Showing 87001 words to 90000 words out of 258256 words

Chapter 30 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu

nan na kwanta ban dade ba abu ga wanda ya gaji barci ya kwashe bani na falka
sai da asuba don na saba tashi a wanan lokacin.
Na shiga ban dakin na dauro alwala nafito nai sallah ban kwanta ba na dade zaune
ina addua kamar yadda na saba yi duk safe sai da gari ya haska na fito daga dakin
bayan na gyara na samu mai aiki tana ta gyaran wuri sai na so taya ta amma sai ta
hana.
Nan dai na taya ta aiki mikayi tare sai tabar min ta tafi hada abin karyawa muna
gab da gama aikin anty tafito daga dakin ta tana cewa.
Dama nayi tuna nen hakan dake Safiya may yasa ba zaki huta ki natsu ba sai ki
fito ki kama aiki.
Murmushi nayi nace da ita ai wanan duk ba aiki bane a gida duk nike wa ummina
aikin da ya dace inyi na.
Murmushi tayi tace yanzu dai ki dan huta tukun kafin na san abinyi a kan ki nafi
son naga kin huta kin kwantar da hankali kafin mu san abinyi a kanki.
Bayan mun yi wanka ne an fito karyawa take gabatar min da yar uwar mijin ta dake
zama dasu sai kaunan ta da ke zaune dasu wai tana karatu naga tana min wani kallo
na rainin wayo.
Ni dai ban kulata ba muka ci abinci inda duk hiran da ni maman biyu keyin shi
akan yanayin garin mu da ta gani ina bata labarin garin namu da abubuwan da muke
shukawa a karlaran mu din.
Mun gama na mike don kwashe kayan tace in barshi mai aiki ta kwashe nace haba
anty kamar dai ba mata ba na kwashe naje na wanke ban dawo inda suke ba na shige
don yin sallah walha.
Dana gama na dan mike don har yanzu akwai gajiya tare dani sai barci ashe ta leko
dakin ta samu ina barci a inda na idar da sallah na.
Ta juya ta koma tare da jawo min kofan ban farka ba sai sha biyu da wani abu na
gyara jikina na fito nan falo na same su da kauna tana mata fada ko da ban sani ba
nasan a kaina don naji tana fadin.
Na dai gaya maki karki yarda ki sawa yarinyar na ido a gidan nan don ba wurin ki
tazo ba indan ma tayi wani abinda ba daidaiba just ki fada min.
Don ban son abinda ya faru da dake da faiza ya kara faruwa akanta don duka daya
na dauke ku don ko ita din ma ni na kawo ta nan din.
A take sai naji kuka yazo min a hankali na juya zuwa dakina da na fito din ba zan
iya rike kukan ba a lokaci kuma gashi ban son suji na ji maganan su.
Sai dai a raina nasa duk yadda kaunan nata take zan iya hade bacin ran da zan
gani a gurin ta don mu rabu lafiya ni da nazo cin arziki ina ni ina fada da masu
gida.
Ina daki dunkule ban fito ba suma basu nemay ni ba ashrle ta fita ne gida sai
shidda na yamma ta dawo gidan nan ta zube a falo inda ta samay su suna kallo.
Nan na fito cikin su tare da gaida su na samu wuri na zauna ta dago kai tana cewa
Safiya kin tashi ai na leka ki har sau biyu na samu kina barci.
Nace wallahi anty sai yanzu na fito nima ban san barci ya kwashe ni ba sai tace
tare da nuna kaunan mijita dake zaune ban gabatar maki da wa yan nan ba bayan
tafiyan ki ne suma suka zo anan suke zaune tare damu yanzu.
Wanan ita ce faiza kaunar maigidan ne auren ta ya mutu ne tadawo nan da zama
wirin mu.
Sai wanan yar uwatace itace autar mu itama anan take zaune yanzu tare dani da
fatan zaku zauna a cikin aminci har kowa ta samu miji tayi auren ta.
Tace kuma wanan itace safiyan da kuke ji ina fadin zata iya zuwa ko wani lokaci
yar uwata ce itama zata zauna damu anan na dan wani lokaci da fatan zaku rike juna
da amana.
Sai naga Fatin ta dago ta kalle ta don jin ta kirani da yar uwa nima ban san
dalilin anty na fada masu haka ba.
Faizan ne tai murmushi tace kai anty lallai kina ji da wanan safiyan ai kin fada
muna zuwan ta tuntuni kuma insha Allahu zaki samay mu yadda kike so a cikin amana.
Sai ta juyo gare ni tana cewa ki saki jikin ki kuma ki ja kowa ajiki saboda yanzu
mun zama daya da junar mu ga gidan gidan Jamma a ne.
Wa yanda ma bamu san inda suka fito ba suna zuwa suci arziki su tafi ni dai abu
daya ne ko kadan bana kaunar rashin gaskiya duk abinda zamuyi mu yi shi a cikin
gaskiya da amana.
Murmushi maman biyu tayi tace indai Safiya ce to kar kiji komai a kanta, saboda
komai daidai gwagwado Allah ya wadatar da ita da natsuwa da sanin ya kama ta daidai
misali.
Ta nisa tace tare da cewa ai shekenan Allah ya zaunar da mu lafiya da junan mu
tace aini naji dadin zuwan ta kwara don in kun watse nakan ji gidan ya koma min
shiru wallahi.
Ita dai fatin tana ta charting din ta ba dago kai ta kalle mu ba balle tasan may
muke fadi ma.
Na ce a raina wanan da gani zamu kwasa da ita sai dai duk abinda zata zo min da
shi zan yi kokarin kawar da kaina akanta.
Muryan maman biyu ya katse min tunane na take tambaya na ko nayi waya da mutanen
gida da nazo nace da ita banda waya a hannu na don wayan da zanzo na barwa su
ummi shi acan don su samay ni.
Tace a a ke ko ana haka ai ya kamata ki kirasu su san kin iso lafiya yafi ke
fati je daki ki dauko min wanan wayan dake saman mirro na ki kawo.
Kamar bataji yar nata ba sai da ta kara maimaita maganan nata ne ta mike zuwa
dauko wayan a dakin ta.
Ta bita da kallo tare da firgiza kan ta tace kai Faiza akwai matsala wallahi sai
kun ta hakkuri da ita don Allah.
Faiza tace aini yanzu nasan halin ta ba abinda zata yi ya dakay ni kuma sai dai
ita Safiya da bata saba da halin ta ba.
Ta kawo wayan tana mikawa yar nata ba tare da ta kalli kowa a wurin ba ta karba
tana ce min ina sim din ki yake na tashi zuwa daukowa.
Ashe bayan na tashi yar take mata fada sai tai hushi tabar falon gaba daya ta
koma daki.
Koda na fito ban gane ta ba na mika wa anty sim din na samu harta cire nata dake
ciki tana cewa ki fara amfani da wanan har in sayo maki naki wayan .
Ta saka min sim din tace karbi ki kirasu su san kin sauka lafiya ko hankalinsu ya
kwanta idan sun jiki.
Faiza tace lalai kan do irin haka hakali baya kwanci sai kaji mutum balle lagos
garin ne mai tare da hatsari sosai.
Na karba kira biyu sai kaunata dake bi mun ta dauki wayan nan dai muka gaisa
nace tabawa ummi wayan muka gaisa na fada masu na iso lafiya nace ga anty.
Ta karbi wayan sun gaisa sosai ummi tai mata godiya tare da cewa don Allah don
ma aikin Allah ki rike min ita amana don gidan nan ba dadi shiya sa ta zabi zuwa
wirin ki ta zauna.
Tace ummi kada kiji komai zaman Safiya a guri na tankar a gida take daku saboda
Allah kadai yasan abinda ke zuciya ta kuma shi ya san yadda nake jin Safiya a
raina.
Ummi tai mata godiya ta bani wayan ina tambayanta sauran mutanen gidan mu tace
duk suna lafiya.
Lokacin sallah da ya gabayo ne yasamu watsewa inda na kula da kowa dakin ta daban
ashe a gidan sai dai duk kan mu ukun a kasa muke sai masu gidan ne ke sama da yaran
su.

Yanzu yar uwa kin kwamace in barki da Allah da kike fitar min da novel waje kiba
rabawa group group ki tuna duniya ba matabbata bane.
Akwai ranan hisabi tsakanin mu dake ban san kin shigo da fuska biyu bane amma
idan baki iya rikon amana ki magana na baki kudin ki don bazan taba yafe kaki ba ko
wace ce ke ubangiji yai gagawan isar min a gare ki idan kika kara fitar min da
novel ga wanda bai biya ba.
Allah yai min sakayya a gare ki ko wacece ke.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , ,


3🧕🏿131
3️⃣
3️⃣
1️⃣ 1️⃣

YAR UWA NOVEL NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA
ZAN YAFE MAKI BA IDAN KUMA KIKA FITAR MIN DA NOVEL UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN
KI, , ,


Washegari misalin karfe goma na safe ina zaune a daki sai ga dayan yan biyu ta ta
shigo dakina tace dani mumm is calling you.
Ban bata lokaci ba na mike nabi bayan ta zuwa amsa kiran sama naga ta nufa don
haka nabi baya yarinyan nata can .
Wanan ne karo na farko dana taba haurawa wa sama dakunan gidan koda muka hau sai
naga saman ashe babba ne da dakunoni kamar kasan.
Ina mamakin girman gidan yarinyar ta tura kofa ta shiga nima na mara mata baya
tare da sallama na shiga.
Na samu tana tsaye tana gyara rigar uniform din ta a jikin ta ta dauko abaya ta
dagwara a sama fara gaida ita nayi nace anty ina kwana ta juyo tana fuskanta na
fuskanta dauke da murmushi tace Safiya an tashi lafiya.
Nace Alhamdullahi ta sake tambayana da kin ko yi break fast don yau banda time
din fita ina shirin zuwa office ne.
Nai murmushi nace yanzu zanyi anty tai saaurin ce aa kada kiyi wasa da karyawa
keda kike shan magani zaki tsaya biye muna kada ki bari tara yayi baki karya ba a
kullum.
Kai na gyada mata kawai alaman to tace dama na ce akira min ke na kara fada maki
don fita zanyi don Allah a kada kishiga shirgin su faiza ki zauna da kowa da zuciya
daya.
Fati ba kirki ne da ita ba don bata da kunya koma kisan hiran da zaki yi dasu don
inda halima ina son ki kama bakin ki akansu maana sirin ki kibar wa cikin ki shiya
sama ban hada kowa a daki daya ba nabawa kowa nata dakin daban.
Tace da fatan zaki fahince ni na ce a sanyaye da eh anty nagode ta sake cewa idan
kina son wani abu ki tambayi mai aiki ko Faiza su baki nace to ta juya saman gadon
ta tace kwashi wayan nan kayan ki fara amfani dasu kafin na dinka maki naki.
Na fara mata godiya sai ta dago min hannu alaman in bari duk da haka sai da na
gode mata din.
Daki na koma batare da na hadu da kowa a falon ba har na shige na aje kayan yadda
na dauko su da zata fita saida ta leka kowan mu sannan ta fice gidan.
Na gyara dakin sai lokacin na bude kayan don in kaisu a wardrabe din kayana kaya
ne masu kyau har kala biyar sai dogon riga daya cikon na shidda kenan.
Na gwargwada sai naga size dina ne ma nasan ta dade dayin su ba yanzu da ta kara
jikin girma ba dai.
Nai murna a raina ranan doguwar rigar na sa don yaba kyauta kenan maishi ya ji
dadi indan ya ganka da abinda ya baka a jiki.
Shiru yai yawa a daki na fito waje anan na samu yaran zaune suna kallo su kadai
suna gani na suka nufoni nan muka zauna ina biye ma shirmay su suna bani labari wai
uncle yace zai zo ya kaisu birch zan bisu ko muje tare eh kawai nace dasu.
Ganin kan su ya tsufa da kitson dake kansu yasa nai shawaran sance masu nai masu
wani mai kyau na hannu don dai indai kitsone Allah ya hore min iyawa ko wani iri.
Faiza ce ta fito ta samu muna kitson karshe dagani daga barci ta tashi tace wai
ashe kuna nan na saba ba in fito ba kowa a falon dole nima na koyi zaman daki ta
kai zaune tana yaba kitson da mukeyi tare da cewa ashe kin iya kitso ne haka ?
Na dai yi mata murmushi a raina nace ai kitson ne ya jawo min wanan alherin da
nake ciki don lokacin da ta fara kawo su har sau biyu tana zuwa amma bana karban
kudin su sai ince su din ai yara nane.
Haka yasa uwar ta daina kawo min kudi a lokacin sai dai wani abin da tafiya yai
tafiya kuma ta fahinci halin da nake ciki ta shiga taimaka min.
Jefi jefi muke hira da ita na gama tare da daura masu ribon don shuku biyu nai
mako waccen su sai take cewa nima gobe zan sance kaina ki mun ghana wiving don shi
nake so nace da ita Allah ya kaimu kawai.
Fati ne ta fito daga dakin ta ko kallo inda muke bamu ishe ta ba zata wuce mu
nace mata anty Fati ina kwana cikinciki ta amsa min gaisuwan ita ko Faiza ta ja
wani tsaki tare da kawar da kanta.
Dining ta wuce ta bubude kulolin dake wurin ta wani tabe baki tace duk ma an
jagule abincin ambar jagwalgwale.
Ba wanda ya kulata sai kuma naga ta zauna tana diba nan ta zauna taci ba tare da
kula mu ba sai dai tana yi tana satan kallon mu a fakaice.
Ni dai ina mamakin ta a raina dayar yan biyun ta nufeta take cewa ta dubi kitson
da Anty tai masu korar yarinyan tayi daga wurin ta ta wuto tana yi tana waigen ta
kamar zatai kuka ganin haka yasa nace zo nan kada ki kuka kyale anty.
Ke naji ta fada kamar wacce ta samu diyarta don haka ban dauka da ni takeyi ba
sai da ta sake fadin ke Safiya bakiji bane san nan na dago kai ina kallon ta.
Tace ban faye son ana shiga harkata ba don haka ki kiyayye yar kice ko yar yar
uwata koda yake ma kalan dagi ce ke don naji anty na fadin wai kema kauna tace ko a
ina ta samay ki oho ?
Ko da yake kila ta wurin mamanta kika fito ban sani ba nan na fahinci ba uwarsu
daya ba ashe kila uba suka hada.
Ni dai ban ce da ita komai ba sai Faiza ce tace mata amma dai kin san ba
girmuwanta kikayi ba da zaki fada mata haka.
Koda yake baki da laifi don ita ta fara kiran ki wai da anty shiyasa kan ki ya
fasu haka kike jin kanki wata babba can.
Ya ishe ki gida dai ne baki iya korana don nima gidan yar uwata ce dariya naji
tayi tace yar uwa ko muna yar uwa ai da yar uwan kwarai ce da kin so abinda take so
ke yanzu baki ji kuyar korar wanan yarinyar a gurin ki.
Nan dai sukai ta cacan baki wanda nake gani ba yau suka fara irin haka a tsakanin
su ba da naji abin yai yawa nace da ita ta kyale ta don Allah maganan ya kare ai
mutum guda bai fada.
Sai kuma ta juya kaina tace wai ai dama taga zubina na munafukai ne don haka sai
dai hassada ya kashe mu don ita ta wuce ajin muko.
A raina nace wata sabuwa kenan kuma nayi gudun gara na fada ma zago in na gudo
gidan mu don inna ga wata kuma na samu a nan yan kuwa zamana nan mai dorewa ne
kuwa.
Maigidan bata dawo ba sai hudu na marance daya bayan daya muke shiga muna gaida
ita da dawowa koshi ban san ta dawo ba sai da Faiza ta fada min sannan na tafi.
Dama yaran na wuri na sun rigani isa don sai da na tsaya nai sallah na fita zuwa
gaida ita din da dawowa.
Zaune take kasa yayin da diyan nata suke saman jikin ta ta mimike kafa suna zuba
mata surutu saman jikin ta na gaida ita ta dago har kullun fuskan ta a cikin
murmushi tace dani safiya yaya muka wuni nace lafiya kalau anty kin dawo lafiya ta
amsa a sake da lafiya.
Sai na juya tace kin ga Safiya debo min abinci na nan don ban iya saukowa kasan
nan yanzu na gaji yau da yawa.
Na juya zuwa dauko mata abincin ashe baya wucewa na sai yar tace mummy kin san
may yau da baki nan mummy fati tana ta fada su Anty tana ta zagin su .
Sai dayar tace sai da wanan anty tai kuka ita gwagon mu batai kuka ba tana bata
amsa sukayi ta fada sosai.
Na shigo dauke da ture tace dani ashe kunsha kitso ne haka sannu da kokari
murmushi kawai nayi na aje mata tana cewa yauwa sannu yar gidan anty na gode.
Na juya na fita dakin har nakai kofa tace don Allah yimin magana da Faiza idan
kin fita nace to anty.
Ina fita na nufi dakin faizan tana zaune tana waya na isar mata da sakon anty na
fito daga dakin.
Sai da ta gama ta fita daki na koma na kira ummi na don jin lafiyan su da sauran
mutanen gida .
Nan take fada min bayan wuce wana ai anyi fada da baba da inna har don bata san
inda naje ba sai daga baya da taji take zage zage wai naje yawon dandi zanbarbada
wa maza cuta.
Shikuma baba ya kasa kyale ta nan dai abin ya kaisu har da duka abin da bai taba
yi wa wata mace ba a gidan nan.
Nace ni kuwa ummi may na tsare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login