Showing 219001 words to 222000 words out of 258256 words
Chapter 74 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
ya shigo a lokacin.
Sai lokacin na lura tun shigowan mu ban ga inna ba a gidan ina tambaya kafin mama
ta bani amsa yaran dake wurin su ke fadin tana daki bata da lafiya.
Subbahanallah nace tare da kara tambayan su bata da lafiya may yasamay ta ?
Ina fita daga dakin dake cike da yan uwana da abokan arziki da suka shigo taro na
da zuwa jin murya na inna tayi dan tambayan yanta sai gata ta fito waje tana
yamusan fuskan ta alaman akwai yani guri dake matsa .
Gaishe ta nayi tare da tambayan yaya gida tana tambayan uncle nace tare muka
shigo dashi gaya can dakin ummi.
Yaran dake cikin dakin khadija ta koro zuwa waje nan dai suka samu gaisawa da su
ummi da mama sai gwago dake ciki zaune dasu.
Sun yi wa ummi yaya hanya Allah yasa makasudiya ce ummi ta amsa da amin tana
dada godiya yana fadin bako mai ai mama.
Muryan baba ne ya shigo gidan da farin ciki dakin dan ganin su sannu da zuwa yake
ta faman yi masu suna amsawa cikin alkunyan daga inda yake yake tambayan ina yaron
yake jin muryan baban mu da nayi yadawo gida yasa na juyo na bar wurin inna din da
nake tsaye.
Yana tambayana na amsa mashi daga inda nake tafe a bayan shi da fadin baba mun
samay ku lafiya na durkusa har kasa ina gaida shi.
Yace tashi tashi yar albarka ashe yau kuna yafe garin namu ne sai da safe Rabi ke
fadin kin ce yau zaku zo.
Murmushi nayi kai na kasa nake fadin baba an dawo lafiya Allah ya karba ibadun
da akayi yace amin amin yana karban yaron da shafiu ya fito dashi wurin abokan su
yaya sani a waje.
Yace ikon Allah yaron ke nan yayi wayau haka tubarkallah masha Allahu abu ko yayi
kyau wallahi sosai yake fadi ni dai murmushi nayi daga inda nake tsugunne ina gaida
baba ya juya zuwa sashen shi dauke da yaron a hannun shi.
Dakin na koma inda na samu ummi tasa khadija ta baza masu uncle da yaya kayan
abinci suna ci a falon nata sai kuma wanda ta bayar akaiwa driver da muka zo dasu
waje.
Dakin na shigo yaya saadu ke fadin Safiya ki debi abincin ki ci mana ga gwago nan
tana cika cikin ta itama nace ai zanci ba yanzu ba yaya .
Sun gama sun tashi zuwa dakin baba don su gaisa nan yaya Saadu ya barshi dakin
tare damu inda yace ummi ina ganin na fita ke nan don zamu kama hanya da wuri muke
son barin garin nan.
Daga inda nake zaune a gefen shi ya juyo yana kallo na tare da fadin ina ganin
sati biyu ko uku zanyi acan so zaki yi kwana goma zan turo Saadu ya zo ya dauke ku
kafin in dawo daga Egypt din .
Wani dadi naji har cikin raina kamar na sani kwana hudun da yace zanyi kawai na
dai dauko kaya daya fi na kwana hudu kamar mai shirin yin wata daya.
Ya kirgo kudi ya ba ummi masu yawa ya kara kirgowa ya ba gwago tare da khadija
sai kuma su shafiu dake dakin suma ya basu already ya bani tun kafin mu zo.
Nan ya fita sun dan jima da baba ya fito bayan yayi mashi alheri yaba su mama
nasu tare da sauran yaran gida bamu samu yaya sani a gida ba ko da muka zo.
Mun fita rakasu ne na hango shi can ya tsallaka wurin datawan unguwan mu da
matasa yana masu alheri abinda ya sauka a gare shi.
Sai dai na lura bada motar zasu tafi ba saboda ganin sun shiga hilux din da
takawo muna kaya da zamu zo haka yasa na gane bada ita zamu koma ba sai wanan
mutumin kamar security yake a gare mu ashe ma a nan zuwa dashi ke nan da mukayi
Ya dawo na dan dade gaban mota muna magana dashi mutane sun kura muna ido a
zaton su wani hiran dadi mukeyi a lokaci.
Amma a zahiri warning dina yake yi da baison yawo ya barni gida ne in dan jima
don ganin yadda yan gidan namu suke kewan gani na.
Wanan abin yake fada min wanda bai sani ba sai yayi zaton wani hira mai dadi
mukeyi a lokacin kasancewar duk fuskokin mu yana dauke da murmushi ne a lokacin.
Nan mukayi sallama suka ja mota suka tafi yau gida yayi bakin abuja cike dakin
ummi yake da yaran gidan mu suna min hira shafiu ko yana makale da Abba bai bari
kowa ya dauke shi cikin yaran.
Sai da suka rage a dakin ya rage sai mu da yan dakin kade a lokacin nake cewa
ummi wai may ke damuwan inna ne haka ta zube a lokaci daya ?
Shafiu yayi saurin cewa injin bakije dakin ta ba anty da sauri na kalle shi nace
may ye a dakin nata da ba a shiga ?
Yace ance ciwon tari ke damun ta don haka baba yayi muna kashe a kanta da kuma
taba kayan da tayi amfani dashi don gudun daukar cutar gare mu.
Wani irin ras gaba na yaba da a lokaci daya nace ummi da gaskiya abinda ke damun
inna ke nan shine ba afada min ba ko a waya.
Hankali na ne bai kai da in fada maki ba ai hakan bai hanata rashin mutuncin da
ta saba yi ba a gidan shiyasa malam ya kafa doka akanta har yaranta.
Nan dai suke muna hira yadda abin yake mata da dalilin daya baba har ya kafa mata
doka mai tsanani a gidan kamar yadda likita yace a kiyayye don gudun daukan cutar.
Gwago ce da zata gida muka fito sai lokacin na ke magana da baba don aba driver
da wanan mutumin da ya bar min zamu zauna dasu don kaini wurare inda zasu zauna.
Baba yace a gyara masu dakin yaya Sani don dama shi driver ya saba zuwa tun
kafin muyi aure da uncle ya zama dan gida yanzu.
Nasa shafiu ya gyara dakin tare da kai masu abubuwan bukata a dakin don bukatun
yau da kullun.
Da yamma yaya Sani ya dawo garin nan ya samu mun zo da murnan shi ya shigo dakin
ummi yana taron mu ya samay ni zaune Abba na kuka ina lalashin shi .
Yace ummi ashe yau baki ne haka a gidan namu khadija ce ta leko daga kuryan daki
tace yaya sani oyoyo yace ho yar birni an dawo tana fitowa yace kai kai kai.
Ummi ki ko ga yadda yarki ta koma wata big girl haka wai ma tsaya naga alaman fa
kin cinye masu kayan abincin gidan su fa khadija.
Nace wane ita tadai ci iya cin ta ta dawo ta bar muna saura yaya ka dawo lafiya
mun zo bamu samay ka gashi har da mutumin ka muka zo yau din.
Yace haka naji tun a waje nazo na iske su Adam nata washe baki yau a jike suke
dumus suke labarta min sai kuma naga musa drivern ku a waje.
Nace nan ya barsu wai zasu kula damu a nan kasan mutumin naka bashi da yarda don
wai kada in ta yawo mutane suna gani na.
Dariya sukayi har ummi tace ai shine maganin matan yanzu da basu mai da fita a
bakin komai ba sai kiga mace ko bada sanin mijin taba ta saba gyale akai ta fita.
Yaya Sani ne yace ummi ai har mata kauye yanzu sun koyi wanan dabian kwana ki
nan rikice ya barke tsakanin isah da matar shi wai taje buki bata fada mai ba sai
dawowa tayi gida ya samu ta
Ummi tace kaga abinda ke sauri halaka mace a yanzu don ace da mijin ka ya dawo
gida daga tafiya ya samu mace bata gida.
Gara ya dawo ya samu gawan ta a gidan yafi sauki amma kin ga matan yanzu basu
damu da wanan abubuwan ba sam.
Khadija dake shiri fita waje tace cabdi yanzu kan ai sai Allah ya gyara kawai
dama akwai irin su anty masu tsoron miji kin ga yadda take tsoron mijin ta kuwa
ummi .
Ummi tayi saurin katse ta da cewa masha Allahu ai gara da naji wanan shedan da
kikayi wa yar uwar ki din don yanzu na gamsu da irin tarbiyan da na dora ku a kai.
Kallon ummi tayi kawai ta girgiza kai irin watau ummi din bata san komai ba ke
nan yaro yayi sallama yashigo da abinci yana fadin inji Saadatu tace ya kawo wa
baki.
Karban abincin nayi ina ma yaron godiya na ce shafiu ya bashi dari biyu a cikin
jakkana dake kusa dashi.
Yaron yana godiya ya fita nace ya gaida ita ummi tace Allah sarki wace ke fama da
kanta kuma har da kokarin kawo abinci haka.
Yaya Sani yace ummi ai shine zumuncin ko yayane kaima dan uwanka shima yasan ka
damu shi ba kullun sai dai aita baka ba kana karbewa.
Hakane inji ummi tace naga tana cikin yanayi ne kawai mijin nan nasu yana ta kan
shi yanzu ba wani sana a mai karfi yake yi ba.
Bude abincin nayi inda naga tuwon masara da miyar busassan kubewa da kifi
bussashe ba wasu manya ba miyan yana kamshin dadawa da kayan yaji.
Zama nayi muna hira da yaya naci abincin sosai don na dade banci irin shi ba sai
mamaki suke yadda nake kai loman tuwon a bakina ina yaba dadin da tuwon yayi.
Yaya sani ya fita ina shan miyar ummi tace da alama miyan yayi maki dadi sosai ko
?
Nace wallahi ummi naji dadin miyar sosai don na dade ban ci miyar kubewa busassa
ba tun bari na gida fa ummi.
Sai bayan da na wanke hannu na dawo na zauna nake tambayan ummi may ye matsalan
mijin saadatu ne wai ?
Tace masu bashi kayan ne da farko suka daina yanzu wai don ya auri Saadatu din
ashe dama wani dan uwan matar shi ne yake bashi kayan yana sayarwa.
Kai na girgiza kawai ba tare da na furta komai ba sai dai cikin zuciyana ina
tunanen may ya kamata nayi akan maganan ne ?
Ranan mun kai wani lokaci muna hira da ummi na inda take goye da Abba a bayanta
acewar ta wai zai dade yana barci idan ya kwanta ga ruwan zafi daya sha a jikin shi
ya gasu sosai a wurin mama da tayi mashi wanka.
Khadija kan tun da ta shigo ta kwanta tana sauke gajiya a gida wanda ta dade
tana kewan gida a ranta don zamanta na abuja a matse take ba fita ko ina.
Washe gari ban tashi da wuri ba don dadewan da mukayi da ummina muna hiran yaushe
rabo tare da ita daren jiya din.
Shogowan dan gidan da Ainau ke aure yar wurin anty da kwanon kosai da koko na
daka wanda yasha kayan kamshi yana tashi a cikin shi yace wai ance ya kawo wa
bakuwa da tazo daga Abuja.
Fitowa nayi don in ba yaron wani abu don naji ummi na sallaman shi tana fadin
kace mata an gode kaji na fito ciki ina fadin ga wanan a bashi kace ina gaida ita
na gode kwarai.
Wanan abin da yan uwana suka yi min naji dadin shi sosai a raina hakan na nuna
yaran gidan mu akwai hadin kai sosai wurin son junan mu.
Ban fito ba sai da nayi wanka na shirya cikin wani dogon riga mai taushi na fita
zuwa gaida mutanen gidan mu.
Dakin mama na fara zuwa tana ciki sun baje da yaranta suna karyawa na shigo
dakin da sallamana a dakin na samu Abba a bayan mama tana goye dashi yana barci.
Na dan dade dakin muna hira dasu sai na tashi zuwa dakin inna inda na samay ta
zaune a falon dakin ta tana zaune ita kadai yaran dakin ta duka suna kofan ummi na
suna karyawa a lokacin.
Na shigo da sallama na nace inna ashe baki ji dadi bane haka ta gyara rufin zanin
da ta rufa a jikin ta tace wallahi ke dai safiya.
Ciwo wasa wasa gashi sai gaba yake min nace inna kuna na asibiti kuwa tace tau
safiya waye zaiyi jimirin kaini asibiti ko wani lokaci.
Tausayi tabani sosai nace to inna sai a zauna da ciwo haka a gida ai gara dai a
tafi asibiti a gani zaifi hawayen da yazo matane ta shere a fuskanta
Tace safiya yan uwan ki kowa gudu na yake yi a gidan nan har malam din kanshi
guduna yakeyi yanzu wakike gani zai kulani a hakan bayan duk suna tsoron zuwa kusa
dani don cutar da nake dauke dashi.
Koma asibitin nace zan tafi ba wasu kudi issasu a hannuna da zasu kaini ance
maganin tsada gare shi wai.
Ba komai inna bari yaya sani ya shigo sai muji yadda za a yi amma ai ba a zauna
haka da ciwo a gida ba kullun yana kara maki illa a jiki haka ?
Abin mamaki sai ga inna tana cewa da bakin ta ubangiji Allah yai maki albarka
safiya na gode kwarai wallahi Allah ya kara arziki , .
Mikewa nayi nace bakomai ina har na kai kofa nace ki ko karya tayi murmushi
kawai tare da fadin abinda akace inci ne ba samun shi nakeyi ba akai akai.
Fita nayi daga dakin inda ban koma dakin mu ba baba bai gida ya tafi zanen suna
tun da safe ya fita gidan don haka na leka waje na kira yaya sani yana zuwa nace
mashi.
Haba yaya sani kasa halin da inna take ciki shine kuma ka kyale ta haka a daki
ko karyawa batayi har yanzu ace mara lafiya bai karya ba har wanan lokacin.
Humm yace safiya jiya da mijin ki yazo ai ya basu kudi ina takai nata nace babu
ruwan ka yaya ladan haihuwa zaka nema a wurin ta ai.
Ba zakayi fatan kaga ka rama mata abinda tayi maka ba kana yaro yanzu har zaka
tsaya yaya duban wai tana da kudi tayi amfani dasu .
Ka sani ko tana da abinda zatayi da kudin data samu jiya don Allah yaya ku daina
wanan hali kune fa manya a gidan nan da zamuyi koyi da halin ku na gari.
Yace wani yanzu ai mun baki girman safiya kece antyn mu kaf a gidan nan mun biki
mun bi Allah don shi ya baki girman dariya ya bani har yasa na kasa karasa maganan
da nake mashi don banbadancin da yake zuba min a lokacin.
Nace ni dai yanzu muje in baka kudi ka sayo mata abinda ya dace zan maka list din
komai ta fara karyawa kafin mu je asibiti da ita.
Yace amfa je asibitin ita ce taki yarda ai mata alluran wata uku da sukace zasu
yi mata wai karya da kazafi ake mata akan ciwon.
Nace inma da tace karya ne yanzu batace ba don munyi maganan da ita daga dakin ta
nake yanzu ma yace tunda ke ce ai yanzu ta yarda.
Mun je dakin na kirga kudi na bashi anan muka aje magana zai dauko wanda zai mata
alluran da aka rubuta mata tayi din da magani sai yazo zamuji ko nawa za a kashe
sai a fara mata alluran ranan.
Kunun da Ainau ta kawo min na zauna nasha ina wurin zaune na dauko waya na kira
uncle yace ya kirani bai samay ni ba gashi zasu tafi airport yanzu Allah ya tsare
nayi mashi muka kashe wayan bayan ya tambayi Abba dasu khadija nace suna lafiya.
Tsaraban kayan abincin da nazo dashi na fara raba sai kuma na shiga rabawa yan
gidan mu tsaraban da nazo ma kowa a gidan mata sun samu turamay zannuwa da sabulai
da man shafa ida maza shadda na raba masu da turare da takalmomi matan sun fi maza
samun tsaraba sosai dana kawo masu.
Yaya sani ne ya shigo da malamin asibiti muka shiga dakin inna dashi inda yayi
bayanin a gaban ta da abubuwan da zata daina ci da wanda zataci har tsawon wata uku
.
A gabanta na biya kudin komai da za a yi mata kukan da ta fara ne yasa na bar
daki na koma dakin ummi jiki a sanyayye ida yan gidan mu kaf suke dakin na ummi
khadija tana masu hiran abuja da bauchi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/12/20, 7:42 AM - Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,
7️⃣8️⃣7️⃣
🧕8️⃣7️⃣8️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Muna tsaye kofan inna muna kallon yadda likitan yake mata allura zabban tausayi har
ya gaba ya fito yana cire safan hannu da takunkumin da ya rufe hancin shi dashi
inda ya jefa a wani leda zai fita dashi.
Nan yake fadi a gaban kowa yace a kikyayi zama kusa da ita a daina amfani da duk
wani abin amfanin ta don ciwo ne mai saukin dauka ga mutum idan da hali a raba
makwanci da ita.
Kuka inna ta saka mai ban tausayi tana fadin ni rakiya yau naga ta kaina na zama
abin gudu har ga diyan da na haifa a duniya.
Daga kofa inda nake nake fadin cikin murya mai rauni inna kiyi hakkuri ciwo ba
mutuwa bane zaki samu lafiya in Allah ya yarda adai kiyaye abin daya fada kawai.
Yaya sani yace yau bagaki ba safiya may ye ba ayiba a lokacin ciwo ki a gidan
nan wanda ba kowa ya sa ai maki ba sai ke inna ina fada maki ki bari amma kamar
zugaki nakeyi a gidan nan.
Har kika fara gaba dani ummi gata da ranta ita tayi min fada akan in bi maganan
ki in bar