Showing 3001 words to 6000 words out of 258256 words
Chapter 2 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
aureta.
Sai inna ta daya aura daga baya a wani kauye tazo gun yan uwan ta ya ganta ya
shiga nema da yake Allah yayi dashi rabon zuria a tsakani kuma.
Don saida yan suka suka dinga suka amma ummi tace sai shi take so tun wannan
lokacin da aka kawo ummi gidan matan gidan suka dauki tsana da tsangwana suka saka
mata tun abin na dan dadi har takai zama ya koma zaman hakkuri kamar yadda matan
hausawa da yawa suke zaman yi a gidajen su.
Idan ka dan yunkura daukan mataki sai ace kayi hakkuri don iyali sin taru suma
matan abinda suke duba ke nan wani lokaci akan idan sun bar diyan su may yai
makomar su kuma gidan gun matan dake gidan.
Suma kan su kishiyoyin ummi din ba barin junar su sukayi ba don zakaji fada ya
gaure a tsakanin ko kan diya ko kuma kayan abinci idan wata zata karbi girki a
cikin su.
Wanan halin da wuya ai kwana biyu cikakke basu samu baraka ba irin hakan wanda
sai mutane sun shigo rabo daga waje.
Haka yasa gidan namu ya kara suna gun mutanen uguwar mu gashi yaran gidan ba
tarbiya ko kadan komai girman mutum zasu iya ci masa mutunci don samun daurin gindi
a gun uwayen su da sukayi.
Ba yabon kai ba don ina dakin ummi a gaskiya ko kwatance za a yi da dakin mu ake
kwatancen masu daman gidan na mu a unguwa.
Da wanan rayuwan muke zama a unguwar mu hakana yau da dadi gobe ba dadi don dai
an fimu karfi ta ko ina a gidan dole sai zama na hakkuri kawai a tsakani tunda
Allah ya riga ya hada zaman mu a cikin su.
Bawai iya mu ba har wani wanda ya rabe mu haka nan suke hassada dashi da bakin
ciki .
Yadda duk ake son tarbiya muna samun shi a gun uwar mu don duk da matsin
kishiyoyin da take ciki batai sake dabawa diyan ta tarbiya ba wanan fannin sai dai
kawai talaucin da rayuwa na kakanakayi da muke a gidan.
Allah ya taimake ni duk diyan dakin namu muna da dan kokarin mu a fannin karatun
mu ba wanda baida kokari a cikin mu.
Wanan ne daman da muka samu zance na rayuwa don da wuya ai hutu wani cikin mu bai
dan samu kyauta ba nabajin ta muna dan samun abin dan more rayuwa a hankali.
Ga irin dan kyaututukan da muke ciyowa a wurin musabika da kuma quzee din mukeyi
a makarantar boko.
Maimakon a taya mu murna a gida sai tarin takaici ko a ce an dai bamu ne kawai
don bakin iya yin mu.
A haka zamu wuni ranan cikin bacin rai a gidan saboda hattara da tsangwaman da
zamu shiga gun mutanen gidan mu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM - Ummi Tandama: BAHAGON, , , , , , ,
2 🧕🏿
2
2⃣2
FREE PAGE
SEENABU MAKAWA
MAISON WANNAN NOVEL ZATA IYA KIRANA DA WANNAN LAYIN DON YIN REGISTER 300 TA BANK KO
RECHARGE CARD NA 400
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENITH BANK 2253380105 SAINAJI KU MASOYA AI HAKKURI DA MU
WRITERS YANAYI NE YA KAWO HAKAN DA FATAN ZAKU FAHINCE MU, , , , ,
Sauri nake ina shirin tafiya makaranta kasancewa yau monday don nasan akwai dogon
assembly da wasu bayanai a irin wanan ranan.
Socks na jawo na fara sakawa a kafana daya yayin da na ji an fara kwala min kira
a tsakar gida.
Haushi da takaici ne ya rufe ni a lokaci daya don nasan wani sabon fitina ina
zata dora min duk wanan saurin da nakeyi zai tashi a zero ke nan bazan samu assemby
din da nakewa kwadayin samu ba kuma wata kila aike ne ko wani aikin zanyi.
Na aje socks din ban saka ba don karba kiran inna din samun ta nayi tana kokarin
dama kunun koko take cewa dani na kwaso kayan zuba kunun ko wani daki na kawo mata.
Na juya rai bace naje karbo kayan na kawo ina kokarin ajewa ne takai idon ta akan
roban dakin mu sai kawai naga tai cilli dashi a gefe daya.
Ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah ta fara zubawa sai data gama zubawa kowa
ta jawo roban ta dan yafuta ta dan zuba muna rabin abinda take awo dashi ta
dangwara mun sai na dauka na nufi daki ina juyawa a hankali ina kallon kunun da rai
bakwai zasu sha su rayu a gidan.
Ina kokarin rufe roban ne naji ummina tana cewa babu kunun ne ko don naga kin
dawo da roban hakana ba komai a cikin sa.
A sanyaye na ce akwai ima anzuba muna ta mike ta jawo roban tana kdllon kunnun
dake a cikin sa sai naga ta dauki roban zata fita.
Da sauri na tare ta nace ummi kiyi hakkuri kusha hakana may duniya don Allah bata
saurare ni ba ranta ya baci tafita.
Ba wai wanan ne karo na farko da Inna ke muna haka ba a gidan koda yaushe in dai
ita zata raba abinci to na dakin mu kan kankare ne kuma ko mutum biyu baya isa a
dakin namu.
Ina ga yau ta gaji ne gashi kuma mun kwana babu ko kwandala a dakin balle ta dan
sai garin kwaki ko kanzo tabawa yara dan abin dake gare mu munyi kitso da wanki
dashi a cikin sati.
Muryan Ummi naji tana fadin haba yaya wanan koko aiko su shaibu ba zai isa ba
balle sauran yaran har akai ni.
Sai naji Inna tace da ita au da kika fito kikai min tsaye a kai zikau dake tsoron
ki zanji na kara maku babu ko may ?
Ummi tace kawowa nayi ki duba ki gani ga sauran roban nagani duk a cike amma
ki duba abinda kika zuba muna don Allsh dai.
Tabe baki tayi tare da fadin yanzu aike akeji kunu ne shi naga daman zubawa idan
kin isa ki diba ki kara maku tunda keda diyan ki kune yan gwal a gidan ku kadai
akaiwa bakin cin abinci cikin mu.
Ummi tace ba sai na diba ba ai idan bazaki kara ba abarshi don ban san wa zanbawa
ba wazan hanawa ba, cikin yaran.
Eyye lalai ma Rabi wuyan ki ya isa yan ka wallahi to bara kiji ke din nan dai da
nake gani baki kai min can ba kunu ne ba zan kara ba sai kiyi abinda zakiyi dama
naga tun da na zuba munafukar yar ki take bin kunnun da kallo tana min wani tsiwa a
kai.
Nifa din nan kujera ce daidai da zaman kowa idan wani abu kike ji da safe nan
daidai nake dake yanzin nan don ban daukan raini da wullakancin kowa.
Don idan mutum yai min tsiya yanzun nan na nada mai dukan tsiya inbuge shi in
bugi banza naga wanda zai rama mai kuma.
Ummi dai bata tanka taba ta duka tana kokarin juye kunun a roba da sauri inna ta
tare tana fadin kada ki lalata muna kunu da wanan kazamin roban naku daya dafe don
tsufa.
Muryan babana naji ya fito daga dakin inna yana fadin wai may nene ya akayi ne
kuma da farar safiyan nan haka ?
Wani irin harara ta watso mashi tace wanan yar kauyen matar taka ke son shiga mun
hanci da kudundune da safen nan akan kunun dana dama na basu.
Niko idan ta kawo rainin da sukewa mutane kaina yanzu zata sha na jaki wanan
iskancin ta tsaya iya kai tai maka shi can bani ba.
Baba yace muga kunun sai ummi ta nuna mai ya kada kai yace haba Rakiya yanzu
wanan dan kunun ace rai bakwai zasu sha shi ai babu gaskiya ga wannan zance yakai
ido ga sauran robobin da aka cika yake cewa wanan nasu waye haka shi ?
Tace ko zaka shigar mata ne naga daga jin muna zancen mu na mata kayi wuf kafito
kana kokarin saka bakin ka ciki.
Fitowan ka ba zai hana ni yin abinda nai niyar yi ba akai don ba wani yai
wahalan dama min ba.
Ita har waye da zata fito tace min wai banyi daidai ba ko iskancin nasu ne zai
kawo gare ni yau kuma ?
Ummi ta wufta da kunun a roban dake gaban inna ta juye tace ga kunun ki nan ki
barshi Allah da ya halice mu ba zai barmu da yunwa ba yana sama yana ganin mu.
Tace da baba kagani ko kaga irin cin kashin da tai min dai a gaban ka ko ita
wacece da zanyi wahala dama kunu ta fito tai min wullakanci dashi.
Ummi ta juya bata ce da ita tak ba ta nufi dakin ta inna ke fadin samun wuri
banza diyan masiyata yar kauye wanda bata da tarbiya ta uwa ta uba.
Ummi ta ce a, a yaya maganan nan iya ni dake ne baikai na iyayye ba fa don haka
ki daina zaga min iyayyena da basu ji basu gani ba da safen nan.
Don ni iyayena ba mutanen banza bane ko da suke kauye ba wanda ya taba ganin su
suna roko a wurin wani.
Dama mahaifin inna maroki ne ya tsufa amma har yanzu yana roko a cikin gari kowa
yasan shi sai inna ta fusata da maganan ummi din.
Tai wuf ta kamo hijjabin dake wuyan ummi ta shake ta har idanuwan ta suka firfito
waje tana fadin rokon sata ne ko maita da zaki min gori dashi.
Bata bata amsa ba ta sake sabon shake ta daga inda baba yake yana karasowa yana
fadin sake ta mana Rakiya kasheta zakiyi ne ko may ?
Kafin ya karaso ta kaita kasa ta danne tana duka tana fadin gobe ki kara zagin
ubana don yana roko roko ai ba sata bane duniya.
Jin sun kicimay yasani fitowa da sauri ga ummi a kasa inna ta haye tana duka
mahaifin mu na kokarin banbareta daga saman ta.
Ihu na saka da karfi har yasa mutanen gidan gaba daya fitowa dama wanda bai tashi
daga barci ba ya falka.
Ya banbareta saman ta shi da mama tana huci tana fafin gobe kice zaki kara zagina
yar iska don an kyale ki har zaki kaiga zagin iyayye na.
Haka kawai don samun wuri yar kauyen banza a kauyen may kuke sha banda ruwan
kasari da gwabe da safe.
Mama tace don dama sunyi hayaniya da yamman jiya a, a Rakiya baki da gsskiya ni
kaina na san baki basu abinci yadda ya dace ba yau ba.
Ta juya kan mama tana fadin bani bayarwa kedin daban ne wurin basu wake kwashe
abincin bakeda yara ki ba ku goma a daki daya katan banza kin tarasu ba moriya.
Daga can Nura dan mama daya taso daga barci ihu na ya tayar dasu yace kada kice
zaki zagi maman mu yanzu rayuka su baci wallahi.
Su dai da kika raina don basu kawo karfi ba ki tsaya a kansu amma mu kan idan
kokai wa maman mu yanzu zaki ji mu don kin dai san mun fiku karfi da yawa kuma.
Da sauri na karasa na daga ummi ina gurza kuka ina mata sannu ummi a cikin kuka
itama din kukan take sharba a lokacin.
Tsawa baba ya daka min wai na raba su da ihu kada na tara mashi mutane a gida a
dauka ko anyi mutuwa ne a gidan tun da safe haka.
Yaya Sani dan wurin Inna din ne mai dan dama a gidan mu yace a, a baba ai dole
ne Safiya ta kuka irin wanan wullakancin haka a daki uwarta a gaban ta don basu da
karfi kuma a hanata kuka ai cin zalun yayi yawa mana.
Ya juya gare ni yana fadin ke ba makaranta zaki ba maza kije ki shirya ki tafi
kada ku makara bar su da Allah kowa ya zalunci wani Allah na gani ai don ba anan
duniya zata tabbata ba ai.
Na dago kai nabi babana da kallo na sake kallon yaya sani din na juya nabi bayan
ummi muka shiga daki.
Sai naji Inna na fadin kaikan sani anyi hasara wallahi yanzu akan kishiya da yan
uba kake fafin wanan maganan haka to tunda kaji haushi sai kazo ka rama masu nasan
ka isa wawa kawai wanda bai san ciwon kan shi ba.
Banji may ce da ita don rashin kunya a gidan mu ba sai na tsaya fadi ba ba abin
kunya bane da yaci wa uwar shi mutunci a bainan jama, a.
Ina kokarin daukan dan tsunman jakan makaran ta ina goge hawaye ummi ke fadin
kuyi hakkuri yar nan mu kuma namu rayun a haka yazo muna gidan nan Bahagon rayuwan
Allah ya nufe mu da gani cikin su.
Yaya sani ne ya dago labulen dakin yana fadin ke Safiya miko min roban kunun naku
naku nan ya dauke da katon roban da inna ta dama kunu a cikin sa gaba daya.
Uwar na daga wurin madafa tana fadin wai ko dan nan ka ka daya kuwa ko an hada
dakaine an mallake min ban sani ba wai ?
Jikina na rawa na dauko roban dake gefe na mika mai ya raba kunun biyu ya juye
muna a roban mu yana fadin maza ku sha ku tafi kada ku makara.
Da sauri na dauka na ciki na fara zubawa yan kanne na don ina gudun inna ta
shigo ta hana mu sha kuma.
Har muka gama inna bata bar zagin Sani ba zagi irin wanda ba a son uwa taiwa
diyan ta shi take faman zuba mashi.
********* ********* *********
Ko da muka shiga school ranan mun makara sosai nasha bulala na na wuce aji raina
a bace ba don bugu ba sai dai abinda na bari a gidan mu na cin kashin da akewa
mahaifiyan mu.
Don ni a iya sani na banga wani hslin rashi biyayyan da take nuna masu ba a gidan
don ko aiki yai masu yawa watarana sai ta taya su idan kuma diyan su ko sune basu
da lafiya zakace wani nata ne ba lafiya ta shiga sintiri gaida mashi ke nan a cikin
su.
Ita ranan da duk wani yaron ta zai kwanta ciwo babu mai lekashi har ya ji sauki
ya mike ba su gaida mutum.
Don Allah maijin kan bawan sa ne da wuya dan dakin mu ya kwanta ciwo a gidan mu
sai can ba a rasa ba zakaji wani cikin mu ba lafiya.
Zan dai iya cewa ummin mu mace da bata da kyashi ko hassada kuma mu kan mu ta
koya muna wanan akidar nata na matukar hakkuri tare da sanin ya kamata .
Ba don halin nan nata ba na irin rayuwan da kishiyoyi da miji suke mata a gidan
na wullakanci amma daidai da rana daya bata mayar da martani irin wanda bai dace ba
a kan su.
Ni na rasa may ke jawo wanan kiyayyan haka akan mu da uwar mu sai yanzu da wayo
ya fara zo min ne na fahinci ba komai bane illa zalar kishi irin na macen bahaushe
kawai.
Don ummin mu yarinya ce a cikin su kuma har yawan haihuwar da tayi bai sa kyaun
ta da dirin ta ya gushe ba gare ta wanda su sauran sai dai kawai zaman rayuwa.
Zan iya cewa a gun mahaifiyan mu yan dakin mu maka kwaso dirin mu mazan mu da
matan mu ba laifi uban mu ma dogo ne sai dai shi baki ne amma baya ga tsayin nashi
komai na mahaifiyar mu muke debowa.
Daga hasken fata tsayin don itama tana dashi zuwa suma hanci da idanuwa manya
masu fari kal dasu.
Don idan zagi ya tashi dashi matan gidan mu ke zagin mu ko yaushe sai suce damu
shegu masu zubin uwar su.
Sai kaji guda ta karbe da cewa ba dole ba tunda tafi miji jaraba dama ai ance
wanda yafi jaraba a wurin saduwa shi da ke biyowa a duniya.
Tun ban san kallaman ba har na fara fahintar ma anan shi idan sun fadi na turo
baki ina maijin haushin kalamin su gare mu.
Ranan dai sunan naje makaran ta ne amma babu wani abinda na iya tsinanawa a
karatuna na dawo gida da bacin rai na samu ummi ta dan gyagiji tana aiyukan ta a
tsakar gida.
Uniform din kannena kwaso duk da tsofi ne amma bana taba barin su da dauda
kullun na dawo sai na wanke muna su na sha idan sun bushe na buge nakai daki kafin
mu wuce islamiya.
Do ba halin na barsu nazo na iske an masu ba daidai ba ko tukunya za a sauke
dasu ake saukewa idan an tashi aiki in suna shanye a waje.
Mun gama shirin mu muka shirya zuwa islamiya mun fito ke nan yaya sani yana zaune
a daban su na yan matasa yace dani ke Safiya zo nan.
Jiki na min bari na nufe shi sai naji yace dani kunci abinci nace eh yaya munci
yace to ki saurareni kiji daga yau duk wanda kika ga zai daki ummin ki ki nemo
sanda kema ki buga mashi ninace a mutu har liman.
Da sauri na dago kai ina mamakin kalamin shi yace eh don abin yai yawa daga
magana sai duka irin haka itama Rabin na fada mata ta daina zama ana mata wanan cin
fuskan tun bakuyi wayo ba har gashi kun tasa ana bu daya a gidan.
Yace baki ji may Nura ya fada bane kowa ma ai uwarshi ya sani don haka ninace ki
rotsa mutum koma waye.
Yace maza ku tafi kada ku makara zance a gun yaya sani muka samu sauki dakin mu
don yafi kowa zama tantiri a gidan mu.
Sai gashi kuma Allah ya dora mu a kan shi yana jin mu a gidan ko dan ladabin da
muke mashi ne oho ?
Don zamu ganshi komai yawan abokan shi sai mun duka mun gaida shi idan kaya muka
gani a hannun shi zamu karba a