Showing 168001 words to 171000 words out of 258256 words
Chapter 57 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
barshi yau ba zan soya
dankali ba ai nan naci gaba da aiki na share ta.
Ta dan jima atsaye sai ta juya ta fita daga kitchen din na gaba na ba kowa nasa
wanka nayi kafin ya fito na shirya cikin wasu atamfan Super mai launin makuba na
fito zuwa wurin shi.
A tare muka fito dashi daya gama shiri tana falo wanan lokacin ganin mu yasa ta
zamo daga saman kujera duk ta daburce da ganin ta bata da gaskiya ko kadan ta na
gaishe shi a daure ya amsa mata.
Bayan kwana biyu gwago ta koma gida tare da abin arziki mai yawa da ta samu
wurin maigida don har injin din tatsar mai ashe ya saya mata duk bamu sani ba sai
da ta koma nakejin labari.
Naso bayan tafiyan gwago in daure ma zarah amma sai nayi shawara na fasa nuna
mata nayi ban san komai ba gaba na da yawa ai.
Sai dai na bar yin komai a gaban ta yanzu na kuma rage bata fuskan da nakeyi
sosai so nake ita da kanta tabar gidan batare da wani abu ya fito daga gare mu ba.
Wata na biyu cur a gidan uncle na canza acikin dan kankanin lokaci saboda abin
more rayuwan da nake samu a gidan shi.
Don babu abinda ya rage ni dashi na fannin rayuwa duk wanda ya ganni sai yayi
maganan canzawa na ni kaina nasan ina daga cikin matan da suka dace da gidan miji.
Banda tunanen komai a raina in ma ina da bai wuce na ciwon dake jikin mu ba kuma
Alhamdullahi muna samun kula yadda ya dace sosai dama abinda ciwon ke bukata kenan.
Haka zai sawo abubuwan kara jini ya sakani a gaba sai munci tare magani kuma
idan yana gari a tare muke sha kullum kafin mu kwanta don ka,idar shan shi ke nan.
Yaya Saadu yazo sau biyu a lokacin don ba a gama gyaran gidan da zai zauna ba
sai yake zuwa yana komawa.
Ranan ina daki kwance dakina da yamma daidai lokacin dawowan uncle gida ta kusa
sai ga zarah ta shigo da sallaman ta dakin tayi sallama na amsa mata ta shigo ba
kasafai take shigo min daki ba sai idan da wani dalili.
Anty kin yi baki tace min na dago daga kwancen da nake ina fadin baki tace eh
suna falo zaune suna jiran ki.
Dama bani zama babu kwaliya a gida tsab nake banda wani kushe a jikina kara dan
gyarawa nayi dakyau na fito don ganin ko su waye suka zo.
Mata na hango zaune su hudu a falo sai dai ban sheda ko su waye ba daga nesa
sai da na karso wurin ina fadin sannu ku da zuwa gaba daya suka juyo sai da gabana
ya fadi.
Fon ganin bakin nawa don ba kowa bane anty Uwa ce da yaranta uku gaba daya a
gidan namu, , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/17/20, 10:17 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , ,
5️⃣8️⃣5️⃣
5️⃣
🧕🏿 8️⃣8️⃣5️⃣
NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA DON
WALLAHI BAN YAFE BA, , , ,
Ganin bakin nawa take naji gaba na yayi wani irin bugawa don tsoro da fargaban
ganin su haka a gida na may ya kawa su kuma nake tambayan kai na.
Muryan anty uwa ne ya dawo dani daga duniyan tunanen da na lula da farko naji
tana fadin a, a tau, amaryan ce wanan masu gari tana bin zanin jikina da kallon
tun daga sama har kasa na binshi da kallo sukeyi.
Allah ya rufa min asiri yau da safe bai fita gidan da wuri ba don haka na sha
kwalliya tun da safe da atamfan brocade a jikina.
Dinkin shi mai kyau tun daga Dubai ya sayo min shi hakana din kakken shi murmushi
na kakaro a fuska na ina cewa dasu sannuku da zuwa tare da sakin fuska sai da na
zauna nake cewa ina wuni Anty Uwa kamar yadda naji anty na na lagos na kiranta
dashi.
Waya na dauka ina latsawa mai aikin mu na kira ina fadin make something special
for our visitor's.
Na gama na dago tareda cewa sannun ku da zuwa duk naga sun kura min ido sai bin
gidan suke yi da kallo sauran yaran nata itako sai faman tabe baki take yi.
Mun gaisa sai dan shiru ya biyo fallon anty uwa din ne ta kawar da shirun da
falon yayi a lokacin.
Ji nayi tace dani maigidan ya fitane ko yana ciki nace ya fita yana gun aiki sai
zuwa yamma zai dawo gidan.
Dakatar, ni , wata daga cikin diyan nata, tayi da fadin ai dama bashi muka zo
gani ba gun ki dai ke snacher muka zo,
Murmushi nayi don jin sunan da suka kirani da shi wanda su ya dace a kira da
sunan tun farko amma sai gashi suna lakakamin sunan don basu da kunya.
Uwar ne ta dakatar da ita da fadin dakata lawisa sai ta juyo gare ni tana fadin
ke wama kike da suna what ever dai ba mun zo bane nan don dogon surutu sai don mu
zo mu ga idon yar kauye kamar ki da har ta iya kwacen maza haka son ranta.
Tun wuri ki san da sanin Nafisa zata shigo gidan don haka ki zauna da shirin
taron ta ke wanan gidan ma ai sam bai dace da irin ki ba yar kauye ga gida har gida
amma wai yar kauye gaja ce irin ki a gidan ba ilimi ba komai.
John ya shigo da tire shake da drinks da sauran abin taba baki ya girke a gaban
su don basu da kunya sai suka zari guda guda suna balla bakin su tare da kafa kai.
Duk da uwar taji kunyan abinda sukayi sai dai banda ita Nafisa din fada ta fara
yi musu akan su natsu mana suyi abinda ya kawo su.
Ina zaune na kafa masu ina kallon abinda ke wakana nasa yatsan hannu na guda na
tallaba haba na dashi tare da kura masu ido.
Bayan sun dan natsu ne uwar taci gaba da fadin yanzu ke har kin san ki yaudari
matar da ta tsamo ki a cikin talauci da wahala ki tsallakata bayan ta gama maki
komai kin gudu kin barta don halin dan adam butulu saboda kina hangen nesa.
Yanzu ke baki ji kunyan asirce ta da kikayi tun farko ba bai maki ba kuma kika
asirce mata kanin miji da bakar asirin ki don kawai kin samu labarin yar waje na
yake nema yanzu.
To ai baki sani ba idan asiri kike takama dashi nafiki idan kuma barikanci da iya
duniyan ci kika ce kin iya duk na dama ki na shanye.
Gidan nan sai Nafisa ta shigo shi ko yau ko gobe ki zauna a cikin shiri don da ta
shigo waje kika yi ke.
Don gidan nan ba gidan zaman ki ba bai dace da mace yar kauye kazama irin ki ba
don haka ki sani, , , , , , ,
Madam yaya gida ya fada ba tare da ya kallo mu ba driver shi na binsa baya da
jakkan shi na ai har ya nufi hanyan dakin shi sai kuma ya juyo yana cewa sorry baki
kikayi ne ?
Murmushi nayi tare da fadin anty Uwa ne fa da yaranta da, , , ji nayi ya katse
ni karasa magana na da tambayan da ya daure min kai.
Uwa waye uwa ya fada yana maimaita sunan cikin daure fuska dan gyara zama tayi
tana fadin Sulaiman baka gane ni bane ?
Uwa sister din yaya Lawal soja dake Lagos minjin maimuna wai kana nufin ka manta
dani uwa na gidan malam garba teacher.
Katse ta yayi da fadin kenan ke sister din lawal ne ko kece ke zaune a nan garin
da sauri tace eh nice ai , yace anzo diba madam ne ?
Wani kunyan ne ya kamata ba ita ba har diyan nata sai da sukaji nauyi don yanzu
suka gama cika baki akan shi gashi kuma ya shigo ya nuna baida halaka da su asalima
bai san su ba.
Yana batun wucewa na bude baki da sauri ina fadin Uncle bakin ka ne fa , don
wurin ka suka zo da mamaki yake kallon fuska na kuma ya dan kallon su sai ya dawo
ya zauna.
Na mike zan nasu wuri ya ce No zauna idan sunzo wurina ai kamar wurin ki suka zo
so ki zauna ba wani abu bane ya juya wurinta yana cewa lafiya ko hajiya ?
Duk sun natsu ta kasa magana sai mai bi ma Nafisan ce ta fara mikewa tana fadin
sai da na fada maku kada muzo gashi munzo an wullakanta mu a banza.
Karamar tace wai kana nufin ba ka masan Anty Nafisa ba ko may ta juta wirin uwar
tace mummy duk wanan abin da akeyi dama bai san ku ba ne ?
Mikewa yayi yana fadin tunda baku ma san abinda ya kawo ku ba zaku iya fice min
daga gida don Allah bana son a shigo ana damuwar mu.
Waima yaba su daman shigo min gidane ya fadi tare da mikewa yana fita hanyan
waje suma da sauri suka mike zasu tafi nace to Anty uwa na gode da ziyaran da kuka
kawo min sai gani na biyu kuma.
Ban san ko ina gidan ko kun fitar dani don yarki yar birni zata shigo niko yar
kauye ne bankai matsayi zama da su ba.
Sai dai zaku ya tafiya da drinks din nace ma yaran tare da nuna masu tire din da
suke ciki nace don naku ne ku aka kawo ma kushi daga haka na juya na fara tafiya
komawa ciki nan na barsu tsaye da takaici.
Suna jin yadda yake ma maigadi fada duk wanda yazo kada ya sake barin shi ya
shigo mai gida kai tsaye batare da an bashi umurnin ya bude mai ya shiga ba.
Ko ba komai naji dadin yadda uncle yayi masu a raina don da bai dawo ba Allah
kadai ya san irin cin fuskan da zasu yi min su tafi sunci bulus.
Da ya shigo nan falo ya zauna yana huce har yana fadin zai kori maigadi da sun
shigo sunyi wani abu fa may zaice shi.
Na dai samu ya sausauta ta hanyar kawo mai ruwa da bashi baki yayi hakkuri ya
kurbi ruwan ya dago kai yana fadin kin san ida Allah bai dawo dani yanzu ba iya
abinda zasu yi maki.
Zan kira in fada ma mijin ta kada ta kara zo min gida may ye hadina da ita da dan
uwanta nake da zumunta ba itaba.
Ya dafe kai da hannu guda tare da lumshe idanuwan shi don takaicin da ke damun
shi lokacin ranan haka ya karasa shi babu wani walwala a tare da shi.
Washe gari da muka tashi yana kule dasu a ranshi ya baci da su sosai sai zuwa
sha daya saura ya fito falo ya zauna.
Na fito da kayan yake farce a hannuna ina son gyarawa sai naji yace da zaki iya
dakin fara gyara min nace Uncle ke nan may zai hana in iya aikin lada.
A hankali na sauko kasa inda na fara da yanke mai na kafafuwan shi gyara nake mai
yana waya sai ajiyan zuciya yake sauke wai.
Har na gama gyara mai kafafun shi yana a kan wayan naji yayi sallama da wanda
yake wayan daidai zan tashi in koma saman kujera in fara yanke mai na hannuwan shi.
Ya kare wayan daidai na dago hannunwan shi zan fara gyarawa yake ce abokina na
Canada yana gaida ke ina sa ran zamu tafi nan da wani dan lokaci.
Da sauri na kallo shi nace uncle dani fa kace ya dan subbanci kuncina yace ke fa
madam nace Allah ya nuna muna lokaci lafiya Amin yace.
Ya soma magana kamar mai rada bakinshi a daidai kunne na naga alaman kina farin
ciki da tafiyan nan ko ?
Nace ai dole uncle don ban taba fita daga cikin kasan nan zuwa wata
kasa ba sai wanan karon.
Ya fiddo da karamar dariya yana matsa hannun dake cikin hannun shi yace tafiya ai
yanzu kika fara shi don tare zamu dinga fita duk inda zan tafi sai dai idan kinyi
ciki ya tsufa zan dan baki hutu a lokacin.
Da shagwaban murya nace uncle ka bari don Allah ni fa ban shirya haihuwa yanzu ba
da sauri ya kalle yace baki da tausayi ne ?
Yanzu duk su Aisha suna da yara wanda ada hakan baya damu sai yazo da nayi aure
naji nima ina son na shigo gida in samu mai min daddy oyoyo .
Shiru nayi ina tunane don nima yanzu haihuwa ne tashin hankalina don wanan ne
karo na biyu da yake nuna min yana son haihuwa sosai.
Don haka ba abinda zan iya farauta mashi rai da shi a wanan lokaci sai daukan
ciki da ya kwallafa rai gare shi.
Na nisa ta yadda yake iya jina yace da sauri naga kamar ke abin bai damay ki ba
ko nace ba hakana bane Uncle.
Haihuwar dai naga baizo inda ake neman shi ba sai wurin da ba a maraba dashi ina
tuna haihuwa na na baya ne kawai.
Da sauri yace kin taba haihuwa ne a hankali na gyada mashi kai alaman eh naji
mamaki da baka san na taba haihuwa ba uncle.
Yace ban samu wanda ya fada min ba cikin masu bani labarin ki a hankali na fara
bashi labarin haihuwa nawa fuskan shi kawai zaka kalla kaga alaman tausayawa a
cikin ta.
Shafo fuskana naji yayi gami da lumshe idanuwan shi yana sauke ajiyan zuciya yace
haka abin yake ya samu yai sakaci da samun shi.
Abin da nake gani ya taba yarinyar don baku amsan treatment a lokacin har yakai
abin ya shafi yarinyar a ciki nace uncle sai bayan haihuwar ta nasan cewa ina da
cutar a jikina.
Koshi sai da yaya Saadu yaga zan halaka ne yasa a kaini asibiti a dubani shine
aka san ina dauke da cutan a lokacin don kowa bai kawo haka ba a ranshi.
Yace ni kin ga tun da na samira ya baiyana na tafi akaimin awo sai aka samu nima
na dauka sai dai nata yafi karfi akan nawa ne.
Sun dai cuce mu nace dashi yace sun cuci kan su dan zunubi akan su yake Allah ya
gani bata zina muka samay shi ba shine saukin mu ga Allah.
Ciwo kuma kaffara ne ga bayin sa kin ga mun samu riba biyu ga abin koma ukku
zance idan ba ta sanadin hakan ba ai wata kila ba zamu hadu ba.
So ki fitar da zancen cewa sun cuta muna don ni tu lokacin na bar ma Allah sanin
sa akai kin ga ta ida ya saka min dashi kuma.
Na gama yanke mai akaifar na tatara na zuba a inda muke zubawa kafin mu binne
wani akaifa da suma da nake tarawa idan sun cika sai na fita baya can in tona rami
in rufe su.
Koda na dawo saman kujera two setter na koma na kwanta nayi rigingine ina lallon
fankan dake kadawa a hankali falon.
Shima dai shiru yayi nasan akwai abinda yake tunane a zuciyar shi wanda kila bai
wuce zancen haihuwan da yaji na taba yi ne koma may ye ai bai nuna min komai ba a
fili.
Sai naji ya jefo min tambaya a bazata dacewa na dauka idan mace ta taba haihuwa
ai ana ganewa ne ?
Murmushi nayi na dago tare da cewa uncle may kake son ka gane uncle a kai sai ya
murmusa kawai yace forget.
Nace tau ni dai tun haihuwana yarinyar bata ma sha nono ba don haka har ta koma
banda ruwa bata sha wani abuba a duniyan nan.
Yace kai labarin akwai ban tausayi wallahi abinda mutane da yawa ke fuskanta ke
nan yanzu har bakin ciki ya kashe mutum yanzo idan da za a fadi halin da mutane da
yawa ke ciki akan lalurar nan sai ka tausaya masu.
Nisawa nayi daga inda nake kwance nace Allah ya sauwa yace amin wayan da aka
bugo ne ya dakatar muna da hiran namu nan dai na mike na shiga kitchen ban fito ba
don yau yana gida na tsaya hada mashi abinci da zamuci.
A kitchen din ya samay ya byo bayana lokacin ina motsa miya sai jin hannayen shi
na ji saman jikina ya rugumay ni ta baya yana fadin.
Na ga dai baki aminta da aikin John a gidan nan ba yanzu na nisa tare da fadin
Uncle da raina da lafiya na zan kwanta kato na yi min girki ina ci.
Juyo dani yayi daidai na gama motsa miyan ya juyo dani muna fuskantar juna yace
idan aikin namiji ne baki so sai a canza muna da mace dama dauko shi nayi a
maaikatar su .
Don banda mace a gida ne nace a bani na miji yafi yanzu kuma tunda kin zo da
magana sai a bamu mace don gaskiya bazan lamunci kina shiga kitchen wanan jikin
naki da nake huta gajiya na a cikin sa ba yana daukan zafi.
Kunya maganar ta bani na yi saurin dukar da kaina daga kallon shi yace ai
gaskiyana fada nafison ki huta ko yaushe sai idan yara sun zo kuma ki ji da namu
lalurar duka.
A hankali na dago nace uncle kana ganin hakan ban cutawa shi john din ba dakai
naga sabo ya shiga tsakanin ku kama a gaskiya yana jin dadin aiki dakai din.
Kada nazo na shiga rayuwan shi in nayi mai haka kamar na toshe