Showing 15001 words to 18000 words out of 258256 words

Chapter 6 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

yana zuka.
Jin sallama na da sukayi dayan yai saurin kashe taban hannun shi shiko dayan ko a
jikin shi bai masan na zo ba.
Sun saka kida na tashi kamar gidan dj mutum ya shiga da kyat na bude bakina
saboda warin taban da yacika wurin ina jin kamar zan yi amai.
Na kara gaidasu cikin murya a sanyayye sai gudan ya amsa min dayan wanda nake
ganin shine dan gwagon mu yana dai zaune.
Sai can gudan yace dani a, a ko ke ce Safiyan a hakalin na bashi amsa da eh da
sauri ya dago kai ya kalle ni, na sake cewa kunzo lafiya.
Mai maganan ya bani ansa da lafiya kalau mun samay ku lafiya ya karatu nace
Alhamdullahi sai nai shiru.
Jefi jefi can yace barin dan taka wurin mai shagon can na sayo abu nasan yayi
haka ne don ya dan bamu wuri.
Tafiyan shi ke da wuya shiru ya biyo baya har na wani lokaci sai naji yace barka
da fitowa.
Nace barka mu da wuni.
Yace ya kike lafiya na bashi amsa.
Na jingina jikina da motar su don na gaji da tsayuwa yace da fatan anyi maki
bayani a gida.
Sai na girgiza kaina nace ba wanda yai min baya ni an dai ce nazo na gaishe ku.
Ya ce Ok in kin koma za suyi maki yace ina dai fatan kin san abu ga makaranta don
naga kamar har yanzu da saura.
Ko da yake wannan matsalar gwagon ki ne nace dashi namu dai.
Yadda na fadi maganan sai ya fahinci ko ban gane dukkan abin da yake fadi ba.
Yace ina baki fahinci magana ba cewa nayi iyayyen mu sun yi cewa zasu hada a
tsakanin mu sai dai ni a tsarin rayina nafison macen da ta mallaki hankalin ta .
Macen data waye tasan duniya ya nunani yace dube ki ina ganin duk baki fi shekar
sha hudu ba in ma kin kai.
Na yi wani gajeren murmushi nace to yaya na iya da zabin a kaina babu komai
sai dai nima in son samu na samu yaro sauriyi mai shekaru kalilan wanda zai rike ni
tsakani da Allah.
Amma tunda iyayye suka sani babu komai Allah ya tabbatar da alheri a tsakani.
Yaji haushin amsan da na bashi yace ba laifi nima hakan zan daure nai maneji
dake kafin kan ki ya waye.
Nace abin na da sauki tunda kaima da wayewar iyayye kake kuri tunda sun sani
nasan da sannu zai waye din kaga ba maganar na waye ko ban waye ba dole ne nayi
biyyaya ga magabata na.
Tun da sune masu iko dani banice ke da ikon kaina ba zanyi biyyaya a gare su.
Ya sake jin haushin magana na amma a fili yacewa yayi ashe ra, ayin mu yazo daya
kenan kan biyyaya ga magaba tan mu sai ki shirya zaman ukuba a tare dani.
Nace insha Allahu in yin hakan shine farin cikin mahaifi na a shirye nake da na
rugumi duk wani ukuba da zan sama a gidan ka.
Sai ki shirya ke nan yarinya don ba zan yi renon banza a rayuwa na nace dashi
Allah ya shige muna gaba.
Nace idan ka gama zan koma ciki hanya a bude take maki zaki iya tafiya sai dai
kina da daman fadawa iyayyen naki irin ra,ayin .
Na dan yi jim na wani lokaci sannan nace dashi idan son samu ne kaine babba kai
ya kamata ka tun kare su da zancen.
Saboda kai zasu fi daukan zancen ka da muhinmanci ya ce yin hakan ba zai yuyu a
gare ni ba amma ba matsala.
Ya fara dube dube a cikin motan nidai duk warin taba ya ishe ne a wurin gani
nake kamar a kamfanin taba na shiga.
Sai naji yace dani ga wannan kya kara kisai littafi da biro, sai na girgiza
kaina ba tare da nakarba ba nace ka barsu na gode ina da wadatar littafi da biron.
Ya langabar da kai tare da karya harshe acikin turanci yace you will regret
later sai kuma a harshen hausa yace ai ba cewa nayi kina da matsalar su ba,
Nace to na gode ban karba ba na fara tafiya yace to shike nan, na soma takawa a
hankali shi kuma ya bini da kallon tsana.
Bayan na ahiga gida dakin mu na nufa yayin da masu gulma an zuba ido a ga abin
da zan shigo dashi.
Tun shigana gida san bani da natsuwa ziciya ta kwata kwata bata natsu da wanan
hadin ba ko banza bai a cikin tsarin mazan da nake so.
Wayewan shi yayi yawa bai laifi yana da tsarin maza amma dai tsarin dan maciji
don farine dogo ga iya gaye komai nasa karfafa ne amma ziciyan sa da jikin shi babu
tarbiya a ciki.
Sai dai ban da zabi akan haka don bani da ikon bijirewa maganan mahaifina don
haka naci alwashin tursasa zuciya na da hakkuri koda kuwa yin hakan zai rasa farin
cikina.
Sai da gwago ta gama abin da takeyi ta fita zuwa waje zuwa can ta dawo ciki da
wasu ledaji a hannun ta.
Ta nacewa ga wannan na sarakkuwa nane kayan mun gani muna sone muka zo dashi zan
dawo idan yaya ya dawo gida mu gana kafin mu tafi.
Har suka tafi ban sake ganin shi ba nadai ji labari cewa sun tafi an tsaida bukin
mu da zaran na gama karatuna wanda yazo saura wata uku mu kanmala.
Ba waya ke gare ni ba balle ya dinga kirana haka yasa ban ji daga gare shi shima
baiji a wurina.
Na dan kwatar da hankalina don na fuskaci jerabawan dake tafe min na final exam
da zamuyi duk da ban sa rai ga cewa zan samu ci gaban karatun nawa.
Kulliyomin ba wani kwaciyan hankali a tare dani gashi duk biyayya da nake keyi ba
gani akeyi ba don saida yakai an hada gwago fada da baba na da ummi wanda nasan
bakowa yai wanan hadin ba sai mutanen gidan mu.
Har yakai ummi na ta kasa hakkuri tai tafiyan ta gidan su sai suka koma fadin
cewa don tagacewa buki na ya taso ne ba ta aje komai ba yasa ta tafi gidan su wai.
Wanan tafiyan na ummi shi ya rage muna walwala sosai dani da kan ne na a gidan
ko yaushe ina daki ina barzan kuka.
Yan kane na sukan damay ni da tambayan yaushe ummi zata dawo idan nace ta tafi
gidan su kila ba zata dawo ba sai su fashe da kuka.
Na rasa mai ke mun dadi gashi nima dake dan kula dasu ana ahirin yi min aure a
lokacin duk da ba wani alaman shirin aure da akeyi a gidan namu .
Don ban gani a kasa ba kamar yadda idan za ai buki ake ta faman shirye shiryen
buki agidan namu.
Ban san may mama tagani ba ta sako dama sherin na wurin inna don ita ce tace wai
ummi na na fadin sai da gwago tasan cewa dan ta bai da tarbiya zata ce a hada shi
da diyar ta.
Ta fadi maganan wurin yan uwan su mama da suka kawo kaya gidan mu su kuma suka
kwasa suka je suka fadawa gwago maganan .
Nan gwago ta shiga fada tana zagin ummi wai damay diyan ummi sukafi diyan ta don
ma za a rufa mata asiri a auri yar ta.
Ta aikowa baba magana akan cewa ya ja wa ummi kune ga baganan da take sake mata
shi kuma baba bai tsaya binke ba yai cikin ummi da masifa har yana cewa tana bakin
ciki da hurdan da yake yi da yan uwan shi.
Shine akan wawiyar yar ta take son hada shi da yan uwan shi ta bata isa ba
wallahi idan bata iya ganin auren haya a bude yake mata ta tafi gidan su.
Ita kuma ummi ta kasa hakkuri ta mayar mashi da ansa cewa ba tai bakin ciki da su
ba sai yan zu inma tayi bakin cikin ai dole ne don ba aiwa yar ta adalci ba ai ga
yannan ta agidan abadasu mana.
Rikici yai rikici don itama ummi ba raga masu ba wannan karon ta rufi idon
tamayar masu da mai zafi.
A karshe sika kwasa da baba har yakai tabar gidan cikin dare duk magiyan da nake
mata bata tsaya ba.
Mama ta sulce jiki ta samu wani wan baba ta fada mashi halin da ake ciki ta kuma
ce a gaskiya ita bata taba jin ummi tai wannan maganan ba.
Baba musa ya samu babana sai cewa baba yayi dashi ta tafi mana idan hakan yafi
mata alheri.
Baba musa yace dashi matsala gidan ka baka bincike baka kuma son a fada maka
gaskiya kun samu boyar Allah kuna cuta mata ita da diya ta cikin gida.
An tabbatar min da cewa bata fadi wanan maganan ba yau kake da Rabi a gidan nan
ya kamata kasan abida zata iya aikatawa da wanda bata iyawa.
Nan dai suka rabu da shi babu dadi ranan da yamma da baba ya dawo gida yana ta
fada da baba musa.
Mama tace dashi ai bai fadi karya ba gaskiya ya fada wa ya taba ji a gidan nan
lokacin da Raba ta fadi hakan.
Sai inna ta caraf tace kina nufin ke nan karya ne sheri akai mata ai idan bata
fada anji ba alama ya nuna hakan.
Yace kin ga idan ke zaki je ki dawo da ita ban hanaki ba ai bani na kore ta ba
sherin ta ne yakore ta balle ku matsa min.
Yaya sani na gida zaune yana cin abinci yace baba a gaskiya maganan gaskiya kuna
cin amanan boyar Allah nan ga mama ta fadi gaskiya tace bata ce ba ai shike nan .
Ke inna in kina rage sheri ki rage don ke ma diya mata ke gare ki gasu nan har
guda biyar maki.
Tace to ubana baki zakai muna ko may yace ni gaskiya nake fada maki tace bako
haka ba.
Ya mike yabar abincin da yake ci yace to tabar maku gidan sai kuyi yadda zakuyi
da diyan nata.
Ya shura takalman shi ya bar gidan.
Sai fada ya koma tsakanin inna da mama tonon asiri ya tashi baba yana zaune yana
jin komai.
Dole gidan ya koma babu armashi kowa na cikin damuwaidan ka cire inna da diyan ta
suke an shuwa a gidan kawai.

********* ********* *********
Kwana uku shiru babu wani motsi a gidan kwakwara mama ta kara samun baba a kan
zan cen.
Ta nuna mashi damuwar ta tana cewa malam ka dubi Allah kaje kadawo da matar ka ta
dubi yaran ta yara sun koma kamar marayu a gidan.
Yace ina son zuwa sai dai ban san da wani ido zan kalli Rabi da shi ba don don
iyayyen ta sun mani mutunci amma ni na kasa rike masu ya.
Gobe zan sami malam lawal ya rakani muje ko zata dawo in kuma ahi zai tafi wala
ba a sa.
Mama cikin nuna damuwa sosai ta ce dashi da haka yafi don ace anyi buki yar ta
bata gida gara dai ayi hakkuri.
Washe gari ana gama sallah asuba baba ya samu malam lawal da maganan yai mashi
bayanin komai bai boye mashi ba.
Malam lawal yace a gaskiya baka kyauta ba da baka bincike a gidan ka ai yaron ka
gaskiya ya fada a tare ake hade kai dakai ana cuta wa Rabi.
Sannan fa ka sani yanzu ba aiwa yaro dole samu da wayawan kai da aka samu ita
yar uwar naka ta nuna dan ta tasani.
Gashi an fara samun haka tun ba a yi auren ba idan anyi akazo aka samu matsala wa
aka cuta yar ka da uwarta.
Daga karshe dai baba ya nuna su tafi su kadai don shi yana jin nauyi da kunya
zuwa ya tun kari iyayyen ta.
Sun isa garin da sanyin safiya sai dai basu samu mahaifin nata ba a gida amma
yayan ta da kannen ta suna gida.
Bayan sun gaisa malam lawal yace dama mun biyo sawun Rabi ne don Allah ayi
hakkuri ta koma tsakanin harshe da hakori ma ana samun matsala bare mutum da mutum
balle zaman aure da ya gaji hakan.
Yayan nata yace haka ne amma naso ace shi malam Audu yazo da kan shi don ko mu a
kauye mun daina wa yaran mu auren dole.
Bayan haka duk hakkurin da Rabi ke yi ita da yar ta baya gani sai da ya kora
muna ita gida dom ya nuna muna ya gaji dasu.
To idan shi ya gaji dasu da ai har diyan nata ya koro muna mu bamu gazawa da su.
Malam lawal ya jijiga kai yace ai dai yi hakkuri a madadi na abokin sa ina bada
hakkuri koma may nene ya hada su tsakanin miji da mata ne.
Hakan ba zai sake faruwa ba tunda idan mukayi laakari ai hakan bai taba faruwa
tsakanin su ba tun suna zamanin kurciya yanzu da aka tara iyali.
Yayan ummi yace eh saboda hakkurin irin nata ba shine zaa ce bai taba faruwa ba
amma ia duk halin da take ciki muna da labari.
Yanzu ko da anin ya isheta ai da kan ta ta ne may mu dama ranan muke jira don duk
abin da yasa kaga Rabi ta bar diyan ta to abin yaya kamari.
Malam lawal bai gaji da bada hakkuri ba har mahaifin ummi din ya dawo gida ya
samay su.
Nan su malam lawal aka shiga gaisuwa dashi nan dai malam lawal ya gabatar da
bukatan su na bikon ummi din.
Tsohon yai shiru can yace a gaskiya Rabi bata taba yaji ba nasan halin Rabi da
hakkuri abu daya zaisa na yarda na mayar da ita dakin ta shine.
Bukin yar ta da yataso amma idan ba haka ba Rabi bata komawa gida nan ya isa
haka na.
Ya dubi dan shi daya yace shi ga ka kira min Rabi, kanin ummi ya shiga kiran ta
ta shirya tafito don amsa kiran mahaifin nata.
Sai fitowanta ne ta ga su malam lawal ta durkusa a gaban mahaifin nata cikin
ladabi tsoho ya dube ta yace.
Rabi ga abokin mijin ki sun zo bikon auren ki don haka maza ki shirya ki bisu.
Take idanuwan ummi ya ciko da hawaye zata yi magana tsohon ya daga mata hannun
tare da cewa.
Haba Rabi ban sanki da mussu ba, ita rayuwa hakkuri akeyi da komai ki yi hakkuri
ki koma daki mijinki ko domin yayan ki .
Tabude baki zatai magana tace baba amma, , , , ,
Ya koma katseta cikin tsawa yace kin san ni sarai bani son mussu aiko ?
Tashi ki je ki shiryo ku tafi.
Badon ummi ta soba haka ta shiga ta shirya tana shiri tana kuka ta fito da
lulubin ta suka nufi tasha da su baba lawal.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,


6️⃣
🧕🏿


INDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL
NE, , ,


Lokacin da suka dawa bata zo gida ba wurin gwago ta nufa malam lawal ya je ya dauko
baba yazo dashi gidan gwago.
Gwago da malam lawal suka su gaba da nasiha akan a zauna lafiya arike hakkin
iyalin abawa kowa hakkin ta yadda ya dace.
Baba yace insha Allahu komai ya wuce zaa gyara da yarddan Allah zai kulla da
hakkin iyalin shi
Da daddare su gwago suka rakota gida ta dawo dakin ta tare da kara mata nasiha a
zauna lafiya ta kyale kowa da halin sa.
Lokacin da suka shigo gidan mutanen gidan suna waje zaune mu kuma muna daga cikin
dakin mu sai naji murya kamar na yar uwar mama na sallama.
Hakan yasa ni mikewa in leka aikuwa nahango tafe da ummi na buga tsale ina cewa
lah ga ummi mu ta dawo.
Mukayo kanta da murna suka shiga dakin komai yana nan tsab yadda ta barshi dakin
ba laifi suka samu wuri suka zauna.
Zauna na durkusa ina gaida su kaunan ummi ke cewa dani wanan wata irin amaryane
ba kwalliya ko kadan.
Na turo baki gaba take cewa ai ko bakya son mijin a dan yi maki gyaran irin na
amare ko ?
Wannan wani gyara zata samu babu kwaciyan hankali ahaka suke ahirin kai ta
gashiko ance mijin nata dan duniya ne inji kaunan ummi gudan.
Aiko ba komai a dan gyara ta in ba haka suke so su kwashe ta sukai ba akara
samun abin fada masu nan gaba.
Take cewa dani washe gari ki same ni gidana da safe da dan abin da zan maki koda
yake ma an makara duk da haka dai hakan za a yi.
Sun dan zauna nan nake basu labarin irin yadda mama tai ta matsa mashi akan ya
dawo da ummi dakin ta da kuma yadda tai ta dan taimaka muna da ummi bata gidan.
Nan da zasu fita suke gaida mama din suna fadin ga Rabi nan ta dawo Allah kauda
tautsayi tsakani.
Mama tace ba komai zama tare ke kawo wani abin amma in an ciza aka hura sai ya
wuce.
Har suna shirin fita daga gidan sai inna tace muda ba a gayar wa sai ace mu mutu.
Baku duk mutuwa ai amma dai baku so ganin hakan ba anso ace bata dawo ba sai
gashi ta dawo din bakin cikin haka zai kashe mutum.
Inna tace bakin ciki ya kashe wa matar da baa bi bayan ta ba ta wanke kafa ta
dawo don kwakwa irin naku.
Tace wa ke nan zaune gida kamar kayan wanki tun yaushe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login