Showing 117001 words to 120000 words out of 258256 words

Chapter 40 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

din da zai kai
mu gidan gwago din.
Mu kafito ni da kauna na da zata rakani gidajen uwayen mu muka hau mashin sai
gidan gwago anan muka shiririce da ita har lokaci yayi mun fito.
Mun tashi muna batun zuwa gida maman mu bayan muyi sallah azahar ta dafa muna
taliyan hausa da manja munci mun fito sai ga kani na saman keke ya biyo mu.
Nace lafiya ka biyo mu haka yace anty wai kizo wasu mutane suka zo wurin ki a
wata irin katuwar mota.
Anty baki gansu ba kamar bature dayan mutumin suna nan sun shiga gida gaida baba
shine ummi tace in zo in kiraki.
Na ce ni fa kace shafiu yace wallahi anty don Allah kiyi sauri don da ganin su
masu kudi ne baki ga motan da suka zo da ita ba fa.
Gwago tace yi maza ki je tunda an aiko kiranki Allah dai yasa muji alheri dariya
nayi kawai sai nace bari mu aje maki sakon su mama anan mi tafi.
Juyawa mukayi zuwa gida tun da muka karyo kwana na hango motan take naji gabana
ya fadi nace to waye yazo har nan wuri na ?
Haka dai muka shiga gidan da fargaba ko waye yazo a kofan ummi muka hango
takalman su ga awakin ina sun zo suna hawan takalmin nasu mama tana korewa muka
shigo.
Wurin mama na nufa ina tambayan ta ko su waye tace haba Safiya ashe abin arziki
muka samu baki sanar da kowa ba sai yanzu da bakin ki suka shigo gaida mahaifin ku
suke sanar damu.
Na danji kunya nace kai mama ho baga shi kun sani ba yanzu ai sai yace cikin
shake muryanta ai baki sani ba tun shigowan su mutumiyar ta shige daki bata fito ba
nace wake nan mama.
Tace wa kika sani banda innar ku uwar yan hassada kuwa ake dai bari shiga dakin
baban ku kiga abin arzikin da suka zo muna dashi.
Yaya sani ne ya shigo da kwalaben abinsha gidan a cikin leda yana sauri ya nufi
dakin ummi dashi nace Allah sarki dan uwa ko ina ya samu kudin da ya karma min
bakin dashi oho ?
Ya fito dakin ya ganni yace a, a ashema kin dawo ga baki mun samu daga abuja sin
zo wurin ki kin kuma zo nan kin tsaya jin na dawo yasa ummi dake zaune a takure
dakin fitowa ta bamu wuri.
Nan na shiga da kunya dakin da sallama na suna zaune saman tabarman da aka
shimfida masu hankali kwance ga dan wake a gaban su da akayi gidan suna dan cokala
suna ci.
Hamza ne ya amsa min sallama na yana dauko dan wake a kwano yace a a amaryan mu
ina kika je bamu baki izzini ba haka.
Dan dariya nayi nace gidan kakata naje don tun da nazo ban je na gaida ita ba sai
yau sai kuma akace min nayi baki.
Nan na dan dago kai na kalle shi bai ko dago kai ba sai cin dan wanken shi yakeyi
kamar bai san ina wurin ba ma.
Yace dama ai ba ita mukazo gani ba mun dai ga wanda muka zo dubawa gashi har
ummin mu ta bamu wanan abincin da na dade ban ciba muna ci.
Nace aiko abu yayi kyau amma sai dai kaci kadan kasan a gidan sarakkai kake yace
ina nan ai yanzu nima na zama dan gida baki ganina a kuryan dakin uwana zaune.
Kara shiga dakin nayi yayin da na dan rakube a gefen dan gadon katakon ummi sai
hamza ke cewa dashi a gara ki fada mai don naga yana batun mubar kwanon kawai.
Nace yaya hanya suka amsa da lafiya nace amma uncle shine da mukai waya dakai
dazun baka fada min kuna haya ba a shirya ma zuwan ku.
Sai yace akwai shirin da yafi wanan ne a gare mu munzo munga mai jiki kima mun
gabatar da kan mu an kuma ce ambamu abinda muke so gaya min akwai abinda yafi
wanan farin ciki .
Sai ya samay hannushi daga kwanon tare da aje fork din da suke cin danwaken dashi
yace naji dadin da ummi tace kin fada mata komai a kaina shi kuma baba ya amince
dani albarkacin madam.
So ni yanzu banda wani shaku na neman ki don naga inda kika fito dakuma yan
uwanki na kuma yaba da abinda idona ya ganan min.
Karya da rashin asalin shine ba a son a cikin zance naga komai kuma na gamsu da
hakan yazu idan na koma munyi waya da madam da mijin ta za a zo a nema min auren ki
kamar yadda sharia da alada ya tana da don na fada maki ban son wanan abin ya dauki
lokaci mai tsawo .
Ina bukatan azumin bana inyi shi da matata a dakin ta don ban son a sakani cikin
gwauraye kuma.
Kaina na kasa duk kunya da nauyi sun cika ni suka ce in kira masu ummi suyi
sallama da ita don zasu kama hanya saboda nisa.
Na daga tsam zuwa kiran ummi din na samu tana dakin mama can na samayta na fada
mata zasu wuce ta taso sunyi sallama da ita bayan godiya suka aje mata kudi suka
mike.
Sai ta bukaci da su je su gaisa dasu mama sukace sun gode nan akai masu iso suka
shiga wurin su kowacen su ya aje mata daurin yan dari biyar biyar a gaban ta.
Yaran gidan mu sai binsu suke yi suna kallo wasu na fadin wai batare ne shi
saboda farin shi suma uncle bai barsu hakana ba sai da yai masu nasu alherinl.
Mun fito muka samu yaya Sani da driver a waje suna ganin mu suka taso nace yaya
sani bakin ka zasu wuce don naga kaine mai ma saukin baki agidan.
Yace ai dole safiya ance min bakin kauna na ai banda zama don murna murmushi nayi
don jin abinda ya fada nace yayana nakaina ke nan Allah barmin yayan mu.
Amin sukace muka karasa wurin mota sai shi hamza yace barin dan ga nan baya yaya
garin yake ne sai ya wuce ya barmu mu kadai daga ni sai shi su yaya sani sin mara
ma hamza baya.
Jin gina mukayi a jikin motar su yace safiya bazan boye maki ba naji dadin yadda
iyayyenki suka tare mu sosai kuma mahaifinki na samay shi yadda nake so don ba masu
kwadayi bane sai anbasu suke karba.
Yace shi wanan yayan naki yaya kuke dashi ne naga yana da kirki sosai sai dai
alamu ya nuna min baiyi karatu mai zurfi ba ko ?
Nace yayana ne kuma mai kula dani sai na dan bashi labarin shi sama sama muna
cikin hira ne hamza ya dawo yace kai muje inba son kake mu kwana garin nan ba dare
fa yayi yanzu.
Yace ni ba bako bane kaine dai bako yanzu don ni in ta kama a kwana gida nazo
hamza ya dan harare shi yace haka zakai min ko Safiya kin dai ji abinda ya fada
murmushi nayi kawai.
Zai bani kudi nace a, a wanda ka bani da zanzo ban kashe ba duka sunanan su nake
da amfani dasu yace to kara kikuma kashe su din don ki kashe wa yan uwa na baki
kagin in godiya.
Ya juya wurin yaya sani sukayi magana da cewa ina fatan idan zata dawo zakai mata
rakiya yaya sani ya washe bakin jin dadi yace ko yanzu ta tashi a shirye nake ni.
Sai naji yace ki tabbatar tare zaku dawo dashi don Abuja nake son ya tsaya ba sai
ya biki lagos ba.
Nace angode indan kin shirya sai ku sanar dani driver zai zo ya daukeki nace mun
gode baiyi magana ba suka shiga mota muna tsaye muna kallon su suka bace muna.
Sai naji wani irin ba dadi a raina nace may nake yi haka ne badai har son
sulaiman ya kamani haka bane maganan yaya sani ta katse zuciyana da samo ansa da
take so.
Don cewa yayi ikon Allah safiya ina kika samo wanan hadeden mutumin mai karamci
diba fa kudin da ya bani bai ko kirga ba ya debo su ya jinka min.
Yaya Nura ne ya iso da sauri yace ina can wurin gina labari ya samay ni wani yazo
gidan mu yana rabon kudi har da yan unguwa sun samu.
Yaya sani dake sa kudin shi a aljihu yace anshaka ai har sun tafi ko mukan muji
dumus a aljhun mu naga yayi wani iri nace yaya Nura kar ka damu in kadawo sai muga
juna.
Muka jera zuwa cikin gida tare inda muka samu suna ta farin ciki da zuwan bako
suna ganina mama tace kaga yar albarka yar tohun lada haihuwan ki tankar da dubu .
Murmushi nayi tace Allah bai maka fada kayi hakkurin ki ya zama maki taki a
rayuwa don yau mukan mun sheda kuma mun gani.
Dakin mu na shiga inda na samu ummi tayi tagumi zaune tana gani na ta wani nisawa
tace sun tafi ko nace eh tace.
Kin ga irin alherin da yazo muna dashi kuwa yar nan ni abin ma na kasa gaskats
shi a raina wai yau kece Allah yaiwa wanan budin haka a gidan nan.
Ga inna ku can harda ita wurin yabo ba kunya kamar ba ita ke tujara ba jiya a
gidan nan nace kyale ta ummi ni bata gaba na fito mata da tulin kudin da ya bani
nace gasu ya bani.
Zaro ido ummi tayi waje tace duka wanan kudin haka kodai sai tai shiru kuma sai
ta kara cewa ni abin fa tsoro yake bani.
Nace ummi addua zamuyi don aikin gama ya gama tunda yace baba ya basu baki ko
kiran da ake min a waje ne ya katse mu na fito da sauri nabar ummi da kidin a gaban
ta.
Ina fitowa akace baba na kirana dakin shi na rude na koma daki na sako hijjab
dina zuwa wurin amsa kiran baba din.
Ina shiga dakin baba idona yai tozali da kayan abinci a gefe guda tare nai
mamakin yadda suka dauko kaya haka a motar su.
Na shiga da sallama na na samu baba ya dan dago daga kwaciyan dayayi nace baba ya
karfin jikin naka ya amsa da lafiya lau safiya sai kuma ga baki mun gani da rana
tsaka yau.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , ,


4️⃣2️⃣4️⃣
🧕🏿 2️⃣

YAN UWA MUSULUMAI INA MAKU BARKA DA SALLAH DA FATAN ALLAH YA KARBA MUNA IBADUN MU
YASA MUNA CIKIN YANTATTUN SHI ALLAH YA MAI MAITA MUNA WANAN RANAN MAI TARIN ALBAKA
A RAYUWAN MU ALLAHU MA AMIN👏

Kai na dukar kasa yake cewa ai da kin sanar damu zuwan su ba sai a san shirin da za
ai masu ba yanzu gashi sun zo babu komai sai dan waken da uwar ki tayi aka basu.
Nace baba ai sunci sosai sun gode yace kayya ai ina da yan kaji da su aka yanka
masu amma dai na fada mashi wani zuwan ya sanar damu ida zai zo.
Safiya ina kika hadu da wanan mutumin ne bafa karamin mutum bane da ganin sa ma
ba sai an fadawa mutum ba.
Na dukar da kai kasa a hankali nace baba kanin mijin maman biyu ne da nake wurin
ta a can lagos.
Sai yai dan shiru sai kuma yace yasan da matsalan da kike ciki kuwa don kar ai
abu a duhu a cutawa dan mutane rayuwan shi irin da sukai maki.
Kaina a duke kasa nace baba ya sani don shima matsalar mu daya dashi shiyasa
anty ta hada ni dashi da sauri yace subbahanallahi.
Yanzu shima yana dauke da wanan lalurar a jikin shi nace baba yana da shi yace
subbahanallahi nace shima aure yayi ashe matar nadashi ba su sani ba saida ta shigo
aka sani.
Yace waiyazu billahi kai mutane basu da imani a rayuwan su mutum kamar wanan amma
an cuce shi an hada shi da may ye sunan ciwon ma nace tsida don ya gane.
Yace Allah ya baku lafiya nace amin baba yana ta jijiga kanshi alaman jimamay a
ran shi yace yazo da bukata auren ki nayi duk wasu kwana kwana amma yace ayi
hakkuri a bashi ke yasan matsalar ashe abinda yake nufi kenan dama.
To nadai bashi baki yace zaizo da magabatan shi a tsayar da rana don bai son abin
yayi nisa sosai don haka zamu iya ganin su kowani lokaci.
Nace to baba yakara dacewa Allah yasa muce gwama da akayi a raina na amsa mai da
amin a fili kuma shiru nayi mashi yace
Ai na tambaya aka ce kunje gidan gwago ne nasan fitinar inna kuce yasa ki barin
gida kada kije ko ina don ta nan gidan kune gidan ubanki.
Sai dai ita ta fita ta har maki gidan amma bake ba nace a a baba ai inna uwatace
don haka inda sabo na saba da fadan ta akaina bani daya kowa ma bata bari ba.
Mun dade da baba muna magana akai sai yaya Nura ya kirani daga dakin baba na amsa
baba ke cewa mai yake sone sai nayi dariya kawai nace baba barin ganshi yanzu in
dawo yace jeki ma ki huta ai kina da gajiya a jikin ki Allah dai tai maki albarka
yasa ku gama da duniya lafiya.
Na amsa amin baba na tashi na fice daga dakin zuwa wurin yaya nura nan na samay
shi a dan gaba da kofan baba yana jirana.
Ina fitowa ya miko min hannu yace bani nawa duk gidan a jike suke sai ni da bana
nan nace muje daki yaya biyo ni yayi zuwa dakin ummi ya tsaya daga kofa na shiga
na dauko mai kudin.
Ina bashi ya washe baki yana cewa sai kin zama matar gwauna da yardan Allah sai
mun je shan jar miya gidan ki.
Inna dake duke tana talgin abincin dare na semon da akazo muna dashi ta kasa
kannewa da kirarin da yake min tace kuke nan da baku san ciwon kan ku ba kai da dan
uwan ka.
Ku baku ko kishin zucin kanku kuyi ma kanku fada ka tsaya kanayiwa mace kirarin
da yakamata aima maza.
Yace kai ina haba ai kema kin sa fadi kikayi ina mu ina kama kafan safiya ai ita
tariga ta take ko sai dai bi yanzu ko mutum bai so.
Sakarai kawai Allah waddai naka ya lalace mama ta katse da da cewa a a fa ai
gaskiya ya fada ke da aka baki baki karba har fa dubu hamsin aka aje maki yau a
gidan nan.
Duk zaman ki a rayuwa kin taba rike dubu biyar na kanki na kan ki aiko kamar
azuba mata fetur nan ta hau sai da baba ya fito duk da halin da yake ciki har yana
sarkewa .
Take nasa masu kuruwa ina cewa dan Allah inna ku bari kada ku kashe muna uba da
fitinan ku Saadatu ma ta saka ihu take muka sa mata kuka muna kama baba dake ta
tari aiko gida ya rude da kuka yara na cewa wayyo baban mu.
Mutanen waje suka shigo gida ya cika ana tambayan may nene muke cewa babane nan
maza suka kama shi zuwa daki .
Inna jikin ta yai sanyi ta koma ta rakube sai ga yaya sani da yaya nura aka ce
dasu ga abinda ya faru aiko ya fito yana cewa uwar in kin kashe shi sai ki huta na
tabbatar ciwon baba na da halaka dake inna.
Amma ke kulun baki saduda maimakon ki rage sai ma kara baiyana halin ki kike yi
nan dai maza suka taru a kanta sukai mata tas suka fice daga gidan.
Muka taru a dakin baba kowa yayi jugun jugun baba yace idan inna ta kara kulani a
gidan nan sai ya saketa.
Wanan fitinan shi yasa inna laushi sosai ta koma shiru shiru a gidan kowa ya fita
batun ta bayan kwana biyu na samu saadatu a dakin su.
Tana gani na ta zauna nace ya kamata ki rage wanan zaman haka kidan rika motsa
jikin ki zai fi kullun kina daki kumshe murmushi kawai tai min.
Na miko mata kudi ta karba tana cewa na may ye nace ki rike a wurin ki ki dan sai
kayan baby da abin bukatan ki.
Ta fara hawaye tace Safiya halin ki na alheri ne a gare mu ko yaushe abin ki bai
taba rufe maki ido ba wanan kaddaran da ya samay ni nayi kuka a zuciya na nayi a
fili.
Da kina nan da haka bai samay ni ba don kudin mai man gyadan da nake daukowa a
wurin shi in na sayar in kai mashi kudi sai kudin ya kare a kaina.
Kin san kudi in ana tabasu ba a kari yadda suke sai kudin ya rushe a hannu na shi
kuma ya matsa min shine daga baya daya ga banda kudin ya nemi da in bashi hadin kai
sai ya yafe min kudin.
Shine na diga zuwa yana amfani dani ya mayar dani kamar wata matar shi sai da
cikin nan ya samu ne ya guje gare ni tare da fadin shi ba zai karbi cikin ba.
Safiya nasan inda ki na nan haka ba zai samay ni ba don zaki san hanyan da muka
biya shi kudin shi ita kuma inna uwace a baki bata damu da damuwar yar ta ba.
Sai dai in kawo mata tayi bushasha shine da ya daina bani ki ka ga muna yawan
samun matsalan nan da ita.
Na share hawayen da ke fuskana nace kiyi hakkuri kin san duk mai rai nada nashi
kaddara a rayuwan shi.
Na fito ina hawaye dakin ranan na kasa barci ina tunanen matsalan saadatu ina
neman mafita a kai.
Karshe dai na samu hanya mafi sauki na da haka na kwanta washe gari muka tashi
kamar kullun a gidan kowa na ta har kokin gaban shi.
Na fita waje acan daban su yaya Sani na samay shi nan na kirashi shi da amin shi
na kut da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login