Showing 84001 words to 87000 words out of 258256 words

Chapter 29 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

hakkuri a raina.
Tace sai kin fitar dasu a ranki ki rungumi kaddara ki mai da alamarin ki ga
ubangiji kamar yadda kowa ke fada maki a kullun duk masoyin ki abinda kawai zai
fada maki kenan a yanzu.
Don kaddara ya riga fata gare ki ki dinga fita kina mu amula yadda kowa keyi a
gidan gida na ubanki ne babu mai koran ki cikin sa koshi bau isa ya kore ki ba
tunda shi ya jefa ki a wanan halin.
Da sannu zasu janye manufarsu a gare ki kowa a dawo daidai dama zaman gashi nan
dai ne anayi har duniyan ma nawa take ga dan adam.
Ba abin mamaki bane ki mara lafiya ki rayu mai lafiyan ya mace ga Allah duk wanan
sau nawa yana faruwa ga dan adam.
Don haka har kulun nake godewa Allah da ba wurin wani hanya mara kyau kika kwaso
wanan cutan ba .
Har kulun ina godewa Allah daya bani yayan da suke da hankali da hangen nesa
Allah ya kara shirya min ku sak na amsa mata da Amin.
Naji dadin wanan nasihan sosai na ummi kiran da a kai mata a waje ne yasata fita
dakin lokacin na sauke ajiyan zuciya na mike tsaye.
Washe gari tun da safe da nai sallah ban kwanta ba na fito na share tsakar gidan
mu tas baba da ya dawo massalaci ya gani ina wanke wanke yake min sannu.
Ya zuba min ido cike da tausayi ya wuce dakin shi yana tunanen a ran shi yana
daya sani ya barni na auri zabi na gashi yanzu yaron ya zama wani abu a gari lokaci
guda ya samu wurin aiki mai kyau yayi aure shi anan garin.
Haka naci gaba da rayuwa zaune a gida in lokacin karban magani yayi in shiga mota
in je in karbo idan zan dawo na dan riko ma yaran gidan mu tsaraba.
Sai kaji suna cewa yaushe ne zan tafi birni in sayo masu abu kaza dana taba sayo
masu acan.
Yanzu hankalina ya kwanta ina samun walwala sannu a hankali har nakan fita zuwa
gidan gwago da yan uwan mahaifiya ta da kawaye na don sun gaji sun daina gudana.
Masu son kaya har gida sukan biyo ni don saya ko ba da sautu a sayo masu wani
abin idan suna so.
Haka sai mu a mula na ya dawo daidai da mu tane ina hurda da kowa babu tsangwama
ko hattaran da suke min da farko.
Na tayar da sana a ta zanga zanga dashi nake samun ina juya rayuwan mu harda na
kanne a gidan don haka muka koma bamu da wata damuwa a tare damu.
Sai dai har yanzu wanan muguwar akidar ta inna nan a ranta da wasu diyanta abin
yana damu na sosai yadda suke nuna min tsana a hili tundai babban yar ta da ake
shirin yiwa aure.
Don da dan abu ya hada mu da ita yanzu zatai min gori da ciwon dake jiki na zata
tsaya tai muna tas a tsakar gida babu kunya ko jin tausayi na ga halin da na tsinci
kaina a ciki.
Yau kasuwan garin mu yaran gidan mu masu sana a suna ta sha anin sana an su da
zasu fita dashi cin kasuwan.
Maganan yara ya taso sai rikici ya hada su da yaran dakin mu dana Inna da diyan
dakin mu subbahanallahi ranan naji tonon asiri da ban taba ji ba a wurin inna kamar
dai ta dade tana shirya muna ne.
Abin da yafi kona min rai shine irin zagin da take min da cewa naje na debo
cuta don mugunta ina son in yada ma gida kowa ya samu.
Haihuwana ya zame masu bakar haihuwa a gidan da barnan suna ko fita sukayi sai
ai ta nuna su basuci ba basu shaba
Wai tun auro ummi gidan ya juye masu da tsiya basu kara gane gidan nasu ba.
Tai ta fadan maganganun har tayi ta gaji karshe ta juya ga ummimu nan sukai
tayi tace itama ai ba sayen shi tayi ba aure ne yaci ta .
Inna tace oho dai da ana muna sallo wai itace mai karatun boko a gidan nan anyi
aure a birni, to yanzu ina bokon yake ?
Wai ina zaune a gida haka zan tabbata ina kallo yan uwanta na aure ni ko ba
halin yin aure a rayuwan na.
Ummi tace Allah ya fi mu sanin daidai don yana sane da komai da kowa a rayuwa sai
da baba ya shigo gidan san nan suka daina.
Watau a gaskiya tunda inna ke fada min bakar magana akan ciwon nan bai taba kona
min rai irin na yau da tai min ba ni dai ina zaune ina kallon ta ina aiki na banko
tanka mata ba har taci ta sude ita kadai.
Sai dai ance ko shiru magana ne don haka shirun da nayi sai yaci mata rai kuma
wai na mayar da ita mahaukaciyan tsakar gida don nasan abinda na jajibo gidan.
Mama ne tai magana da cewa haba dai ya kamata ki tauayawa yarinyar nan kin dai yi
fadan nan bata tankaki ba baki bari hakana.
Ta koma kan mama kuma wai ai ta san mama bakin ciki take da mijin da yarta
tasamu don yafi na yar ta shiyasa take kyashi yar nata.
Mama tai dariya tace kuma dai an ba a san maci tuwo ba sai miya ya kare .
Tace ai tun yanzu Allah ya baiyyana an sani in bashiba da ita ake zancen da zata
saye ya zama nata nan dai baba ya kara shigowa ya raba su fadan.
Yaran suka fita da sanaa su gidan ya koma shiru ina kwance a dakin ummi na sai
ga kanina ya dawo daga kasuwa tare da sakon dana bashi ya sayo min idan zai dawo
gida.
Ina waje ina aikin miyan danyen kifi ne sai ganyen zogale na gyara ban hada ba
yar wurin mama da ta dawo talla nace ta hada muna nabata kayan hadin ta gyara muna
ta raba taba kowa nasa.
Na gama na shiga daki na dibarwa kowa miyan na aika masu dashi sai Inna tace a
dawo min dashi.
Yaya Sani yana gida lokacin yace mata saboda may za a mayar mata ya ansa hannun
yaron da na aika dashi yana ma uwar nasiha.
Shiru shiru kowa ya dawo sai yar wurin ta babban da ake shirin yiwa aure ne bata
shigo ba .
Ina jin mama na tambayan ta har yanzu Saadatu bata shigo bane tace kila ta tsaya
amsan kudin ta ne.
Har magariba shiru bata dawo ba nan hankalin uwar ya tashi ta yafa ta fita bata
gane ta ba.
Can sai gata ta dawo tana fadin ban san ida yarinyar nan ta shiga ba na duba har
layin da suke aje sana ar su ban ganta ba.
Shiru shiru an baza yara ko ina ba a gane taba nace wa ummi na bari na fita in
duba ko Allah zai sa a dace.
Tace dani ki zamawa agun uwar su indai wanan matar ce barta inda kika ganta nace
wa ummi aini ba don ta zani ba.
Don yar uwata ne da baba don naga hankalin shi ya tashi sosai tace sai na dawo .
Har goma da wani abu na dare muna yawon bidan ta babu labarin ta hankalin gidan
mu duk ya tashi.
Muna tsaye kofan gida cirko cirko da wasu yan uguwan mu cikin zulumin ina ta
shiga baban mu hankalin shi duk ya tashi na bada shawaran aje gun yan sanda a sanar
dasu.
Baba da yaya sani suka nufi wurin yan sanda da daren nan suka sanar dasu abin da
ake ciki har daya da wani abu na dare dole muka hakkura muka shiga gida hankali
tashe.
A cikin gidan ma ba kwantawa mukayi don babu mai hankalin kwanciya sai yara
kanana kawai sukai barci.
Dole baba ya hakkura suka shigo gida bayan duk an bincika gidan yan uwa da
abokan arziki ba a samay ta nan ba.
Wani irin ihu da kururuwa Inna tasa da daren nan tabamu tausayi muka koma bata
hakkuri amma ina bata ko sauraren mu.
Can wuraren biyu da rabi na dare mota ya tsaya kofan gidan mu da sauri baba ya
bude dakin shi shi da su yaya sani suka fita don ganin ko nan ne motar ta tsaya.
Kafin sukai ma har an fara dokan kofan gidan namu da sauri baba ya bude tare da
tabayan ko waye ?
Suka ce yan sandane ya bude kofan suka fice nan muka fara bude kofunan dakunan mu
muna fitowa don jin may ke faruwa yan sanda gidan na mu da dare haka.
Sun ja baba gefe suna mashi bayani muna tsaye cirko cirko cikin jimay abinda ke
shirin faruwa Inna baba ya kira inda suka karasa bakin motan muna biye dasu a bayan
su.
Wani irin ihu Inna ta saka duk sai da muka firgice mun zaci ko gawan Saadatu inna
tagani a motan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , , ,


3🧕🏿030️⃣ 0
3️⃣0️⃣
3️⃣


YAR UWA NOVEL DON NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU
PLEASE, , , , ,


Idan nace zaman danakeyi gidan mu akwai dadi nayi karya zama dai nake yi na wacce
ta rasa gatan ta da madafa saidai dadin .
Abin ban dogara da sai abin gida ba ina tsaye ina nemawa kaina mafita ga rayuwa
shiya sa abin yazo min a cikin sauke,
Don ban kallon abin wani sai ma su su kalla a wuri na a nema in bayar akuma yi
min gori daga karshe.
Gidan da sai an nema aci ai kin san gida ne na mawuyacin rayuwa ga bawa don
ranan da bai suma ba kowa tashi fisshe shi da yaran ta.
Duk da yake mahaifi mu mutum ne mai zafin nemawa kansa bai dogara ga sana a daya
ba buga nan buga can yake yi har a samu ubangiji ya rufa asiri.
Yau ma mun wayi gari baba ya wuni bai samu kudin da za ai muna girki ba har
kwana biyu ga kuma Inna bakin halin nata ya motsa sosai.
Don da yar ta ta fara a daki ta nemi kudin a gunta ta rasa dan sana, an mai da
takeyi jarin yana kokarin karye mata sai inna tace ta basu su sayo abinci da zasu
ci tace bata da kudi.
Nan take ta fada tun tana yi a daki har ta fito waje da jidalin a bakin ta ganin
ta shiga daki yasa na fito don dora muna girkin abinda zamuci a dakin mu.
Ba wani abin tsone ido nayi ba dafaduka ne na taliyan da make sayar wa na dauki
biyu in dafa muna adan kau da miyau sai da dare nake son in muna tiwon masara.
Tunda ta kyala ido ta ganin a bakin murhu ta fara irin maganan ta da cewa gida
ya koma muna wurin gwada tsara muda diya.
Mun koma kamar kishiyoyi a gida da mu da ku ai gara ma ke Saadatu ba a debe
tsamanin aure a gare ki ba do baki da cuta amma wata kan ai haka zamu zauna muna
nuna hali da mu da ita.
Tafito ba komai takeyi ba amma taje ta dawo a tsakar gida tana dauke dauke a
tsakar gida kamar mai sabon hauka.
Da ummi taji abin yayi yawa sai gata ta fito waje da sauri na dago don jin
motsinta nace da ita don Allah ummi kada kice zaki tanka mata.
Tai tsaye tai shiru sai taka koma daki ko ba a fada ba maganganun na Inna sun
bata wa ummi rai sosai.
Yar ta Saadatu ne tafito daga dakin su tace da ita wai ke inna akan naki taba
kudin mutane ne kike wanan magana har kina hadawa da Safiya may tai maki yanzu ?
Mafarin kija fitina ku kama fada da tononasiri da ummi a gidan nan ke baki taba
fadan gaskiya sai ayita akare kece baki da gaskiya kulun.
Nan kuma ta juya akan Saade din tunda bata samu wace zatayi da itaba tace ke gara
can shanyayya kawai an hada dake an shanye keda dan uwanki.
Nidai nagama aikina na shige dakin mu na raba na aikawa kowa gidan da nasa, muka
zauna nida kanne mukaci namu.
Bayan mun gama cine nace wa ummi da take zaune tayi shiru a dakin namu tana
kallon mu.
Ummi gaskiya barin gidan nan zanyi na dan kwana biyu, da sauri tace dani ina zaki
tafi inda yafi maki nan din ?
Nace ba wani wuri zan tafi ba gun maman biyu zani in dan kwana biyu a can kin
gama zata tace ban yada ita ba ai.
Tace dani kina ganin magafinki zai barki ki tafi kada ma ki soma wanan magana
rayuka su zo su baci ga banza tsakanin mu da shi.
Nace ummi don Allah kiyi hakkuri kibar ki barni in gwada sa ata na gani ko zai
yarda in tafi wallahi idan ban gusa naba inna wuri ba wata raba ana abinda ba
daidai ba a gidan nan.
Ummi tace ai saidai kada akara amma kan Allah dai ya sauwaka kawai za a ce ma
zancen nace amin.
Ummi na dauka nabar zancen ne niko iya gaskiya na kenan na fada bayan kamar
kwana biyu na samu baba a kofan shi zaune bayan ya gama cin abincin dare nake fada
maishi kudirina nason yin tafiya zuwa wirin maman biyu.
Sai da ya kurkure baki ya watar da ruwan da ya gunda a baki yace dani anyya
Safiya ba zaki hakkuri ki zauna nan ba ki barwa Allah alamarin sa yafi.
Gyara tsuguni nayi da kyau nace dashi baba ai ba zama zanje nayi ba zuwa zanyi na
ganta kwana biyu sai na dawo gida.
Yace safiya bawai naki tafiyan ki bane ai wanan matar tana da mutunci da zaa
gunta amma kinsan halin da kike ciki yanzu
Yan uwan ki ma da kuka fito ciki guda dasu suna nuna maki kyama balle wata can
da girma da arziki ne ya hada ku kawai.
Nace baba ba haka na bane ita ta bukaci da naje gun ta, na dan kwana biyu sai in
dawo don kawai nai mata alkwari ne zan zo nake son zuwa ai.
Yace Allah ya kaiki lafiya nace amin baba na gode baba yace ba koma har na mikr
tsaye naji yace dake dawa zaku tafi sai na danyi shiru sai kuma nace ni kadai zan
tafi baba.
Yace tau Allah ya kyauta agaida su Inna na kofar ta bata san maganan may mukeyi
da baba haka hankain ta yana gurin mu .
No juya na nufi daki naji tana cewa a yanazu kuma mai cuta a jiki tafi ko wani da
gidan nan samun ido , nidai wuce wa niyi ban kula taba sai magana take tana
dariya.
Tun ranan da mukai magana da baba na fara shirin tafiya zuwa lagos gun mama biyu
sai da na shirya tsaba na fitar da zancen tafiyan gun mutanen gidan mu.
Aiko a take inna ta kasa boye jan halinta tace zaki koma a dora daga inda aka
tsaya ne na hadi wasu yawin bakin ciki nace niba wurin gwagona zan tafi ba.
Naji tana son daukan zancen da zafi daga zan tafi lagos gobe mata take ta kasa
boye min bakin cikin ta a fili ta nuna hassada akan tafiyan ban tsaya kula taba
washe gari na dauki hayan zuwa garin lagos.

********* ********* *********
Ban isa ba sai dare sosai na iso garin lokacin ya fara yin shiru don haka ban
sha wahalan zuwa unguwar su maman biyun ba da ba don dare ne abin hawa sun rage
zirga zirga a hanya lokacin .
Nazo na samu sun rufe gida sun kuma canza mai gadi kusan ma,aikatan gida duk an
canza su an kawo wasu.
Don haka basu gane ni ba araina nace kodai ba gidan bane nazo sai mai gadin ne
ke tambayana wurin wa nazo nace dashi madam Hauwa sai naga ya juya zuwa ciki na dan
lokaci ya dawo yana tanbayan daga ina nake na fada mai sai gasu tare sun fito da
ita.
Tana farin ciki da murnan gani na muka kwasa zuwa cikin gida tare farin ciki gani
na duk ya cika mata zuciya.
A raina nace ikon Allah gidan mu suna kyama na wasu kuma bare na farin ciki da
zuwana cikin su haka duniya ta gada.
Naga halarci agun mutanen gidan na samu kaunata tazo da kuma yar uwar mijin ta
suna zaune da ita sai kuma gani na zo.
Amma duk da haka basu nuna min rashin jin dadin zuwa na ba sai ma taro na arziki
da na samu a guri su.
An cika min gaba da abinci ban iya ci sosai ba don nisan tafiyan da na kwaso sai
dai ina kallon abincin ina tuna su ummi da kanne na ko yanzu wani hali suke ciki
oho ?
Da zan bar gida na mikawa ummi na waya na kwashe nombobi na akan idan na zo ja
samu yar karamar waya in saye don wanan ta ji jiki sosai.
Ban dade zaune ba sai gata ta fito daga dakin ta dake sama take cewa dani Safiya
taso akaiki dakin da zaki zauna don ki huta naga kin gaji da yawa.
Na mike tare da daukan hand bag dina muka nufi dakin daki ne babba wanda ya
kumshi gado da mirro da ban daki da tv da AC acikin sa.
Bata dade ba tafita na sauke ajiyan zuciya tare da bin dakin da kallo ina mamaki
ban bata lokaci ba na fada bandakin na watso ruwa tare da dauro alwala nafito na
rama sallolin da ake bina .
Daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login