Showing 33001 words to 36000 words out of 258256 words
Chapter 12 - Bahagon Rayuwa by Zainab Idris Makawa Seenabu
don sana,an zobon da nakeyi ya bunkasa
sosai naji dadi ina ta zuba mai godiya mukai sallama ya wace.
Da ya tafi na kirga kudin sai naga har sha biyar ne cif din su banyi sanyi a
kafa ba na shirya na shiga yar kasuwar uguwar mu na sai kayan amfani na dasu da
abinda zan dan rika ci da rana.
Ashe da yabar gidan gidan su ya koma wurin mahaifiyar su ya ke fada mata duk
irin abubuwan da dan uwan nashi yake min.
Sai ko ta hau fada da cewa dama tsiyan dan tallaka keman bai iya samun wuri ba ta
tsamoni cikin wahala tasani ga rigan mutunci ina bidan in tona masu asiri.
Da nake cewa yana sha, shan ya hana ya kyautata min ne duka kuma in banyi mashi
laifi ba ai ba zai duke ni ba , a gidan mu wani irin wahala ne bana sha nazo nan a
saka ni cikin rigar mutunci shi zai ma danta sheri.
Yace mummy yarinya ga fa diyan dan uwanki ne halal malan aka dauka aka baki badon
taso ba ko uwar ta taso ai kama yayi ki tsawata mashi yadaina shigo mata da maye da
matan banza baki goyi bayan shi ba haka.
In tana ahan wuya a gidan su nan ai aurene ya kawo ta kamata yayi ta samu sayin
rawa ta huta ba wahala irin haka ba.
Tace to ubana dama ai ka saba min fada sai kayi ita kuma ta zuba ruwa a kasa
tasha tunda ta hada ni da diyana fada.
Sadiya dake gefe tana saurare tace mummy ai gaskiya yaya ya fada gaskiya abinda
yayan ke wa Safiya baya kyautawa idan mu akaiwa haka bafa zaki ji dadi ba.
Harara ta watsawa Sadiya din tana cewa ai duk kuna da bakuson dan uwan ku da
alheri daga yarinya taimai kake kun dauka kun haye ke nan kun yarda da abinda ta
fada.
Saadun yace mainene daga ciki kake wanda ba halinsa ba cikin abinda ta fada din
ina duk halin da ta fada kin sani yana yin su sarai.
Nan dai yaran suka barta tana ta fada tana fadin ai zata je gidan zamu hadu gobe
bazan kara fadawa wani sirin mijina ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM - Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , ,
1111
11
1️⃣
1️⃣
1️⃣
1️⃣
INA MAI BAKU HAKKURIN RASHIN JINA KWANA BIYU WUTAN MU YA LALACE
YAR UWA IDAN KIN FITAR MIN DA NOVEL DON KAN KI KE KI SANI DON KIN SAN DAI HAKKIN
WASU NE.
Ina duke ina wanki bansan hawa ban san sauka ba sai jin bugu nayi daga baya na sai
da na kife a jikin roban da nake wanki din.
Bai hakkura ba ganin na fadi kasa ya kara kai min duka bazan iya kare kaina ba na
fadi kasa gaba daya yana ta duka da zagi.
Sai da ya gaji don kanshi ya barni nayi ligis a kasa yashe ban ko motsi ruwan da
nake wanki duk ya zube min a jiki na yana huce yake fadin.
Baki ga komai ba idan kin ce magana zaki dinga dauka kina kaiwa gidan mu shi
wanda kika fadawa yazo yai maki maganin abin na gani mana.
Mata yanzu ma na fara shigowa dasu gidan nan gidan ubanki ne ko gidana da zaki
kafa min doka akai.
Yar iska jiki matan da nake bi din basu fi min ke ba, ke har mace ce may za a
samu a gare ki banda wahala.
Har ya shige ciki ya fito yace ban ga daman kawo abinci ba ki aika wa uban ki
mai dakunanen hula ya kawo maki in ya mayar dake wata tsiya.
Yar iska nida gidana har kina sin kafa min doka nakawo mace ki hanani naji dadin
da nake so idan kin isa.
Nikan zafin bugu sai wani gumzi nake yi kamar raina zai fita ya shige na dade
wurin ko kafana bana iya dagawa a lokacin.
Da kyat naja kafa na shiga dakina ko ina sai ciwo yake min don zafi da cowo kuka
nake ina tunanen rashin imani irin na yaya Ahmed.
Bai kara bi ta kaina ba sai shaye shayen shi yake a cikin falo ina jin shi warin
giya da taba har dakin da nake ciki.
Sai dare naji yana rufe gida ya fita da kyat na ja kafana zuwa falo nan na samu
yai baja baja da kayan da yai shaye shayen wurin.
Kitchen na nufa na dan hada ruwan liptop na don a lokacin shi kadai nake iya
saqa cikina ga wani irin zazzabi ya na neman rufe ni.
Ranan tunane kala kala nayi gadai kudi a jiki ina son gudu in koma gida don dai
na san motan zuwa arewa bai gagara na zuwa.
Amma kuma nasihan Ummi yana min yawo a raina da tace dani yar nan komai wuya
komai dadi ki natsa kafan ki a dakin ki wuya baya kashin bawa.
To amma kuma a haka ake son na zauna cikin wanan irin ukuban babu dadin rai ko
yaushe sai fitina kamar ankawo mai jaka.
Nidai tun zuwa na gida ba zan ce ga rana daya wanda naji dadin zama da shi ba
daga ni har shi zamane na dole muke yi da junan mu.
Washe gari abin yafi na gare ne duk fuskana ya kumbure ga hannu da kafa ban iya
daga wa ko kadan don ciwo.
Ina cikin wanan halin amma ya saka kida yana tashi ina jin sautin na shiga min
har cikin rai na ba halin in magan ta.
Ganin da yayi kayan wankin da na jika ya kwana ya wuni yasa shi shigowa dakina a
fusace yana cewa ke don ubanki kayan nan da kika jika suna wa mutane wari baki
kwashe su wurin nan ne.
Sai ya samay ni cikin wani hali banko san ya shigo dakin ba lokacin tsayawa yayi
a kaina yana kare min kallo sai kuma ya juya ya fita.
Ko ina nawa ya hakke ya kumbura dan bugu da ciwa gashi ba mataimaki yan kitso na
sai zuwa suke suna tafiya.
Wata boyar Allah da nake kira mama biyu don tana da tagwaye tana kawo su kitso
wuri na tai karfin halin fadowa har cikin daki na.
Sai da ta dan yi ihu don ganin halin da nake ciki tace dani amarya waya maki
haka ko hatsari kika yine wai.
Na bude idona da kyat ina kallonta dishi dishi nace buguna yayi tace amma mijin
nan naki baida imani ita na samu ta taimaka min har na da wanka .
Ta dan sayo min abinda zanci da dan magani na sha tai ta jamashi Allah ya isa
yafi a kirga ta shirin tafiya ne sai ga yaya saadu ya shigo gidan yace yazo ya
sallamay ni nao zai tafi.
Hankali yace bai kwanta ba ga yadda ya barni ranan sai kuma yazo ya tarar da
abinda ya faru dani.
Matar take kara yi mashi bayanin halin da ta samay ciki aikuwa bai tsaya ba ya
juya zuwa gidan su kai tsaye wurin mahaifiyar su.
Ya je ya sameta yake fada mata irin taasan da yayan nashi yai min maimakon tai
fada sai cewa tayi fada kota tausaya mashi sai ta fara fada dani tana cewa.
Ai maganin ta kenan yarinya bata da kunya sam ga sa ido ga abin da bai shafe ta,
gunma da yai mata dukan tsiya goma bata karawa ai.
Ya ce mummy na fada maki yarinyan nan tana cekin wani halin a yanzu idan ba zaki
dauki mataki ba ni zan dauka don wallahi zanyi karashin gurin yan sanda akan zai
kashe yarinyar mutane.
Da sauri tace dashi dan uwan naka zakai kara har kana fadi da bakin ka akan wata
Safiyan ce ?
Yace ita din ba yar uwar mu bace mummy da zaki ce hakan wa take dashi a garin
nan bayan mu ka wata sani in bamu ba.
Waya ta jawo ta kira wayan Ahmed din ya amsa mata a kadarance da cewa mummy aiki
nake yi fa banson kira yanzu.
Tace kazo ga Saadu nan ya zo ya tayar min da hankali akan makiran yarinyar nan
safiya wai ka mata duka har ta kwanta kuma baka kaita asibiti ba.
A cikin fada ya na daga sautin muryan shi yace wai ina ruwan shi da matana ne
wai
May yasa yake son shiga harkan gidana ne matar shi ko mata na don haka babu ruwan
shi ko kashe ta nayi.
Yana tsaye yana huci ya ansa a fusace da haka kace to wallahi jira kaga matakin
da zan dauka a kanka ai akwai hukuma a kasan ko sai ya fita a fusace uwar na kwala
mashi kira amma bai dawo ba.
Mike tayi a firgice tana fada tana shiryawa tabi bayan shi tare da kiran habiba
ta raka ta.
Ina kwance bayan na samu taimakon daga maman biyu tadan bani dan ruwan tea na
sha nakoma na kwanta sai dai hannu na ba dama na daga da kafa.
Tana tsaye a kaina suka shigo gidan tun daga kofa take kwala min kira a gigice
tana cewa fito muna fukar banza da wufi kawai ganin ban fito ba yasa suka nufi
hanyan dakin.
Sai sukai kocibis da maman biyu a kofan dakin kallon kallon sukai wa juna sai
gwago din tai karfin halin fadin ina ita Safiyan take ne.
Dan jan jikinta tayi a kofan shiga dakin sai suka samu wurin shiga dakin a
kwance suka samay ni sharkaf jiki ba dadi gaba daya na sundule saboda bugu.
Sai ta sasauta fadan da takeyi ta fara cewa uhmm uhmmm aishe abin yayi muni ne
haka ban sani ba.
Maman biyu da bata san ko su waye suba sai tace wanan tsinanen mijin nata mara
mutunci da tarbiya an baka diya amana don rashin mutunci kai mata wanan dukan kamar
zaka kashe ta.
Sai habiba tadan juyo tace mata ai mijin ta ne sai dai itama tabar mai shigan
tsagal ga alamarin shi.
Matar tace haba yar uwa ko ke ce ai ba zaki dauki hakan ba mace banza har cikin
gidan ki don rashin tarbiya da tsoron Allah.
Tana kokarin cewa na tashi na zauna ta gani sai maman biyun tace ina ga kamar fa
ta gwauce ne ko tayi tarmashe.
Don bata iya daga wa sai an kamata maman biyu din ke magana cikin tsigar tausaya
wa.
Sai gwagon take cewa na daga ta gani mana.
Habiba tace in ko don taji ana karawa abin gishiri bazata daga ba yanzu.
Aiko maman biyu tai kanta da sabon fitina tana cewa amma dai ke baki da tausayi
idan da yar uwar ki ce aikaiwa haka abinda zaki fada ke nan.
Wanan ai rashin tausayawa ne ke fa mace ce kin san zafin wanan abin mutum kobaida
tausayi dole ya tausaya mata.
Ta neme fada mata maganan banza tace kama kanki kin kuwa san ko ni wace ce yan
zan saka dake da mijin nata a kulle min ku baki daya don kashin kai ya so yi anan.
Sai da taga da gaske maman biyu keyi kuma ta kalleta taga ba raini a jikin ta da
gani watace ko matar wani a garin hakan yasa taja bakin ta tai shiru, gwago sai
fadi take .
Kaddarane ai ya kawo hakan fada tsakanin mata da miji ba a shiga sai mutun yayi
kunya idan ya shiga.
Maman biyu tace amma dai irin wannan abin dole a tausaya wa mutum bari ai ya dawo
zan tsawa ta mashi.
Tace yanzu a taimaka akaita asibiti kada yarinyar mutane ta halaka ga banza don
shi na mijin kawai na ta yaya kai kaiwa yarinya sanadin haka.
Amma kana ganin ta cikin wani hali ace koda dan paracitamal wanan bazaka iya saya
mata ba don tsaban iskanci wallahi ni sai nasaka a adana mun shi bawani abu bane.
Gwago tace a dai yi hakkuri a dan sawo mata dan magani tasha ko zata samu sauki.
Tace What da karfi wanan case din fa ba avin a zauna da ita gida bane.
Sai ga yaya Saadu ya shigo yana fadin a fito da ita mu tafi asibiti fa mota nan
na samo a waje gwago tace har asibiti za aika bari a bata magani kawai.
Don kar aje suce sai an kira mijin nata maganan ta zama babban case kuma .
Yace ya zama mana waje ya zama don may zai duketa kuma ya kawo ido yana kallon
ta haka kwance a gida.
Maman biyu dake tsaye a kaina tace asibiti kan sai an kaita don wanan bana zama
gida bane mutafi tare zan san abinda na fada masu.
An kama ni an fito waje sai maman biyu taga motar hayace suke nufin a shiga tace
dasu sallami mai motar ga motar na nan mutafi.
Da motar ta muka tafi ta kaimu wani asibiti na kudi da farko sunce idan duka ne
sai anzo da yan sanda sai maman biyu ta dauko id card din ta ta nuna masu sai suka
yarda zasu dubani.
Nan aka dubani ni ansamu nayi tarmashe da kuma raune a hakarkarina suka ce dole
sai sun bani gado.
Duk maganin da aka rubuta da awo da sauran su itace ta bayar da komai aka bani
gado a wani daki ni kadai a ciki.
Nan yaya saadu ya daga wayan shi ya kirashi yake sheda mai yazo an bani gado a
asibiti ya fada mai sunan wurin.
Nan ya iso yana mazurai da ido yana kamay kamay sai fadi yake waya kawota asibiti
nan na kudi kun san dai bazan kashe kudina ga wanan mara mutuncin ba ga banza.
Maman biyu da take gefe tana kokarin hada min maganin da aka bani insha tun
shigowan shi take hararan shi.
Ta dago kai ta harare shi tace amma dai kai ka kai mara mutuncin gaske wallahi ma
jin dadin naka yayi yawa da har zaka kashe yar mutane so ba a hukunta ka ba zaka
zo kana muna maganan banza a nan.
Ya bita da kallon kallamin ta zuwa gare shi daidai lokacin da take dago ni daga
kwance tana bani magani,
Sai faman murde murde nake yi saboda zafin da ciwo da nake ji a jikina ya tsura
min ido yana kallon yadda na koma ga ciwo a fuka da hannu duk na goge wurin bugu.
Likita ma ya shigo yana dudubani sai da ya dan bata lokacin shi sosai a kaina ga
dan karen tambayoyi da suke min duk yabi ya tsargu sai dai na boye wanda yai min
haka don cewa nayi a duhu ne ban san su ba.
Nan nadama yazo mashi gwago ce taja shi zuwa waje ta fara yi mai fada akan ya
rage wanan zafin rai don kar yaje ya kashe yar mutane yajawo masu magana.
Idan ma tai maka laifi ne ai basai kai mata mugun duka ba haka har yakai taji
rauni maganar yaya Saadu ne suka ji a bayan su yana fadin.
Amma mummy bai kamata ki na haka ba fada ya kamata ki masa kin san fa girman
abinda yayi badon wanan matar yau ba abinda zai hana ba adaure shi ba.
Idan ba a daure ni ba sai kai kaje kasa a daure ni mana wai may ye dalilin ka na
min shishigi a gidana irin haka matar ka ce ko mata na.
Yaya Saadu yace kauna tace kaga ashe ina da right din da zanga ana cutan ta in
saka baki na akai.
Ya zaburo mai shima ya zabura mashi kamar zasu buga gwago taga suna batun tara
mata mutane sai ga maman biyu ta fito tace wanan wani rashin mutunci ne haka.
Wallahi in bakai hankali ba sai na sa an daure mun kai yau don baka da tausayi
mutumin da ya cece matar ka har zaka zo kana son mai rashi mutunci.
Ta harare shi ta wuce zuwa wurin motar ta sai da ta dan gwauta ya juya yake
tambayan su wacece wanan matar ne.
Gwago tace a tare muka samay ta da Safiya a gidan ku ya bita da kallon mamaki
har ta dauko abinda zata dauka ta koma ciki koda ta dawo ta sallamay ni nayi barci.
Don haka tafito tana gyara gyalen dake jikin ta tana cewa waye zai zauna da ita
a nan don ni zan tafi gida sai suka fara gardama tsakanin gwago da Habiba din.
Taja tsaki ta wuce tana mai jin haushi da Allah waddai da rayuwan su gasunan da
ganin su marasa tarbiya dasu kawai ta dan tsaya tana cewa gwago kizo na maidake
gida ita yarinyar sai ta zauna.
Ya zama dole subi umurnin ta don sun hango ita din wata ce shiyasa suke kyale ta
suna binta a sannu.
A hanya su da gwago take dan binciken ta tana jin wani abu a gamay dani sai take
lurar da gwago din nauyin amanan dake kanta na tare da fada mata cewa idan ya kara
min irin dukan nan zata sa a daure mata shi.
Gwago ta tsora ta tace insha Allahu ba za a sake ba wanan ma akasi aka samu ayi
hakkuri dai zata sauka takawo kudi taba ta tana ta godiya.
Yaya Saadu yace zai tafi wani wuri ya dawo sai ya bar yaya Ahmed da habiba zata
fara mashi tsegumi ya katse ta da cewa ke raba ni dan Allah da anyi an ce.
Sai taja bakin ta tai shiru ta tsargu ta koma gefe daya ta rakube wuri daya tana
harare harare wa mutanen dake sintiri a haraban asibitin.
Ya fita ya dawo