Showing 93001 words to 96000 words out of 258256 words

Chapter 32 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

ko sai mun kaika mararaba mun ma wanka ne
zaka daina tsaron mata.
Yace kai don Allah bari wanan ma ta gama secondry ne tace tun yau she ta kare
Allah da gaske nake yi inda kana ciki sai in kama ma kawai musha buki.
Take ya daure fuskan shi alaman ba wasa a tare da shi tace kai ke nan da an
maganan aure sai ka bata rai may kake nufi ne wai ?
Bai bata amsa ba sai ci gaba da yayi da hira da yaran dake gaban shi sai da ta
kawo mai zancen aikin da akeyi mai ta samu ya sake fuskan shi.
Ni ko tunda na juya na wuce ina ta mamakin haduwan wanan mutumin da anty tace dan
uwan daddy ne mijin ta kuma wai may kudi naji anty na cewa.
Na gaji da tunane na watsar da zancen na kama sha anin gabana daya damay ni kwai
sai ga fati ta shigo dakina abinda ban taba gani ba tun zuwa na gidan.
Tana shigowa ta fada saman gadon dakin nawa da yasha gyara sai kamshi ke tashi a
dakin tako ina na dakin.
Safiya kin san kowa yau ina cikin farin ciki ga uncle can a falo yazo tun dazun
yazo yana falo na dade dakina ina leken shi ta fada saman gadon tana wani irin
dariya.
Nikan kallon mamaki kawai nake binta dashi don abin ya daure mun kai sosai tace
wai kin san wani abune safiya na gyara zama tare da cewa aa.
Tace wallahi anty tana kawo min kubsawa don sam bata son zance da guy din nan ni
kuwa duk yadda zanyi in ga yaso ni sai nayi kin san abinka da yan uba.
Sai nai saurin kallon ta don jin kalamin ta gamay da anty duk wanan halarcin da
take mata amma wai tana kiranta da yan uba.
Ta kara lumshe ido tana ce min guy din ya hadu ne sai ma in kin ganshi wallahi
yanzu tashi zan yi in dake kawai in je mu gaisa dashi ko bata so ni ban damu in dai
bukatana zai biya.
Nace haka za a yi kije ku gaisa ko ki samu shiga ai ba a bori da sanyin gwiwa
tace ai shi na gani wallahi.
Ta mike tana wani juye juye tace yaya kika gani na hadu ko da gyara nace cikin
daga kai komai tsab wallahi.
Ta fice daga dakin na bita da kallon mamaki nace oho zamani ina zaki damu mata
cusa kai ga maza haka ?
Acan falo tun da anty taga ta tun karo wurin su tace kin ga Fati kira min safiya
ta hada ma uncle fruit salad wai abinda yake so ke nan.
Tace anty bagani ba zan iya hada mashi ai tace don Allah ki raba ni da shirmay ki
ranan da ta hada masu bacewa kikayi ke baki iyaba.
Sai tace ai naga yadda ta hada din kin ga kira min Safiya nace don Allah ban son
shirmay ki hakan nan.
Ta wuce tana mai jin haushi yar uwar nata data kwabsa mata a gaban shi sai gata
dakina tana cika tana batsewa tace tana kiran ki .
Niko ina cewa yaya anyi nasara dai ko kin samu magana dashi tace ina yar bakin
cikin zata bari ai komawa zanyi ko bata so.
Nace antyn ne yar bakin ciki tace to in ba bakin ciki ba ko zama bata bari nayi
ba ta koreni da karfi da yaji ban san abinda take nufi da hakan ba.
Mikewa nayi zuwa amsa kiran anty na je da sallama na ce anty ance kina kirana
tace eh kin ga don Allah wanan gwauron zaki hada ma fruit salad wai yake son sha
yau.
Ban tsaya ba na juya zuwa kitchen din ya dan kalle ni ta witsiyar ido a ranshi
yace ba laifi yarinyan sai dai akwai shamaki a tsakanin mu.
Ban dauki wani lokaci ba wurin hadawa don akwai komai na bukata kankara na jefa
yadda zai yi saurin yin sanyi bayan na hada din.
Na nufo dashi nan na tsikayi Fati zaune tare da su tana wani kwarkwasa yar nata
nata hararan ta bata damu ba nazo gaban shi na aje yace dani thanks kawai na juya
zan wuce..
Anty tace dan tsaya ki zuba mashi nima ki zubo min karya shanye ba sha ba nan na
juya na sake dukawa gaban shi ina diban mata kamshin turaren madina dana shafa ya
dokan hancin shi sai lumshe ido yake yi cikin sytle.
Na diba na bata na dago muka hada ido da Fati sai naga tana harara na ni dai na
wuce abina ban kara juyowa ba.
Sai gata dakin ban bari tayi magana ba nace kai amma Fati kunyi balain dacewa da
wanan mutumin gaskiya.
Da da fushi ta shigo amma jin abinda nace yasa ta washe baki tana fadin gaski
Safiya nace kwarai kuwa kiyi kokari anty tafahinci ki .
Tace haka za ayi ai don haka sai na zauna ki fada min ta inda zamu bullo mata
nace niwa aini yar kauye ce ban san komai ba wallahi..
Da yamma muna falo gaba dayan mu Faiza ke cewa wai ni yaushe Yaya sulaiman ya
wuce dazu ne ?
Kafin anty ta bada amsa Fati tai carab tace ai kedai yau ya dade gidan nan sai
anty ta balla mata harara tace ke aka tambaya ko kin san wucewar shine.
Wai ke may yasa baki da hankali ne Fati sai tai wani turo baki kamar karamar
yarinya nace anty kin sani ko za ayi yar gida ne.
Tai saurin cewa haba Safiya don Allah kibar wanan zance ki kyale ta da shirmay ta
can so take mukai ga yadda ba a so.
Ita ke haukan ta nan shi yana da wace zai aura ko ina ma zai kai ki haka kazama
dake sai tai fushi ta daga wurin Faiza tace da gaske anty ya samu mata.
Tace insha Allahu muna fatan hakan amma sai komai ya kankama zamu je ayi magana
don ba yar kasan nan bace yace.
Nan ta hau murna don jin dan uwan nata ya samu wace zai aura ashe maganan ya fada
kunnen Fati dake wuce wa.
Sai da na dawo daki ta samay ni da maganan nace tayi kokarin cusa kan ta dai in
Allah yayi ai ba wanda ya isa ya hana ta sauke ajiyan zuciya tace shiyasa nake son
ki wallahi don fadin gaskiya.
Ni dai na samu ta fita na rufe kofa na asuba ta gari sai kuma in Allah ya kaimu
lafiya muji da wace zata zo min kuma a gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , , , ,


3️⃣3️⃣3️⃣
3️⃣
🧕🏿 3️⃣3️⃣


YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDINE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU
PLEASE DON BAN YAFE BA IDAN KON FITAR MIN DA NOVEL UBANGIJI YA SAKA MIN A KANKI
CIKIN GAGAWA.


Wanan abin yasa yanzun muke shiri da Fati don ko yaushe tana dakina muna hira abu
daya kullun na yadda zata shawo kan shine a gidan.
Zata shigo ta fadi nidai ina ta mata dariya indan ta gaji ta fice ta koma dakin
ta, sai dai abu daya ne wanda ban yarda da shi ba.
Irin yadda take kushe maganan anty ko take sukan ta da munana kalamai marasa
dadin saurare.
Don haka sai na dakatar da ita nace idan zamuyi hiran mu mubar saka sunan kowa
mudai nemi mafita akan yadda zamu fito mazancen ta da sulaiman din.
Taso tai hushi alokacin amma sai tai tunanen ba ida take kai maganan ta ba tare
da wani yaji ba sai gurina, sai gashi ta dawo da kanta.
Ina kwance daki sai gata ta fado min daki tana dariyan jin dadi nace halan
mutumin ya shigo ne.
Tai wani far da idanuwa tace dani bai shigo ba tukun amma naji mijin anty na waya
dashi wai su hadu karfe hudu nan gidan.
Nan dai mukai shawaran abinda ya dace tayi tabar dakin tana ta murna nikan fitan
ta dakin na kwanta abina don ina fashin yin sallah a lokacin ban son shiga mutane.

Kamar yadda Fati ta fada hakan ne yazo gidan bayan hudu ya dan gwauta kadan yana
falo da anty daya sama a falon ita da yaran ta.
Tun shigowan shi take faman sake murmushi a fuskanta kamar yadda ta saba indan
sun hadu.
Ya zauna suna gaisawa da ita yace komao lafiya ko ta amsa mai da lafiya kalau
muke, tace yaya aiki kuma?, ya lumshe idon shi yana cire hular kan shi .
Yace aiki muna kai wallahi yai ajiyam zuciya yace yanzu ma mijin ki ne ya kirani
koda yake dama yau ina da niyar shigowa gidan naku.
Sai ga mijinki ya kirani kuma tace ka kwana biyu baka shigo nan din bane ya sake
cewa wallahi yau nake da niyar shigowa don ina son in baki wani aiki ne.
Ta nisa tare dacewa tau fa, ina jinka rankaya dade,
See you nine ranka ya dade kuma ni dai kisa a hada min wanan abin don yau dashi
zan tafi don ina son shi sosai wallahi.
Mikewa tayi don yaran sun shige don bude tsaraban da ya shigo masu dashi da zaizo
don haka babu yaro kusa sai anty taje kirana da kanta.
Tana wucewa Fati ta fito acikin wani irin kwaliya tana kashe ido wai tana mai
sannu da zuwa takai zaune a dayan kujeran falon.
Niko ina daki na kwanta wuri daya na dunkule wani iri kamar maijin sanyi idan ka
ga yadda na kwanta.
Tabani, tayi tana kiran sunana a hankali, inda na bude ido na sauke a fauskanta
ina mai kallonta cikin magagin barci sai naji ta tambaye ni dacewa lafiya kike kuwa
kike ta barci haka ?
Na murza idona tare da cemata anty barci ne kawai ya dauke ni tun dazun tace to
tashi don Allah aiki zan saka ki don wanan bakin batauren ya shigo wai fruit salad
yake son aimashi.
Na sake murza idona nace to anty barin tashi yanzu zan fito ta mike don barin
dakin nawa har takai kofa nace ina mike wa Fati na nan ne muyi tare.
Tace Fati ko mashiririciya may zata iya wanan don Allah fito ki hada mashi tunda
har yai magana kada ya tafi ba a hada mai ba kuma.
Hankalin shi naga wayan shi baiko san tana zaune a wurin ba ita kuma sai wani
gyare gyare take yi daga zaune kamar wacce ake tsunkulan ta.
Anty ne ta iso gurin tun da ta ganta ta daure fuskan ta har tazo ta zauna ba
walwala a fuskan ta.
Ta zauna tare da cewa ke kuma may kike anan din kije safiya na jiranki ki kama
mata aiki.
Ta juya inda yake tana murmushi tace ina jinka sakon may kake magana akai ne
wai ?
Ok dama account dinki nake so inyi amfani dashi in tura ma wani kudi miliyan
hamsin mun sai injin ne a gurin sa .
Sai bayan sati biyu zaa fitar da kudin kinga kenan kema zaki iya samun wani abu
daga yin hakan .
Tace sulaima ba matsala gayin hakan dagowa yayi yana mata dariya yace idan da
matsala ai ba zan saki a ciki ba kedai ki bayar zaki gane abinda nake nufi.
Sai ya fara mata bayani a takwaice yace ashe ke matsoraciya ne kina tsoron kada a
yaudare ki ko da irin haka yawancin mutane suke dagawa ina son inga account dinki
yana motsine.
Nan ta shiga dariya don ta gane mafusa arlallan business yake son sakata ciki
itama nan ta shiga yi mashi godiya daga mata hannu yayi yace haba madam ya idan ban
maku ba suwa zan taimakawa ?
Yace sai dai gida da fili danake son saya a Abuja ta saki baki tana kallon shi
don jin irin bayani da yake mata na gida da filin da yake so.
Ta sake cewa yanzu sulaiman ga gida ga fili kake shirin saya haka yace ai wanan
ba komai bane sai tai wani irin shewa.
Tace iyyye tun yanzu ashe bari mu fara shirin buki ashe,
Dariya ya fara mata yace ba a sayen gida sai za ai aure ki rufa min asiri tun
dawowan mu kudin nan nake son in sai gida da fili dasu, don ina yin wani aiki acan
Abujan kuma dai ina ganin anan zan zauna don nafi son zama arewa da nan din.
Tace kayi dabara wallahi shawaran da nake ba daddy su kenan ko yaushe amma naga
shi ra, ayin shi baison zama arewa sam.
Yace arewan ne babu dadin zama saboda mutane yan sa ido ga abin da bai shafe su
ba sai suyi tama zargin banza ba gaira ba dalili kai kana neman nakan ka amma
mutane idon su na kanka.
Mijin anty ne yashigo sai suka can za firan suka fara gaisawa dashi a daidai
lokacin da na fito dauke da tiren a hannu na da na shiryo mashi.
Daddy din na fara gyarwa sai shi sai daddyn yace Safiya kike ko kina gidan nan
ban gani ki sai nike tsamanin ko kin koma ne ban sani ba.
Murmushi nayi kawai sai anty ne ke cewa ita wanan ai in ka ganta waje su yan biyu
ne suka fitar da ita dole zaman daki baya isan ta ko yaushe tana ciki kumshe.
Na gama jerawa zan wuce sai naji tace yauwa daddy shine nace ma mutumi na ko zai
fada neman Safiya ne ya tsaya yana min kwana kwana.
Don Allah ba sai yar gida gida ba kawai ga mata har gida ya samu ba niba har
mijin nata wani irin kallo yai mata nidai na wuce na barsu nan.
Ina ganin sun dade a wurin sai dai ban san maganan da sukeyi ba dagani dai
maganan tana da muhinmanci a gare su.
Sai can naji fitan mazan daga gidan wanda ban debe tsamani sallah suka fita yi
don lokaci da yayi yan biyu ne tazo take ce min mummy su na kiran su.
Ban tsaya ba na jawo dankwali na dora a kaina muka fito tare da yarinyar da tazo
kirana din .
Tana zaune tana hada wasu takardu dake saman table din gaban ta tace kinga bai ko
sami tafiya dashi ba yadda yace anan suka shanye abinsu shida major.
Ina kwasan kayan nake jin yadda anty ke ta faman yabon sulaiman din har take ce
min wallahi safiya idan na samu nai wanan hadin a tsakanin ku kowa naki ya huta
indai Sulaiman ne don bai da matse na tare dashi balle matar shi mutum ne mai sakin
aljihun shi sosai wallahi.
Nidai abinda na saba nai mata watau murmushi sai dai a raina nace kardai anty ta
zamo cikin masu rufe ido ayi cuta da ita kan abin duniya.
Ni dake da lalura har take zancen hadani da wani wanda baida matsala irin nawa ni
yanzu aiko mai irin matsalata banda lokacin shi balle mai lafiya in cuta mai.
Na kwashe kayan zuwa kitchen da zan fito ma ban dawo wurin ta ba sai nai hanyan
dakin na don zancen ta ba abin saurare bane a wurina.

********* ********* *********
A can gida kuwa ummi da kanina shafiu sun rike sanaar da na bar masu dakyau don
takar ina gari ne don yaron bai da wasa ko kadan.
Saadatu inna ta kwaso ciki tun ba a gane ba har mutanen gidan mu suka gane ana ta
kumbiya kumbiyar zubarwa sai dai Saadatun taki ba Inna hadin kai a zubar da cikin
tace tsoro take ji.
A wani dare basu san baba yana waje yana alwala ba rikici kan azubar da cikin ya
hada ta da inna a dakin su tun bai sauraren su har takai baba ya saka kunne ga
maganan su.
Nan yaji abinda ya tayar mashi da hankali ya koma dakin shi sai kuka koda gari ya
waye bai fito ba har wani lokaci.
Mama ne ta shiga dakin shi don taga may ya samay shi ta samay shi a cikin wani
hali take hankalin ta ya tashi.
Zata tara mashi jamma a yace taje dai ta kira mai inna da su ummi da yaya Sani su
zo.
Kowa ya taru suna jiran suji may zai fada masu sai can yace ma mama yanzu har da
ke ashe za a hada kai a cuta min gidan nan.
Abu na faruwa haka amma an rasa wanda zai iya fada min sai da Allah ya sanar dani
jiya da dare nan ya kwashe abin da yaji tsakanin inna da Saadatu yake fada masu.
Nan Inna ta kama fadan karya wai baidai ji da kyau ba mama ne tace haba Rakiya ko
makaho ya lalube saadatu ai yasan halin da take ciki.
Don baki samu bane shiyasa muka kawo ido muka saka maku kawai amma batu duk ya
gama bin gari ai.
Shiru wurin yayi sai yaya Sani ne ya kawar da shirun da cewa Inna kin kai ga
yadda kike so ba abin da baki fada akan matsalan Safiya agidan nan.
Yanzu gashi ke Allah ya nuna maki nashi isharan sai ku san yadda zakuyi da ciki
ai maza basu son ta da aure amma suna son ta da lalata.
Baba yai magana karo na biyu yace ba mai zubar da cikin nan a gidan nan don bani
kunya biyu abarshi ta haifi abinta kuma duk wanda yace zai yi yunkurin zubar da
cikin nan sharia ce zata raba mu dashi.
Nan ko inna ta aza hannu akai wai dama ta sani baba bai kaunar ta da diyan ta ai
yafi son yaga sun lalace a gidan.
Yace yadai ji amma ba mai zubar mai da ciki a gidan shi sai inna tace zata kaita
wurin yan uwanta a wani kauye a zubar can.
Amma ba yace bai yarda ba da kuyan lahira ya kwmmace yai na lahira don zunubin
shi bai kona shiba na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login