Sani sukayi suna tambayan shi wai yanzu may na zama ne sun ga
na waye da yawa idona ya bude sai yace masu kai yanzu fa ta wuce sanin ku.
Don wani hamshaki daga Abuja ne yazo neman auren ta sukace gaskiya kan na ganta
haka idon ta ya bude da yawa.
Sun fito suka kiramu ankan ya yarda zai karbi cikin nace ita fa to sai ya fara
shafan gumi alkali dai ya tillasta mai akan idan ta haihu za a daura masu aure.
Muka samu madafa akan ta sai da naji ta sauke wani ajiyan zuciya don a kusa da
ita muke da muka fito yana yi min magana ban tsaya ba.
Muka dawo gida sai da dare na muka samu baba ni da yaya Sani mukai mashi bayani
halin da ake ciki kan Saadatu din.
Bai iya magana ba sai hawayen da yake yi kawai muna bashi hakkuri har ya daina
mun fita ne ya kira su mama gaba dayan su yana masu bayani abinda muka zo mashi
dashi.
Nan inna ta tsaya tai tagumi ta rasa abinda zata ce sai kuka aka bata hakkuri
haka dai suka watse ni har na kwanta sai ga inna dakin mu.
Ina ganin ta na mike zaune don ban san da may tazo ba wuri ta samu takai zaune
sannan ta soma maga Safiya wurin ki nazo nace to inna gabana yana faduwa.
Ban san abinda zance maki ba ga kokarin da kikayi ga yar uwar ki indan bake ba da
haka zama zauna da wanan bakin cikin a rayuwan mu.
Don Allah kuyi ta hakkuri damu karkubi ta namu kishin mu ba karewa zaiyi ba sai
ranan da muka kare nai murmushi nace inna kudai yi hakkuri da junan ku.
Ummina tana zaune batace muna komai ba har inna ta fita tace munafuka kamar da
gaske nayau ne kawai baikai ciki ba don bata san kuya ba har zatazo wai wani
godiya.
Nace kai ummi baku dai barin halin ku wanda kukeyi a kan shi ma yana fama da kan
shi bai son fitina wallahi.
Ummi tace tadai bari ita da ta dauki duniya da fadi yar bakin cikin mata kawai na
kwanta ina mata dariya nace kishin ku dai bai karewa.

Kwana goma na kara jikin baba yayi sauki sosai na fara shirin komawa don kullun
su yan biyu waya suke suna tambaya na yaushe zan dawo sai ince masu gobe.
Damuwan da sukeyi yasa nace zan koma nan muka fara shirin tsaraba abin da nasan
suna so shi muka saya zan je masu dashi tsaraba.
Sai da na shirya na sa ranan tafiya mu nan yaya sani ya zake dama yana damuna
yaushe zamu tafi sai gashi nace mai ranan asabar mai zuwa zamu wuce.
Ranan ina zaune na dawo sallaman uwayena ta famnin ummi na ina cire kayan jikina
dana sa waya na yai kara ina dauka naga yaya Saadune.
Da murna na na dauki wayan nan na zauna a bakin gadon ummi nace yaya ina kashiga
nayi kiran wayan ka yafi a kirga baka dauka ba.
Yace kedai bari wasa wasa nayi tafiya zuwa ghana sai gani har togo shiyasa ba a
samu na ko an kirani.
Nai mashi sannu da zuwa yake ce min yanzu ma yazo ne matar shi zata haihu shine
yadawo gida yace kin san halin gwagon ki.
Idan bani nan ba komai zasu yi ba shiyasa na dawo gida don ayi komai a gabana
nace Yaya ashe zamu samu karuwa kwanan nan.
Nace idan na dawo lagos zan zo inda kuke yace zakizo lagos ne nace ai yayanan
nake yanzu.
Yanzuma nazo gidanane baba baida lafiya shine nazo amma ya samu lafiya yace
subbahanallahi may ya samu baban ?
Nace ya samu sauki ai amma yaji jiki sosai wallahi amma yanzu yana samun lafiya
yace a gaida mashi baba insha Allahu zai shigo kafin ya koma.
Yace yaya labari safiya ina fatan komai na tafiya daidai ko nayi murmushi nace
yaya komai lafiya sai dai mun hadu kawai yace akwai labari kenan ?
Dariya nayi nace ya gaida matar shi yace zataji zan fada mata kin ce zaki zo nace
insha Allahu zan zo.
Mukai sallama na kashe wayan ina jin dadi a raina na yaushe rabo ina fada ma ummi
ya na gaishe su wai matar shi nada ciki zata haihu.
Addu a tai masu ta na Allah ya raba lafiya nace amin muka dan taba hira da ummi
akan matsalolin duniya na gidan mu dana waje.
Sai ranan jumma a inna tasan da tafiyan mu duk ta rude sai ta kira yayan a daki
tana ce mashi yanzu kai don kasada binta zakayi baka san mutum ba baka san sanaar
shi ba.
Baka gudun aje a yanke ma kai ko a sayar dakai kaida ganin wanan mutumin kasan
kudin shi ba na kai sake bane kuma gashi yaro ina zai samo kudi irin haka ?
Da sauri ya katse uwar da cewa ke inna zaki fara ko zaki fara halin ki yanzu duk
halarcin da yarinyan nan tai maki baki gani ba zaki nemi wani sheri ki lakaka mata.
To ki iya bakin kin ki kada ki je ki zauna da wani kiyishi ya fita muji kunya
yarinya na bin mu da arziki ke kina binta da sheri Saadatu dake zaune tace fada
mata dai ko zata ji .
Yace nidai zan bita ki min addua Allah yasa karshen zaman banza ne yazo in samu
abin yi acan in dawo maki da arziki sai lokacin tace to Allah ya sa hakan ne kadai
kula da kan ka don Allah.
Ya fito nikan shiri nakeyi na zabi kaya cikin wanda nazo dashi naba Saadatu na
raraba masu kayana wanda naje lagos dashi don yanzu ban iya sa su naba mutanen
gidan mu.
Da dare driver ya iso don sammako zamuyi tun da safe zamu bar garin ranan mun
raba dare da ummi muna hira sai wani lokaci muka kwanta tun da safe muka kama haya
nabar su da kewan mu muma muna kewan rabuwa dasu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , ,


4️⃣3️⃣4️⃣
4️⃣
🧕🏿 3️⃣3️⃣4️⃣


YAN UWA BARKAN MU DA SALLAH DA FATAN MUN WUNI LAFIYA YAYA AIKI YAYA SHAN KAMSHI
ALLAH YA MAIMAITA MUNA AMIN.


Mun yi nisa ga tafiya yaya Sani da driver nata hira ina naya ina karatu a wayana
har muka kai wani gari driver yace zai tsaya yasai ma iyalin shi abu.
Suka fita suka barni a cikin motan nan na dago kaina ina kalle kallen garin
mutane nata hada hadan su.
Nace a raina kowa yanzu wirin nan da abinda ke damun zuciyar shi atake na tuno a
yadda na bar gidan mu don dai na tabbatar da inna kiran da taiwa yaya Sani jiya da
dare magana ce a kaina.
Hango su nayi sun riko ledoji ga abin saya inkai tsaraba babu hali don nasan
jirgi zanbi in koma kamar yadda nazo.
Suka dawo suka shiga mota muka fara hanya sai lokacin nace wa yaya Sani mutanen
gida dai na tuna.
Yace ai baba ya samu lafiya yanzu baki ga har kofan gida ya rakomu ba nasan
tunda yace afito mai da tabarma anan zai zauna.
Nace ni ban san lokacin da rikicin gidan mu zai kare ba kullun ace sai
makwabbata sun shigo rabon fada a gidan mu.
Yace ai ba laifin kowa bane sai inna kin ga ana shigowa raba mama da ummi fada
inma har matsala ya afku a tsakani su ba mai tsawo bane kowa ya bari.
Amma ita inna da kowa tana yi a gida har baba har yaran gida kin ma san abinda ta
fada min ne jiya kan tafiyan nan namu ?
Sai nace inna dai nidai Allah yasa su bari yace to amin amma da wuya su bari din
don ko kowa ya bari na tabbatar inna ba zata bari ba.
Sai dai yadda kuke hakkuri kuna take halinta kucigaba dayi har Allah ya kawo muna
dauki ajiyan zuciya nayi nace Allah ya kyau ta.
Karfe biyu saura muka shiga Abuja nan yaya ya dinga baza ido wurin kallo nima
din ba a barni a baya ba don kallon abin mamaki da aljabi nakeyi don garin yadda
yake komai a tsare.
Direct gidan Sulaiman muka nufa don daddy ya koma lagos ko tun satin da mukazo
dashi sulaiman din ne ya fito ciki bayan mun shiga mun zauna a wani irin yanayi.
Da ganin sa baijin dadin jikin shi sai dai yana dauriya irin na maza cikin karfin
hali yana muna sannu da hanya.
Mun gaida shi a cikin ladabi da biyayya ya samu wuri shima ya zauna yana kara
yiwa yaya sani yaya hanya yaya sani daketa washe baki ya amsa da lafiya.
Ya tambayi jikin baba muka amsa mai da sauki sosai tun wanan maganan naja bakina
nai shiru suke hira sama sama yayin da mai aikin shi ke ta faman jera abinci wanda
nasan don zuwan mu aka girka shi.
Driven da muka zo dashi ne yashigo falon yake gaishe shi ya amsa mai cikin dakiya
irin na masu gida da yaran su yake tambayan shi yaya hanya ?
Ya amsa mai Alhamdullahi ya mike zai fice sai sulaiman din yace kada kai nisa don
four zaka kai madam airport zata tafi lagos yau.
Sai lokacin na sauke ajiyan zuciya na dan dago na saci kallon shi ban san shima
kallon nawa yake yi ba sai ya dan murmusa yace ga abinci can an shirya maku
bissimillah ko.
Dagani har yaya Sani ba wanda yake da alaman motsawa sai naji yace barin dan fita
na baku wuri kunji dadin sakewa sai dai ba dadewa zanyi ba zan dawo.
Ya mike ya fita ya barmu nan sai lokacin na dago na kalli yaya sani nace yaya
kaci abinci gashi can saman table anjera.
Ya juyo yace kefa nace a a yaya ban jin cin komai yace may kikaci tun fa karin
safe da mukayi gida ne a cikin ki nace yaya ban iya ci ne gaskiya.
Mikewa nayi shima ya tashi ya bini zama nayi ina nuna mai yadda zaici koma duk
ya rude yaga abinci kamar a banza.
Ya sake jiki yaci sosai ina kara fada mai ya rike amana da gaskiya don zai yuyu
gwada ka zai yi ya ga halin ka yace .
Safiya kada kiji komai akaina insha Allahu zaki samay ni kamar yadda kike son in
kasance nace nagode yaya.
Yace safiya aini keda godiya ina na taba tunanen zan zo irin wanan wirin a
rayuwana gashi ta dalilin ki Allah ya kawo ni.
Yace wanan mutumin waliyi ne Safiya akwai mutunci a gare sai dai muyi fatan
Allah ya sanya Alheri ga alamarin.
Kamar yadda yace ba zai dade ba haka din ne kuwa ya shigo muna da sallaman shi
mukai mai sanu da dawowa yaji dadi har cikin ranshi.
Ya nasa a zuciyar shi dama ace nazo kenan ba tafiya zan yi ba don yau da ya samu
masu mashi sannu da zuwa agidan shi har yaji daban.
Ya samu wuri ya zauna yana cewa i hope kunci abinci sai nace mun ci yake cewa
good yaya ne yace a a Safiya nayi da ita taci bataci komai ba.
Yace a wani irin cool voice why Safiya ko kina ganin zan cuta makine da bazaki
ci abincin gida na ba ba fa anan aka girka ba odan shi nasa akai maku don gidana
gidan gwauro ne.
Nace ba hakana bane na koshine yaya Sani yace haka take bata son cin abinci ko a
gida sai yace a a baki ko kyauta min ba.
Why kike wasa da cin abinci bayan kin san halin da muke ciki don Allah ki bar
wasa da cin abinci please ?
A sanyaye nace mashi tau yace good sai yayi dan shiru can ya nisa yace zaki
barmin yaya Sani anan idan mun gama abinda ya kawo shi zai koma gida.
Nace an gode yada dan harare ni ya ce ban so na fada maki ko yanzu nima basu zama
yan uwa na bane ?
Nace ban ce ba.
Yace barin dan shiga na fito sai ki shirya nan ya mike ya shige ya barmu a
falon yaya sani ya bishi da kallo sai ya juyo ya dube ni.
Yace Safiya kin dace kin samu miji dai dai da halinki murmushi nayi nace Allah
yasa yaya don ni yanzu tsoron auren nake yi don ban san halin da zan tarar ba
saboda auren Ahmed ya sani tsoron maza.
Kibar wanan maganan don Allah auren Ahmed ai auren kaddarane ga kowan mu kibar
tunawa don Allah.
Kuka na fara yaya sani na bani hakkuri yana cewa ki bar kuka don Allah kada
mutumin nan ya fito ya samu kina kuka bamu da abinda zamu fada mai.
Jin haka yasa na dakatar da kukan nawa nace yaya dole in kuka don in ina tuna
wanan auren sai inji dama mutuwa nayi.
Yace subbahanallahi safiya kibar wanan magana don Allah hakkuri zakiyi mana gashi
ubangiji na son ya musaya maki da alherin sa cikin hikima irin ta ubangiji.
Kan shi ya cuta idan yayi maki ne don ki wulakanta suka ci amanar ki Allah ya
tausaya maki yaba ki wanda ya fishi ta ko ina.
Shiru kowan mu yayi zuciyar mu tana tunane kala daban daban sai ji mukayi ya fito
daga dakin haka yasa mu natsuwa .
Sallah yace muyi kanfin na wuce suka fita da yaya sani zuwa yin nasu sallahn suka
barni nan zaune
Da yake ba sallah zanyi ba nan na zauna naci gaba da damuwa a raina ina mai jin
ba dadi a zuciya ta tare da bin gidan da kallo.
Sai gashi ya dawo nan yake cewa na shirya nace eh yace na tashi mu tafi kai yadan
dafe nace sannu sai ya sake yai murmushi.
Nace kamar baka da lafiya ko kallona yayi yana girgiza kai yace yaya akayi kika
sani ?
Nima murmushin nai mashi nace tun shigowan mu naga hakan a tare da kai ban dai yi
magana bane kawai.
Yace don baki damu dani ba komay ?
Nace bagashi na maka sannu ba yanzu?
Yace yana kokarin tashi wallahi jikin nawa ne yadan motsa min kwana biyun nan
kuma laifina ne nai tafiya ban dauki magani na ba.
Nace haba dai may yasa kai ko ?
Yace da rabon insha wahala haka ne.
Yace tashi muje kada lokacin ya wuce muna nan yau na shiga uku da madam don na
fada mata azo airport a dauke ki.
Mikewa nayi yana gaba ina binshi baya zuwa wurin da mota ya ke kafin mu karasa
inda su ke yace kayan na nan sutura naki ne sai tsaraban mutanen gida kuma sai na
zo idan naji sauki.
Nago, , , ban saki kimin godiya ba kaina nayiwa don yanzu hakkina ne na baki
duk wani kula da kike so numfashi na sauke.
Don ya hanani magana ina isowa driver ya bude min mota muka na shiga shima ya
shiga yaya Sani da driver a gaba.
Ko da muka isa ban dauki lokaci ba jirgin mu ya daga sai lagos shida da rabi muka
sauka inda naga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login