Showing 150001 words to 153000 words out of 258256 words
Chapter 51 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
dauka yana cewa yar halas yanzu muke maganan ki don ga takwaran
kinan ta hanamu shakat sai kuka take muna nace subbahanallahi.
Kun bata magani kila cikin ta ke ciwo ina jin yana tambayan Samira ko an bata
magani tace bata bata ba.
Ya juyo gareni yace yaya garin kina lafiya yaya logos nace ni ina gida yaya yace
kina gida tun yaushe ?
Nace sati daya ke nan lafiya kika je gida yanzun Safiya kodai auren ya tashi ne
ban sani ba ?
Nace aure sai dai ayi fatan dacewa da zaman lafiya yanzu yace may kike nufi
tukun nace abinda na fada yanzu yaya.
Wai tsaya don Allah da gaske kikeyi ko wasa nace wallahi ko yau baba ya daura
min aure daga zuwa tambaya sai daurin aure daya ni.
Yace don Allah ki bari ni ina nan ina cewa ni zan bada ke don asan ba zumuncin
wasa ke tsakanin mu ba ashe baba ya rigani.
Nace wallahi yaya ni yanzu duk abin ma ya daure min kai wallahi duk na shiga rudu
wallahi ban shirya komai ba yaya.
Yace Allah yasa haka yafi zama muna alheri nace amin yace yaushe ne tarewan naki
yanzu nace ban sani ba yaya amma dai naji yace in two weeks yake son in tare.
Yace haka yayi yanzu ki bari zamuyi waya zan kiraki ansan abin yi kafin in zo
nace yaya kada kace zaka wahal da kan ka don yace baison inje da ko tsintsiya gidan
shi mata ya nema mata za a kai mashi.
Yace ayi haka bari dai mu gani zan kiraki da safe in nayi shawara mukayi sallama
ya kashe wayan.
Na sauke ajiyan zuciya tare da kifa wayan nawa ina mai sauke numfashi tare da
lumshe idona sai na mike zubur na fada ban daki tare da dauro alwala na fito.
Na dade zaune ina kai kukana ga ubangiji da ya tabbatar min da alheri ga wanan
auren ya kawar da duk wani abin ki a gare mu.
Na dauki lokaci mai tsawo a zaune itama ummina tana nata a falo sai kanne na ne
ke ta kwasan barcin su hankali kwance na shafa tare da mikewa na nade abin sallah.
Sai naji Ummi tace min kin idar na amsa mata tare da fitowa falon na samay ta na
zauna anan.
Take cewa dani gashi dai yau Allah yayi ikon shi kina da aure a kan ki a gidan
nan abinda kowa bai zata ba akan ki.
Don haka sai dai muyi fatan Allah yasa ma auren albarka Allah dai yanufa shine
mijin ki kece matar shi kada kisa kowa a ranki ita ma wace tayi maki wanan dalilin
aure kada ki yarda ki yashe ta komai ritse don ita din ba abin yaddawa bane a gare
ki.
Ki manta da komai ku zauna lafiya don alaka ya sake hadaku dama duk wa yan da
zaki samu a zurian shi ki zauna lafiya da kowa.
Kin daiga shi abin duniya bai rufe mai idon shi ba to kema ki zama haka na ga yan
uwanshi da nasa sai a zauna lafiya.
Yanzu sai mu jira dawowan shi muji yaushe yake son ki tare dakin ki nayi saurin
cewa ummi waifa a cikin sati biyu yake son in tare.
Sai naji ummi tace to shike nan mana Allah yakai mu lokacin nace ummi may aka
shirya da za a biye mashi don yace cikin sati biyu yake son in tare ?
Tace akwai Allah shi zai hore muna abinda zamu kai masu a matsayin gara bashi
kenan ba sai ki tare shike nan sai kuma a jira suna idan muna da sauran kwana.
Cike da jin kunya na sauke kaina kasa ina cewa kai ummi sai tayi dariya tace to
may za a jira kuma yanzu bayan wanan sai maman ku ta shiga zuwa reno.
Kunya naji nace kai ummi tin yanzu har an fara wani maganar haihuwa can a dai
samu a tare din don dazun Faiza ke fada min wai anty uwa tana lagos gidan anty kan
maganan.
Sai naji ummi tace ai basuyi kamar Allah ba don aure ya riga ya dauro a tsakanin
ku ko ba kuma zasu iya rabawa ba insha Allahu.
Mun dauki lokaci muna magana kafin mu kwanta barci da safe ma da muka ta shi da
maganan muka tashi kuma a dakin mu.
Kiran shi ne ya shigo min na dauka da ladabi ina gaida shi bayan mun gama
gaisawa yace Safiya a gidan ku wa kike ganin ta samu kebewa da Nafiu kanina da suka
zo.
Gaba na ne ya fadi dam nace a gidan mu kuwa gaskiya ban sani ba don ni ina daki
har suka wuce yace ki dai bincika din akwai wace ta fada masu wai.
Rufa rufa za ai min kina da cuta a jikin ki abincika kafin ki tare don kar a cuce
ni da sauri nace ba kowa zai min haka ba sai inna .
Yace wacece inna nace dashi maman su yaya Sani don itace kadai zata iya yimin
haka don tasha fadawa mutane hakan.
Yace subbahanallahi nan na fara bashi labarin zaman ukuban da nakeyi da ita tun
tasowa na a gidan har zuwa yanzu.
Yace ok ita din ce na fada ma hajiya baaba da ta tuntube ni da zance nace ba
gaskiya bane sai da mukayi gwaji dake kafin mukai ga matsaya nasan kuma ta gamsu da
magana na.
Zan kuma kara yi mata bayani yadda zata fahince ni amma dai wanan matar ko bata
da hali mai kyau yace zan gaya wa baba da kaina don ya dauki mataki akan ta kada
yan uwa na suzo ta bata auren.
Nan dai ya kwantar min da hankalina muna gama waya na kira ummi na ina fada mata
ita kuma bata tsaya ba ta kira mama tana sheda mata abinda ke faruwa.
Mama tace a bari baba ya dawo gidan ai ba kyale ta za a yi ba dole ai mata magana
wanan karon.
Basu gama magana ba sai ga baba ya shigo a fusace tun daga kofan gida yake
kwadawa inna kira mama tace gayacan ma shigo ko yaji ne ma ?
Inna tafito tana cewa malam wanan kira haka kamar makaho ni har gabana ya fadi
ai.
Yace gaban ki ya dade bai tarwatse ba munafukan banza muna fukar wofi kawai ta
Allah ba taki ba.
Munafincin ki bai ciba sai ki canza wani kafin ma ki canza badai a gida na bakan
don safiya bata tarewa kina gidan.
Fadin haka yasa yaya sani dake bayan shi yana sauraren maganan baba din yace
saboda may baba ?
Yace sani wanan uwar taku wani irin hali ke gareta yanzu ace duk halarcin da
yarinyar nan take muna agidan nan kaf bata debe kowa ba wai amma Rakiya bata gani.
Sai tabi baya ta yi munafinci akan auren Safiya don ta kumsa muna bakinciki kawai
duk a taru a lalace uwa zaune diya zaune a gida kamar yadda take da yar ta a daki.
Yaya sani ya sake fadin may ya faru ne baba may kuma innan ta sake yi ne wai ?
Yace sani wai ka diba ashe zuwan mutanen nan garin nan Rakiya ta sillace jiki ta
ja daya daga cikin bakin nan ta fada masu wai ba lafiya ke ga Safiya ba ayi bincike
kafin ta tare.
Sai gida ya dauki salati dama kowa ja waje cirko cirko a tsaye ana sauraren baba
yaya Nura yace an ko yi haka wallahi dama nayi tunanen in ba wani abin zata fada
mai ba don naga lokacin da ta fito suna alwala ta kirashi gefe ni kuma muna shagon
musa mai tereda zaune wallahi na ganta.
Kai munafuki da ka ganni sai akace abinda na fada mai kenan ko may yace nidai na
gan ku tsaye wallahi ba wani ya fada min ba da idona na ganki inna.
Baba yace yanzu yaron nan ya kirani yana fada min sakon da aka kaima uwarshi gida
don haka ban zama da macen da bata son diyana da karuwa a gidan ki tafi gidan ku
har, , ,
Yaya Sani ne yace don Allah baba kada ka karasa don Allah sai ya fashe da kuka
sauran yaran suka dauki kuka gaba daya.
Ummi tace malam kayi hakkuri ko don yaran nan idan ka sallamay ta yanzu ga
Saadatu da ciki ina zata yace inko ban sake ta ba yanzu bata zaka min gida sai
safiya ta tare.
Nan dai gida ya dauki kuka kowa da abinda yake fada yafice yabar gidan nace
gidan mu gidan danger.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON
5️⃣3️⃣5️⃣
5️⃣
🧕🏿 3️⃣3️⃣5️⃣
NOVEL DINA NA KUDI IDAN KIN FITAR MIN ALLAH YABI MIN HAKKINA A KAN KI IDAN KI
KARATA BAKI BIYA BA BAN YAFE BA NA FADA NA SAKE FADA A KIYAYYE DON ALLAH DON CIN
AMANA BALA,I NE, , , , ,
Shigana daki yayi daidai da shigowan wayan Faiza nayi saurin dauka don nasa magana
ya samu ke nan ina dauka tace wai safiya may ya faru ne daga jiya zuwa safe dai
surfa maki zaki ake a gidan nan babu kakautawa.
Tace bari dai zan kiraki ina zuwa sai ta kashe wayan nata na bi wayan da kallo
kamar shine faiza na bashi amsa da cewa sunji zancen auren ke nan.
Shigowan gwagom Ummi na gidan ne ya dawo da kowa a cikin sai tin shi don ta
shigo gidan ne da gudan ta tana fadin ayyurriri amarya Allah ya kawo mu lokaci ya
kawo mu yan bakin ciki kunji kunya masu hassada kubi bango ku narke don Saifiya da
Sulaiman zama daram.
Su yaya Nura ne ke fadin gwagon ummi gudan bai isa ba sai ta kara fadin ayyurriri
Amarya.
Yar shagali yar biyan bukata yar galari , makulin mota ke akaba na kofan daki ke
akaba sai yaya Sani ya manna mata kudi a goshi nan ta kasa karasa kirarin nata ta
saike guda tana fadin Amarya bakya laifi, ina amaryan take ne.
Sai mama tace a a gwago karkizo ki sa min yarinya kuka fa munyi arziki tunda aka
daura aure bata wani bata rai ba.
Gwagon ummi ta juya ta kalli mama tace kuka kuka fa kikace
Yo kukan may ina so kina so sukayi fa kinji ki da wani zancen badai yaran
yanzu kuka kan.
Aiko na munafunci basa yi koda kuwa budurwace sun daina kuka tace yo Allah na
tuba wanan din ma ai tayi kawaici da watace da yanzu ta kafa muna DJ a gida ta ruda
unguwa da gaiyatan shedanu masu hana auren zaman lafiya.
Ummi ce ta fito fuska a daure tana yiwa gwagon sannu da zuwa ta bi yar dan uwan
nata da kallo tana amsa gaisuwa nan tabar mama da sauran yara tsaye ta nufi dakin
umin nawa.
Kara gaisawa sukayi ta kasa daurewa tana tambayanta make faruwa ne naga ranan
farin ciki a gare ki gashi kuma kin bi fuskan ki duk kin daure ?
Ummi bata iya yin magana ba sai hawayen dake zubo mata sai nice nayi karfin
halin fito ina cewa gwago an shigo tace a a kina ciki dama ?
Nace na kwanta ne dama tace may ya samu uwar taki ne haka kuma ranan farin ciki a
gare ta gata tana kuka kuma ?
Nace ba wani ubu bane zancen Inna ne dai shine takema bacin rai ,
Innan taku tayi wani abune mara kyau ne kuma nace gwago takan rasa ne ai mai
hali baya barin halin shi.
Zuwa tayi ta fadama ma dagin mijin antyn mu wai suyi bincike anty mu na da cuta
a jikin ta amai rufarufa ne don acuce shi.
Salati gwagon ta saka tun kafin taji karshen maganan tana fadin amma dai anyi yar
banza mata anan .
Da ita nufinta haka za a hada auren bai san halin da take ciki ba to mu bamu da
gadon sheri a tare damu.
Yanzu may ake ciki tana sake tambayan Aisha kauna na don ta san ni da ummi ba
zata gane komai a wurin mu.
Aishan tayi mata bayanin komai yadda zata fahinta tace hakan da malam din yayi
yana da kyau tunda dai Rakiya bata da niyar gyaran halinta.
Nace ni gwago na rasa mai nayi wa inna a duniya tun ina karama bata kauna na
haka.
Tace bazata ko kaunace ki ba don indan kika ga mutum da yafaye wanan halin yaje
bakar bincike binciken ta an fada mata abinda ya tayar mata da hankali shi ne abin
yake wahal da ita haka.
Kin san wasu basu da dogaro gun Allah da zaran kishiyar su ta samu ciki zasu je a
bincika masu mai zata haifa da sauri nace kai haba gwago tace Allah sarki ai wanan
abin abu ne da ya kewaye birni da kauye don ko ina akwai marasa imani.
To duk yadda akayi irin haka ne ke damun Rakiya taje an mata buncike an fada
kata cewa abinda zaki haifa na da arziki sai ta ce a jefo mao kaddara da karshe
kuma ba mai iya hana ikon Allah sai kaddaran ya juye Alheri ga bawa.
Shiru mukayi muna sauraren gwago da al,ajabin abinda take fada muna tace don
yanzu an daina wasu abu saboda wayewan kai da mutane suka samu.
Amma har gobe a kwai masuyin zagon kasa don su basu bar gida ba don haka yake da
kyau mutum ya nema wa kansa rigakafi tun kan rana ya baci.
Don haka kema yanzu ki saurare ni don zaki tafi cikin bakin fuska da baki san su
ba baki san halin su ba .
Don haka zan baki makarin kwarce ko wani zai maki ba zai kamaki ba murshi nayi a
raina nace kai gwago ho.
Zaki samu kwai na zabo guda ukku sai ki samu kayan aduwa 99 a hada su da
kwanzaben nan a dafa sai ki hada bawan kwan da kayan aduwa a dakesu adinga zubawa a
kunu anasha.
Maganin walwale turbuda shine turbuda kuma idan kina zargin wani na maki asiri
shine,
Zaki samu ruwan tsami ko ruwan tsami da ganyen zogala wanda aka shuka iyankan
gona sai ki jika da kai kayi koma kan mashekiya ki hada da ruwan tsamin da zogalan
na iyakar gona kiyi wanka ki sha.
Da yardan Allah komai mutum ya dauko a kanki sai dai ya koma mai badai ya kamaki
ba.
Wayana yai kara sai na mike na koma daki na bar gwagon nan falo zaune da ummi da
su Aisha.
Na dauko wayan da sauri gabana ya fadi don ganin lambar anty na kira na a
lokacin wada dama ina tsamanin hakan ko yaushe.
Na dauka da sallama ta, sai naji ta katseni da cewa amarya ke nan ke nan kai
duniya ina zaki damu ashe tsintaciyar mage dai bata taba zama mage.
Lalai mutane sunyi gaskiya da suke fada min cewa ke din tsintaciyar mage ce a
gare tabbas ko ya tabbata hakane.
Kafin in magana sai naji ta kashe wayan ta dip ajiyan zuciya na sauke tare da
sake murmushin bakin ciki lokaci guda.
Na a sanyaye na fito falo inda suke na zauna ban iya cewa na fahinci hiran su
alokacin sai da naji tace ai kinga idan yaro ya na dauke dauke zaki samu kaucin
malge a samu kashin mai satan a hada da malgen a shaya in ya bushe a daka in ya
zama gari sai a dinga sa ma mai shi a kunu ko shayi yana sha har kwana bakwai da
yar da Allah zai bar satan don da yaje daukan abu warin kashin shi dayaci zai hana
shi daukan abu yaji satan ya fice mashi a rai.
Sai kuma mallaka da sai abinda kika ce a gidan zaki samu kaucen gwanda na daji ki
dake shi ya zama gari a samun kan tunkiya da ta kosa adafa su tare in ya dahu sosai
ki zauna kici duka amma bada kashin ba.
Allah sa mu dace naji tace sai lokacin na kallo ta ina cewa ummi yanzu anty ta
kirani fa.
Da sauri tace yaya kukayi da ita ta sake fadin taji ke nan dai ko ?
Na gyada mata kai da alaman eh gwago ne tace may taji auren sai ummi tace eh
gwago tace dama bata sani bane Aisha dake zaune ummi ta kalla sai tayi shiru.
Na ce ummi ai yanzu ba maganan boyo bane tunda abin na ta kamari tace wai may ke
faruwa ne kumbar mu a duhu haka ?
Ummi tace ummi kin san sun samu matsala da uwar rikon nata tace subbahanallahi
shine baku fada muna ba asan abin yi.
Ummi tace abin ne wallahi da daure kai zaman su ba wani matsala sai daga baya ne
kuma wani hali ya shigo masu.
Don ita bayan ta hada su da kanin mijin ta sai kuma daga baya bata son hadin wai
tana son hada shi da wata yar yar uwar mai gidan ta.
Shine ita ta risketa tana waya suna fadin wai zasu zo suyi kata korar kare a
gidan da take zaune shine shi wanda ta aura din ya bata shawaran ta dawo gida.
To shine da nake fada ma malam halin da suke ciki sai malam din ya yanke shawaran
cewa da sun zo tambaya sai a daura aure da yani.
To yanzu nasan taji ne shine wai ta kirata yanzu din sai gwago tace may tace dake
to ?
Nakwashe abinda ta fada min na fada mata sai tace aikin banza ai Allah ya riga
yayi ikon shi ko a