Showing 39001 words to 42000 words out of 258256 words
Chapter 14 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
dauko ba abin da ya damay ni da ita.
Wanan wani sallon yaudara ne ka dauko kaika dade bakai muna sheri ba cike da
tsoro na ke magana a, a yaya na fada mane don kawai ka dauke kafan ka.
Na sake cewa cike da tsoro na dan kalle shi nace na fada ma a gaban shi ne don ka
san gaskiya nake fada don ka kiyaye.
Ya dago jajayen idonuwan shi ya ce dani indan baibar shiga maganan ki dani ba a
gidan nan zan iya mashi komai tunda bai da mutunci.
Bai kai aya ga maganan shiba saiko yaya saadun ya taso mashi kamar zai dake shi
da kyat na samu suka hankura ya fice gidan a fusace.
Ranan nasha duka sosai a wurin shi sai dai bai yarda ya kaini kwance ba amma na
zagu a gurin shi .
Ban damu ba don zargi da sherin da yake son muna da yaya saadu shine abin da ya
tsaya min raina tun lokacin da ya fadi hakan.
Amma yau sai naji na samu sukuni akan wanan maganan na gyagije naci gaba da har
kokina kamar kullan.
Na koma yin kitso idan yakawo in dafa muna kowa ya ci indan bai kawo ba kuma na
dan jawo kayan abincin da maman biyu ta kawo min na hada wani abu na ci.
Wani lokaci haka zai dawo gidan da abin amfanin gida duk ranan da naga ya shigo
haka nan nasan yar arzikin na a kai.
Zai zauna baisha min taba a falo ko giya ba sai dai yai ta yawan waya da matan
banza ranan kuma duk matar da tazo kitsu ranan sai dai ta koma bakitso don bai bari
nayi .
Yakan zauna ranan mace nake yakan wuni darza na sai ya gaji ya kyaleni don kan
shi indan yai haka yakan dade bai neme ni ba kuma sai lakacin da yai mashi dadi a
rashi zai kara kusanta ta.
Ranan da naje gaida gwago dakuka na dawo gidan mu don tun case din da na fada ma
yaya saadu abinda ya fada ashe sun je can gabanta suyi kaca kaca da juna su a gaban
ta.
Tun wanan lokacin taka nema na ta fada min kada inyi sanadin raba kan diyan ta
da munafunci na dana iya a tare na gansu kuma tare zan barsu.
Idan na kara hada diyanta fada sai daukeni ta mayar dani gidan matsiyacin ubana
naje can mu karata can dasu.
Zagi ta ida take shiga ba nan take fita na har cewa tayi wanan kaddararen aure
nawa da ta tauye ma danta jin dadi dashi.
Ban wani dade ba don ko ruwa ban sha ba a gidan na juyo na dawo gida ina kuka a
idanuwa na,
Nazo kofan gida na samu maman biyu tazo gidan bata samay ni ba tana shirin wuce
wa sai gani tafe ina sharan kwalla a idona.
Ta tsaya da mamaki tana kare min kallo tare da tambaya na ke lafiya kike tafe
kina kula haka .
Nan nake fada mata duk abin da ya faru a bayan ta har dukan da yai min tace wanan
mijin naki ya zama abinda ya zama sai addua kawai gare shi.
Ina kuka nake cewa da ita ni gaskiya gidan mu zan koma na gaji da wannan halin
baida ranan gyara halinsa sai dai gaba gaba dakeyi.
Tace kada ki fara cewa zaki gidan ku don mahaifin bazai barki ba ba kuma zai goyi
bayan kiba don haka gara ki zauna kiyi hakkurri da halinsa tunda kin saba yanzu.
Mutun sai kace mara imani komai a ziciya har yanzu fa bai daina abin da yake yi
ba yanzu har rashin kwana a gida ya tsiro dashi.
Tace kardai ince wurin matan banza yake kwana ta fiddo ido waje don mamaki tace
wanan kuma sabon sirfan da ya dauko don mugunta fa.
Nan na soma kuka ina fadin san anty ba sona suke yi ba sin cuce ni sun cuci
iyayye na, sun muna rufa rufa an hada ni da alkakai na soma kuka wiwi.
Tace meye haka kuma Safiya so kike ki tayar min da hankali nima cikin kuka nace
da ita ba haka bane anty.
Wallahi ni kadai nasan halin da nake ciki yanzu haka abinci sai yaga daman bani
zai kawa a gidan nan ga uwar shi har fadi tayi wai ina mashi wayo ina karbe mai
kudi.
Kenan ashe tasan dan ta yadda yake amma taiwa mahaifina rufa rufa ta aura wa
danta ni hakana.
Hakkuri tai ta bani kan indan kara bashi lokaci idan bai daina ba zata bani
kudin mota in koma gidan iyayyena da zama.
Ranan bamu rabu ba sai da ta kaini har gidan ta na gani kamar ba a kasan nan suke
zaune ba mutum zai dauka a Amerika yake don kyawon shi.
Naci na sha ta bani kyautan suturu masu kyau da tsada dama tun da nazo ko kyale
bai taba hada ni dashi ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGO, , , , , , , ,
1414
14
1️⃣
1️⃣
4️⃣ 4️⃣
YAR UWA WANAN NOVEL NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,
, , , ,
Tafiyan dare mukayi sai wajajen sha daya da wani abu na rana muka isa garin mu duk
jikin yai min tsami dama yaya jikin yake balle an tabashi kuma.
Mun sauka yaya ya nema muna mashin muka hau zuwa gidan mu tare da kaya na niki
niki shi yai wahalan daukan kayan da kansa.
Suna hada hadan su na safe sai jin sallama na kawai sukayi yara suka dauka ga
Safiya ga safiya tazo.
Da gudu kanena suka sheko suka rungumay ni suko su mama sun fito da mamaki suna
kallona mama ne tace safiya kuna tafe ashe ke daya ne take sai idanuwa suka ciko da
kwalla.
Na shige dakin mu ina kuka shigowan yaya Sani da kayana niki niki ya na kokuwa
dashi yasa aka samu masu taimaka mashi daukowa.
Kowa sai mamaki yakeyi sunyi tsaye cirko cirko suna mamaki Inna tace babu lafiya
kan gaskiya.
Wanan tafiya da gani bana dadin rai bane sai aka fara lekowa don gulma wai ana
gaishe ni da zuwa sai a fita ana dariya waje don sheri.
Inna ta koma kan yaya sani wanda ya gama aje kaya a wahalce dashi ta tsare shi
da idanuwan ta tana cewa daga ina ka tsinto Safiya kai kuma.
Baiyi magana ba sai samun wuri da yayi ya zauna yana neman ruwan sha yana jin
inna ta matsa tambayan shi saida ya gama kwakwadan ruwan shi ya sauke numfashi.
Ya dago kan shi yana fadan can lagos mana inna sai ya mayar da kan shi a kwanon
da yake shan ruwan.
Cikin mamaki da dafe kirjin ta tace har lagos katafi ka dauko ta dakin mijin ta
kana ko da hankali kuwa.
Sunyi tsaye akanshi cirko cirko suna sauraren shi maimakon ya yi magana sai ya
mike kawai ya fita daga gida batare da ya tankasu ba.
Can waje ya samu yan uwanshi su yaya Nura yana basu labarin rashin mutuncinn da
ya samu mijin nawakeyi don haka ya hade kan su akan suyi wa baba tawaye ga zancen.
Don gulma baba har ya fita kasuwa sai inna ta tura yaro ya kirashi a kasuwan don
tasan bazasu ji komai a wurin yaya Sani din ba.
Tun shiga na dakin ummi kuka nake yi ban iya magana ba har da ruwa da kunun da
ta aje mun ban iya shan ko daya ba a ciki.
Kanina ta tura ya kira mata gwagonta da sauri a gidan su don tasan ba lafiya ba
wanan zuwan nawa kan.
Ta fita ta kira su mama da inna kafin gwago din ta zo nan suka sakani gaba da
tambaya amma basu samu amsa komai ba ban da aukin kuka da nakeyi.
Gwago ta taso hankali a tashe tazo gidan namu cikin tashin hankali da son ganina
kamar karta shigo na kara sautin kuka na ina fadin ban komawa wallahi gwago kasheni
zai yi kinga duka,
Na shiga bude jikina ina nuna mashu ga tabo nan ko ina a jikin nawa ba iya ka
take ummina ta fashe da kuka inna ne kawai batai kuka a wurin .
Sai ga baba da yaron da ya tafi kiranshi sun dawo tun a kofan yake fadin ina
Safiyan take ne lafiya ko tare suke da mijin nata
Nan take gidan yai tsi kowa na sauraren abinda zai fito bakin na amma sai kara
sautin kuka na da nakeyi kawai.
Tsawa ya dakamin tare da tambaya na dacewa ke ki ba mutane amsa kin tsaya sai
kuka kike zubawa mutane, kukan ne zai fishe ki.
Daga kofa suka tsinkayo muryan yaya Nura da yaya sani suna cewa baba mijin nan
ta dan iska ne wallahi da ce anan arewa yake zaune ba abinda zai hana mu casa shi
wallahi.
Baba ya daka may tsawa da kai rufe muna baki don Allah yanzun dai may ya kawo
nan a wani dalili tazo .
Yaya Sani ya karbe zance cikin dakewa yace a dalili na tazo don ni naje har
lagos na dauko ta na zo da ita gida kar ya kashe ta ga banza kar mara galihu da
gata .
Wani kallo baba yake mashi ya ci gaba da cewa diba baba ka gani yadda duka ya
mayar da yariyan ga duk ta koma kamar wata ta baba wallahi.
Baba ya daka mai tsawa da kai dakata kaina ubanta ko kaine uwar ta ya girgiza
kai alaman a a baba yace to kada hurumin dauko ta ka dawo gida ita .
Baba ta yaya zanje na samu yana dukanta da zagi akan taki dafa masu abinci shida
karuwan shi ya doke ta yana zagi na fitan arziki.
Ina ruwan ka baba ya firfito da indo waje ya sake cewa nace ina na ruwan ka wa ya
aike ka zuwa dauko ta idan ya ga dama ya kashe ta mana ai mijinta ne kuma dan
uwantw.
Gwagon Ummi tace a a malam wanan ba hujja bane gaskiya kace fa ya kashe idan yaga
dama da yar uwar shi ce aiba zai mata wanan tsinanen duka haka ba.
Baba yace cikin daure fuskan karki saka bakinki ga zancen nan don ba maganan ki
bace diya dai diyatace kuma dan yar uwana na bawa ita.
Don haka ko yanka ta yake yi gunduwa gunduwa sai ta koma gidan nan shidin da
yaje ya dauko ta shi zai mai da ita dakin ta ta zauna ai kowa hakkuri yake a dakin
shi.
Mama tace bako da duka ba har da su tarmashe da sauran su sai dai wani abin kadai
tsaya ai bincike kada a dauki yarinya a mayar wani abu yaje ya samay ta ta halaka
fa.
Baba ya amshe zancen nata da cewa idan ta halaka aure ya halaka ta nace aure ya
halakata sai ummi na ta fashe da kukan bakin ciki yace sai kiyi amma komawa sai ta
koma wanan gidan ba fashi .
Ya juya ya fice gidan da banbami shiko yaya sani fadi yake yi ba inda zan tafi
wallahi abar shi yaje ya kashe ta din ba shike nan ba ai yar shi ne yace.
Wanan kalamai na yaya sani suka tayar min da hankali ina ihu ina fadin yaya Sani
kataimake ni bana komawa gidan nan kashe ni zaiyi wallahi.
********* ********* *********
A can lagos din bayan tafiya na bai tafi gidan su ba har tsawon kwana biyar yana
hadiyan bacin rai shi kadai.
Da farko ya dauka wasa ne yana cewa in tafi mana ya huta da wahala da yar kauye
maganganu dai na batacin yake fada gamay da ni din.
Sai yazo ina dan ya dawo zaiga gidan yai mashi girma ga wani irin duhu ba gyara
shi kuma bashi da time din zama yai gyaran.
Don haka ya bugo waya gidan su kannen shi suje su gyara mai gida basu so zuwa ba
suka tafi dole.
Sun dawo suna kwarara amai da zubar da miyau na kazantan da suka gani a gidan
amai ne ragowan giya ne kai komai sun gani a gidan.
Suna fadawa uwar su kan cewa basu kara zuwa gyara mai gida sai ta hausu da fada
inda take shiga ba nan take fita ba.
Idan ya rasa kudi babu mai bashi yadda yake samu ya amshe dan kudin da nake samu
ga maman biyu ko wurin kitso.
Yanzu babu inda yake samu sai dai ya arro ko kuma asai mai giyan kyata don
mashaya akwai su da wanan kara.
Sai ya kara sanin ashe ba karamin karya nake mashi a gidan ba gaskiya ne da aka
ce mutum dan adam yana da rana.
Ga yariyar da ya raina yaga ranan ta tun ba, aje ko ina ba gashi yasan
muhinmacina a gidan yasan ina hakkuri dashi to amma kuma shidin ya kasa kyautata
min ne bai san dalili ba.
Ina da matukar mahinmaci sai yanzu da ban gidan ya gane hakan duk da bakwa yake
dani ba sai ya ga dama amma sai tafiya ya zamay mashi yashin hankali da rashin
kwaciyan hankali , ya rasa may ke kawo mai jin yawan tsana na a rashi.
Kodon yawan zagina da mahaifiyan shi keyi ne a gaban take fadin kwadayin
mahaifina ya jawo min haka yana gani ita sakarai ne don kawai ya bata diya sai ta
bude mashi bakin aljihun ta na kashe mai kudin ta, ba dai a kan wanan diyar tashi
ba dai.
Wani yammaci sai gashi yazo gidan su dayamma nan mahaifiyar ta tare shi da zance
na tana zagi tana aibanta ni tare da zagin iyayye na kamar yadda ta saba yi idan
yazo.
Yai shiru yana sauraren ta sai can da abin ya isheshi yace mummy zuwa zakiyi fa,
ki dawo da ita don ba zan sake taba .
Uwar dago cikin mamaki tace haka zaka ce ni ina ganin bata dace da kai ba sam,
Yace mummy idan ba ita ba da iyayyen ta wata mace ne zatai hakkuri damu gaba
daya duk abinda muke mata tana zaune tana hakkuri sai zuwan dan uwata ya gudu da
ita.
Ke kanki kin san cewa indan yar ki akewa hakan bazaki taba lamunta haka ba .
Don haka ki kama hanya zuwa arewa ki dauko ta kidawo da ita nan shine saukin mu
bai kamata ace don ki aka dauki yarinya nan aka bani ita.
Don kwai ina danki ace baki kaunan ta ai gaskiya saadu ne da yake fadi da
taimakon ki muke wani abin.
Duk ke ke kara lalatamu muke abin da muka ga dama abin da bai dace ba idan munyi
sai baki iya hana mu , sai muga cewa shine daidai don bamu da masu yi muna fada a
rayuwan mu.
Shi wanan tsohon ya na shagamu can yake sha a nin shi bai damu ba da halin da
muke ciki a garin na babu ci babu shan shi.
Nan dai ya takewa uwa gidan wuta akan sai taje ta dawo mashi da matar shi ya
zube mata kudin mota anan ya fice yabarta tana tunane akai.
Yaushe yaran nan ya fara son Safiya hakan nan ban sani ba kodai shima sun
magance shine yadda suka magance yaya a gidan shi.
Yanzi ni idan naje da wani ido zan kalli mahaifin yarinya nan dashi nace na rike
mai ya amana ko mai.
********* ********* *********
Acan gida bayan baba ya kare fadan shi ya kare da cewa zai hada kudin mota da
zaran sun cika bani kara kwana mashi gidan shi.
Bayan fitan shi ne gwagon ummi ta rarashe ni da mama na samu na danci abinci da
aka aje mun sai dai ban iya cin komai ba ruwan kunu kawai na iya sha.
Dana dan gyagije namike naje nai wanka na fito har lokacin gwago tana nan zaune
na sa kaya a jikina,
Sai lokacin na fara ciro masu tsaraban da nazo dashi da wanda na sara ina
gwadawa mahaifiya ta nan dai muka cire ma kowa tsaraban shi.
Na fitar wa aka fitar ana tallata min ne diban ma maman Amina kawata aka kai
mata take tambayan nazo ne yaron ke fada mata cewa nazo tun jiya ina nan gidan mu.
Nan da nan aka saye kayan don na sake su da sauki sai gulma ya fara tashi a
gidan mu daga dakin inna suke fadin ai gwai dama sun san cewa yaran gwago ba su da
kamun kai.
Sundai yi shiru ne naje na dan dano ai maganin mu kenan uwa cikin ukuba diya ma
haka ai kadan muka gani.
Na dan samu sukuni don har na fara maida jikina da haske naje na gaida maman
Amina kawata mun dade muna hira da ita na dawo gida kada baba ya dawo bai samay ni
a gida ba don satan hanya nayi nazo gidan su.
Wai duk da halin da nadawo gidan mu ciki Inna sai da tai bakin ciki da gani na
haka na kodan dan kayan da na saro ne ake saida min ban sani ba.
Wani lokaci taimin gori akan rashin dace miji wana sain kuma ai min habaici wai
ina wa mutane takama natafi birni na waye.
Don dan kayan da nake sai daiwa yasa mutane na ribibin zuwa sayan unders na yara
da yan dogon riga na mata nashan iska da sauran tarkace.
Shine dalilin da inna ta rasa sukuni a cikin zuciyar ta tace wai ai gara na koma
akarasa ni can ko yaushe cikin ba