Showing 231001 words to 234000 words out of 258256 words
Chapter 78 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
jikin maimu yana barci saida na
karbeshi suka fito daga motan tare da daukar min jakkan hannu na muka nufi kofan
shiga gidan.
A rufe gidan yake na dan danna bell ajima kadan sai aka bude Nura ce ta fito tana
ganin mu tace ah wellcome madam.
Thanks nace mata ta matsa muka shiga tare da kanne na dake bina a baya tsakiyan
falon na nufa na shimfede yaron saman kujerun falon da suka sha gyara.
Na juya naje kuna Ac da fanka a lokaci guda take falin ya fara canza yanayin shi
daga zafi zuwa sanyi.
Har yanzu su maimu basu zauna ba nace dasu ku zauna mana gaku kamar masu tsoro da
sauri suka zauna a takure saman kujeran duk sun matse juna.
Zama nayi ina kokarin dauko key din daki na a cikin jakka na can kasa naji key
din na fito dashi daidai lokacin da Nura ta kawo muna ruwa da juices din kwali
gaban mu da kofuna ta aje.
Goran ruwan na dauka na fara tsiyaya a cup tare da masu nuni da su dauki ruwa su
sha mana suma da sauri kowa ta dauki cup din zasu zuba ruwa nace bazaku sha lemon
bane muna sha maimu tace min da sauri.
Bayan na shanye ruwan na aje cup din na mayar da jikina ga makarin kujeran tare
da lumshe idanuwa a hankali na danyi tunane sai kuma nayi ajiyan zuciya.
Wayana yayi kara daga cikin jakka na na jawo jakkan ina duba wayan yaya Saadune
yake kira na alokacin na dauka tare da fadin hello yaya .
Yace Safiya yaya hanyan na amsa da Alhamdullahi yaya.
Yace kuna ina yanzu ?
Gamu gida yaya na bashi amsa a takaice.
Yace ashe kun iso ke nan , ?
Eh yaya
Yace OK sannun ku da zuwa gani nan tafe yanzu mu gaisa
Sai kazo yaya kawai nace na kashe wayan ina kara mayar da kaina yadda yake da
farko.
Mikewa nayi na bude dakina yayin da su malam musa ke ta shigo muna da kaya cikin
gida shi da wanan security din Nura ta tarawa daidai kofan kitchen din mu.
Dakin na shiga sai duhu na kunna wutan dakin tare da jefa jakkana saman gado kaya
na fara cirewa a jikina na shiga wanka na dan dade ban fito ba.
Sai can na fito na sauya kayan jikina na samu Abba ya tashi daga barcin da yake
yi tv na kunna kafin in zauna na kalli dining naga Nura ta jera muna abinci a
wurin.
Makulin da nafito dashi daga daki na bude wani daki a kusa da na mummy nace da su
maimu ku taso kuga dakin ku ko.
Da sauri suka taso zuwa inda na kira su wanda sai kayi dan tafiya zuwa wurin nace
nan yayi maku ko yanzu dai gaku a cikin gidana.
Fushi ya kare maimu da baba dakin muka shiga dukan mu sai baza ido sukeyi kamar
matsorata a raina nace rayuwan kauye baiyi ba gaskiya.
Ji yadda yara ke wani iri kamar wa yanda basu yarda dani ba ko wani saman gadon
dakin na zauna nace suma su zauna Abba nake kokarin cire ma kayan jikin shi a
lokacin.
Nace kunga ga bayi nan don Allah banda kazanta don shi zai hadani ku ba komai ba
a kullun a wake bayin nan sau uku ko sau hudu a rana.
Taso muje in gwada maku yadda zakuyi amfani dashi nan dai na nuna masu komai
nace su kwaso kayan su sushigo dashi dakin a tare muka fito ina ce masu suyi wanka
muci abinci.
Sun gama sun fito shima Abba wanka nayi mai muka fito muka ci abinci muna kan ci
yaya saadu suka iso gidan shi da samira.
Ina ganin su nace chewgun ke nan kina lake ko yaushe masu miji ke nan ina kuma
kuka baro min diyata ?
Tana wurin uwarta tace ganin yaran yaya ce ina kuma kika kwaso wayan nan yan
kauyen haka hararan shi nayi nace ina kaga yan kauye kuma anan ?
Tace ke ko kin so dawowa ji yadda kika koma kin je kin cinye ma tsofi abinci kin
ki dawowa.
Na lumshe idona nace bari samira wallahi gida akwai dadi kamar karna dawo nake ke
ji sai naga gidan nan yayi mi wani irin girma wallahi ba hayaniya ba motsin kowa.
Kajiki da wani zance har yaushe kika bar nan din da zakice wai wani gida dadi ai
da ki zauna gida in baki dawo kin samu munyiwa uncle din ki aure ba.
Samira ke da kanki ke fada min haka lallai wata shigowan kishirya ki ya tsaya don
wanan watan zamu kawo maki wanan karfen kafan da ta leke wa yayana.
Don Allah Safiya ki daina zancen wanan gajan matar da ta tashi aiki don wulkanci
ta rasa wanda zata lekewa sai mijina yar iska.
Yace ai shike nan tunda kin san takon ta kuma da tayi maki tsiya bani go ahead
kawai safiya na shigo da hafsat kai tsaye
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/15/20, 7:06 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , ,
8🧕181
8️⃣
8️⃣
1️⃣ 1️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Bayan tafiyan su samira da basu dade ba na shige daki nayi laasar na fito muka
fara gyara kaya da Nura su maimu suna taya mu.
Kafin wani lokaci muyi ma komai muhalin shi mu aje a inda ya dace kuma na nuna
masu wanda zasu ci inda suna bukatan ci din.
Falo na dawo inda kanne na suke suna kallon na zauna sai dai ni ba kallon nake
yiba waya nake amsawa daga mutanen gidan mu suna tambaya na mun sauka lafiya .
Abincin dare suka ci ina zaune a kasa idan na sallamay sallah ishai wayana yayi
kara uncle ne ya kirana a lokacin na dauka da sallama tare da karawa a kunne na.
Uncle ina wuni na fara fadi ya sauke a jiyan zuciya kadan yace madam kun dawo ko
kuna can har yanzu nace uncle gani daki na muna ta kewan ka, gidan ya koma ba dadi
da baka nan.
Murmushi yayi tare da fadin I miss you to my wife ina Abba dasu mummy nace ga
Abban nan hannun maimu mummy kuma bata dawo ba.
Maimu ya maimaita sunan da na fada nace eh tare da su nazo ita da hindatu sin zo
muna hutun kwana biyu ne .
Yace bana ce ki samu yarinya kizo da ita ba idan zaki dawo don ki samu abokiyar
hira a gida nace ko yanzu ga su suna debe min kewa a gidan.
Bai kara yin magana sai cewan da yayi kara ma Abba waya inji muryan shi sai na
manna ma yaron waya a kunnen shi nan ya fara yin gwalanci kamar ya san abinda ake
nufi mika ma maimu wayan nayi tace ina wuni yaya yace a a ke yar kauye ashe kun
shigo gari sai yarinyar tace eh.
Amshe wayan nayi ina fadin kin yarda ke nan ke yar kauye ce ko na kara ma hindatu
tace cikin muryan ta mai sanyi ina wuni yaya ya amsa mata tare da tambayan da wa
nake magana tace hindu ce.
Sun jima yana masu tambayoyi wani su bashi amsa daidai wani kuma su fada mashi ba
daidai ba
Mukai sallama dashi yana fada min kada in rufe gida yanzu zaa kawo min sako in
kar ba godiya nayi mai tare da tambayan shi yaushe zai dawo ?
Yace kin damu in dawo ne ko wani abin kike so madam nace babu komai sai dai kewan
ka da mukeyi na rashinka a kusa damu.
Kararawa kofa yayi kara ni da kaina na tashi na bude gidan malam musa driver ne
da ledoji da kwalaye ya shigo dasu ya koma ya dauko sauran sai leda daya miko min
hannu da hannu na karba .
Bayan na karba na fahinci maye a cikin ledan don jin zafi danayi daga cikin
ledan yana tashi da kamshi.
Yayi muna sallama nace ya tsaya ina zuwa yace a a hajiya nima maigida ya saya min
nawa na gode wallahi sai da safen ku yana dan dukar da kai kasa alaman girmamawa
gare ni .
Yana fita na koma wurin kayan daya shigo dasu ina duba inda naga kayan tea ne
mayan gwangoni madara biyu sai na milo da nescafe da ovoltin sai katon din sugar na
kwali.
Dayan kuma fruit ne a ciki iri iri masu kyau fresh one murmushi nayi don akwai
wanan abin daduk aka sayo muna a gidan.
Ledan da kamshi ke tashi a cikin sa wanda tun ban bude ba na fahinci may ye a
cikin wanan ledan kaji ne gassasu guda uku kosassu sun gasu dakyau irin gasuwan
resturant din nan da albasa da kabeji da sauran tarkace wanda yakan sawo muci a
gidan.
Yaran dake satan kallo nace hindatu ta dauko plate a kitchen guda uku kowa ya
dauki kazan daya yaci maimu tace anty duka nace eh duka maimu.
Ban koma ta kansu ba ina faman dakilan wayana suna ci suna dan magana kasa kasa
danaji maganan yayi yawa na dago ina cewa dasu wai may kuke fadi ne kasa kasa.
Wai cewa tayi kada mu cinye duka mu rage gobe muci saura nace akan may zaku rage
idan kuna iya ci duka kuci mana.
Basu iya cinyewa dukka ba duk zalaman su anan suka barshi nace suje su saka a
fridge ban ci nawa sai fruit din naci kawai bamu dade ba nace suje su kwanta su
huta.
Sai da na tabbatar sunyi barci na dauki Abba zuws dakina na kashe wutan falon
komai daya kamata in kashe na kashe na shiga na kwanta asuba ta gari.
Da safe muna tashi bayan munyi sallah nace suje suyi wanka kuma kullun da sunyi
sallah haka zasu dinga yi suka shige daki don yin wankan dana ce suyi.
Abba nayiwa wanka na shirya shi na dauke shi nakai masu dakin shi na dawo nayi
nawa wankan na shirya.
Nura ta iso ta fara aikin hada muna breakfast din safe a lokacin na shiga kitchen
din nace kada tayi wani mai yawa don ba a ci sosai.
Bayan mun karya ne muka zauna su kallo ya dauke masu hankali waya na na dauko na
kira samira muka dan taba hira da ita nace idan ta samu lokaci ta shigo don Allah
ina son tayiwa su maimu sayayya kayan sawa don ni ba dama in fita uncle bai gari.
Tace zata shigo zuwa rana asan abinyi din akai nan muka kashe wayan nima kallon
na kama yi don shine aikina kawai tunda ba fita nakeyi ko wani abuba.
Sai idan uncle yana gari ne watarana nakan shiga in muna abincin garagajiya don
yana so ita kuma Nura bata iya ba sosai.
Hajiya baaba na kira don mu gaisa tace na dawo ko ina gida har yanzu nace hajiya
mun dawo jiya muna Abuja yanzu.
Tace yaya muka baro su nace suna lafiya suna gaida ku baaba tace to yanzun dai
kinje gida hankali ya kwanta ko ?
Don Allah safiya ki bi mijiki a yadda yake so ku zauna lafiya don Allah yanzu
tunda kin san halin shi kibishi a yadda yake ban son yawan fitin da kuke wayan yi
ko yaushe din nan.
Insha Allahu baaba zanyi yadda kikace din tace nasan komai safiya nasan kina
hakuri sosai dashi shima din halin shine kawai haka bawai yana yi cikin son ranshi
bane.
Godiya nayi mata na kashe wayan ina tunanen maganan da mukayi da hajiya din
shigowan samira gidan ya kawar min da tunanen da nakeyi.
Samira ta shigo na bata kudi nace taje dasu don kada a samu akasi tace bata zuwa
da kauyawa ko ina nace watarana kina ganin su nan sai sun fiki wayewa.
Tana masu sheri suka fita taja motan yaya tabar gidan tare dasu haka yasa na samu
kwaciya nayi barci sosai dani da Abba kadai a gidan.
Zuwa rana suka dawo da kayan da ta sawo masu din kayan sunyi kyau sosai na bata
atamfofi a cikin kayana da zata kai masu dinki.
Nace ina son yaran nan suyi clean ne samira su din rabin jikina ne da komai nawa
watarana sune wa yanda zasu tallafa min a lokacin da nawa kadfin ya kare.
Tace gaskiya ne Safiya da har ina ganin wautar ki na dauko su sai yanzu na gane
hikimar yin hakan da kikayi akan su.
Zasu taimaka maki kwarai a rayuwa ki don naka sai naka haka abin yake wallahi
Allah ya taya ki rokon su nace amin samira.
Sannu a hankali nake koya masu komai kuma suna ganewa sosai don sun sauya kamar
basu ba don da gani sun saurari fadan da akai masu da zasu zo.
Sai da uncle ya kara sati biyu ranan alhamis ya dawo da dare ni dai ina barci
naji wayana yana ruri na dauka muryan shi naji yana fadin bude min gida don Allah.
Da sauri na mike tare da daukan key na fita daga dakin na bude gida da sauri
yana tsaye yadan jigina jikin shi a bango suith din shi na sagale a kafadan shi.
Mirmushi na sake a fuskana tare da fadin sannu da zuwa uncle hannuwan shi ya bude
da sauri na shige ciki .
Yana rike dani muka shiga gidan bai nufi dakin shi ba sai da ya tafi yaga Abba
dake barci na wuce na bude mai daki tare da kunna naurorin dakin na hada mai ruwan
wanka.
Kayan shi ake shigowa dasu gidan daya dawo dasu sun gama na rufe gida tare da yi
masu sai da safe.
Ya dauko yaron ya nufi dakin shi dashi a kafadan shi nan na gama komai nabi bayan
su nima tari naji yana yi sai muryan shi daya dan shake bai fita sosai.
Uncle baka jin dadi ne dan murmushi yayi yana kara gyara ma yaron shi kwanciya da
kyau ya juyo gareni yana fadin .
Mura ne ya kamani kin san yanayin sanyi da ake yi yanzu acan ya fara kokarin cire
kayan jikin shi na juya na fita zuwa kitchen inda na hada mashi shayi da cita da
kanunfari na kowo mai dakin har lokacin bai fito daga wanka ba.
Bakin gado na zauna ina jiran shi koda ya fito yana goge ruwan dake jikin shi
tari ya kama yi a lokacin tashi nayi na fara tsiyaya mashi ruwan tea din dana hada
mashi a kofi.
Ya gama yasa kaya a jikin shi ya nufo inda nake jiran shi da cup din tea din da
nake dan motsawa a hankali cup din na miko mai bayan naga ya zauna a saman gadon.
Karba yayi yana tari sosai hankali na ya daga sosai ya dan kurba kusan sau biyu
yace na kwana biyu ina tarin nan tun acan.
Sannu nayi mai nace yi kokari ka shanye tea din zai taimaka maka ka samu barci
da sauki don wanan tarin dake damun ka.
Ido ya dan lumshe kadan yace yaya kibaro mutanen gida nace duk suna lafiya suna
gaida ku sun ce kuma ai masu godiya sosai.
Da akai may yana miko min kofin daya shanye tea din na aje a saman dan drower
dake gefe na hawayayi saman godon ya dan dukule a wuri daya kamar mai jin sanyi.
Hankali ya tashi ga yanayi da naga yake ciki sai dai yana kokarin kwantar min da
hakali da fadin ai murna ne kawai ke damun shi a lokacin.
Ki kwanta yace dani haka na kwanta a sanyayye tare da tausayin kan mu ga halin
da muke ciki na rashin lafiya a jikin mu .
Ni yanzu in uncle ya mutu ya barni yaya zanyi da rayuwana jamma, a da sauri na
kawar da wanan tunanen a raina tare da kai hannu na na dan shafa Abba dake barci a
gefe na.
Ina sauke ajiyan zuciya hannu na guda nakai a saman goshin uncle wanda idon shi
ke a lumshe a lokacin.
A haka barci ya dauke mu dama karfe uku na dare yayi ko haka yasa mu makara da
safe ba laifi ya samu barci kamar yadda nace mashi din zai samu.
Washe gari ban fito daga dakin uncle da wuri ba don makaran da mukayi yan matana
har sun fito sun zauna falo kin san dan kauye bai barcin safe shi.
Sai raba ido suke suga inda zan fito a gidan har Nura ta shigo ta fara aikin ta
sacen na fito ganin inda na fito ina sabale da Abba daya tashi daga barci nayi mai
wanka acan.
Da sauri suka taso suna gaida ni da kwana na amsa masu cikin dadin rai ina fada
masu baban Abba ya dawo jiya da dare .
Sun nuna farin cikin su a hakan daki na shiga tare da kiran su muje dakin nawa a
lokacin a saman gado na aje Abba na juya dauko mashi kaya in saka mashi.
Hindatu ta dauke shi tana mashi wasa maimu tace anty na zata kin fita ne da ban
ganki ba nace aini maimu ban faye fita unguwa ba sai idan ya kama.
Mun gama muka fito falo bayan na shirya suna zaune suna jirana a dakin sai da
nagama tsab muka fito lokacin had Nura ta hada abinci a table na dan duba nake fada
mata dawowan uncle tea din jiya na kara hada mai tare da bude fridge na dauko hadin
tsoho na zuba a cup na nufi dakin shi.
Na samu ya tashi yana zaune yana duban wasu takardu a hannun