Showing 63001 words to 66000 words out of 258256 words
Chapter 22 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
wan nashi yaki ya
saurare shi.
Ganina da tayi cikin wanan halin kuncin fa ciwo ga yunwa da bakin ciki ya fi
komai bata mashi rai.
Ya kasa jure gani na cikin wanan halin ya fita waje ya barmu a yadda ya samay mu
shiko gogan harara ya watsa min yace.
Ban san abinda yasa kike son hadani da dan uwa na ba a dalilin ki bamu shiri
yanzu da shi.
Sai liliya tace munafunci mana munafuka wai harda cewa zata zubar da cikin jikin
ta da da akace ki zubar uban wa ya hanaki zubarwa.
Ke kilaki rufe ma mutane baki don ba a kasa dake ba a zancen nan kibar masu
magana suyi.
Nan cacan baki ya kaure tsakanin mu don bazan in mata bane ko banza tafini karfi
ga tsayi ga komai turwa kawai nakeyi ina maida mata martani ganin shi zaune.
Shiko gogan taba ya jawo ya dinga kunnawa yana zukewa yana fesar da hayaki sama
kwakwalwan shi ta dinga caji yana neman mafita.
Yaya Saadune ya dawo ya samay mu a haka da kayan abinci niki niki ya jani zuwa
dakina ya bani magana da kalamai masu kwatar da hankali.
Yace safiya na fahinci matsalar ku muddin bai daina hurda da matan bariki ba
zaku samu zaman lafiya ba.
Nai maki alkawri zan kula dake da abincikin cikin ki har ki haihu bazan taba
batin ki kwana da yunwa ko kishin ruwa ba.
Safiya ban san abin ya kai maku haka dashi ba har yana horon ki da yunwa ga kuma
karuwa ya dauko maki a gida.
Nan dai ya sani gaba har saida yaga na ci abincin da ya sayo min din saidai na
kasa cin abin kwarai a lokacin don ciki na ya kulle sosai.
Ya rasa abinda zai yi ya fice ya daho ruwan zafi tea ya hada min mai zafi shina
samu na dan sha a lokacin sai kuma na fara shega amai.
Yana ta faman yi min sannu waya ya dauka ya kira habiba da safiya suzo su kwana
dani .
Shedaniyar ko bata san yana kulle da ita ba jira yake yaga hankalina ya kwanta ya
koma kansu.
Sai cewa tayi amma wanan abin da kake mata baiyi ba wallahi kune ke kara
shagwabata takeyin abinda taga dama.
Sadiya kawai tazo habiba tace wai kanta ke ciwo itama ta tausaya ma halin da
nake ciki sosai tace bakida lafiya har haka amma bamu sani ba kuma gashi yaya suna
zuwa gidan mu shida lilliya.
Suna nan zaune inda suke yaya saadu ya fito yabar ni da sadiya ta taimaka min ya
dawo wurinsu falo.
Lilliya tasa halin shi sosai bai daukan raini tun farko ya tsane ta sosai don
baison taraiyan ta da dan uwanshi .
Ahmed har yaushe zaka zauna macen banza tana dinga juya ka a gidan ka tana yiwa
mutane iko haka, na tausaya wa rayuwanka da ka kare a gidin wanan matar da duniya
ta gama yayinta.
Tasan halin sa sarai tana son magana tana gudun jibga yace idan matar nan bata
bar gidan nan ba sai na sa andaure min ita a garin nan.
Fada yake yana zare idanu halinshi ba dama dai tai magana tasha na jiki a gurin
shi da daren nan mikewa tayi ta shige daki.
Nan ya zauna yana suna magana nasiha nasiha fada fada dashi karshe dai yace wai
yayi kuskure zai gyara .
Amma zancen Lilliya tabar gida bai taso ba shi kanshi ba fa dadin ta yake ji ba
don ta gama isarsa dan kwanakin da sukayi tare amma kamar jaraba bai iya rabuwa da
ita.
Shi kuma yaua ya kafe akan lalai sai tabar gidan tunda ba auren kwarai sukayi da
ita ba.
Lalai kuwa Safiya ba zata zauna da wanan yar duniya a gidan nan ba kaji na fada
maka tun wuri kasan abinyi.
Yasan yaya saadu ya fishi zama dan duniya sai ya dafe kai ya rasa abinyi do
maganan shi ta girgiza shi ainun .
Muna daki muna jin badakalar da suke kwasa tsakanin su jikina yai sanyi don
kirikiri ya fifita da ni yadda yake maganan aibanci gamay dani.
Jiki na yai sanyi sosai tsananin tausayin kaina ya kama ni na tuna yadda nake
cikin yan uwana yau gashi an kawo ni dani da tutu duk daya.
Hawaye ne ya wanke min fuska itama sadiya dake jin fadan da sukeyi kuka takeyi
karshe dai shigewa yayi yabar kanin nashi a falon yana fada.
Dakin ya shigo wurin mu ya kalle ni tausayina ya kama shi yasan duk mahaifiyar
suce ta jefa ni wanan halin .
Don tasan halin data sarai amma ta nace sai yayi aure a zurian ta wai ko zai
daina abinda yake yi wanan yarinyar haka ina zata iya shirya wanda ya haura
talantin da wani abu can.
Yace Safiya ni zan tafi dare yayi nai maki alkawrin da sannu zan dinga warware ko
wace irin matsala a rayuwan ku muddin ina raye.
Ko ina gari ko bana nan tankar kauna na da muka fito ciki guda nake jin ki mijin
ki yayi nisa sosai da bariki sai addua lamarin sa.
Yai muna sai da safe yana ma sadiya tuni da ta tabbatar da naci abinci da safe na
sha magani na.
Bayan tafiyan shi munajin suna hayaniya a dakin su nan sadiya ke kara fada min ko
wacece lilliya da halayen yayan nasu da abin da yasa uwarsu ta auro mashi ni din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , ,
2️⃣
2️⃣
YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN SU
PLEASE, , , , ,
A can gida sani Allah sani annabi aka samu ummi ta dawo dakin ta amma har ta dawo
tana nan akan bakan ta na bata zama gidan da bata da yancin kanta balle diya.
Inda ba a san darajan mace ba da yara ake masu mulkin kama karya a gidan baka da
wani tacewa sai yadda akayi dakai.
Yan uwanta kuma suka mara mata baya sai da baba ya koma yana karamin murya da
sani Allah sani Annabi mahaifinta ya kara tursasamata ta dawo gidan.
Sai dai dawowan a tsatsaye ta dawo masu gidan bata shayin kowa da anmata abu
yanzu ne zata maida martani akai.
Hakan ya dan saman mata sauki a gidan gashi tun bayan ni da nai aure ba wanda ta
kara aure a gidan mu nima din danayi sunan nayi ne kawai.
Yanzun dai suke fitar da mazajen auren don haka kowa shirin aurar da yar shi yake
yi a gidan in ka debe ummi na daga cikin wacce ke kumsan bakin cikin yarta.
********* ********* *********
Zaune nake a kasa saman dan center carpet din falon abinci a gaba na sai
kira,an dana kunna ina saurare ina bi a hankali.
Nayi wani irin fari duk wanda ya ganni sai yai maganan farin dana kara cikin
jikina ya turo sosai don ya girma yanzu.
Banji shigowan shi falon ba sai ganin shi nayi a tsakiyan falon yana ce min
wanan wani irin abune kin ruda gida haka da karan karatu idan bi kike baki rage
karan yadda zaki ji mai shigowa gidan.
Ban kula shi ba sai dai ina mamaki a raina shida yake sake kida ya kure karan
kamar gidan zai tashi don kara baac mai komai ba sai ni yau da na saka kira,a gidan
yake fada
Ban saure shi ba ya dauki remote ya rage karan ya juya ya shige dakin shi kai
tsaye.
Kiran sallah magariba akayi don haka na mike zuwa daki na don yin sallah har na
idar banji motsin shi ya fito daga dakin ba.
Don haka na mike na leka dakin kwance yake yana sharar barci ko kaya bai cire ba
yadda ya saba yi indan yadawo gidan.
Muryana ya dinga ji a tsakiyar barcin shi ina tada ya tashi yau sallah bai
saurare ni ba ya gyara kwanciya yaci gaba da barcin shi.
Saida yaga dama ya tashi don kanshi yai abinda zai yi ya dan fita nasan giyan shi
ya je ya dirka sai dai bai bugu ba ya dawo da ledodi da yasayo abin breakfast din
mu.
Na kashe wutan daki na kwanta ina jin motsin shi a falon barci ya daukeni
motsin shi da naji a dakina ne ya tayar dani daga barcin da na fara yi.
Yace na kasa barcine shiyasa nazo taya ki hira namiji baida ta ido ko kadan nida
yace ban iya komai ba yake fadawa wanan maganan haka.
Nidai na matsa mai ya hawo ya kwanta daf dani naji ya fara shafana a hankali.
Idona na lumshe ina maijin tsanar shi a raina don ban iya mantawa da cin fuskan
da sukai min gidan shida lilliya.
Ya juyo gareni yana cewa may ye azuciyar ki may yake yawo a kwakwalwar ki gamay
dani.
Nace kai dan uwa na ne na jini kuma mijin da mahaifina ya zaba min dole komai yai
zafi ina tare da kai duk rintsi komai wuya komai dadi ina tare da kai a gidan nan
amatsayin matar ka kar kayi tunanen daukan fansa a gare ni don kai dan uwana ne
kuma mijina.
Wani iri yaji har acikin zuciyar shi don yasan ya cuta min ta ko ina harda ma
inda ban sani ba sai dai kawai ayi hakkuri da juna.
Nisawa yayi tare da gyara kwanciyar shi yace to ki daiyi hakkuri da komai.
Nace hakkuri kan na yi amma yaya bazan sake irin hakkurin da nayi a baya ba amma
zama kan yamin dole a gidan ka.
Shiru yayi ya kasa barci yana ta juye juye ya tsinci kansa a wani yaniyi tabbas
ya san ya zulunce ni tako ina duk kokarin da nakeyi baisan may yasa ba ya gani ba.
Yarinya ba inda ta gaza dashi tsabta da girki da kula da kayan gida da kokartawa
da bashi hakkin shi duk ta yanda yazo mata amma shi ya kasa daina barikin shi a
zauna lafiya.
Ga saadu kanin shine na baya amma har ya fishi hangen nesa ya hanngo mai abinda
bai taba tunanen hangowa ba a rayuwan shi.
Ya tashi ya yai zaune yana maici gaba da tunanen abubuwan rayuwa a ran shi.
Har barci ya fara dauka na naji matsin shi yai yawa na haska hasken tocina don in
ga may yake yi a lokaci tare da cewa ba kayi barci bane ?
Yace yau na kasa barci ne ban san abinda ke damuna ba haka nace Allah ya kyauta
ko may nene amma da zaka koma dakin ka ka barni zaifi min in samu barci.
Ban dauki lokaci barci mai nauyi ya dauke ni ya lumshe idon shi yana mai kare min
kallo na dunkule a wuri daya ina barcina hankali kwance.
Sai wuraren asuba ya samu barci ya dauke shi bai wani dade kwarai yana barcin ba
ya dinga jin murya na ina tadashi yai sallah.
Bai saure ni ba sai barcin shi yake yi nan na barshi a kwance na wuce nai wanka
tare da dauro alwala har na fito bai falka ba.
Nata da sallah na harna idar sai nasari yake kwasa a cikin barci duk ya wani
rudamin daki dashi.
Na idar ina addua na sake ta dashi da yaga kamar damun shi nakeyi sai ya dauki
filo ya danne kanshi dashi.
Har na gama anbinda nakeyi yana nan a kwace min dirin a daki yana barci matsa mai
nayi sai ya tashi.
Nan ya mike a harzuke ya hauni da masifa meye damuwan ki da rashin tashina
kibarni lokacin da duk na tashi zan iya yin sallah na.
Ban samu barci da wuriba jiya da kyat na samu barcin ya dauke ni yanzu kuma kinzo
zaki matsamin ki kyale ni nai barci na karki sake tasheni.
Nan nima nace a harzuke zan tashe ka dole in tashe ka ko sau nawa zaka koma barci
muddin bakayi sallah ba sai na ta dakai.
Haka kawai ana sallah kana kwance kana barci katashi in kayi sallah sai ka koma
ka kwanta yafi, magana da nakeyi na damay shi.
Ya mike a hasale zai koma dakin shi ya kwanta yana fama dani na daure nace yanzu
kai bakajin, kunya ko tsaron Allah kaine fa yakamata ace ka data dani nayi sallah
amatsayi na kaunan ka ko matan ka.
Amma ana sallah asuba kai kullun kana kwance kana barci a daidai lokacin da Allah
yake sauke rahamarsa ga bayin sa.
Yana kuma yi ma bayin sa gaffara yana raba alheri ga masu rabon samu ya sa imani
azuciyar masu imani, amma kai sai dai ka kwanta kawai kana barci ko yaushe.
Bai kula ni ba ya shige dakin shi ya kyaleni ina wa,azina koda ya shiga ya koma
barcin shi bai damu da surutun da nai mashi ba.
Sai wajajen takwas saura ya falka yai wanka tare da yin sallah ya fito da shirin
zuwa aiki a falo ya samay ni zaune.
Ina ganinya fito na mike zuwa hado mai abin karyawan shi dama na gama yana aje.
Na tsugun na gaban shi na aje tare da mashi ina kwana ya amsa min adakile, ban
daga ba daga wurin ba nace dashi.
Yaya don Allah ka daure da yin ibada bai kamata ba magidanci da kai kana wasa da
addinin ka, may yasa kuna diyan musulmai kuke sakaci da ibada.
Hannu ya daga min ya dakatar dani daga maganan da nakeyi yayi da hannuwa don haka
naja bakina nai shiru tare da komawa gefe na zauna.
Yagama ya fice abinshi lokacin naji gidan kamar an debe min kaya da nauyi akaina
na mike na shiga gyaran gida dakyat na samu na gama .
********* ********* *********
Kwana biyu banda matsalan komai da shi a gidan sai dai ba sakin fuska akaina
wanan bai damay ni ba indai hat zaibar zuciya ta ta samu saida.
Ranan na samay shi zancen zuwa asibiti a duba ni don ina fama da ciwon mara idan
dare yayi bana barci da dadi.
Ya kawo kudin zuwa ya bani yace na shirya ya sauke ni indan zai fita nako shirya
da wuri na zauna jiran shi.
Sai da ya gama abinda yake yi ya fito muka kama hanya a can wani unguwa ya kaini
wani asibiti mai kyau na kudi .
Yace idan zan dawo ga yadda zanyi ga yadda zanyi nace na gane na yanki kati nabi
sahun masu ganin likita a wurin.
Can layi ya kawo kaina aka ce nai fitsari aka kuma debi jina na dan aunawa an
gama na koma na zauna sai da layi ya sake kawo kaina na shiga.
Ba matsalan komai ba likita yai min yan tambayoyi irin na likita karshe sai ya
rubuta min magani sai kuma yadan dubeni yace dani idan ba damuwa yana son nazo da
mijina yana son ganin shi gobe.
Banji komai a raina ba nace zan fada mai ya bani wani dan note yace dashi zai zo
idan zaizo din na karba nai mashi godiya na fice.
Na dawo gida a gajiye na samu bai dawo ba na kwanta na dan huta don na sayo
abinda zanci a hanya da zan dawo.
Ban tashi ba sai wajajen karfe uku na tashi a gagauce nai sallah najira akai
la,asar na hada nayi sai na mike na dora girki dare.
Har na gama bai dawo ba lokacin da ya saba dawowa kafin magariba na shige sallah
na gama ina sauraren dawowan shi, naji shiru nan na fara tunanen ko ina ya tsaya.
Shiru bai shigo ba har nagaji na kashe kayan kallo na kwanta sai wuraren sha
dayan dare naji ya shigo gidan a cikin maye.
Inna lillilahi nayi a raina ina jinshi yana ta hauragiyan shi shi kadai a falon
na tashi na kargamay kofan dakina don ma kada ya shigo min dakina.
Haka na kwana ga ciwo ga bacin rai nasan mairaba shi da wanan halin sai Allah duk
wani wa a zi da sauransu bai shigan shi don yayi nisa.
Gari ya waye ban fito da wuri ba sai wuraren takwas na fito ina yan aikace
aikace na duk da nayi nauyi ban iya dukawa sosai yanzu.
Ya fito yana wani murzan idanu kamar wanda barci bai isheshi ba, ashe shi din ne
kuwa don ya na cikin sauran maye har yanzu, .
Dan juyowa nayi na kalleshi na mayar dakaina naci gaba da abinda nakeyi nace mai
ina kwana a takaice ba tare da na fuskace shi ba.
Shima yai mamakin a yadda na gaida shi don ba haka nake gaida shiba din yadai
amsa min ne kawai don yasan wai fushi nakeyi ke nan.
Ya zauna yana tambaya na abin karyanwanshi na ba shi amsa dacewa dashi ban yi
ba har zai yi magana sai kuma ya tuna bai sayowa ba daren jiya da zai dawo gida don
a buge yake lokacin kuma masu kaya sun kwashe.
Zama ya dan yi na wani lokaci yai shiru sai can ya furzo iska daga bakin shi yana
mikewa yake tambayana jiya kin samu ganin likitan ?
A takaice nace mai eh nagan shi yama bani takarda wai yana son ganin ka asibitin
sai ya dago da sauri yana kallona yace.
May zanmai ba ya dubaki ba shine kuma zai ce sai na je ya ganni ni ban iya
lalurar su na likitoci don Allah.
Nace to kasani ko wani abin ne yake neman ka din kamaf tai magana sai kuma ya
fasa ya karbi takardan dake hannuna yana cewa idan na fita zan biya nagan shi.
Tun wanan lokacin bai kara min magana ba nice ma dana tambaye shi yake cewa yaje
yace ya dinga sai min kayan karin jini ne.
Da alama