Showing 75001 words to 78000 words out of 258256 words

Chapter 26 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

likitan yai shiru can kuma ya dan dago kai ya kalli baba din yace a gaskiya
ba yar ka tana dauke da cutan tsida mai karya garkuwan jikin dan adam.
Baba yace ban fahince kaba hawanjini komay kace likitan ya girgiza kai yace
gwaji ya nuna muna tana dauke da cuta mai karya garkuwa jikin dan adam watau HIV.
Ban san lokacin da na yanka ihu ba baba yace ke may ye haka kuma daga bayani ki
yanka muna ihu tashin hankali.
Likita yace tana da right din yin haka don ba karamin masifa bane ya samay ta.
Baba tace likita may kace yace ina nufin ciwon da ya samay ta yana da wuyan sha
ani sai ya fara yiwa baba bayani yace.
Sai da ya kawo wiri aure ya ce mace na dauka ta mijin ta idan mijin ba mai
tsayawa ga matar sa bane yana neman mata a waje shine dalili daya na tambaye ku
mijin nata yana ina?
Da sai mu ga gwada shi mugani shike da ciwon ko ita anan zamu fahinci wanda ya
sawa wani ciwon a cikin su.
Baba ya miki yace ke tashi muje kin ji ai ba nan kawai bane asibiti akwai wasu
guraren zuwa bayan nan.
Da kyat na miki don duk illahirin jikina yai sanyi baba na ta faman fada niko
tunane nake yi ko shiyasa yaya saadu ya matsa in je asibiti.
Yasan dan uwan shi nada ciwon ne yasa ya damu da zancen azo dani asibiti a duna
dai aga may ke damuna ne.
Mun shiga gida ana fadin kun dawo baba ya na fada kaji min dan iskan likita kawai
ka rasa abin dafa mata sai mugun ciwon da kowa ke guda.
Nan da nan aka firfito waje don saure inna ce tace may akace yana damun tane
wai ?
Yace bar mugun liki wai wai Safiya na dauke da wani ciwo ko tsida ko may tace
badai kanjamau ba yace wai shi .
Nan da nan Inna ta dafe gaban ta munshiga uku mun lalace a gidan nan muke zaune
da mai kanjamau sai ya dakata fadan yana kallon inna din da ta rikice.
Yace ke kuma may nene duk kin bi kin wani rude dake ?
Tace malam kanjamau fa akace irin ciwon da ya kashe dan gidan malam sahabi kwana
ki har akaki taba gawan sa.
Nan jikin baba ya fara sanyi yace don Allah ki bari ke ma kin yarda ke nan tana
da wanan ciwon ?
Tace bani yarda tunda mijin ta karuwai ne abokan hurdan shi ko yaushe cikin su
yake yana like a gidin su yaya bazan yarda da maganan likita ba.
Ummi na tasaka kuka mai tsuma zuciya mai sauren ta tana cewa na shiga uku na
lalace yau ni Rabi may zan gani a rayauwa.
Tayi dakin ta tana kuka cikin dakin ta samay ni nima kukan nakeyi in cewa ummi
yaya Ahmed ya cuci rayuwa na.
Ummina na mutuwa zanyi in barki in barki da yan uwana da kowa naki ni safiya na
shiga uku.
Yar nan Ahmed bai cuce ki ba malam ya cuce ki shida ya bashike duk da yasan halin
yaron ya kuma amince da ya hadaku.
Kuka muke yi nida ummi da kanne na adakin baji ba gani sai baba ya tsaya daga
kofa yana cewa wai baku barin kukan nan ba a fa sheda cewa shine abinda ke damun ki
ba kun aza ma mutane kuka haka a gida.
Dole mukai shiru irin yadda yake ta faman fada sai dai ummi bata tsagaita nata
kukan ba da take yi gwanin van tausayi ance uwa uwace bakowa ke karba sunan ba.
Baba ta samu an tsagaita kukan ya kwantar masu da hankali dan kwana biyu ga
damuwa ga ciwo naci na baba ya ki kwantar da hankali ya fahinci komai.
Wanan karon an jijigani sosai Yaya sani sukai waya da yaya saadu yana tambayan
shi yaya jikin nawa ?
Ya fada mashi ina jin jiki anje asibiti ga abinda likita ya fada innalillahi yake
maimaitawa yace dama ina tuhumar haka ya faru .
Don shima Ahmed din tun fitan Safiya baida cikakan lafiya tare dashi yace a kaiwa
baba waya su yi magana.
Bayan ankai sun gaisa da baba yake cewa baba naji ance kun kai Safiya asibiti
likita ya fadi abinda ke damun ta kun karyata.
Baba yace gaskiya ne haka akayi wani likitane mai mugun nufi ya zarga mata wanan
sherin don kazafi irin na likitoci.
Yaya Saadu yace baba ka saurare ni kaji yace ina jinka yace don Allah don Allah
kukai yarinyar nan asibiti ta karbi magani in ba so kuke mu rasata ba gaba daya.
Abinda likita ya fada ba karya bane haka ne don na dade ina zargin haka shi ya da
ita don mijin ta ma nemin mata ne ga shan giya idan ya sha baya laakari da irin
matan da yake hurda dasu.
Baba kukai ta asibiti a san abinda ake ciki su dora ta ga maganin da ya dace
tasha tin bai mata nisa ba.
Baba yai mashi godiya sama sama sukai sallama ya dukar dakai yana kukan nadama ya
cuce ni ya cuci mahaifiya ta dashi kan shi.
Tun wanan lokacin ya koma kamar baida lafiya a gidan washe gari ma bai tafi
wurin bidan kudin shi ba.
Ina daki mun bana fitowa don da na fito yanzu kowa zai kama kan shi babu mai
zama dani balle idan na taba abu wani ya taba.
Daga ni sai yan dakimu nake hurda kawai a gidan suma kamar ana kyanaman su din
kamar ni.
Abinda yasa na fara ganewa yadda mama ta dauke kafanta ga sha,ani na agidan ba
ruwanta dani yanzu.
Ba may son ace yana hurda dani kamar zan lika masu cutan a jikin su koda yaushe
ina daki ga jikin ba dadi min.
Shi baba har lokacin bai yarda ba saidai nadama ya shige shi sosai na yadda yaba
da ni ga dan gwago duk da yasan bana kwarai bane shi.
Ya dinga tuna irin badakalar da suka kwasa da ummi a gidan kan aure na , ashe
tafishi gaskiya da ta nuna rashin yardan ta da aure.
Ashe mafalkin da tace tayi dani mara dadi nada na saba da abinda zai faru da nine
gaskiya idan haka ne gwago taci amanan zumunci.
Ga ciwo ga saki ga haihuwa ba yar tazo a wani irin yanayi takoma ni ina zan kai
alhakin wanan yarinyar a kaina.
Sai hawayen nadama da dana sani suka fara zubo mai yana fadin Safiya ni na cuce
ki da kaina da na tursasa maki auren wanan yaro akan ki.
Kwana biyu baba yayi cikin wani irin yana yi ga ummi na kullun tana faman kuka a
daki gwagon ma haka.
Kwana bakwai da faruwan wanan maganan sai ga yaya saadu ya dira garin da dare mun
dai ji zuwan shi amma bai shigo ba don dare yayi lokacin.
Da safe ya shigo gidan ba wani taron arzikin da ya samu gun mutanen gidan mu sai
a wurina da ummi na da bata gwada mashi komai ba.
Don ni nasan irin taimakon dayai wa rayuwa na a likacin da nake bukatan taimako
ba kowa a kusa dani.
Ya gaisa dasu ya shigo har dakin mu ina kwance na mike da kyat da kwance da nake
ina mashi sannu da zuwa.
Yace dani sannu Safiya ashe kuma haka abin ya kasance ban iya bashi amsa ba sai
hawayen da ke zuba min a idon .
Ummina ma kukan takeyi yana share hawaye yace dani bari kuka Allah na sane dake
safiya kowani mai rai da irin tashi jerabawan.
Allah yasa mu iya cinye jerabawan mu ummi tace dashi amin mun gode da kulawan ka
gare mu yace nazo ne mu kaiki babban asibiti ki karbi magani da ya dace.
In Allah ya yarda zaki samu lafiya in dai kina shan magani Allah da yai cuta shi
keda maganin sa.
Sai ga baba ya shigo dakin namu ya kalle ni yace sannu safiya yaya jikin na amsa
dakyat da da sauki baba.
Daga inda yake tsaye hawaye ya fara zuba mishi yace haka Allah ya nufa dake
zumunci nai wa suka ci amanan ki.
Yaya yace ayi hakkuri baba in Allah yaso zata samu lafiya indai tana shan magani
ai yanzu an samu maganin cutar.
Yanzu baba asibitin birni zamu da ita inda zamu ji mafanin da ya dace a bata tana
amfani da shi.
Ikon Allah kana ganin zata samu lafiya idan ana shan maganin yace kwarai kuwa
don ai mutane da yawa na dashi amma saboda suna amfani da maganin ba a ganewa.
Yace a shirya ta sai in san da suwa zamu tafi mota na nan da nazo dashi dashi
zamu tafi.
Abin mamaki da baba ya fita ya lalubo mama don tafiyan sai cewa tayi gaskiya
bazata samu zuwa ba adaije da wani.
Muna jin ta daga dakin mu ina kuka ummi na kuka tace oh Allah mutum da ranshi ya
koma abin gudu.
Yaya saadu yace babu komai mama insha Allahu zata samu lafiya tace baka san halin
mutanen gidan nan ba.
Tun yanzu sin tsane mu sun tsagwamay ta kyama da tsoron mu suke ji wai zamu saka
masu cuta mu halakasu.
Yace babu komai mama a dai bari ta fara sha maganin a gani suda kansu zasu daina
ai sai dai ta kiyayye rezan da take amfani dashi kada ta bari jinin ta ya fita wani
ya taba.
Da wanan masullan kitson naku na mata idan an kiyayye hakan ba abin da zai faru
da kowa duk fadan mutane ne kawai amma banda haka ana mua mullar komai da mutum
kamar kowa.
Tace kayya yarinya dai ai ta nakasa yanzu ba zancen aure a gare ta ke nan har
abada ko samun zuria a gare ta.
Yace aa mama duk dai wanan a barshi har Allah ya bata lafiya yace mama ki shirya
mu tafi dake kawai ina jin rikicin wanda zai tafi akeyi a waje da baba.
Mama ki rungumi yar ki kar ki yarda ki biyewa mutane ki kyamace ta sai kowa ya ji
dadin kayamatar ta a gidan.
Ummi ta share hawaye tace babu komai ai idan na kyamace ta wa zai duba min ita
ya riga da ya cuce ta yariyar nan ta bisa bakin ta da cewa baida tarbiya .
Amma malam ya rufe ido yaci muna mutunci a gidan nan har yana ikirarin korana a
gidan.
Yazu da haka ya cika da ita wake wahala dani da ita a daki kawai ke wahala ba
wanda ya damu da mu a gidan nan har da wa yanda ke zuga shi kan zancen.
Baba ne ya shigo rai a bace yace duk sun ce bazasu tafi ba sai ummi tace ni zan
kai ta da kaina barin tashi na shirya.
Suka fita shida yaya saadu suka bar mu ummi na shirin tafiya sai ga gwagon ta ta
shigo gidan nan ta samu ummi na shiri take fada mata abin dake faruwa a gidan.
Gwagon tace baki zuwa zauna ki fake yaran ki ni aiki may nake da sai kin je da
kan ki kamar baki da kowa duniya.
Ta juya zuwa gida din ta shirya tai sallama da yan uwan ta bata dauki lokaci ba
ta dawo dama yaya yana waje suna jiran a fito dani.
Ummi na da gwago suka tallaboni zuwa wajen mota duk yan gidan mu sun zubo muna
ido wasu na ce muna sannu wasu kuma sai kallon tsoro suke min.
Mama ne take tambaya dawa zamu tafi gwago tace da ita za ai tafiyan sukai mata
Allah ya bada lafiya.
Aka kamani na shiga mota na zauna da kyat gwago ta shiga suna tsatsaye suna
kallon mu yaya sani yai magana da cewa
A a bada mama za a tafi bane gwago tace ai sun gama nasu ranan wuya sai naka ai
sai kawai yace ina zuwa barin zo dani za a tafi.
Ya shiga gida da sauri sai gashi ya fito da shirin shi uwarshi na kwala mashi
kira yace sai ta dawo zan raka safiya asibiti ne.
Nan tashiga da fada wai sai yaje an halaka shi ya mai she ta baya amma una baiji
ba mota ya daga yaya saadu yaja babana yana gaba mu muna baya muka tafi.
Mun bar ummi da jin bakar magana a gidan mussanman inna da ke ta zage zage dan ta
daya bi.
Har saida ummi ta gaji ta bata amsa tace ai itama ba saye tayi ba kuma ba qurin
yawon banza ta kwaso shi ba.
Yanzu kuce haka amma lokacin da kuke zuga baba a kan auren baku nuna bacin rai ba
sai yanzu da ta baci kowa ya zamau jikin shi ya na nuna mata kyama.
Allah da ya jarebeta dashi bai manta da ita ba yana sane da halin da take ciki
kuma kowan ku bai wuce nan ba ai.
Sai mama tace Rabi bai kamata ki fadi haka ba kuwa yaya zamu kyamace ta ai mun
san ba ita ta dorawa kanta ba.
Sun dai cuce ta kuma sai Allah ya saka mata don Rakiya da danta ba suyi ba
wallahi abaku yarinya da lafiyan ta ku illanta yar mutane ko waiwaye babu.
Yadda sukai wa yarinyan nan sai ubangiji ya saka mata ummi tace ai ba Rakiya
kawai da duk wanda ke da hannu a ciki ubangiji ba zai barshi ba da yarda Allah.
Mama ta shiga damuwa da maganan ummi ummi ta shiga daki tana kuka tabi ta tana
bata hakkuri ummi tace wallahi ba zan taba yafe wa ba yaya.
Kiyi hakkuri Rabi komai da kika gani ya faru da bawa Allah na sane dashi ummi
tace amna yaya ya dace yadda kuke kyamatar yarinyar nan abin har mu ya shafa.
Wanan maganan na ummi shi ya kawo laushi ga mama har ta tsawaci yayan ta a daki
kan su daina guduna haka bai da kyau su kyale inna dama haka take son gani fa kowa
a gida burin tane taga an koma baya.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,


2️⃣
7️⃣


YAR UWA NOVEL DIN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU
PLEASE, , , , , , , , , ,


Yaya Saadu yana tuki yana min sannu yana jin wani tukuki a zuciyar shi gamay dani,
yana ji kamar ya rabani da wanan ciwon gaba daya a jikina.
Tausayi nake bashi jina yake tankar yar uwar shi da suka fito ciki daya ba komai
ya yasa yake ji dani ba sai irin girmama shi da nakeyi.
Wanda ko wayanda suka fito ciki daya basuyi mai yadda nake mai ya lumshe idon
shi tare da nisawa.
Yace a ranshi Safiya nai maki alkawari zan dinga kula dake muddin ina raye insha
Allahu zan baki kulawa daya dace.
Baba ne ke magana dashi amma baiji shi ba sai da baba ya sake maimaita maganan
shi yaji shi.
Saadu kayi hakkuri kasa imani da addua a a ranka nima abinda nayi nayi nadamar
shi ban wa yarinyar nan adalci ba.
Wallahi ban san abinda dan uwanka da mahaifiyar ku kuntatawan da suke wa yarinyar
nan yakai yakai haka ba.
Ya nisa yace baba abinda ya faru ba wanda ya isa ya goge shi sai dai tabbas tun
farko anyi kuskuren aura mata shi don sanin ko waye Ahmed din sam bai dace da
kamilar yarinya irin Safiya ba don sani ko shi waye da akayi.
Yace yanzun haka karuwan da ya saki Safiya a kan ta ta gudu ta barshi bayan ta
gama yashe shi kaf bata barshi da komai ba.
Shima yanzun haka din ya fara jinya don ciwon nasa ya fi na Safiyan nisa sai
yanzu ne wai mummy take data sani dashi.
Bayan a lokacin da yake miyagun halayensa ta kasa tankwara shi ta dauki son
duniya ta dora a kan shi.
Itama karuwan naji ance takai kwance a inda take tana bukatan taimako.
Ina zaune a bayan mota ina jin su na lumshe idona don bakin ciki sun cuce ni sun
illanta min rayuwa na.
Mun isa garin muka nufi asibitin direct nan ya bar mu cikin mota suka fita dashi
da yaya sani zuwa ganin likita.
Gwago ta ga mai ruwa ta kirashi ta saye muna tabani nasha baba na kallon yadda
nake shan ruwan da kyat yana min sannu Safiya.
Gwago ne tace Allah ya isar maki yar nan ya saka maki da gagawa sim cuce ki sun
illanta rayuwanki ga banza.
Baba yana jin ta hawaye yake na nadama yana gogewa yace gwago banyi wanan hadin
da wata manufa ba a rayuwa na.
Sai don zumunci ya kara karfi a ysakanin mu iyayyen mu duk abu guda suke ta uwa
ta uba shine da tazo da wanan zancen naga dacewan shi nayi.
Yaya Saadune suka dawo dauke da keken da ake sa maralafiya yace a kamani asa
sama yaya sani ya ciciboni ina wai ya dora a keken.
Wani daki ne muka nufa ashe likita ke ciki ya dan yi min tambayoyi su yaya da
baba ke amsa mai yai rubutu ya bayar yace zasu dan kwantar dani inda masu irin case
dina suke in sha magani na kwana biyu a gani.
Aduniya ban san irin godiyan da zan ma bawan Allah nan ba sai dai ince Allah ya
biya shi da alherin sa.
Nan take ya sayo magani da ruwan da za a kara min da abubuwan gina jiki kuma yace
ba zai tafi ba sai yaga yadda jikin nawa ya kasance.
Baba kuka yake yana mashi godiya yace baba komai nai wa Safiya kaina nai wa don
yar uwata ce ta jini.
Na samu kulawan da ya dace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login