Showing 126001 words to 129000 words out of 258256 words
Chapter 43 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
fadin anya malam ba a bin abinga sannu ayi
binciken wani irin miji yarinyar ta kwaso muna kada idon mu ya rufe.
Yace nima dai abinda nake tunane kenan yaya Sani yace zaka iya yin bincike
mutumin da keda company na tayoyin mota da da gidajen mai zaku tsaya yin wani
bincike.
Su wayanda take wuri su amana basu san ya kamata bane da zasu hada ta dashi basu
hana ba ya mike yana fadin ni zamu shiga birni yanzu sai na dawo.
Kaunana baba yace ta lalabo ni a waya sai aka samu akasi ba layin neatwork wayan
bai shiga ba lokacin.
Zuwa rana su yaya sani suka zo da mutane masu aiki har cikin gida suka shiga aka
shiga aune aunen gidan da baysn gida inda filin baba ya tsaya.
Za a fara daga dakunan su inna don haka zasu fake a wani wurin sai ko inna tace
bata san da hakan ba sai da baba yayi da gaske yace sai dai tabar mai gidan shi.
Mutane suka shiga tsakanin su duk wanda ya tambaya sai a fada mai mijin Safiya ne
da ta samu ya aiko a rushe gidan nasu.
Karamin gari da daukan magana sai magana yabi gari washe gari suka tashi da masu
aiki a gidan.
Inda suka koma gida jen yan uwa da zama suda yaran su ummi na kan gidan gwagon ta
koma ita da yaranta da kayan su.
Mama ma haka inna kuma gidan yan uwanta ba wanda ya yarda ta koma can dole
family house din su baba ta koma.
Ko wani gida yaya sani yakai masu abinci kamar yadda aka umurce shi yayi aiki ake
yi ba dare ba rana gari duk an dauki maganan kwaaaa.
********* ********* *********
Jinya yayi so sai duk ya ramay ya fita hayacin shi karshe ma sai da ya dawo
gidan gwago akai jinyan shi.
Yanzu kowa yasan abinda ya samay shi don tun a karuwan shi aka san suna dauke da
cutan an kaita gida ta mutu can.
Gwago kulun kuka takeyi tana fafin Ahmed baka kyauta min ba kasa na cuci diyar
mutane gashi yanzu ni da garin mu amma ina kunya zuwa.
Don ko naje ban san da wani ido zan kalle su ba kasa na rabu da dan uwana mutumin
arziki da sanin ya kamata.
Yarinyar nan tana da ma bidi amma don a raya zumunci ya rufe idon shi yace sai
kai kuma akayi hakan.
Ahmed dake kwace saman wani tsohon katifa yace mummy kada ki bleming dina ni
kadai a cikin maganan nan ai gaban ki nake dauko mata tun ina yaro na amma baki
hanani ba.
Sai yanzu da abu ya baci muna ne zaki tsamay hannu ki ciki duk waja muna saboda
fitinar ki baba ya bar garin nan .
Kin hana ya zauna kusa damu ya ga halin da muke ciki ya kwabe mu tun yana zuwa
har ya daina zuwa yanzu ya tare a gurin sabuwar matar shi.
Tace abinda zaka fadamin ke nan ko bayan komai a kanka ne ya faru don yana
ganin yarda nake sakar maka kudi yai magana nace ina ya fito.
Nan dai sukai ta sa insa da dan nata sai da sadiya ta shiga tsakanin su taja
gwago din waje kar abin yai masu yawa gashi kwance ba moriya.
Zuwan yaya Saadune ya kaishi asibiti suka karbi magani har ya fara jin saukin
jikin shi ya tatara ya koma gidan shi sai dai hakan bai sa yabar halin shi ba.
Yaya saadu yazo gida kamar yadda yai alkawari ya samu ana aikin gidan mu gadan
gadan ya samu baba yaji sauki sosai har yana dan fita kasuwa.
Yai masu alheri ya dawo bai tsaya lagos ba don wurin matar shi dake shirin
haihuwa ya wuce direct sai da ya isa ya kirani washe gari da karfe hudu.
Ban daki na bar wayan na caji sai da na shigo ne na samu miscall din shi a nan
nan nai mai kira biyu bai dauka ba ga na uku matar shi ta dauka tana cewa bai nan
ne.
Nace madam yaya kike yaya tsufa ta amsa min da murmushi da lafiya tace ke haka
akeyi baki lekomu ba kuma kina lagos.
Nace kada ki damu idan kin haihu zan shigo sai nayi maki one week zan koma tace
kamar da gaske nace bari ki gani ko yanzu shiga daki ki haihubin banzo ba .
Ta kwashe da dariya tace to Allah ya kaimu lafiya idan ya dawo zan fada mashi kin
kira baki samay shi ba.
Mukai sallama na kashe wayan na koma har kokina sai dai ban faye fita irin da ba
don gidan in ba anty ke nan ba kamar suna shan kanshi.
Shiya sa ban damu da shiga harkan kowa ba a cikin su sai dai ina tunanen Ita
Faiza idan fati na fushi dani ne akan dalilinta na son sulaiman .
To ita akan may take fushinta dani ni dai ban san nayi mata wani abu ba kafin in
wuce gida.
Abinda ban sani ba ashe baya na ashe sunyi meeting a kaina kan nazo na samay su a
gida anty ta fifitani a kan su .
Bata kallon kowa da gashi a gidan sai ni su tun yaushe suke ba a nema masu miji
ba sai ni da zuwa don nazo da sihirin mu na yan kauye sai ace nice ake kokarin zuwa
dani wuri.
Sai suka yanke shawaran su hade mi kai ta yadda in na dawo zan rasa gane kan su
sai na raina kaina a cikin su.
Wanan dalilin yasa ban gane ma kan su sai waccan tabi can wanan tabi nan sai su
watse su barni ni kuma dana ga hakan sai nima na fara share su kawai.
Gashi yanzu na dawo sai shige da fita nake yi na doke sanin su sai suka shiga
gulma wai kila ba gida naje ba mun hada baki ne da anty ta turani wurin maza na
samo kudi.
Tun sunayin zancen a boye har na tsura su sunayi nan nai masu tas sai suka shiga
rokona wai inyi masu hakuri kada anty taji nasan korar su zatayi a gidan.
Nace amma idan na karajin wani abu makamancin haka zan fada mata dan ta dauka min
mataki akansu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,
4️⃣5️⃣4️⃣
4️⃣
🧕🏿 5️⃣5️⃣4️⃣
YAR UWA KI TUNA NOVEL NA KUDI NE DON DARAJAN ANNABI KADA KI FITAR MIN DA NOVEL WAJE
KE KUMA IDAN AN FITAR KIKA KARANTA BAKI BIYA HAKKINA A KAN KI, , , , , , ,
Bayan anty ta fita wurin aiki ita da yara na gama abinda zan iya taya funke na
fannin aiki sai na koma daki na kwanta abina.
Can barci ya soma dauka na sai naji anturo kofan dakin alaman mutum ya shigo haka
yasa na bude idona don ganin ko waye ya shigo din.
Faiza ce fuskanta dauke da murmushi tace ba dai kin kwanta ba ne nace na kwanta
eh barci nake son in dan yi na wani lokaci.
Zama naga tayi a bakin gadona abinda ta dade batai min ba sai gashi yau tazo tana
yi don haka nasan da wani manufa tazo.
Magana muke yi amma sai bin dakin nawa take yi da kallo kamar mai son ganin wani
abu tace gida fa ya karbe ki safiya.
Kin ga yadda kika sauya gaba daya kamar bake ba sai nayi murmushi nace kin san
gida dadi gare shi ai.
Tace sai kuma naji wani labari a bakin anty da nai mamakin jin shi wai Sulaiman
zaki aura ba da dadewa ba ?
Faiza ke nan idan haka ne ai gida guda muke dake da a bakina zaki ji labari sai
tace gaskiya kan ai na dauka da gaskiya ne sai in ce halan baki san abinda ke
damuwan shi ba.
Da sauri nace may fa ?
Sai tai shiru tace kardai aji a bakina fadi ba a tambayeka.
Nace ai ya kamata na sani don kariya sai tace dama ji nayi ana fadin kila yana da
cutane a jikin shi shiyasa bai son ai maganan aure dashi.
Haka naji a gida suna fada shiyasa nace barin fada maki don ki sani kada matar
gidan nan ta cuta maki don kudi.
Baki ganin yadda take nan nan dashi ta kwace ma kowa shi idan ba itaba babu wanda
yake shiri dashi a cikin yan uwan mu kaf.
Ita kadai ya yarda da ita yake mu,amula da ita itama din nasan don kudin shi ne
take hurda dashi fiye da kowa.
Mamaki ya hana ince mata komai sai sauraren ta da nake yi rashin magana na baisa
ta fasa magana ba.
Taci gaba da fadin kin gashi nan haka yake kamar bakin bature komai nashi a
ka,idance yake yin shi.
Idan bai so ba sai ya nuna kamar bai sanka ba , babu dan uwan dake jin dadinsa
sai wanda yaso.
Haka shima bai kula kowa yana takama da kudi a cikin dangin idan kinga gidan da
ya kera a bauchi sai kin kama baki.
Babu kowa a ciki sai mahaifiyar shi da kaunar shi dake bangare guda amma duk
girman gidan nan part din shi a rufe yake bai sa kowa a ciki ba.
Ni ina ma mamakin yadda idan na gaidashi anan yake amsa min a sake don a gida
baka ko ganin shi balle ma ku gaisa dashi.
Nace aiko wanan halin bai kamance shi ba sai ka ganshi kamar babu ruwan sa ashe
haka yake ?
Ta mike ta na cewa barin koma dama shiya kawo ni in fada maki in baki sani ba
kada ai maki rifa rufa saboda kudi.
Nace amma ni sai banga wani kudin da zai rudi anty dashi ba don ko mijin ta ma
yana dashi itama ba a zaune take ba.
Sai tace Safiya kenan.
Wa yaki kudi ko wa yaki kari a rayuwa balle ma ita ai ba abinda take so kamar kudi
ta fadi tana kara nufar kofan fita daga daki sai ta juyo tace amma fa maganan nan
ya tsaya dagani sai ke.
Nan ta fita ta barni da tunane fan a raina duk kokarin da boyar Allah nan take
muna amma suna fakewa a bayanta suna zagin ta.
Nan dai nayi ta tunane kala kala har nagaji barci ya kwashe sai dai a cikin
tunanen nawa ba abinda nake tunawa kamar abinda ta fada gamay da sulaiman din.
Sai kuma abin ya tsaya mun a raina nace kardai zan kara tsundumawa ne ga auren
ukuba a rayuwa nace ni kuma haka rayuwa tazo min a bahaggon rayuwa komai zan gani
sai akasin sa.
Karan wayan ummi na ne ya tayar dani daga barci na mika hannu na jawo wayan dake
caji don na samata ringing din mamana mamana mai share hawayena.
Na yi sallama ta karba nan muka shiga gaisawa ina tambayan mutanen gida tana bani
amsa da suna lafiya.
Tace yar nan shi kuma wanan bawan Allahn haka yasama kan shi lalura akan mu nace
ummi wake nan fa ?
Tace mai neman ki mana ya turo yayan ki sani da abin arziki doya sai da aka shake
bayan mota da shi da manja muna murna.
Ashe magana bai kare ba sai ga sani yace wai ya turo shi a rushe gidan mu a gyara
a cikin wata daya anya yar nan kinyi bincike a kan sa kuwa.
Kwance nake bansan lokacin dana mike zaune ba nace ummi a rushe gidan mu fa
kikace ?
Ta au ke baki ma sani ba ke nan ai yanzu duk bamu gidan kowa na gidan su sai inna
ku ce a family house yan uwanta sunki yarda ta zauna masu a gida don sanin halinta.
Assha baiyi kyau ba tace halinta ya ja mata koda akazo da zancen gyaran gidan ai
sai da tai halin nata mama ku ne kawai tai ta samaku albarka kedashi.
Taki kwashe kayan ta sai da mutane suka taru a kanta tonon asiri zallah abin ba
dadin ji wallahi nace Allah ya kyauta.
Amma ummi ni abin ya bani maki don ko yau da safe mun gaisa dashi amma bai sanar
dani zancen ba.
Watau yana son ya bani mamaki ko kuma baison godiya kamar yadda yace bai son yayi
alheri a tsaya ana mashi godiya.
Sai naji ummi tace ikon Allah shine kyauta sahihi wanda ake so Allah zai saka ma
mutum da alheri.
Nisawa nayi nace ummi nifa yanzu har tsoro nake ji bakiga kayan da ya saya min ba
da zan dawo har akwati guda shake da kaya.
Ummi tace ikon Allah shi bai gajiya ne ?
Na amsa mata da kuma bai son godiya.
Tace Allah ya kyauta kuma ya saka da alheri ni abinda na fahinta shine bai son
azo daurin aure a raina ma inda ya dauko mata ne shiyasa yace ai gyara a cikin wata
guda kacal.
Nace ummi ai kowa yasan ni yar tallakane tun da ubana ba kowa bane da aka sani
tace Allah ya sanmu ai nace shi kan.
Mun dade muna magana da ummi a waya har ta bani gwago buka gaisa nayi masu godiya
tace akan may ai nan gidane ga ummi.
********* ********* *********
Sai da nayi sallah na fito daga daki ban dade da fitowa ba anty ta shigo gidan
mun tare ta da sannu da zuwa kamar kullun.
Security din gidan yana biye da ita da kayan da ta dawo gidan dashi na mike na
karbi kayan daga hannun shi zuwa ciki .
Bata zauna ba ta wuce dakin ta nasan kaya take son sauyawa tayi sallah kafin ta
fito cin abinci don haka take yi idan ta dawo a wanan lokacin.
Ta sauko lokacin ta sauya kayan jikin ta tana zuwa ta zube tana fadin don Allah
ku taimaka min da abinci.
Ni na mike naje hado mata sai take cewa su Faiza wai ku baku da aiki sai
kwanciya ko mutum na magana bakwa dagawa.
Faiza ne tace kai madam kafin mutum ya daga safiya ta tafi hado maki sai fati
dake ta faman dakalan wayan ta dago tace ba yar neman suna bane.
Komai sai tai ta nuna ita ta kamar tafi kowa alhalin bata kai kowa acikin mu ba
ita ma yar kauye da ita ba a raina ta ba zata raina mutane.
Kallon ta anty keyi tace Fati ina wanan magana ya fito haka daga bakin ki har
kike kokarin aibanta yar uwata a gabana.
Bari kiji ba a raina mutu idan kaga mutum baka san abin da Allah zai mai dashi
ba wata rana kafinta karasa sai fati tace.
Ba dai wanan banza ba za ace wai tafini wata rana may zata iya gwada min ko
ayanzu inba farin fata ba ni ma idan ina so sai in sayo a shago inyi.
Amma ke baki da hankali sha sha mara hankali ke wai sai yau shene zakiyi hankali
a rayuwan ki ?
Ta mike ta shige tana guna guni na aje abincin a gaban ta don nasan bata tashi
zuwa dining ci yadda take kiran yunwa take ji.
Nan muka zauna da anty tana cin abinci tana bamu labarin iri kayan da suka kama
a office din su na yan smogal.
Nace anty yanzu may zakuyi da kayan tace idan sun dade basu iya kwata ba sai muyi
option din shi gama su so.
Nace wai amma anty sai kuma nayi shiru tace fadi mana tana kai spoon din abinci
ga bakin ta nace babu komai.
Sai tayi dariya tace haka aikin namu yake Safiya sai nayi murmushi kawai nace ai
na fahinta har yamma muna wurin zaune sai sallah muka tashi zuwa yi.
Ban fito ba ko da na idar sai anty ni ta aiko kira na don haka na tashi na tafi
amsa kiran nata bata falo tana dakin ta don haka na haura sama.
Tana zaune a kasa tana waya na shigo don haka na samu wuri gefe daya ina jiran ta
ledan da ta shigo dashi ta nuna min da hannu alaman in dauko mata.
Na dauko na ajeye taimin alama da in bude na durkusa a gaban ta ina bude ledan
ina gama budewa ta fara ciro kayan dake ciki.
Tana dubawa ina binta da kallo wanda kayane nasi yan biyun ta a ciki nace a raina
ita dai bata gajiya da kwaso ma yaran ta kaya.
Na nisa tare da cewa a raina haka sulaiman yake so na dashi ya cika ni da suturu
ni kuma ban saba da hakan da yake son koya min ba.
Muryan anty ne ya katse ni da cewa kayan suna da kyau Safiya na fara tanadin
kayan da zasuyi bukin kune dashi don naga sulaiman bada wasa yake yi ba.
Kin san shi idan ya tashi yin abin shi bai tsaya bata lokaci naso ace kun dan
kara fahintar juna dashi.
Amma kuma naga har daddy ya goya mashi baya wai ai ba bukin saurayi da budurwa
zakuyi ba may za a tsaya jira kuma.
Jiya ma mahaifiyar shi ta kirani akan maganan naku nake mata bayani abinda ake
ciki a zancen.
Nace anty ashe gida daya suke da mahaifiyar shi ta dago kai da sauri tace waya
fada maki safiya ?
Sai nayi shiru tace don Allah a ina kikaji nai murmushi tun da ta hadani da Allah
nace Faiza.
Sai naji tace munafuka yaya tayi ta sani duk wanan boyon da nake masu munafuka
sai da ta gane.
Kai faiza akwai gulma wallahi.
To da suke gida guda da mshaifiyar shi ke ina ruwan ki tunda sai wani dalili
yake