Showing 12001 words to 15000 words out of 258256 words

Chapter 5 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

bani karfin gwiwar da tayi akan na hakkura naga ya gudun shi
in yasu sai nayanke hukunci akai.
Sulaiman mutumin kirki ne sosai a yadda na fahinci shi ba a garin yake zama ba
zuwa yake duk karshen wata kokuma farkon wata.
Idan zaizo yakan yo muna sayayya yadda ya kamata ya zo muna dashi har kullun yazo
bani sakewa dashi amma shi sai yake daukan hakan da kurciyane kawai.
Tun yana zuwa ban sauraren shi har yakai na fara sauraren shi ina dan bashi
lokaci sannu sannu har kowa ya fara sanin shi a gidan mu.
Dan idan yazo zai ba da kudi da kayan rabo irin su sabulu da manshafi a rabawa
mutanen gidan mu, inda ni kuma yakan kawo min kayan provition na amfanina.
Wannan abin shiya tsone idon mutanen gidan mu don walwalan da suke ganin mun samu
a gidan.
Tsegumi da kazafi yaki karewa a gidan sai cewa suke wai babana yaga kudi shiyasa
idon shi ya rufe bai iya magana wai har cewa sukeyi .
Sulaiman na dauka na da mota muna fita yana yawo a cikin gari maganganu dai
marasa dadi suke kai da kawo akan zancen.
Sai dai ummi na hankalinta yakan tashi dajin wannan zancen sai da dare tan tayar
dani daga barci ta sakani a gaba da cewa.
Yar nan kirufa min asiri ki kamaka kan ki karki tona min asiri a cikin abokan
zama abin na da suke fada gamay dake Allah yasa ba gaskiya bane kodai daya ke
nasan ki nasan halin ki.
Nasan abin da zaki iya da wanda bazaki iya ba amma dai dolene na kara tsawata
maki akan hakan.
Don Allah ki kafa mutuncin ki ki rufa muna asiri yar nan bani kadai ba har da
mahaifin ki nakan son rantse mata cewa ba gaskiya bane sai ta dakatar dani da cewa
bar ni na fada maki yar nan.
Nice mai fada maki gaskiya duk duniyan nan ku nake da ku nake gani ina alfahari a
duniyan.
Idan ummi tafadi haka nakan ji wani irin tausayin ta a raina wana abin yasa
sulaiman ya rage zuwa gidan mu wanda
Hakan kuma suma ya shafe su don dan abin da suke samu ya daina zuwa yana basu
sai kuma suka koma cewa .
Ya gama dani ya gudu suna dariya suna fadin na goga masu tsiya a ranan da sukai
dariya a ranan kuma yan uwan sukaima suka zo wurin babana da kaya niki niki na nema
wa sulaiman aure na.
Amsan da baba ya basu shine sai yayi shawara da matan shi don ina da yanne har
hudu a gaba na ..
Yara suka shigo da kaya ciki niki niki kowa ya fito yana gani ana sake magana
nidai muna daki da mahaifiya na ba wanda yaleko daga cikin mu.
Ana cikin wanan haya niyar gwago lagos ta bugowa mama waya ta layin Nura yana bawa
mama ba, a jin abinda take fada sai da mama ta shiga daki.
Tace wai hayaniyar may kuke yi a gidan ku ne haka ina jin na hayaniya kamar
mutane da yawa wurin.
Mama ta ba ta amsa da muna kallon kayan da aka kawowa Safiya ne shi meke ta
surutu.
Gwago tace wacce safiya ba dai safoyan naku da nake son naiwa yaya magana ba a
kanta.
Mama tace Safiya dai yar wirin Rabi na nan gidan nake maki magana sai gwago tace
kaya kayan fa?.
Akwai matsala ne inji mama take tamabayan ta akwa matsala kan don dama ina son
nemawa yaron nan auren ta ne yanzu kuma naji wani magana can.
A, a ta yaya za ayi gida bai koshiba akaiwa daji dole asan nayi dai akan haka
amma dai zan fadawa malam di don ya sani a san abin yi.
Nan dai sukayi kulle kullen su da mama har suka gama mama ta kashe wayan tun da
mama ta fito take anna shuwa da guda a tsakar gadan karshen ta suka shige daki da
inna.
Shiru shiru basu fito ba sai wani lokaci mai tsawo suka fito suna murna suna
dariya tun nan Ummi na tasha jinin jikin ta.
Washegari da safe magana ya fara fitowa a gidan mu cewa wai dan gwago na lagos
za a bani da farko jin su mukeyi sai ranan da sulaiman yazo zan fita babana ya
dakatar dani.
Ya tashi ya fita zuwa wurin shi bansan may ya fada mashi ba sai tashin motan
sulaiman kawai naji ya tafi.
Baba yana dawowa cikin gida ya kwala min kira da sauri nafito daga dakin mu yake
cewa dani .
Safiya wanan yaron dake zuwa wurin ki na dakatar dashi don zan hadaki da dan
wurin gwogon ki na lagos ne.
Saboda haka daga yau bani sin jin zancen wanan yaron a gidan nan duk abin da kuka
san kunci na shi ku tattara mashi a mayar mashi da abin shi.
Gaba na ne ya fadi na dago kai a razane na kalli babana zan yi magana sai hawaye
ya hana ni fadin komai muryan baba ne ke cewa kin dai ji abanda na fada maki.
Nace a sanyayye naji baba ina mikewa ya kwala wa ummi kira yana cewa ina rabin
take ne kizo kiji ke ma hukuncin da na yankewa yar ki.
Ummi ta fito duk jamaan gidan sukayi tsit suna sauraren shi yace yar daga yau ban
son na kara ganin wani yazo gun ta.
Kuma ku hada nashi i nashi tun wuri ku mayar shi da kayan sa kinji magana na ya
karasa kamar mai fada.
Daga kofan inna inda take zaune tace, hum,in a, she akwaita kuwa a gidan nan,
yo wasu kaya kayan kayan da ake shigewa dasu daki muku,muku a cinye ina za a samay
su ai yau ga ranan ta.
Ummi ta kada kai kawai ta wuce zuwa dakin ta koda ta shiga ta samu na kifa kai a
gwiwa na ina kuka.
Cikin kuka nace ummi kin ji abinda baba yace,
Naji amma yaya zamuyi kin san halinsa baban naku sarai balle maganan da aka
shirya yin shi akan mu.
Dom haka kar ma kisaka wa ranki damuwa akan abinda ki kasan bamai hanawa sai
Allah
Tace dani ba kuka zakiyi ba don kuka bashine mafita ga wanan zancen ba samun
mafita shine abin yi.
Da yake cewa dan gwagon ki zai hada ku dashi shidin ma ya san ki ne ko kuwa dai
wani irin hadi zaiyi.
Nace ummi Allah yasa dai ba wanan mai shan taban bana yake nufi ba zai hada ni
dashi aure.
Yanzu dai ki bari kisamu gwago da safe ki sanar da ita halin da ake ciki don mu
san mafita.
Nace ummi kina ganin baba zai yarda da maganan gwago har ya yarda yajanye maganan
shi .
Tace sai mun jeraba mun gani tukun don a gaskiya in dai yaran laraba ne ban ga
mai tarbiyan da zace zaki aura a cikin su ba.
Yaran da idon su ya bude da duniya basu kallon kowa da daraja a idon su kowa a
hankade suke ganin shi.
Kuka na saka wa ummi a cikin daki tu tana saurare na har tagaji ta kwanta ta
bar ni nasan itama dai ta kwanta ne ba wai barci ta samu yi ba.
Da safe ban shiga makaranta ba gidan gwagon ummi naje na saka ta gaba ina ta kuka
da kallamai masu tsuma zuciya.
Gwago tai rarashin duniya ta ga ina batan shiga cikin wani hal dole ta aikwa
diyan ta suzo tana neman su.
Sin zo sun samay ni take mayar masu da abin da ke faruwa kowan su yace gaskiya
takuran yai yawa har da auren ma baza a bari inyi wanda nake so ba.
Sun yake magana cewa zasu je su sami babana akan zancen don su dauki matakin da
ya dace.
Sai dai baba bai saurara masu ba ko kadan inda yake shiga ba nan yake fita ba
yana cewa wa ya haifa mashi yar da zai fada mai yadda zai yi da ita.
Karshe dai aka tashi baran baran dasu da shi kowa na kunfan baki ran su ya baci
suka tafi.
Bayan tafiyan su ya kira mahifiyana ya sauke mata kwadon balai har t
yake ikirarin cewa kan zancen nan sai ummi na tabar mashi gidan shi.
Ga zaton shi ummi zatai shi amma ga mamakin shi sai yaji tace da yafi nono fari
wallahi indai kagani haka shi yafi maka to ka matsa.
Ta shige dakin ta tana bakar magana wanda sai yaune take mayar mashi da ansa a
tsakar gida.
Su ko inna dadi suka ji yadda baba yake muzanta ummi dani a tsakar gida suna jin
dadi sai cewa sukay mai abu ja mara abu ja.
Samun wurin mahaifi ya ya yanke sha wara kan diyar shi amma don karfin hali za a
zo a ce ga yadda zai yi.
Bani ci bani sha nabi na ramay dana fito tsakar gida yanzu zakiji su inna na
cewa yarinya an cuce ki an hadaki da tsoho wai a cewan su Ahmed ya tsufa baiyi aure
ba za a daukeni yarinya karama a bashi.
Su dinga fadin wai ai karyan kilibibi ya kara min don ban ga wurin yi ba a gidan
gwago don bazan kawo mata haka ba gida.
Daga ummi har ni bamu jin dadin mutanen gidan mu habaici da yaben magana bamu da
shakat a gidan ko kadan.
Har takai rainin wayon yana son taba mutuncin ummi hakan yasa ranan nai magana wa
mutan gidan .
Dan wurin inna ya dauki roban ummi yai wanki dashi maimakon ya mayar ida ya dauka
sai ya barshi a tsakan gida ummi tai magana ya taso kamar zai duke ta uwar na gani
bata tsawata mashi ba.
Bansan lokacin da nasa baki ba ga maganan fadan ya koma nawa duk da nasan ba
iyawa zanyi ba.
Uwar tace ina na fito takama mu tai muna tas ni da ummi da sauran yaran dakin mu.
Baba ya dawo inna ta kwashi karya da gaskiya ta fada mashi inda yake shi banan
yake fita ba a gidan.
Ga inna irin matan nan ne dabasu so a taba su diyan su amma suna iya yiwa dan
wani ka mita magana daya sai anyi kwana barkatai ana maimaita shi.
Fitina ya ishi ummi tace kai yaya ina dai anyi wanan zancen ya wuce aiko ta
hayayyako wa ummi da masifa da jidali .
Wanan abin ya kara jefa ummi cikin damuwa da kuci da takurawan ta kasance cikin
tashin hankali haka yasa na kara shiga damuwa da halin da mahifiya na ke ciki.
Damuwa yayi min yawa ga auren da akeson min na dole a kaina ga halin da ummin mu
take ciki da mutanen gidan.
Ranan itace da girkin gida girkin da ba komai ake kawo masu nahadi cikkake ba sai
mutum yayi dabaran da kan sa.
Da taimakona ummi ta samu ta kammal aikin ta na dauka nakaiwa kowa nashi dakin su
na koma dakin mu na zauna sai dai na kasa aiwata komi akaina na rasa manene abinyi
don kawo sassuci na alamarin namu a gidan.
Haka na kwana da wanan damuwar a raina ban samu barcin kirki ba tara dani dama
tun da wanan zancen ya fara bani barcin kirki a tare dani.



Kuyi hakkuri please kadan kuka samu



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON , , , , ,


5️⃣
🧕🏿

DON ALLAH YAR UWA IDAN BAKI IYA HAKKURI DA YANAYI, NA ROKEKI KI AMSHI KUDIN KI TUN
RAYUKAN MU BAI BACI BA DA JUNA , KOMAI NA RAYUWA ALLAH KE BADA IKON YIN SA DON
HAKA MUYI HAKKURI DA JUNA, , , , ,
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA.
IDAN KIN FITAR MIN DA NOVEL ALLAH ZAI KARBAN MIN BASHI NA A WURIN KI
Da asuba na fito tsakar gida ina shara don kasancewan ummi ca mai girki ranan.
Ummi na gani ta fito daga dakin ta cikin zumbulelen hijjabin ta na sallah
idanuwanta na zubar da hawaye.
Kai tsaye ta nufi hanyar kofar gida tsatsiyar dake hannuna na aje na nifi wurin
ta da sauri tare da riko hijjabin ta nace.
Ummin mu ina zaki ?
Tajuyo hawaye na zuba a idon ta cikin raunaniyar murya tace dani.
Gidan mu zan tafi .
Take nawa idanuwan suka ciko da kwalla don nasan wannan tafiyan da zatayi bana
lafiya bane cikin rudani nace mata.
Ummi may yasa zaki tafi kibarmu cikin gidan nan ?
Batayi magana ba sai hawayen daya karu a idon ta ta juya taci gaba da tafiya
atake na fashe da kuka mai tsuma rai.
Na bita muka fita waje ina cewa ummi hakkuri zakiyi dan tafiya kibar mu a haka
cikin wannan gida ba shine mafitaba.
Tace dani gidan mu zan tafi na gaji da wannan zaman na kunci da bakin ciki.
Na sake cewa da ita kiyi hakkuri ummi watarana sai labari, sai ta dan kalle ni
tace dani .
Haba yarinya da ace za a daina ai da an daina shekara nawa ana bu daya shikenan
mutum tsakanin ka da mutane babu zaman lafiya .
Duk gida an tsane ka har ku yashafe ku sai yaushe wanan halin zai kawu.
Ina shirin bata amsa baba ya fito don zuwa sallah yana ganin mu har yaso cewa su
waye a nan ?
Ko ya gane mune sai yaja tsuki ya ce ai ki kyale ta tafi tunda har yanzo ita bata
san tai hakkiri ba sai ya wuce.
Nace da ita ummi ki daure don darajan mu ki koma tace yaya basu hana na kwatar wa
kaina yanci ba.
Dakyat ta yarda muka koma ciki munyi arziki mutanen gidan basu fito ba har ta
koma ta shiga dakin ta.
Shi kan shi baba da yaga bata tafi ba da alama yaji dadin hakan don yasan abune
mawuyaci ta tafi gidan su su kyale ta ta dawo din.
Hakana muka wuni agidan cikin bacin rai sai dai ina yi ina kara kwantar wa ummi
din da rai.
Da dadare baba ya dawo baiga dan dakin mu a waje ba ya shigo dakin namu ganin ya
shigo yasa mu fita dakin na shimfida mu tabarma a waje muka zauna.
Ummi na zaune a bakin gadon ta ya samu wuri ya zauna a kusa da ita yace Rabi
niban san ina hakkirin ki yaje ba yan zu.
Har yarinya karama zatafiki tunane, ina iya hakkuri na gurin naga na kyautata
maku amma hakan ya gaza samuwa.
Kiyi hakkuri don Allah ki yafe min ba laifina bane nakan rasa may ke yawan kawo
maku wanna matsalan.
Ummi dai bata tanka shiba ta kawar da kan ta gefe daya don bata son ko kallon shi
balle ganin shi.
Ganin haka yasa shi mikewa yabar mata dakin yana cewa a bani abinci na ci ya
fice.
Ya nufi hanyan fita ta bishi da hararan tsana don kwata kwata ta gaji da shi
zaman auren dai sukeyi ita bata ga wani amfanin hakan ba.
Ta mike tana jin wani tukukin bakin ciki a ranta ta rasa yaya zatayi ta magance
matsalar dake damun ta a ranta batare da wani yaji ba.
Matsawan tana son kawa karshen auren nan sai dai idan nata auren zai tabo ne
hakan kuma tonon asiri ne gurin yayanta

********* *********
*********
A gurin mutanen gidan mu muke jin wai su gwago zasu zo ai maganan auren mu da
dan ta .
Zan iya cewa kowa a gidan mu bai san wanan mijin da ake cewa anyi min ba a cikin
yara don haka aka matsu da su zo din .
Ba wani yi gyara ba balle kwalliya don taron bakin da zasu zo, ranan weeken ne
don haka kowa yana gida bamu fita ba.
Muna zaune a cikin dakin hira muke da ummi na ina dariya mukaji ana masu sannu da
zuwa da bakin lagas.
Gwago ce ta fara shigowa gidan ita daya mutanen gidan mu sai raba ido suke suga
mikin nawa.
Suka kwasa sukayi dakin mama a ca aka shiga zuwa gaida ita dakin na mama
Ummi ce ta fara zuwa cikin mu taron ta gidan yawa da gulma nan aka saka ido akan
ta.
Ta gaida gwago bata tsaya ba ta dawo dakin ta ta umurceni da naje na gaida ita
din , na saka wani tsohun hijjabi a jiki na fita.
Daga kofa na tsaya nake cewa gwago sannu da zuwa ta juyo da sauri tana cewa
karaso mana ciki Safiya.
A hankali na taka na shiga dakin na tsugun na kasa take cewa dani a a baki san
yau zamu zo bane banga kiyi kwalliyan taron mijin naki ba.
Na dukar da kai na kasa take cewa dani tare muke suna nan kofar gida kin san shi
ba mai son shiga mutane bane.
Haka yake tun yana karami da gudun mutane amma yi saa ya yarda ya biyo mu ne.
Sai mama tace ai shi hali shi tun na kurciya yana nan mashi ke nan baya son
hayaniyan nan dai kamar yadda na san shi ashe ?
Ina suke ban dago ba take cewa dani maza ki shirya ki samay su a kofar gida.
Na tashi simi simi na fita daga dakin na koma dakin mu na zauna ban fadawa ummi
abin da tace dani ba.
Sun dade da mama daki sun kashe murya sai zuwa can mama ke cewa safiyan tana can
waje ne har yanzu.
Yar wurin mama ta amshe da cewa bata fita ba tana nan gida sai mama din ta taso
tazo har dakin mu da kan ta tana min fada.
Hijjab din ummi na salla na zura a jikina na fita idanuwan yan gidan mu caaa a
kaina
Na samay su su biyu a waje na karasa wurin su da sallama a bakina ko wanin su ya
kunna taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login