Showing 42001 words to 45000 words out of 258256 words
Chapter 15 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
babana mugun shawara take a gida.
Ina da sati uku da zuwa gida ne safiyan wata asabar sai ga gwago ta sauka a garin
direct gidan mu ta yo sun tare ta kamar yadda suka saba mata idan tazo har da ummi
na bata nuna mata komai ba a zuciyar ta.
Hakan yasa gwagon dan sake jiki bayan sun gama gaisawa da mama sai gwago tace
dada wanan yaron haka yaje yai muna, ya dauko kaunan shi ya zoda ita gida bada
sanin mu ba.
Sai mama din tai murmushi tace muma haka dai muka gansu kwatsan a gari sai dai a
gaskiya abin baiyi dadi yadda suka zo muna da labari .
Anyi abu don dadin rai kuma sai abu nason ya koma tsiya haka don ma malam daya
tare maganan ya hana kowa ya fadi yace yana tara kudin mota ne , ta koma dakin ta.
Gwago taji sanyi a ranta sai dai taji mama tace a gaskiya dake har wanan yaron
baku rike amana ba sam abin baiyi dadi ba wallahi don ma dai anyi kawaici andubi
baya .
Gwago tace to ai dada yanzu dai kuyi hakkuri kamai aka ce munyi mun dauka sai
dai muba da hakkuri kawai.
Mama ta sake cewa ki sani diyar malam diyar ki ce ba sai an fada ba don in anyi
laakari da irin diyaucin da ya nuna tun daga kan auren har kawo yanzu amma sai ga
labari mara dadin ji ya samay mu kuma mun ga alama don ga shedan bugu nan da tazo
muna.
Yadda duk akeyi mama tayi don ta fadi gaskiya yadda ya dace har da zancen kudin
da suka bar ma gwago ta ja min jari sukayi tace wai mijina ya karbi kudin
Amma zatai mai magana ya dawo min da kudina na dinga juyawa da kaina zaifi tana
ta ban hakkuri can dai ta tashi zuwa dakin mama ne tayo mata rakiya wurin ummina.
Nan ma hakkuri ta bayar suna cikin dakin ne baba ya shigo gidan wanda inna ta
aika a kira shi yazo wai ga gwago tazo.
Yana shigowa yai dakin mama aka ce suna dakin ummi sai ya kama fada yin may ina
ruwan ta da ita aiba ita taba ki dayin ba.
Nan dai yake ta sababi irin na maza da iyalin su basu da tacewa sai su kaida ke
kafa dokan su a gidan yadda ransu yaso.
Bai tsaya sauren ta ba yace binta kinzo dama ina son zuwa wani sati in mayar
maki da yarinyanan .
Sai hakkuri yake bata abin ya bani mamaki naidai tuna yadda take zama ta kare
mashi zagi da yankar kauna .
Amma shi yana nufanta da alheri ya kuma bata go ahead akaina yace tana da iko
akaina ta tsawa ta min ba sai nazo gida ba.
Hannu na sa akai ina ihu baba yace indan ban rufe masu baki ba yanzu zai debe min
albarka dole mama tasani yin shiru mama tana fadin adai tsaya abin abin a sannu ba
a hakana,
Tsawa ya daka ma mama tare da cewa indan bata kama mashi baki ba yanzu zai da ita
dani mu bar mashi gidan shi.
Duk yadda akeyi mama tayi amma ita inna cewa tayi indan ma na zauna gidan may zan
yi ai kawai gara na koma daki na, na zauna shiyafi.
Baba ka taimake ni karka mayar dani idan ka mayar dani kashe ni zasuyi wallahi
wayyo baba ka taimake ni yace idan ban isa gare ki ba sai dai kibi duniya.
Ummi na saboda kawai ci kala bata ce dashi ba amma zuciyar ta kamar zai tsage
take jin shi ansa rana, ranan labara zamu tafi.
Don gwago zatai dan sayayya da zata tafi dashi na sana an ta can sai wani nan nan
dani takeyi don ganin idon mahaifana.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , ,
1🧕🏿313
1️⃣
1️⃣
3️⃣ 3️⃣
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON WANAN NOVEL DIN KUDI NE.
Ummina dake barci ta falka cikin matsanacin firgici daga barcin da takeyi wanda
kwana uku kenan a jare ta mafalki dani.
Kuma mafalki mara dadin takeyi a gamay dani din wani lokaci sai taga na gwauce
zan fada rami ko tagan ni a ruwa mai zurfi ina iyo.
Ina gudu ana bina zaa kashe ni da wani guduma a hannun mai shi ire iren wanan
mafalkin takeyi koda yaushe hakan ya tayar mata da hankali.
Ta shiga cikin damuwa sosai ta dan saka abin a ranta don haka yau ta kudiri
aniyar fadawa baba na idan ya dawo dakin ta.
Haka akayi sai da yagama sauren ta kaf yaji abinda take fada bai bari takai aya
ga zancen ta ba ya ko hauta da sababi har yana daga murya sauran mutanen gidan suna
jin shi.
Mama ce da taji fadan yayi yawa hakana ta tako zuwa kofan dakin tana cewa haba
malam ayi hakkuri koma may nene tunda ka taba fada ai ya isa ko.
Yace a hasale bari matar nan da abin haushi auren yariyar take son kashe wa don
rashin sanin ciwon kai.
Yariya na gidan mijin ta zaune lafiya hankali kwance zaki tsiro da wani tsurku
wai kila ba lafiya take ba ke kina yawan mafalkin ta ke kila wani abu zai samu yar
ki.
To Wallahi ahir din ki da zancen Safiya a gidan nan idan ba haka ba rayuka zasu
baci sosai akan haka don sam ba zan lamunta ba.
Har yayi ya kare bata ce dashi uffan ba da safiya kuma ya tusa jidali inda yake
shiga ba nan yake fita ba.
Sai inna ce ta sa mashi baki tana fadin ai kasan dan tallaka bai iya samun wuri ba
in bashi ba abin farin ciki yar ki na can lagas tana aure amma ke bakin ciki ya
hanaki ki gane haka ki kwantar da kai kici arziki.
Mutum mai bakin ciki da hassada ai har kanshi yake yi saboda mugun hassada daya
huda jiki na sheri, har taci ta sude ummi bata tankasu ba sai share su da tayi
tana aikin ta a cikin gida.
Kwana biyu hakana suke da baba sama sama sai da taga ya dan fara mantawa da
zance ta roki fita unguwa gidan gwagon ta.
Bai hana ta ba illa cewa da yayi a gaishe ta ta gama abinda takeyi ta shirya ta
tafi gidan nasu kamar yadda muke kiran gidan gwagon nasu.
Bayan sun gaisa da gwago tana tambayan ta yara da sauran muta ne gidan take cewa
gwago dama nazo in fada maki ne kwanan duk na kwanta barci farkin yar nan nake yi
ba dadi wallahi.
Nan de ta kwashe yadda take mafalkin ta fada ma ta shiru gwagon nata tayi sai
zuwa can tace wuri ne bakusa ba in ba haka ba da sai a shirya aje a gane ta.
Sai dai addua duk inda take Allah ya tsare muna ita kawai zamuce wanan shawara
na gwago ta dauka har tadan ji saukin abinda take ji gamay da ni a zuciyar ta.
A hanya tana dawowa tafe take tana tunanen ko a wani hali nake sai Allah kawai ya
sani don yanzu kusan shekara daya ke nan da tafiya na amma babu wanda ke da labarin
halin da nake ciki.
Yaya sani zaune yake gaishe ta amma bataji shi ba har sau uku yana mata magana
tayi nisa a cikin tunane.
Sai da ya kara kiran sunanta da karfi taji shi ta sauke wani ajiyan zuciya da
karfi take amsa mashi gaisuwan da yake mata din.
Yake tambayan ta lafiya dai na ganki a cikin damuwa tai murmushi kamar kada ta
fada mai sai take cewa babu komai.
Yace wani matsalane kuma ya taso ki fada min, sai ta fara haye take fada mai
yawan ma falkin da take yi dani ta kara da fadin gashi tun tafiyan ta babu wanda ya
ji labarin su itama gwagon naku ta bar zuwa yanzu kamar da datake zuwa akai akai.
Shiru yayi yana tunane sai can yace lafiya take ummi mafalkine kawai ke zuwa
haka na amma bari nayi maki alkwarin zan bincika inji.
********* ********* *********
Na samu masu kitso na yawan zuwa neman kitso a wurina da kuma sayen kayan sanyi
da nake sayarwa a gidan.
Haka ya hana ni shiga damuwa da halin da nake ciki don yanzu takai bai bani
abinci sai dai inyi dabara inci wa cikina.
Dan neman kudin da nakeyi Allah yai ma abin albarka sai gashi ina samu sosai duk
abin da na taba da sunan kudi sai Allah ya sama abin albarka .
Ga anty maman biyu yanzu ta mayar dani kamar wata yar uwata na jiki nakan dauki
lakaci naje nai mata gyaran gida da sauran aikin da shafi na mata dai.
Wanan ya kara kawo muna shakuwa a tsakanin mu har yakai ta tutube da zancen karo
karatu tunda taga takarduna suna da kyau.
Murmushi nayi kawai nake cewa Anty nasan ko nai mashi magana ba bari zai yi ba
koma ya bari ita mahaifiyar shi ba bari zatayi ba.
Don haka na hakkura da wanan zance zan tsaya inda Allah ya ajeni Allah bai manta
da kowa ba ina ji ina gani na koma dani da wanda baiyi karatu ba duk daya.
Tai shiru tana kallona can ta nisa take cewa yanzu idan zaki iya sana,a sai mu
duba muga yadda za a yi don dai wanan kitso Safiya bazai fishe ki ba.
Nai murshi nake cewa zan iya mana anty tunda ba wani abu nake yi ba tace to za a
diba a ga binda ya dace dani.
Nai shirin komawa gida don karfe biyu ya wuce ta hada min goma na arziki kamar
kullun na nufi hanyar gida ina sauri don in koma inyi abinci.
Bai bani kuma indan bayin ba fada ne idan na dafa kuma ya lashe, sai dai ashe na
makara don na samu ya dawo gidan ko.
Ina kokarin shiga ne naji an shako ni ta baya sai da idanuwa suka firfito don
wahala yana fadin yar iska ina kika fito kin fito wurin biyar mazan ki.
Gaba na ya fadi don jin sabon sherin da ya kulla min kuma nai karfin halin fadin
Allah yai min tsari ga shiga halaka da duk wani muslimi mai imani.
Nace ni wurin maman biyu na fito don ina mata aiki tana dan bani abinda zanci
yanzu can na fito zaka iya binkawa kaji gaskiyan abin.
Yana huci yakai idon shi ga dan jakar kayan da na shigo dashi gidan sai ya fisge
jakar ya shiga bincike nasan dama kudi yake nema ba wani abu ba yana ganin dubu
biyar ya saurin dauka yana huce yana muzurai da idanuwan shi ya hankadani gefe daya
ya fice gidan.
Nakai kallona ga kayan da ya wawatsar min a kasa na duka na fara kwashewa tare da
ajiya zuciya idanuwa na zubar da hawaye.
A hankali na zare hijjab din dake jikina na shiga adana kaya inda ya dace da
komai a cikin shinkafa naga wani leda an dukule abu ina budewa na ga kudani da
takarda a ciki da sauri na dauka ina karantawa kamar haka.
Nasan mijin ki ba zai barki da kudin motan dana baki ba shiyasa na saka maki
wanan a cikin nan don in kin gani ki boye ki samu na amfani dashi.
Safiya ki ci abincin da na baki idan ya kare kada kiji kunyan dawowa ki fada min
a shirye nake da in taimaki don rayuwan ki na bukatan taimako.
Ina hawaye nake karantawa nagama ina mata addua nasan Allah ne ya turo wanan
matan a rayuwa na don ta taimaka min.
Idan badon Allah da ita ba da ban san yadda rayuna zai kasan ce ba a garin da
bani da kowa sai Allah amma gashi ta rike ni tankar jinin ta tana taimaka min.
Da safe da wanki na tashi a gidan da gyaran gida komai na gyara na dora girki
dayake ina da komai a hannu na girki nayi lafiyayye na zauna naci.
Na shiga wanka na fito ina shiryawa naji shigowan shi sai dai kamar ba shi kadai
bane tashi nayi na leka tare yake da wata mace mai siffan kabila da dan riga karmi
ajikin ta wata yankwamama da ita ta sa gashin doki akan ta.
Baka ce bata da wani kyau na ga ya rungumo ta yana tsotson sassan jikin ta da
sauri na sake labulen ina runtse idona.
Wani irin kuna nake ji a raina har na koma na zauna sai wata zuciya tace dani na
fita na yi masu magana.
Koda nafito sun shagala a cikin abinda suke yi basuji fitowa na ba daga dakin har
naje gurin fridge na dauko goran ruwa mai sanyi ban tsaya jiran komai ba na bude
goran na kwarara masu ruwan akai.
Wani irin zabura sukayi da karfi yace kina hauka ne zuciyana ya dake nace yanzu
dai na fara haukan .
Zan kara zuba masu ruwan ya daga hannu ya sharara min mari sai da na gigice na
dako nai kan yankwamaman da duka sai shi kuma ya shiga duka na sai da yai min lis .
Da kyat na kwaci kaina a hannun shi na bude kofa a gigice na fito gidan haka nabi
hanya ba komai a jikina sai gidan gwagon mu.
Na isa da kukana tana gani na ta zabura tsaye tana fadin ke lafiya may ya faru
da Amadun ne yayi hatsari ne komay ?
Duk suna tsaye a kaina sai faman rusa ihu nake yi da kyat na tsagaita kukan da
nake yi nake cewa duka na yayi gwago don ya shigo da mace gidan nai magana.
Sai bude baki tayi tace ke mai ya kaiki yi mashi magana gidan shi ko naki har
wani dadi ki yaji da zaki ce kar ya nemi matan da yake so.
Dakatar da kukan da nakeyi nayi ina kallon ta cikin mama tace kin ga bazan hana
shi jin dadin rayuwan shi a kan ki ke ma in kina iyawa jiki kiyi shaanin gaban ki
lagos bariki ne kazo na zo ba mai shiga shanin wani anan.
Yo wanan wani abu ne da kullun zai zama abin masifa a kanki kin hana yaro shakat
a ruyuwan shi.
Habiba tace mummy ai duk laifin ki ne da kika hada shi da wanan kucakar yarin sam
bata dace da zama matar shi mutum kamar doluwa gata nan.
Sukai min kaca kaca suka korani haka na fito ina kuka na nufi gidan don ban son
in tafi gidan mama biyu saboda gidan zumu ba kasuwa bane.
Na dawo na samu sunyi shaye shayen su a gidan sun bar baje kwalaben giya sun
shige daki sai kida ke tashi daga ciki.
Hakana na shige tare da bakin ciki a raina ranan dai yadda naga dare haka naga
safiya.
********* ********* *********
Yaya sani yazo ya sallami ummi da dare da cewa zai yi tafiya kamar yadda ya
sallamay ta haka ma ya sallami kowa a gida ba tare da wani yasan idan zai tafi ba.
A cikin daren nan yabi mota sai garin lagos shigan safe yai wa lagos din bai sha
wahala ya samu motar zuwa unguwar mu.
Gidan gwago ya nema ya samu suna cinikin safiya mutane da yawa a wurin ta masu
karya wa sai ganin shi tayi kwatsan.
Da mamaki take maimaita sunan shi tana cewa sanu kaine a garin namu injin dai
lafiya yace lafiya lau ta saka a kawo mai abin karyawa ya karya dama tun abincin da
yaci a gida bai sake karya ba har lokacin.
Bayan ya karya ya bukaci a kaishi wuri na sai ta fara yi mai kwana kwana don
tasan cewa daren jiya nasha duka wata kila ina can ina jinya jiki na.
Da dai ya matsa Sadiya tace bari ta kai shi gwagon bata so haka ba tare da
Sadiyan suka zo gidan mu,
Daidai lokacin ya tsaye yana surfa min zagi wai naki fitowa in dafa masu abin
karyawa yana cewa don ubanki ki fito nace dakin nan tun ban biyo ki na kara maki
ba.
Aka turo kofan shigowa gidan na fito karuwan ta fito daga ita sai dan tawul iya
cinyan ta tana cewa wai may ke faruwa ne sai ma a lokacin nasan wai bahausa ne ita
don hausan da tayi.
Kallon kallon akeyi wa juna kamar daga sama na ga yaya sani a gidan ban san
lokacin da nayi ihun murna ba na rugumay shi sai kuma na fashe da kuka don murna .
Shikan Ahmed shiru yayi don ya san duk banbamin da yake a kaina yaya Sani yaji
shi ga kuma karuwan shi a tsaye da dan tawul tana cewa wai bazata dafa muna bane
komay ko lalatsa muna yar iska.
Wani tsawa ya daka mata sai da ta zabura ta kama kanta tare da mashi wani irin
kallon ko ta fahinci abinda yake nufi ne sai tai shiru.
Yaya Sani yace bari kuka Safiya yau Allah ya gwada min abin da ummin ki kata
mafalki a kai.
Lalai ba gidan uban ta bane ashe kai baka da mutunci baka da kima ga kwalaben
giyan su nan a zube da suka sha daren a jiya ba a kawar ba.
Na shiga rawan jiki da yaya na ina ce mashi ya zauna a baude nake tafiya ga
kumburi a fuska na baki ya sundule min.
Shigewa yayi baya yagama hararn Sadiya da ta kawo shi gidan yaya Sani bai iya
kara furta komai ba yai